← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 167 OF 226

Sashe 167

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

     Tare suka jero da malam din suna hira jefi jefi har suka qaraso gidan,da kansa malam din ya bude masa sitting room yace ya shiga ya zauna,bai musa ba ya shiga ya zauna din yana qarewa falon kallo,ciki malam ya koma ya sake kiran sumayya ya shaida mata duk abinda take ta baro ta taho tayi baqi,cikin mamakin wanne irin baqi tayi haka tace masa tana dab da shigowa unguwar ta iso tuntuni.

       Cikin sanda ta shigi soron,idanuwanta kan takalmin sau ciki dake qofar sitting room din,cikin gidan ta wuce kai tsaye,mama ta taras a falo tana wanke wani rubutu,tun da tazo taga tana yinsa kullum da yamma batasan dai ko na meye ba,baki sake maman ta kalleta
"Me kika shigo kuma yi?,baqon ai yana sitting room"gabanta ke faduwa hakanan da wani irin tsoro
" waye mama?"
"Idan kin shuga kya gani,tsaya ki karbi wannan ki shanye tunda kin riga da kin shigo" inji maman tana juye wani rubutun daga wata jarka wanda ke gauraye da zuma ta miqa mata,bata musa ba ta karba ra kwankwade,sannan ya zare niqab dinta daga saman zabgegen hijabin dake jikinta,don tunda tazo ta koma wannan shigar,sakamakon yadda aketa tanka canzawar da tayi,bugu da qari da yawan kallon da take fuskanta wajen maza idan ta fita,jakarta ta sabule ta ajjiye saman kujera ta dubi mama
"Kayana an kawo gugar?"
"Akwatin ma a hade yake,ba jibi ko gata zaki wuce ba?"
"Eh amma mama nikam banson tafiya wlh,da sai ranar daurin aure kawai" harararta maman tayi
"Ban koya miki sabawa umarnin miji ba,randa yace ki tafi koda yau ne tafiya zakiyi" murmushi ta saki kawai ta juya ta fice,tunda tazo maman bata da aiki sai ja mata kunnen tabi miji.

       Tun kafin ta kai ga shiga dakin take ji qamshin wani turare kamar ta sanshi,hannu ta sanya ta yaye labulen bakinta dauke da sallama,idanu ya zuba mata yana dubanta,baki daya ko ina na jikinta a lullube yake tun daga saman qafarta har zuwa kanta da hijabi,wani sanyi yaji ya ratsashi,karon farko yaji shigar tayi masa,ba abinda ke nunawa a jikinta,idanu suka hada ta saki labulen tana takawa a hanakali kamar mai taka qaya,wani shegen kwarjini yayi mata,ya cika mata idanu baki daya,bai fasa kallonta ba har ta qaraso kan daya daga cikin kujerun dake zagaye da falon ta yiwa kanta matsugunni,gababshi kewaye da ruwa da lemuka saidai babu wanda ya taba
"Sannu da zuwa" ta fada tana dubanshi qasa qasa
"Ina kika je?" Ya tambayeta maimakon amsa
"Gidan aunty na,aunty salma"
"Wa kika tambaya?" Wannan karon dagowa tayi ta zuba masa idanu cikin mamaki,taga dai dole idan tazo ya sani zata gidan 'yan uwa dai,janye nashibidanun yayi wannan karon,kallon da take masa yana sake kasheshi da narkar da duk wani sashe mai muhimmanci dake jikinsa
"Tashi ki dauko kayanki mu wuce?" Ranta ya baci,take idanunta suka hada qwalla
"Amma sai jibi ai zan wuce abujan ko?,yau fa kwana na shida fa anan din?"
"Haka nake da buqata idan kuma ban isa ba to" idanunta ta kawar qwallar na zirarowa a idanunta,ta miqe tamkar zata rushe da kuka ta fice.

