← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 226

Sashe 54

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

       Dawowa tayi inda suke kowa ya kammala mai adaidaitan dake kaisu ma ya iso ta dubesu
" mamanku fa ta dawo jiya da daddare"ta tsammaci zata ga tsantsar farinciki a fuskokinsu,sai taga babu yabo ba fallasa,babu wani zumudi ko doki,nuwaira kuwa tsoro da fargaba ne ma ya mamayeta,a haka ta rakasu suka fice sannan ta dawo ta gyara falo zuwa kitchen ta barwa mai aikinsu wanke wanke idan ta iso tayi wanka ta leqa bangaren hajiya,sai ta sameta tana bacci,saboda haka ta mata 'yan gyare gyarenta ta fito ta barta ta dawo falo ta zauna tana jira sha daya da rabi tayi ta karya,sai ta kunna t.v tana kallon arewa 24 don ta debe mata kewa,zuwa yanzu sum shaqu sosai da yaran,idan basa tare duk sai taji babu dadi kasancewarta mai son yara.

       Tana jiyo qarar bude qofar karima amma bata maida hankalinta kai ba har sai da taji cikin taqama tana fadin
"Ina yara na" cikin ladabi kamar bawa da uban gidansa taji lukman na cewa
"Eh sun tafi makaranta ai sumayya ta turasu" cikin harzuqa tace
"Eh wato suma an shige musu za'a shanyesu a rabani da su kenan?" Sai ta saki wani shu'umin murmushi tana kada kai
"Mu zuba mu gani,muje ka rakani naga hajiya nata salon ita kuma" ta fada tana yin gaba,jiki na rawa yana tafe yana waiwayen sumayya yabi bayanta,kai ta jinjina bayan fitarsu
"Innalillahi wa 'inna ilaihi raji'un" ta fada tana kada kai ganin hannun agogo nason komawa baya game da lamarin lukman din.

Zuwanta gun hajiyan ta taddata fiye da yadda ma ta barta,don fada hajiyan ma ta mata kan dalilin tafiyarta wani gu bayan tana da aure,sosai hajiyan keji qarfin zuciyarta sam babu wani dar da taji balle taji tsoron karimar,sai lokacin ta yadda lallai idan kayi sakaci da addu'a babu abinda ba zaya iya faruwa da bawa ba duk da cewa akwai QADDARA amma babu abinda ke sauya qaddarar irin ADDU'A.

Ko da rana da yaran suka dawo sun gaidata,baki ta saki tana kallon yadda suka sauya baki daya,tana kallon yadda suke girmama nuwaira da islam,lallai sumayya ta sauya mata yara,ya akayi bata sanya an musu farraqu ba ita da au ta barsu suka shaqu haka,tana gani suka sauya kayansu zuwa na islamiya bayan sunci abinci,suna sanya hijabansu sumayya na tsakiyarsu tana hada musu litattafan islamiyar su kariman ta banko qofar dakin tana huci,tsayawa tayi tana dubansu fuska a tsuke,sumayya data kalleta saita maida kai taci gaba da abinda take
"Laaa,mama bakiyi sallama ba fa,kuma babu kyau shiga gu ba sallama" nuratu ta fada,mamaki ya kama kariman sai ta waiwaya tana kallonta amma sai ta wayance da cewa
"Ku cire kayan nan,babu wata makaranta da zaku sake zuwa daga dawowarku daga boko ko hutawa bakuyi ba" islam ce ta maqe wuya tana cewa
"Mama ki barmu muje,idan mun dawo ma huta din,idan kana fashi fa ana wuceka a karatun" ido ta kuma zarowa mamki na sake kasheta,lallai sumayya tayi amfani da irin surkullensu ta rabata da yaranta,tsawa ta daka musu tana cewa
"Don ubanki da ni kike jayayya,ku cire kayanku nace babu inda zaku" sumayya ce ta bar abinda take ta tako zuwa inda take tana cewa
"Haba maman nuratu,meye na zagi har haka?,ina cewa ke zaki fi kowa farincikin zuwan yaranki makaranta,ba girmanki bane" sai ta waiwaya ga yaran da sukayi carko carko suna kallon karimar
"Maza ku wuce ku tafi mamarku ta haqura" da sauri suka fice kuwa daya bayan daya,sai da suka kammala ficewa tas sannan karima ta kalli sumayya
"Yaro man kaza,ke da su baki daya baku da bambanci a gurina,lokaci na baki shi nake jira" tana gama fada ta fita
"Allah ya fiki,Allah ya isar min da ke akan dukkan wani nufinki,alkhairin ubangiji nake nemawa rayuwata" ta fada tana gyara dakin yaran da suka bata tare da killace kayan makarantarsu gu guda kafin su dawo su wanke

Baki daya sai aka koma 'yar gidan jiya kan halayen mukhtar,yayin da bangare guda sauyawar yaranta da hajiya ke ciwa kariman tuwo a qwarya,saidai ta kammala dukkan wani shirinta na maida hannun agogo baya ranar kawai take jira,wanda hakan ya sanya ta sanyawa kowa ido,wannan kuma ya bada damar da shaquwa mai qarfi taci gaba da gudana tsakanin sumayya yaran da hajiyar.

