← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 200 OF 226

Sashe 200

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Tana saman kujera zaune kanta a qasa,ranta a tsananin bace yake,don me zata dinga neman cutar da ita?,tana tunanin dai dai gaggawar unguwar zoma ta bari a haihu ko?,ta bari su hada miji tukunna,meye na hanzarin son cutar da ita tun yanzun,saqar data dinga yi kenan cikin zuciyarta,qara qofar dakin eesha tayi,itace ta bude ta fito,tana tafe dai dai ta hura hanci,idanunta da suka kada saboda bacin rai ta zuba mata
"Aisha..." Ta kira sunanta cikin kakkausar murya wadda ta sanyawa eeshan tsayawa ta kuma juyo tana dubanta
"Jan kunne nakeso nayi miki na qarshe....duk abinda zakiyi kiyi qoqari ya tsaya iya ni,kada ki bari sarkarcinki da haukanki ya sake taba wani cikin gidan nan,yanzun da kin karya musu yarinya kuma kice me?,haka rannan kika watso ruwan zafi saura kadan a fuskar sajida,kina gidan kakanninta kina cin arziqinsu kina neman salwantar musu da jikoki?"maganar sumayyan ta qarshe ta sosa mata rai,ita zata yima gori bayan ita ya cancanci ta yiwa gori
"idan kuma banji jan kunnen naki ba me zaki iya diyar malamai masu ci da buzu da tawada?"murmushi ta sake mata sannan ta bata amsa cikin nutsuwa
"alhamdulillah da na kasance diyar malamai magada annabawa,zancan rashin jin gargadina kuwa....koni zan iya miki hukunci.....amma da yake ni din mai uwace a gindin murhu,kunnen mutum daya maganar zata je kiga yadda dunuyarki zata gigita" ta fahimci sarai tana son hadata da almustapha ne ko shi ko baba,to har gwara ma baban akan shi din,kuma ta sani sarai qarshen lamarin bazai mata da dadi ba
"Duk abinda zakiyi baki isa ki hanani shiga gidan almustapha ba wallahi,baare ma ya sameshi bare kuma na gida" murmushi ta kuma yi
"Kan me zan hanaki dama?,nima fa wata ta taras,sannan kuma ba kanku na soma zama da abokan zama ba,abu guda kawai nakeso daga gareki.....koda zaki auri almustapha to ki kiyayi taba lafiyar jama'ar da basu ji basu gani ba.....ki taqaita haukanki....ki adana shashashanki har zuwa sanda zaki shiga gidan nashi"tana yunqurin maidawa ummi tayi sallama,hakan ya sanyata dole yin shiru,bata ji ke suke fada ba taga dai sajida kwance
"a'ah lafiya kuwa?" Ta tambayi sajidan tana dubanta
"Ruwa ne ya zube sai na fadi" ta bata amsa,gefe ummin ta samu ta zawa
"garin yaya ruwa ya zube a wajen?" Ta tambaya cikin mamaki,wannan karon sumayya ce ta karbi zancan
"Wallahi ummi,sashen dai ba kowa,ni da ita kuma tare muka sauko sai ihunta kawai naji" waiwayawa ummin tayi tana duban eesha
"Aysha ya akayi ruwa ya zube wajen?"
"Nima ummi ban sani ba"
"Bake na bari wajen ba kina karyawa?" Sai ta langabar da kai
"Tea ne ummi,ina so ma goge kuma na mance naje na kwanta"
"Amma ya kamata ki dinga kulawa tunda kinsan yadda wajen nan ke da santsi,ko su lami kika saka zash goge,yanzu da amira ce ta taka wajen Allah ne kadai yasan me zai faru,ki kula sabida gaba"
"To" ta fada tana zumbura baki ta koma daki,ranta cike fal da baqincimi,ita wacce iriyar mara sa'a ce,kuma wai ummin har take goyon bayan wata bare a kanta,lallai kam ba zata qyake wannan abu ba zatayi mai gaba daya ne kawai komai ta fanjama fanjam,ruwa ummi ta buqata ta gasawa sajida wajen,sajidan tace ai anty ta gasa mata,hakan yayiwa ummin dadi,daya daga cikin abinda yasa har kullum take sumayyan ke sake shiga ranta kenan sanin ya kamata,ba qaramin jin dadin zama take da ita ba,ba shakka da zaiyiwu riqe sumayyan zatayi wajenta har ta haihu,amma tasan hakan ba maiyiwu wa bane,ita kanta tasan alkunya almustapha kawai yake mata,wanda dukkan alamu sun nuna ya fara gajiyawa,don ya soma yi mata qananun qorafi,ko haka kawai ba gaira ba dalili sai ya dinga tashinta cikin dare yana sata kaiwa sumayya waya.

