← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 226

Sashe 33

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        Kwananta biyu kwance cikin dakin babu abinda take iya hasalawa,daga kwanciya sai bacci,ga wani shegen zazzabi da yaqi sauka daga jikinta,duk lokacin da ta yunqura ta yiwa kanta duren shayi tofa qarshensa ya dawo baki daya,abinci kuwa ko kadan bata da sha'awar cin komai,hakan ya sanya ta haqura ta zubawa sarautar Allah ido,banda ruwa babu abinda take kurba,roqon Allah take ya sassauta mata ko ya jefo mata wanda zaya taimaketa,hatta da wayarta bata san inda ta cillata ba,a haka ta shafe kwana hudu cur bata ga kowa ba rana gurzar ciwnta ita daya,duk da cewa taci ranar girkinta har ta fita amma bata ga idon mukhtar ba,to idan da sabo dama ta riga data saba da hakan,data ga irin hakan tasan an karbi kwananta ne an qarawa zainab.

      ****     *****     *****

     Cikon kwana na biyar din cikin ikon Allah ta ji sauqi sauqin jikinta,tana jin qwari qwari a jikinta,har ta iya shiga da yammaci gab da magariba bandaki tayi wanka,tana fitowa ta soma laluben wayarta,can cikin jakar da ta dawo daga gidan anty dije ta ganta,a nan taci karo da dubu ukun da abdur rahman ya bata,sai taji dadin kudin don bata da ko siai a hannunta,to ina ma taga mai batan tunda ita ba sana'a take ba,caji ta sanya a socket din dake daura da madubinta,ta dawo bakin gadonta ta zauna ta soma shafa mai,daga inda take zaunen tana iya hango kanta sosai cikin madubi,ta rame sosai tayi wani fayau da ita,sai uban fari da ta qara kamar wadda ta hadiyi qwayar qara hasken fata.

        Tura qofar dakin nata da akayi shi ya maidota cikin hayyacinta,ta dubi bakin qofar,mukhtar ke shigowa,sanye da yadi tissue na maza orange wanda ya ciza,yayi kyau sosai amma sai taga kamar ya rame,duj da bata sani ba ko idanunta ne,don idan ba makuwa tayi ba rabonta da shi yau kwanaki shida cif. Kanta ta dauke don bata ga dalilin ci gaba da kallonsa ba,ta soma lalubar mayafinta ta lullube jikinta saboda guntun towel ne kawai daure a qirjinta.

       Shikam kallonta yake ci gaba da yi yana son lalubar sonta cikim zuciyarsa amma ya rasa duk da dumbin qaunar da yake jin tana zanga zanga cikin zuciyarsa wadda ya azata a bigiren tausayi,uban haushinta da yake ji yau babu shi kamar yadda bai jin soyayyarta cikin zuciyar tasa. Bata sake bi ta kansa ba har ta gama shafa manta,ta bude drower dinta ta fidda kayan da zata sanyasai a lokacin ta kuma dubansa
"Ka fita don Allah zan sanya kaya" ta fada idanunta tsakar nashi
"Me ya sameki haka sumayya naga kin rame?,ko duk shegen kishin da kika sanyawa ranki ne kamar yadda zainab ta fada?"ya fadi ba tare da yayi duba ga qorafinta na farko ba
"Kan bala'i" ta fada cikin zuciyarta,wani baqinciki na takore mata qirji,wannan rainin hankalin da me yayi kama?,ita yake tambaya ma meke damunta?
"Ba wannan ne a gabana ba,ka ficen a daki" ta fada ranta na suya,sai ya fara takowa inda take,wani shauqinta na fusgarsa,son kasancewa kawai yake da ita,yayi kewarta kwanakin bakwai din nan da bai ziyarceta ba
"Bari na qaraso ki gayamin nawa muka hada muka gina gidan da har dakin ya zama naki". Qarasowarsa ke da wuya qamshin turarensa ya daki hancinta,wani tashin hankali ya ziyarceta,take ta saki kayan hannunta ta buqaci bandaki,nan ta fara kelaya aman da yayi sanadiyyar ficewar ruwan tea din data samu yau ya zauna mata.

