← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 221 OF 226

Sashe 221

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Alhj abdus samad dake dafe da kanshi wanda tuni hawaye suka wanke fuskarshi sharkaf ya matso ya kama hannunta bayan ummi ta debe yaran ya soma neman gafararta,ya tabbatarwa da kanshi cewa ba shakka yayi babban kuskure na sakaci da sanya ido a rayuwar da iyalinahi keyi a matsayinsa na uba,wanda yake mai kiwo ne za'a tambayeshi a kan abinda aka bashi kiwo
"na yafe maka daddy...amma ko nan gaba Allah ya azurtaka da wasu yaran ka kula da su,na tabbatara addininmu yana da tsari wajen bawa yaro tarbiyya kabi wannan tsarin,ina da yaqinim shi kadai ne ingantaccen tsari" hawayenshi ya dinga sharewa yana jera mata addu'a suna amsawa,wanda yana gamawa ya miqe ya fice,wata nadama na shigarsa,shi kansa sai a yanzu ya farga,meye amfanin dukiyar da yake yunqurin tarawa wadda ta hanashi tsayawa ya duba gidanshi da rayuwar da suke kai?,qememe su'ad din taqi yarda ta kalli mummyn ko tayi magana da ita,so take kawai ta ganta bata dakin,kaman wasa abun amma sai gashi ta birkice da gaske,tilas mummyn ta fita hannunta saman ka tana kuka.

      Ranar baki daya sumayya ta dinga kula da su'ad din,sosai su'ad din taji dadj,don addu'o'i ta dinga tofa mata wajen da tace yana mata ciwo,duk inda ta mata addu'ar kuwa sai taji ya lafa sai kuma idan ya sake tasowa,qarfe shida na yamma almustapha yace su wauce masauki ya kaisu,qi sumayyan tayi tace a barta a nan,ummi tace bazai yiwu ba ga yara,duka duka kwansu talatin ko arba'in bata cika ba,duk da nauyin ummin da take ji amma hakan bai hanata sake roqarta ba,baba ne ya sanya baki su barta din,tunda dakin baida maraba da gida ba wata matsala bace,fuskar su'ad kawai zaka kalla kasan taji dadin hakan,sai ta saki murmushi,ranan kusan kwanan zaune sukai da su'ad din,tuni 'yan biyu sukayi barci,itakam tana zaune,tayi sallah ta zauna ta huta,duk motsin su'ad din tana ankare da shi,itama su'ad din idanunta na kan sumayya,sai yanayin nata ya dinga burgeta,sam batasan da wannan rayuwar ta yawan yin sallah ba,banda ma almustapha ya tsaya kanta a tsaye sallar ma ta farilla ojoro take mata,sai daga bisani ya sanyata ta gyara da qyar
"Zanso nima inyi sallahr nan haka,akwai lada ko?" Murmushi sumayya ta saki,tana jin tausayinta har cikin zuciyarta,kana kallonta kasan gagarumin ciwo ke cin jikinta,a haka ma akwai kulawa kenan
"Akwai lada mai tarin yawa,sallah tana kusantar da bawa zuwa ga ubangijinsa" kai ta kada
"To ya za'ayi ina son nayi nima,king tun isha'i ban sake ba"miqewa tayi ta iso gareta saboda ganin tana yunqurin gyara hannunta,a tausashe ta gyara mata tana cewa
"ba lallai sai sallah ba kadai zata kawo miki lada,ko jinya ma idan kanayi ai kankarar zunubi ce,idan kina so kina iyayin istigfari salatin annabi da sauransu kina daga kwance"
"Ok,kaman yaya?" Koya mata tayi,ta kama ta dinga yi,a hankali ta dinga jin sanyi da sauqi cikin jikinta da zuciyarta,ta dinga satar kallon sumayya sanda take shayar da ummulkhair tana sha'awar rayuwarta,ashe rayuwa mai dadi nutstsiyar rayuwa itace rayuwar da addinin musulunci ya tanada ya kuma koya mana?,lallai iyayenta sun yiwa rayuwarta babban gibi.

