← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 226

Sashe 19

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

             Kira ya qwalawa sajida ya sanyata suka dinga jidar kayayyakinsu yana tayasu suna kaiwa dakin sumayya wadda ke zaune kurum tana ji da ganin sarautar Allah,sai da suka kammala tsaf yaya yahansun na dakin fa'iza suna cecekuce,ganin abun na sake qamari ya sanyashi shiga dakin ya janyeta yana fadin
"Kiyi haquri yaya yahanasu,kizo ku zauna dakin sumayya tunda itan da kuke so ta qiya" sai ta waiwayo ta bishi da ido galala tana kallonsa,mukhtar din da baison bacin ranta?,mukhtar din da baiso a tabata amma yau an mata cin kashin data jima rabon ta da irinsa amma ya kasa cewa uffan,kardai mallaka fa'iza tayi masa wadda baya iya qetare umarninta?,ranta ya shiga suya ta shiga fatar cewa Allah yasa ba haka bane,bata da wani zabi a yanzun illa ta bishi,idan yaso daga bisani tayi tunanin mafita a tsanake.

            Bayan sun shiga dakin ta zauna sannan ya kira sumayya ya fice zuwa dakinsa.

           Zaune ta tadda shi dafe da kansa,a hankali cikin kasala ta zauna gefansa,ta sanya tafin hannunta tana shafar bayansa a hankali,tasan fushin mukhtar din,saboda haka ta tabbatar ransa na a bace ne,kusan minti goma baice komai ba kafin daga bisani ya dago ya dubeta
"Sumayya" ya kira sunanta,a tausashe ta amsa sannan ya dora
"Gasu yaya yahanasu nan zasu zauna dakinki,kinsanta sarai ita da yaranta baki daya,baki buqatar muraja'a kansu,na shaideki da haquri wannan halinki ne,to amma don Allah ki nunka haqurinki,baqunta zasu mana na wani d'an lokaci,insha Allah zanyi qoqari na kammala musu gyaransu cikin qanqanin lokaci,idan da na kammala ma gini na sabon gida na can zan ara musu su zauna gudun fitina,kiyi haquri da su don Allah ki sake ninka kawaicinki" kai ta girgiza
"Haba ya mukhtar,ai ba roqona zaka yi ba,umarni kadai zaka bada,da kai da kaya ai duka mallakar wuya ne,nima yaya take agurina,insha Allahu babu wata matsala ko damuwa"
"Na gode,Allah yayi miki albarka"
"Amin yaya" ta fada tana sakin qayataccen murmushinta wanda har sai da ya sanyashi tsura mata idanu,hannu ta turo sautin idanunsa kamar zata tsone masa yaja baya suka saki dariya baki dayansu.

             Cikin dakin ya barta ya fita sallah,kasancewar tana faashin sallah sa'an nan kuma dakin nasa na hargitse don fa'iza ba kasafai take tsayawa ta gyara ba ya sanyata tsayawa tana dan kakkabe dakin haka ya dawo ya cimmata,kafin ya kai ga zama fa'iza ta fado dakin hannunta riqe a qugunta,shi ya fara cewa
"Me aka girka" ran nan nashi a hade tsaf wanda ita a nata zaton aikin da take kansa ya fara tasiri,saboda haka kanga tsaye tace
"Yau duka ma banyi girki ba wlh a gajiye nake" ta fada tana yatsina,sam ya tsaneta har yau ya kasa jinta dai dai da qwayar zarra cikin zuciyarsa,bata dameshi ba dama bisa lalura kawai yaje rabarta,qoqarin adalci ne kawai irin nasa tunda ta riga da ta rataya a wuyansa bisa alfarmar igiyoyinta uku dake hannunsa.