****** ******* ******

Qarfe daya na rana ne wanda saika dauka qarfe takwas ne na safe saboda yanayin sanyin da ake zabgawa a garin,tuni ta kammala abincin rana ita da mai aikin gidan qwaya daya saboda biyu na rana yaran zasu dawo ta baiwa kowa haqqinsa,kasancewar tunda karima ta dawo gidan bata ko dubi kitchen ba.

Tayi sallar azahar dinta sai ta qudundune kan gado kafin yaran su dawo,bude qofar dakin nata da akayi shi ya sanyata daga kai ta kalli qofar,karima ce cikin kwalliya da daurin ture kaga tsiya,jambaki kamar zai digo daga bakinta,itace a gaba lukman na biye da ita janye da trolly,sallama kariman tayi wadda ta bawa sumayya mamaki,qarasowa tayi bakin gadon tana duban sumayya
"Mijinki ko mijina?....oho koma meye,shi na rako ya miki sallama zaiyi tafiya,wadda itace zata kasance sallama ta qarshe tsakaninku" ta qarashe tana dariya dariya,ta waiwaya ta dubi lukman dake tsaye,fuskarnan tamkar zai sanya kuka ,amma tana dubansa sai ya saki murmushi
"Bari na baku guri ko don kuyi sallama sosai" sai ta juya ta fice.

Sakin akwatin yayi ya qaraso inda take ya zauna gefanta,sai ta tashi daga kwanciyar ta zauna sosai tana kallon fuskarsa gabanta na faduwa
"Kiyi haquri sumayya,kiyi haquri don Allah,ba laifina bane sumayya,haka nan nake jin bazan iya ci gaba da ke ba,haka kawai nake jin idan naci gaba da zama da ke akwai cutarwa,sumayya ki yafemin akwai QADDARAR dake bibiyar rayuwata,ina sonki har cikin zuciyata amma bazan iya zama da ke ba...."
"Ya isa lukman,ka fadi abinda kake son fada,ka fadi a wuce gurin" ta fada cikin rawar murya,bai kai ga cewa komai ba karima ta sake shigowa dakin,cikin daga murya tace
"Wai me kakeyi ne hakan har yanzu,kasan dai jirgi baya jira saidai a jirashi ko?" Ta fada tana tsareshi da ido,cikin sanyi jiki ya sanya hannunsa a aljuhunsa ya fiddo takarda a ninke ya miqa mata,hannu kawai ta sanya ta karba,koda baiyi mata bayani ba tasan takardar meye,saboda haka bata da buqatar budeta,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki haka ya miqe yaja akwatinsa yana waiwayenta har ya fice karima ta rufa masa baya.

Cikin dogon tunanin da batasan tsawon lokacin data dauka cikinsa ba taji islam na girgiza kafadarta
"Momy,tun dazu muke sallama shiru baki amsa mana ba" sai ta daga kai ta kallesu,dukkansu suna tsaye gabanta suna kallonta cirko cirko,alamun damuwa duka sun bayyana kan fuskokinsu,tausayinsu sai ya lullubeta duk da a yanzu tafi jin tausayin kanta,don nasu mai sauqi ne,qwalla ta cika mata idanu amma sai tayi ta maza ta hadiyeta,ta qaqalo murmushi tana cewa
"Wa'alaikumus salam warahmatullahi wabarkatuhu,banjin sallamar taku bane,muje maza a shirya yau kun dawo a makare ko?" Ta fadi tana saukowa daga kan gadon,biyo bayanta sukayi kowa na bata labarin yau na makaranta,tana shiryasu tana biye musu,yayin da qarqashin zuciyarta ke a cunkushe,tausayinsu naci gaba da lullubeta musamman nuwaira,duk da tana da yaqinin insha Allah ba zata tozarta kamar baya ba tunda a yanzu an samu kan 'yan uwanta da kakarta,sosai tayi jarumtar danne damuwarta,saidai duk da haka nuwaira sai da taso dagota,don ta saci kallonta sai daya taga tana dauke qwalla,duk sai yarinyar ta tsargu taqi sakin jiki,duk inda sumayyan tayi tana biye da ita da idanu,har suka gama dabdalarsu bataji motsi ko giftawar karima ba,da haka ta shiryasu suka fice,ko sanda zasu fita din sai data juyo ta sake kallonta ita kuma ta rakata da murmushi.

Sai data fara hada kayanta sannan taji kuka ya qwace mata,bakin gado ta koma tayi kuka san ranta sannan ta hada duk abinda zata buqata cikin akwati ta zira hijabinta ta janyo akwatin nata bayan ta saka takalmanta.
Chapter 54 · 0% Book details