      Kuka ta sanyawa maman da qyar ta ciyo kanta ra gaya mata abinda ya faru,idanu maman ta zuba mata
"Shikenan don yace zaku wuce zaki zo kina rusan wannan kukan?,da can kinsan zaki zo din ne ka din ya barki?,so kike ku taru duk ku zama taron tsintsiya babu shara,ai da nasan abinda kike wa kukan ma da tuni naci mutuncinki,tashi ki dauko kayanki" maman ta fada tana miqewa zuwa uwar dakinta,waya ta dauko ta kira malam ta shaida masa,yace Allah ya tsare baya kusa ya fita daga unguwar amma ta tabbata sun tafi,idan ta zauna me zata musu.

         A tsaye ta sameta a falo tana goge hawaye riqe da jakar matafiya mai taya,hannun maman dauke da wani babban kwali
"Ga tsaraba nan ki kaiwa surukar taki"
"To mama,abdallah fa?"
"Zasu zo da malam daurin aure ran asabar din in sha Allah idan babanshi ya barshi,shi bai ta taki ma,ko maganarki ake bai damuwa,Allah ya riga ya sanya masa son jama'a,Allah ya tsare hanya sai munyi waya,kibi mijinki shine aljannarki"
"Na gode mama" ta fada tana karbar wani rubutu cikin jarka a hannun mama sai qamshin kanunfari da zuma yake ta saka jakarta duk da batasan na meye ba.

        Maimakon taga sunyi hanyar airphort sai kawai taga sunyi gidan baba dake kano,bata tanka masa ba har suka isa gidan,shima waya yake tayi da ma'aikatan asibitinsa har suka je din,fes suka tadda dakin nashi kamar da mutum a ciki,hakan baya rasa nasaba da ma'aikatan dake gidan kulli yaumin koda masu gidan basa nan,gefan gado ta zauna har yanzu idanuwanta na fidda hawaye,kayan jikinsa ya soma cirewa saboda yana da buqatar wanka,baiko dubi sashen da take ba,hakanan kukanta ke taba zuciyarsa fiye da ko yaushe,meye abun kukan?,toilet ya shige ya rufo qofar.

       Har ya fito a nan ya taddata,ya gama shiryawa tana nade a wajen,silifas ya zira ya bude qofar dakin ya fice,miqewa tayi a hankali ta fidda hijabin jikinta ta shige toilet,wanka tayi ta hado da alwala ta dawo ta fidda kayan shafawarta,sallar ta soma yi,sannan ta shirya tsaf cikin sababbin kayan data siya a wani gurin saida kayayyaki,gown gown ne fitted masu roba wanda suke saukowa har qauri,matsatstsen dogon hannu gareta,rigar tabi lafiyar jikinta sosai ta fitar mata da qira,gashinta ta shafawa mai ta taje sannan ta daureshi da qaramin ribbom,hakan ya bawa jelar damar fitowa sosai da nuna irin yawan da gashin yake da shi,gefan kujera ta samu tayi zamanta abunta,ko dankwali bata nema ta daura ba,sai ta jawo wayarta tana danne danne tana duba watsapp dinta,wanda tunda aka bude mata bata bi ta kanshi ba sai yanzu,har yanzu ranta a dan bace yake,saboda tana ganin yana mata mulkin kama karya ne kawai,a duk sanda yaso tafiya da ita saidai ta ganshi kwatsam,kuma yace lallai ta taho su tafi haka ake?.

Qofar aka turo,almustapha ne hannunshi dauke da takeaway,amsa sallamar tayi ba tare data daga kanta ba,hakan ya bashi damar qare mata kallo son ranshi,karon farko da ya ganta cikin irin shigar turawa
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya fadi cikin ranshi saboda wani abu da yaji na yawo cikin jikinshi
"Komai ma yi mata kyau yake ne?" Ya sake tambayar kanshi har zuwa sanda ya qarasa qasan carfet ya zauna yana fidda abinda ya siyo,harar kayan tayi a fakaice tana rayawa cikin ranta itakam ta gaji da wannan ciye ciyen,wato za'a koma 'yar gidan jiya,da iliminta na iya girki gaskiya ba zata zauna ta qare a takeaway ba,ta lura baki daya aqidun turawa sun ratsashi.

