← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 144 OF 226

Sashe 144

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wayar ta sauke daga kunnenta tana duban mahaifiyarta dakezaune gefanta,wadda itace ta karanta mata dukkan abinda zatayi din
"Nifa mom gaskiya ina jin tsoro,ina son mijina kada naje nayi abinda zai zame mana dana sani,nasan halin almustapha sarai baya daukar raini" harara ta galla mata tana huci tamkar ita aka yiwa kishiyar
"Ai sai ki zauna dan ubanki,ke yanzu ba abun kunya bane gareki ace wai an miki kishiya?,uwarki ma har ta qaraci quruciyarta har zuwa tsufanta bata zauna da kishiya ba?,ki tashi ki masa hauka ki qwaci 'yancinki,rashin qwatar 'yancin naki shi zai haifar da abinda kike tsoron na rasa mijin naki,kishiya bala'ice masifa ce annoba ce,ke kishiya ta wuce duk inda kike zatonta,ki tabbatar ya zaba ko ke ko ita,ke yarinya ce baki sani bane,inda ina da ita 'yancin da kika samu a rayuwarki da baki same shi ba,ban taba sanin hajiya kilishi da gaske har yau bata qaunata ba sai yanzu,daboda ita ta zauna da kishiya shine suka hada baki suka yi miki,dama can ba jituwa muke ba,aurenki da danta ne ma ya sake sawa muke hulda ta dole,to wallahi zata ga tsantsar rashin arziquki,ki tashi tsaye kada ki raga mata har sai kin raba tsakaninsu,sannan duk wanda ke gidan kada ki raga masa ciki harda hajiya kilishin,ku juye rashin mutuncinki son ranki,har sai kowa yayi laushi ya nemi daidaito da ke,indai nonon khaulat kika sha rainon america ce ke" kalamai masu nauyi ta dinga amfani da su tare da nuna mata cewa ba zata taba mallakar almustapha ba matuqar yana da wata matar,kalaman sunyi tasiri matuqa a kunne zuciya da gangar jikin su'ad,hakan ya sanya ta soma hada kayanta haiqan don isowa nageria ta bashi zabin zama da ita ko zama da amaryarsa,wanda baki daya haushin jama'ar gidan takeji musamman data samu labarin diyar aminin baabaa prof ce,tana jin dama can suna adawa da ita,suna adawa da zamanta da mijinta,saboda ya dauke mata komai tana juyawa da takunta yadda taga dama,ba shakka ba zata raga ma kowa ba indai akan almustaphanta ne.

To masu karatu,ku biyoni muje.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

7⃣7⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

___________________________________

      Bayan sun shiga cikin jirgi bata sake ganinshi ba,batasan inda ya zauna ba sai da suka sauka,cikin motocin gidan aka zo daukarsu,tana tsaye har ya shiga sannan itama ta bude ta shiga,yana zaune daga daya bangaren itama haka,motar tsit,shi yana danne dannen wayarshi yayin da ita kuma ta bige da kallon titi tamkar yau ta soma ganin garin a haka har suka qarasa.