            Hannu ya miqa mata a daqile yace
"Bani muqullan locker din kayan abinci na" ba musu ta fice don dauko masa,ya juya ya dubi sumayya
"Yau ba'ayi girki ba gida na,me kuka bawa yaya taci ita da iyalanta?" Kanta ta duqar qasa sannan tace
"Ka mance na tambayeka zani kitso?,tunda na fita ban samu na dawo ba sai bayan la'asar,dana shigo kuma nima yadda ka taddasu haka na taddasu" kai ya gyada ba tare da yace komai ba,ta dawo da muqullin ta miqa masa,kai tsaye ya danqa su ga sumayya
"Jeki ka samar mana da abinda zamuci" hannu biyu tasa ta amsa kana ta danyi jim,da kamar taqi abinda ya sata din,sai kuma taga hakan bai dace ba,idan bai isa da fa'iza ba ita ai ya isa da ita,miqewa tayi zata fice fa'iza ta saki wani mugun murmushi,ga zatonta sumayya ta shiga cakwakiya mukhtar zai soma azabtar da ita kenan,fadawa tayi saman katifar kusa da shi tana fadin
"Ammmmm......idan kin gama kizo na gaya miki me mi kuma zaki dafamin" wannan karo kasa hadiye takaicinsa yayi sai da juyo yace
"Da yake baiwar gidan ubanki ce ko,wato saboda kinga na miki shiru ne ko......hmmmmm.....ki kiyayi ranar qin dillanci wallahi,wuce kije sumayya",sai ta juya ta fice din,itakam ta ma rasa na cewa gaba daya,gaban fa'iza ya fadi,kaddai jiya i yau ne dai mukhtar din,sai ta kasa hadiye qanin zagin da yayi mata ta miqe tsaye
" wacce rana ce ranar qin dillanci,ba ranar da hajar mai gari ta bata ba?,idan ba'a ganta a gun fa'iza sai me?"ta murguda baki tana niyyar ficewa,zuciya ce ta ciyoshi ya miqe cikin zafin nama ya fincikota ya zabga mata wani lafiyayyen mari,a gigice ta dafe kuncinta don bata zaci haka ba,karo na farko da mukhtar din ya soma taba lafiyarta,ashar ta danna sannan tace
"Ni ka mara muntari,kayyasa kace yau da bala'i,wallahi baka daki bulus ba sai na rama" .

           Daga hannunta tayi da niyyar kaiwa fuskarsa mari ya cafe hannun tare da murdeshi har sai ta qashin hannun ya bada wani qasss da alamu ya targadata,tsananin azaba ya sanyata sakin qara wadda ta sanya sumayya dake kitchen barin abinda take ta taho dakin cikin hanzari,dadin da taji data lura su yaya yahanasun da suka qure kallo cikin t.v dinta basu san me ake ciki ba,tun fara masa rashin kunyar duk cikin kunnenta ne saboda muryar fa'izan na sama ne sosai.

             Sanda ta isa dakin ya daga hannu da niyyar sake bata wani marin,cikin hanzari ta shiga tsakiyarsu taba riqe hannunsa,cikin taushi ta langabar da kanta tana duban tsakiyar idonsa wanda hakan shi ya karya lagonsa,ya zare hannunaa daga nata,bakinta bai mutu ba sai data wurga masa kalmar
"Wallahi wallahi sai kayi dana sanin dukan fa'iza,sai ka biya farashin duka na da kayi,zaka gani,ke kuma ku zuba mu gani" sannan ta fice.

         Tabbas ba don har tanzu bai cimma qudirinsa ba akanta da yau babu abinda zai hanata kwana cikin gidan ubanta,gefensa ta zauna ta sanya hannunta cikin nashi sannnan tace
"Sam hakan ba girmanka bane ya mukhtar,tunda nake ban taba gani ka daki wani ba ma bare matarka ta aure,yin hakan ba daidai bane,na roqeka don Allah kada ka sake sai ka fara bani tsoro ai" ta qarasa fada a shagwabe,sai ya dago yana dubanta da murmushi,take kaso saba'in cikin dari na bacin ransa ya zabge ga fadi sai ya dora hannunsa shima saman nata
"Banaso ki fara jin tsoro na sumy ta,idan kika fara tsoro na na zauna da wa?,bazan sake ba,kiyi haquri" kai ta girgiza tana murmushi
"Kai ya kamata nace kayi haquri yaya ka yafe mana,yau mun sanyaka cikin bacin rai" kasa magana yayi sai ua rungumeta kawai cikin jikinsa yana jin duminya,yana ganin girma da qimar wannan halitta mau tsananin hankali da biyayya a gareshi,shikam mai zai hana shi faranta nata matuqar yana da iko?,me ya isa ya hanashi sonta a duniya?,babu shi,babu shi ko mene,koda QADDARA ce baijin tana da wannan qarfin ikon,baya fata ma QADDARAR tazo masa ta wannan sigar,gwara ta kowacce siga amma banda wannan,wala'alla ya iya jurewa.