Abincinsa ya fara ci hankali kwance yana qarewa shigar tata kallo a fakaice,ta zama tamkar wata 'yar baby ko yarinya 'yar sha hudu
"Zo nan" ya fada yana wani cin mur,daga kanta tayi ta kalleshi,babu faraga saman fuskarsa hakan ya sanya ta miqe tsam ta soma takawa zuwa inda yake,kasa dauke idanunshi yayi daga kanta,komai yana juyawa da kuma motsawa tamkar wadda ake bawa umarni,zakayi tsammanin da gangan take aikata hakan,saidai ko kadan haka nata salon tafiyar yake,haushin da take ji ya sanya bata ma yi tunanin saka hijabin ba,salon tafiyar tata ya sake kashe almustapha,abu na farko da yake marmafi da muradin wajen macen da zaya auda tun da can bayan,sanin wannan dalili ya sanya su'ad koyon irin tafiyar da yake so din,saidai duk yadda ka kai ga aro abu ka yafa ba kamar yadda yake a halittar ka ba,nuni yayi mata da kusa da shi,cikin shan mur ta zauna har ma fiye da inda ya nuna matan,qamshin turarukanta suka soma kai saqo qwaqwalwarsa,nuni yayi mata da plate din da yake cin abinci,kamar zata saki kuka haka ta sanya hannu,saidai baki daya ta kasa sakewa bare taci,ga idanunshi da suka mata nauyi wanda ya azasu kacokam a kanta,so yake lallai sai ya gano wani abu na daban dake tattare da ita,wanda yake haddasa masa jin wani irin mai nauyi cikin zuciyarsa da qirjinsa,ya rasa meye wannan mai qarfi dake yawan fusgarsa zuwa gareta.

Shi ya soma tsame hannunshi,ya shiga toilet yayi brush,kai tsaye saman gado ya nufa ya zauna,ya kawo laptop dinsa ya soma aiki,jifa jifa yana dubanta tana zaune gaban abincin wanda har yanzu kusan wasa kawai takeyi da shi,kasala da wani irin feelings da yake ji ya hanashi ci gaba da aikin,sai ya kashe cumputer baki dayanta ya ajjuyeta saman bedside,hannayenshu ya hade guri daya cikin zuciyarshi yana wani dan tunani,ya dan bita da kallo sanda ta miqe tana tattara kwanukan,ta gyara wajen tsaf,sannan ta shiga bandaki don sauya kayan baccinta ganin har ya sauya hasken dakin,idanunshi bisa kanta sanda ta fito din,abinda yake ji ya dinga bunqasa,ya hanashi sukuni,tilas ya miqe yana fidda numfashi ya miqa hannunshi ya kunna fitilar gefan gado,waiwayowa tayi suka hada idanuwa
"Dauko min ruwa" ya fadi yana lumshe idanunshi numfashinsa na fita da sauri,ganin sauyawar yanayi tattare da shi ya sanya tayi tsammanin bai jin dadi,sai ta miqe a hankali,ta isa ga freezer ta ciro ruwa ta hada da kofi,gadon ta haye baki daya ta tsiyaya ruwan ta miqa masa,hannunshi ya sanya ya karba ya kafa kai ya shanye,miqa mata ya sakeyi ya mata nuni da idanu kan ta dado masa,sake tsiyayawar tayi ta miqa masa,amsa yayi sai yayi jifa da kofin tare da fincikota cikin jikinsa wanda tuni ya soma rawa numfashinsa na fita da sauri,lullubeta yayi cikin qirjinsa yana lalubar bakinta,tsoro ne ya kamata wanda hakan ya bayyana har cikin idanunta,ganin hakanne ya sa ya sauya salo,cikin kunnuwanta ya shiga gaya mata wasu kalamai wanda suka mata nauyi a qwaqwalwa da kunnenta,sannu a hankali suka zare duk wani tsoro da ya mamayeta,suka cire duk wani qarfi da yayi saura a gabbanta,zata iya cewa bata san ya akayi ba,saidai ta sake tsintar kanta cikin duniyar mustaphan,duniya mai cike da al'amura masu nauyi da tsayawa a zuciya ruhi da gangar jiki,wannan karon yaci galaba wajen sanyata sake masa,ta bar mata ragamarsa ya jata inda yaga dama,ba laifu wannan karon ma taji a jikinta,cinyoyinta suka dinga mata ciwo.
Chapter 167 · 0% Book details