***** ******** ******

Kimanin takwas ne na dare yau ta kwanta da wuri,so take tayi bacci sosai,jin kanta take kamar wadda ta shekara batayi bacci ba saboda yau tayi tashin wuri,don haka yau tun magariba ta kashe wayarta don ta huta sosai,har ta kwanta qishirwa ta tasheta,ta miqe ta zura hijabinta ta sauko qasa,cikin sandata bude fridge ta dauki ruwa saboda duk saman babu ruwa mai sanyi,ummi ta hana ta sha shi yasa ake ajjiye mata mara sanyi,ita kuma qaunarshi take,idan bata sha ba har wani abu take ji ya tokare mata qirji.

Tana tsaka da bude robar taga fitowar eesha ta haura sama,da alama wajen ummi zata,kamar tace mata ummin na sashen baba sai kuma ta fasa tunda ba shirginta take shiga ba,ta kammala shan ruwan ta ta maida robar ta rufe ta kama matattakalar benen ta soma haurawa saman,tana tsakiya eeshan ta fara saukowa,bata dubeta taci gaba da hawa abinta,tana step din qarshe eeshan ta iso inda take,wata wawuyar bangaza da bata zata ba bare tsammata eeshan tayi mata,wanda hakan ya sanya sumayyan yin taga taga baki daya tayi baya,ta gama saddaqarwa ta gama yawo,saboda step.ne ya kusa ashirin wanda ba shakka idan har ta samu nasarar komawa da baya sai ta gangara ta kan kowanne,cikim azama tare da kiran sunan Allah taji kamar an turata gaba,singalin qafarta ya daki qasa ya bafa wata qara,ta sanya hannayenta ta dafe qasa sanda take faduwa,wanda banda hakan da saman cikinta zata fada,suma hannayen qarar suka bayar ta zube ta gefen hannunta na dama daidai sanda taji muryar ummi cikin qaraji tana fadin
"Hasbunallahu wani'imal wakil,innalillahi wa inna ilaihi raji'un aisha!!" Ta qarashe fadi tana haurowa saman cikin wata iriyar sassarfa da gaggawa,idanu eesha ta soma fiddawa gabanta na wata matsananciyar faduwa,tasan tata ta qare,ya akayi har ummi ta iso wajen bata lura ba?.

Tuni ummi ta isa inda sumayya ke yashe,azaba da radadin da hannunta da qafarta daga buge kadai sun isheta,ambaton sunan Allah akwai take tana jin yadda qashin qafarta ke zugi da tsuko,a rude ummin ke tambayarta da qyar ta bata amsar qafafunta,ta matsa qafar sai ta sanya qara sabida azaba,cikin matsanancin bacin rai ummi ta waiwaya ta dubi eesha
"Ashe baki da hankali eesha?"
"Wallahi ummi....." Ta soma fada cikin rawar jikibda rawar murya,tsawa ta daka mata wadda ta sanya hantar cikinta kadawa tana gaya mata ta bace da wajen,sai da taga saukarta sannan ta maida hankalinta ga sumayya taba mata sannu,tausayinta na kamata,taimaka mata tayi sai data jinginata da kujera sannan ta dauki waya ta kira baba da anty maamaa.

Kusan lokaci daya suka shigo,salati anty maamaa ta dinga yi,shi kanshi baban shiru yayi ranshi na sosuwa,ba bata lokaci ya kira driver yasa ya fito da mota suka sanya sumayyan ciki
"Inaga ba asibiti ya kamata aje ba,wajen masu gyara za'aje a duba mata qafan da hannun,tunda Allah yasa bata fadi kan cikin ba" inji ummi,hakan ya sanya baba ya kira mutumin dake musu irin wannan aikin,basu da nisa sosai shi yasa bai bata wani lokaci ba ya iso.