       A hankali motar ke kutsawa cikin unguwar tasu,tana kallo suka wuce qofar gidan anty dije,kamar tayi tsalle ta fita haka take ji,saidai ba yadda zata yi,yanzun a qarqashin wani take dole,ajiyar zuciya ta saki tana sauke jumfashi,a yau a kuma wannan lokacin gata ta sake dawowa cikin gafin,saidai cikin wanu matsayi na daban,ta dawo cikin garin a matsayin matar wani kuma surukar gidan baabaa professor,ma'ajiyar motoci motar ta tsaya bayan mai gadin ya bude masu wakekiyar qofar gidan,a hankali ta sanya hannunta ta bude murfin motar bayan tsayawar motar,qafarta ta zura guda daya waje ihun amira ya karade kunnuwanta,kafin tace wanu abu tuni ta ruqunqumeta
"Wayyo amaryarmu oyoyo oyoyo" murmushi ya subucewa sumayya,da ido takewa amiran nuni da bayanta,sam bata ankara ba karadinta kawai take
"Ke matar nan kiji tsoron Allah,har an fara sanin dadin miji ko?,anty ta bani labari daga zuwa ganin doctor sai kawai ayi mai gaba daya,kodai......" Bata kai ga qarasawa ba ya fito daga cikin motar,wanda hakan ya tilasta mata sanyawa bakinta fulasta sabida kallon da ya jefeta da shi,magana ce fal cikinta amma tilas ta saita kanta,a ladabce tace
"Barka da isowa yaya"
"Sake mata hannu ko?" Ya fadi ba tare da ya damu da amsa gaisuwar tata ba,hannun ta saki tana baata fuska ta janye gefe,kafeta yayi da idanu yana mata alama data wuce yana yin gaba,binsa tayi a baya amira ta rufa musu baya,duk da haka bata haqura ba sai data tsaya saitin sumayyan murya qasa qasa
"Wannan hadi yayi kyau,Allah ka nunamin idanuwan su'ad naga ya zata yi" ta gefan idanu ta jefa mata harara amma hakan bai sanya ta fasa ba,waiwayowar musty din ne ya sanyata ja da baya tana raba idanu.

      Kai tsaye bangaren ummee suka soma shiga,a hankali suke takawa jere da junansu tamkar wasu shaqiqan masoya,su biyun ke zaune a falon ummee da maamaa,da alama suna tattauna wani abu ne,amsa sallamar sukayi kowacce fuskarta a sake,idanun umme bisa fuskarshi,shi ya soma yiwa kansa matsuguni kan daya daga cikin kujerun falon kafin ta qarasa takowa a ladabce zuwa cikin falon,kanta a qasa a kunyace ta qarasa amira na gefanta,wata kunya da nauyinsu take ji a yanzu wadda ta ninka ta da,musamman ummee wadda dama can ba wani sakewa ko sabo sosai tsakaninsu,gefe ta zauna qasan carfet kan ta a qasa
"Tashi ki koma saman kujera mana,wacce irin tafiya ce haka almustapha?" Ta tambayeshi tana dubansa,kanshi ya shafa yana yana yiwa ummeen magana da idanu zuwa sashen da su sumayya suke,ta fuskanci mai yake son fadi amma duk da haka bata fasa sake magana ba
"Babu sanarwa ba komai,halan ma baka barta ta kintsa ba ka tattago ta ko?" Inji ummeen tana bata rai,don tuni amira ta fesa mata yadda ya dauko sumayyan,cikin salon bada uziri yace
"Ummee,umarnin baba ne"dauke idanunta tayi ta maida kan sumayyan wadda suke gaisawa da anty maamaa,cikinnurmushi ta soma gaidata
"Ummee ina yini"
"Lafiya qalau ya gajiyan hanya"
"Alhmdlh" ta fadi cikin ranta tana fadin wacce gajiya gurin mutumin da yayi tafiya a jirgi
"Anty kun yini lpy?" Cewar almustapha yana miqewa tsaye
"Lafiya qalau almustapha,ashe kuna hanya babu sanarwa bare ayi abun tarbar baqi" qaramin murmushi kawai ya saki na gefan baki,bai amsa ba sai ya jefo tambaya
"Baabaa fa?"
"Ya fita,yana can suna lissafin gidajen gonar nan"
"Ok" ya fada a taqaice yana takawa zuwa hanyar barin falon,ko motsawa sumayyan batayi ba,wanda hakan ya burge ummee da anty maamaan baki daya,ta tabbatar da cewa da su'ad ce da tuni miqe ta rufa mishi baya
"Kada ka rufe sashen idan ka shiga,anjima zamu kawo amarya" inji anty mama
"Ok" kawai yace yana ficewa a sashen,kamar jira amira takeyi ta buga tsalle ta iso gaban sumayyan
"Tashi muje namecy" harara ummee ta buga mata
"Saura ki hanata sakewa kuma bare ta huta gajiyan data kwaso ko?" Dariya amira tayi yayin da sumayya ta miqe ta bita tana murmushi kanta a qasa.