       Sanda almustapha ya kawosu da safe sannan ummi tace ya dauketa ya kaita gida ta huta anjima sai ta dawo,ba musu ta amsa,kowa yaji dadin yadda yaga salama tattare da su'ad din,suna tafe cikin mota shiru,yana dauke da amatullah wadda ke barci yana wasa ya hannunta,yayi kewar yaran sosai,sai yaga kaman an qara musu girma da wani wayo,sosai kamanninsu ke fitowa da shi,zuciyarshi a cunkushe take matuqa,babban abinda ke gabanshi yanzu yadda zai cimma doctor james,duk da alhj abdus samad yace ya qyaleshi kaman yadda su'ad din tace ita ta jawa kanta,duk abinda mutum yayi kanshi,saidai sam zuciyarshi bata nutsu da haka ba,har suka isa dakin daya kama musu a hotel din wamda babban falo ne da dakuna uku a ciki baice komai ba,ya kwantar mata da yaran sannan ya miqe suka hada idanu,duk itama sai take jinta ba dadi
"Ki wanka ga abinci can,ina zuwa" ya fada yana juyawa,binsa tayi da kallo kawai tana kada kai,baki dayansu sun zama abun tausayi cikin qaramin lokaci har ita din.

       Cikin kwana goma sha hudu sumayya ke kwana da su'ad din,zama suke cikin asibitin tamkar ya da qanwa,a nan ta koyawa su'ad din wasu abubuwan da take ganin ya kamata ace ta sani,sukan zauna suyi hira sosai da ita cikim sakewa kaman sun jima da soma mu'amala,jikin su'ad din da sauqi sosai,har takan iya zama sumayyan ta jinginata,ita ke gyara mata jikinta,ta bata abinci,ta daura mata alwala idan lokacin sallah yayi,tana yawan sanya sumayya ta jera mata amatullah da amatur rahman tayi ta magana da su kaman wasu manya
"Ki musu tarbiyya irin taki don Allah" hakan su'ad ke yawaita fada,murmushi sumayya keyi tace
"Tare zamuyi musu har ke,kema mamarsu ce"
"Zanso hakan" abinda takan fadi kenan wanda sumayyan ta kasa gane me hakan yake nufi.

Hatta almustapha yaga sauyi qwarai wajenta,da ya shigo takan gaidashi ko tayi masa sannu da zuwa,abinda bai taba gani ba,hakan ya masa dadi qwarai ua faranta masa,yakan zauna cikinsu ya bada wasu mintuna suyi hira su duka,duk da bai zama waje daya,ba wanda yasan inda yake zuwa daga shi sai Allahnshi,idan dare yayi yazo ya musu sallama shikenan sai gobe da safe.