Sai daya duddubata sannan ya tabbatar musu qafarta gocewar qashi ce,hannun kuma targade ne,zaiyi mata gyara,dui wanda ke wajen sai daya tausaya mata,tasha wuya sosai wajen gyaran,haka ta dinga hada gumi taba kiran sunan Allah kaman zata suma,murqususu take ga ciki a gaba daya fara tasawa,kafin a gama ta hada gumi sharkaf,ya gama ya baiwa ummi maganin da za'a ringa shafa mata da kuma yadda za'a kula da wajen,yace duk bayan kwana bibbiyu zaizo ya dinga dubawa,godiya baba yayi mishi sannan ya sallameshi.

Kusan kasa runtsawa sukayi baki daya,sai daga bisani baba ya fara tafiya,anty maamaa kam bata iya tafiya ba ita kanta sai wajen biyu na dare,ummi kuwa kwanan zaune tayi tare da sumayyan,sajida ma da qyar tayi bacci,duk tausayin sumayyan ya cikata,eesha kuwa tunda ta shige ba'a sake jin motsinta ba,ita so tayi cikin ya zube idan yaso ayi mata hukunci baki daya,ran ummin ya kai maqura wajen baci,tausayin sumayya kawai ya isheta,ta riga ta gama yanke hukunci a gobe aysha zata bar gidan,kome mamanta zata fada saidai ta fada,don ba zata yarda tana jibtana gani a bata amana ba kuma ta kasa riqewa,me zata cewa almustapha idan wani abu ya samu cikinsa?

A dakin ummin ta kwana,nan ummi ta kawo mata ruwa da roba ta daura alwala saboda yadda qafar tayi mata tsami,a hankali ta waiwayo tana gaida ummin bayan ta idar da sallar,amsawa tayi tana tambayarta jiki ta amsa mata alhmdlh,sannu ta sake mata tare da bata baki kan abinda eeshan tayi,ita kunya ce ma ta kamata,sai kace ummin ce ta aikata?.

Qarfe biyun rana ummi ta isa dakin eeshan ta taddata kwance,zumbur ta miqe tana gaidata,a tsautsaye ta amsa tana ajjiye mata kudi
"Ki tashi maza ki shirya ki wuce gida,koda wasa kada kice zaki sake dawowa gidan nan a yanzu,tunda ba yau ashe kika soma qoqarin aikata mata hakan ba,idan banda tsabaar rashin mutunci eesha bata ci darajata ba a wajenki?,ko duka bata ci darajar wannan ba ai taci darajar dan tayin dake cikinta ko?,to ki tashi ki shirya ki wuce gida" kuja eesha ta saki,abinda take bege wato so yake yayi mata nisa,garin neman gira zata rasa idanu
"Yanzu ummi sabida ita zaki raba zumuncin dake tsakaninmu?" Cikin mamaki ummin ta waiwayo tana dubanta
"Van raba ba,amma a yanzu dai na raba har sanda zata bar gidan nan,na riga na gama magana da mamanki" ta juya tana ficewa,abun takaicin ma sam bata ga nadama tattare da ita ba,don ko qafar benen bata taka da niyyar zuwa dubata kan abinda tayi mata ba.

Wunin ranar yini tayi tana tofa fatiha a wajen,haka ya kawo mata sauqi sosai kan radadin dake damunta.

****** ***** *******

Ranar da abin ya faru baki daya bai samu zama sosai ba,ayyuka sunyi musu yawa can company,sau uku yana kira yaji a kashe.

A gajiye ya dawo,a falo ya sami su'ad din,tana kwance dai dai saman kujera,sanye da gajeran wando da qaramar vest iya ciki,ko ina baja baja da kwalayen data gama ciye ciye,yayin da bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita,tsallaketa yayi ya nufi bedroom dinshi kai tsaye ya rage kayan jikinsa,duk abinda yake tunanunta na mqale a ranshi,yau daya tak da baiji muryarta ba jinsa yake kaman maraya,yayi tsammanin zai iya share mata kaman yadda ta shareshi amma sai yake ji abun ba mai yiwuwa bane a wajenshi,towel ya dauka ya wuce bathroom yayi wanka.
Chapter 200 · 0% Book details