Hira ce sosai ta barke tsakaninsu,sumayya kallon amiran take,da alama auren ya karbeta qwarai,ta sake haske ta murje,tsokanan da amiran keyi mata ya soma isanta hakan ya sanya itama ta soma tsokananta kodai ta samo musu baby,wannan ya taqaita tsokanan da take mata ta barta ta sarara mata,sai da akayi sallar magariba amira ta shiga alwala sannan ta kira antyn ta shaida mata isowarsu,ta soma roqonta ta turo mata laila
"Madalla amarsu,su laila zasu zo amma ban fadi yaushe ba,ke ke da ki gansu ma sai na gamsu da yadda kike zamantakewarki" kai ta langabe kamar tana gabanta
"Kai anty,haka zamuyi dake?"
"Har ma fiye da haka idan baki zama jarumar mace ba,baki kuma yi fiye da yadda nake son gani ba" ta fada tana datse layin,dariya ma maganar anty ta bata,bayi ta shiga itama don sauya pad din jikinta bayan fitowar amiran.

Gefan gado ta kuma zama ta lalubi lambar yaya yahansu don taji abdallah,bugu uku aka daga,shi din ne ma ya daga,murmushi ta saki kan yadda yayan ke shagwaba abdallah
"Amminaaa" ya fada cikin muryar quruciya
"Abdallah na,kai baka damu kaga amminka ba ko?" Dariya ya qyalqyale da ita yana cewa
"A nan ma ai ina da wasu ammin,ga mama ma,ga anty jamila,ga anty yaya(yaya yahanasu)"taji dadi qwarai cikin ranta jin bai tare da wata damuwa,amma sai ta dan tsokaleshi
"Shikenan na sake komawa abuja na barka ai"
"Nima bana son zuwa,su kullmun ana gida,nan kuwa zamuyi wasa da su walid,amma kicewa daddy na wannan wanda ya daukeni a motarsa ina gaisheshi" sarai ta gane almustapha yake nufi,sai tayi murmushi kawai ta kauda zancan
"Me kake so a kawo maka yanzu"
"Ba komai ammi,dazu ma da inason indomie anty jamila ta dafa min naci na qoshi,ta kuma bani bobo"
"To an gaida anty jamila,ayi karatu da kyau abdallah,banda rigima"
"Ai bazanyi ba,tunda ga malam dina dazu ma naje wajensa" dariya ta saki sannan tace
"Ok ilove you my abdallah"
"I love you too ammina"tayi hanzarin datse layin jin yaya yahanasu na qoqarin karba,nauyinta take ji sosai bata jin a irin wannan yanayin zata iya magana da ita
" ki gama cin amarcinki zuwa zamuyi mu dauko abdallahn mu"cewar amira,murmushi kawai tayi din bata jin mutanan kano zasu iya basu abdallah,musamman yaya yahanasu da take jinsa kamar mukhtar,bata son ya motsa ko nan da can,shima kuma yaron kamar yasan yadda aka rabu da mahaifinsa cikin kewa baya yadda ya yiwa gida nisa,bai wuce gidansu ko gidan yaya yahanasun ko na wuni daya kuwa.

Bayan sallar magariba suna hira sama sama anty maamaa ta shigo dakin
"Amarya taso baabaanki na fada yace na miqa ki dakinki" a kunyace ta motsa ta miqe,gabanta na wani irin faduwa,fargaba ta cikata,haka ta fito antyn na riqe da hannunta amira na biye da su,a falo suka samu ummee,antyn ta dubeta
"Ummeen yara zaki rakamu ne?" Ta fada cikin salon tsokana,wanda tasan ba zata din na,baki ta tabe tana murmushi gami da girgiza kai
"Um um,sai kun dawo,ki dai jawa d'anki kunne idan yana nan" ta fada tana miqawa sumayya wani babban kwali,amira ce ta qaraso ta amsa tana taya sumayyan godiya sannan suka fice.
Chapter 144 · 0% Book details