       Wani dare bayan kowa ya tafi ya barsu,yan biyu na saman gado cikin neat suna bacci su'ad ta kalli sumayya
"Wai baki kewar maan,naga ko sau daya baki taba binshi ba" murmushi ta saki
"Kin manta jinyarki nake,ladan kuma da ake samu wajen yin jinyar mara lafiya ba kadan bane" kai take gayadawa cikin gamsuwa,duk wani furuci da sumayyan zatayi akwai qaruwa a cikinsa
"Wai nikam rannan kaman naji kina min magana kan rayuwarki,bani labari mana?" Dariya ta saki tana kallonta
"Kina son ji ne?" Kai ta kada
"Eh idan babu takura,don na tabbatar zan samu wani darasi a ciki"
"To qara kunne biyu" dariya ta saka
"Na qara" a nutse sumayya ta warwarewa su'ad labarinta,gyada kai kawai take,jikinta yayi matuqar yin sanyi qwarai,wato akwai mutane shigenta ko irinta da yawa a duniya
"Gaskiya rayuwarki baki daya darasi ce,ke din ta daban ce" ta fada tana jinjinawa yadda sumayyan ta fuskanci rayuwa haka,gyaran murya sumayya tayi wanda ya janyo hankalin su'ad daga duniyar tunanin data tafi
"Nikam in roqi wata alfarma mana wajenki"murmushi tahi,ki roqa ko mene idan baifi qarfina ba
" so nake ki yafewa mommy,kada ki manta uwa uwa ce komai lalacewarta,na tabbatar soyayyar da take miki ce ta kaita ga kasa tasawatarwa da tsayawa kai da fata wajen ganin ta hanaki aikata abinda kike so matuqar ba dai dai bane,ta kuma doraki kan dai dai din,ba zaka taba iya biyansu abinda suka yi maka ba har abada"murmushi ta saki ta kamo hannun sumayya
"Mummy,ina son mummy sumayya,saidai yadda ta tarwatsa rayuwata ta kasa gyarata tana qona min rai a duk sanda na tuna hakan,na jima da yafe mata sumayya,na mata haka ne ko don gaba,duk da cewa ko a yau na tafi na barta ba zata sake samun wasu yaran ba,amma wannan ya isheta izinar da zata bawa 'yan baya labari"kai ta kada
"naji,amma gobe ki furta mata cewa kin yafe mata,ki daina gudun ganinta don Allah" murmushi ta saka sumayya na sake shiga zuciyarta
"Naji in sha Allah zanyi,nasan tunda kika dage kan maganar kika gyaramin babu kyau abinda nake,zanso ace zan haihu da na sakawa 'yata sunanki" ta fada wani abu na taba zuciyarta,hawaye ya sauko saman fuskarta,goge mata sumayyan tayi tana cewa
"Ki daina kuka,ki godewa Allah da lafiyar da kike samu"
"Na gode" ta ce da sumayya
"Ba abun gode min,haqqina ne dama na kula dake din koba komai miji daya fa muke" murmushi suka sakarwa juna,ranar sunyi hira sosai da su'ad din har take gaya mata
"Naga amira na sonki,da fari haka nima ta soni,halina yasa ta gujeni,ki tayani bata haquri don na mata ba dai dai ba da yawa wanda yasa ta daina hulda da ni"
"Amira bata da riqo,kuma ke matar yayanta ce,na tabbatar komai ya wuce a wajenta,don kullum sai ta kirani ta tambayeni jikinki,abinda ya hanata tace na baki duk sanda ta kira kina bacci,ni kuma banson tada ke" murmushi ta saki don maganar ta mata dadi,sai da suka raba dare sosai sannan sumayya ta daura alwala ta tada sallah,ta baiwa su'ad carbi ita kuma taci gaba da azkar,sanda ta idar ta waiwaya sai taga carbin ya fadi hannun su'ad din,idanunta alumshe alamun bacci yayi awon gaba da ita.

*Bayan awanni uku*

Zaune take kawai a gabanta ta zuba mata ido tamkar mutum mutumi,sam kukan da yaran ke tsalawa bai shiga kunnuwanta bare tayi yunqurin daukarsu,dubanta kawai take lokavi bayan lokaci tana kiran sunanta,saidai babu wani alami dake nuna motsa bare ta amsa,tun kan ya qaraso dakin yake jiyo kukan yaran,hakan ya sanya ya qara sauri cikin hanzari ya isa qofar dakin ya bude ya tura,a kansu su biyun idanunsa suka sauka,sai ya sauya akalar tafiyar tasa daga wajen 'yan biyun zuwa inda su sumayyan ke zaune,kallo daya ya yiwa su'ad dake kwance gabanshi yayi mummunar faduwa,tamkar wanda aka bigewa gwiwoyinshi ya qarasa bakin gadon ya duba hannyenta zuwa saitin zuciyarta inda take aiki,abinda yaji ya tabbatar masa da cewa babu rai jikin su'ad din,duk da haka zuciyarshi ta kasa gasgata masa,take ya hautsina kayan aikin dake dakin,ya dinga gwaje gwaje,wanda yana tsaka da aikin abokinsa mai asibitin ya shigo dakin da niyyar duba mara lafiyan,kallo daya ya mata ya tabbatar ta mutu,hakan ya sanyashi janye almustaphan cikin harshensa na turanci yace
"Kayi haquri,ta rigamu gidan gaskiya man,Allah ya jiqanta" tuni sumayya ta qarasa rushewa da kukan dake cinta,suka hadu ita amatullah da amatur rahman suka gauraye dakin,baya almustapha yayi ya jingina da bangi yana furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un.

*bayan awa daya*
Chapter 221 · 0% Book details