          Sai da suka fara jiyo qaurin girkinta sannan ya saketa ta miqe da hanzari ta fice tana ce masa tana zuwa.

*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍✍✍✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣7⃣

________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*ma asaba min musibatun fil'ardi wala fi anfusikum illa fi kitabim min qabli an nabra'aha*
_______________________

             Cikin mintuna qalilan ta kammala jallope din taliyar ta rarraba cikin coolers,mukhtar din ta fara kaiwa,tana niyyar juyawa ta fita yace da ita
"Wannan cooler din fa na waye?" Ta dubi cooler din sannan ta dubeshi
"Na fa'ixa ne a ciki"
"Ajjiye a nan" ya fada yana gwada mata inda zata ajjiye din da idonsa,bata kawo komai cikin ranta ba ta ajjiye din ta nufi dakinta.

            Can ta taddasu sun baje suna kallo,duk da cewa kallo daya zaka yiwa yahanasun kasan tabbas har yau ranta a bace yake,ta dire cooler din tana cewa
"Ga abincinku yaya" wani banzan kallo ta watsa mata
"Eh zamu ci ai kuma zamu ambaci sunan Allah,in sha Allahu babu abinda zai samemu,makira,idan ma shiga kika tsakaninmu da fa'iza har take wannan tashan rashin kunyan to ni zanyi maganinku ke da iyan baki daya" kai ta kada ba tare da tace komai ba ta shige uwar dakinta,ta tube kayanta ta sauya na bacci,sai tayi zamanta gefan gado ta janyo RIYADUL JANNAH littafin addu'o'inta da malam ya bata wanda bata rabi da shi ta soma duba wasu shafuka.

          Sumayyan na fita ya dauki cooler din baki daya ya fita da ita waje,wasu almajirai da rabonsu ya rantse ya samu qofar gida zazzaune ya basu,take suka karba suka rabe a tsakaninsu suna zabga godiya banza ta faadi garesu.

             Yana kammala rufe gidan sukayi karo da fa'iza wadda ta dawo daga dakin sumayya ta bankade labulenta ko kallo su ya yahanasu basu isheta ba ta qwallawa sumayya tambayar ina abincinta,tana daga cikin dakin ta gaya mata yana gun yaya mukhtar.

          Dubansa tayi"ina abinci na?"banza ya bawa ajiyarta yayi wucewarsa,sai ta bishi da kallo,bata haqura ba tabi bayansa tana sake tambayarsa,wani wawan birki yaci wanda sai da ya sanyata ja da baya
"Baki daku ba kenan ko?,tare muka hada muka siyo abincin?,ko kinzo da bayi ne daga gidanku?,uban wani ne ya hanaki dafawa kici,ki fice min daga nan tun kafin na hasala na sake kikkifa miki mari" tana qunquni ta juya ta fice ranta qunci fal,ga uwar yunwar dake sakadarta,abinka da mutum mai shegen ci ta riga da ta saba.

            A tsakar gida taci karo da jamila na wanke hannunta,da gayya ta bangajeta tayi taga taga ta fadi,sai ta miqe kuwa ta lailayawa fa'izar ashar abinka da itama tana ji da tata rashin kunyar,ai kuwa fa'izan tayo kanta zata huce bisa kan nata,dai dai sanda yaya yahanasu ta qaraso tayi hanzarin riqeta ta gabza mata mari dama tana ciki da ita ne,tana waiwayowa kuwa ta cakumi wuyan yaya yahanasun take jamila ta shigarwa uwarta nan fada ya kaure tsakanin su ukun.
Chapter 19 · 0% Book details