       " lafiya sumayya?,meke damunki?,me ya sameki?"haka ya dinga fadi yana riqe da ita,dukkan alamun tashin hankali sun bayyana a fuskarsa wanda hakan yayi matuqar daurewa sumayya kai,mukhtar din tamkar wani bugun jinnu haka ya koma,idan yaso ya dinga gasa mata aya a hannu shi da matarsa,amma wani lokaci sai ya dinga yunqurin juyewa ya koma mata yaya mukhtar dinta sak wanda ta sani a can baya.

       Ganin qamshin turaren ke sake dugunzuma tunaninta ya sanya ta buqaceshi da ya matsa ya barta bata so,haka ya koma baya ya zuba mata ido har ta kammala ta gyara wajen ta dawo bakin gadon ta zauna tana maida numfashi
"Kishirya na kaiki asibiti,ni bansan baki da lafiya ba" duk da yadda take fidda numfashi dai dai amma hakan bai hanata maida masa magana ba
"Bani buqata,me magani zaya yimin?,shin wai damuwa kayi ma da wata sumayya?,na tabbata bakaqi na mutu ba,tunda har zaka iya hanawa a bani abincin gidanka ina a matsayin matar ka" ta qarashe maganar tana sakin kuka don sosai batun ke ci mata qoqon zuciya,ba wai don ta damu da abincin ba,a'ah,ta dauka tafi qarfin komai a gidan mukhtar din,ta dauka ita din mai iya dauka ce ta bayar ma kyauta,sai gashi ita ake hanawa abinci
"Wallahi ni bansan lokacin da akayi hakan ba,waye ya gaya miki ni na hana?"maganarsa ta ratsa kunnenta,sai ta daga ido tana dubansa tana daga kwancen,gani take kawai raina mata wayau zai yi,aljanu gareshi ko farfadiya ce ta kamashi lokacin da ya bawa zainab din umarni?,baqinciki ne ya hanata magana,ganin tayi shiru ba tare da tace komai ba sai kukan ta data ci gaba da yi yasa yace
" duka mubar wannan maganar muje asibitin a dubaki tukun,zanje nayi sallah ma dawo"ya fada yana ficewa.

        Da fari taso taqi yarda,amma jin tsaiwa na niyyar gagararta sanda zata bada faralin sallar magariba yasa ra taushi zuciyarta ta amince,ita kanta zata so taji meke damunta bawai tayita zama da ciwo ba,tunda tunda take bata taba jin irin hakan ba.

        Ba jimawa da idar da sallar sai gashi ya dawo,zuwa lokacin da qyar ta samu ta gama tata sallar aman ya sake tsinke mata,jikinta yayi laushi tubus sai numfashi da take maidawa,yaso taimaka mata wajen fita amma tace bata buqata,haka ta dinga bin bango har suka isa cikin motar.

         Wani private hospital dake cikin unguwar tasu ya kaita,bayan taga likita ya bata takardar gwaji taje lab,minti goma ta karbi sakamakon ta koma dakin ganin likitan ta kai masa
"Alhamdulillah,sai ka godewa Allah,madam na dauke da juna biyu"baki dayansu wuta ce ta dauke musu kada ma sumayya taji labari,sai ta fara girgiza kai hawaye na sauko mata,magana take son yi amma bakinta ya gaza furta komai
" likita don Allah ka daina mana irin wannan wasan sai ka dauki haqqinmu"ta fusgi kalaman da qyar,sau ya dago kai ya dubeta
"Bama yiwa patient wasa cikin abinda ya shafi lalurar da ta kawo su,ki baki yarda bane hajiya,ai muna da na'urar daukan hoto bismillah ga gado can hau in nuna miki" kasa tashi tayi baki daya,ga rashin qwarin jiki ga luguden da maganar tayi mata,mukhtar dake son tabbatar da gaskiyar labarin shi ya taimaka mata har suka isa bakin gadon.

       Cikin qwarewa ya shiga nuna masu dan qaramin tayin dake cikinta wanda duka baifi wata biyu da rabi ba,basu iya ganewa amma sun lura da wani dan digo wanda shike alamta yaronsu kenan,wata doguwar ajiyar zuciya ya saki tare da lumshe ido yana jinsa cikin wata sabuwar duniyar,yayin da sumayyan ta fashe da kuka,jikinta baki daya rawa yake,ashe tana daga cikin mata masu haihuwa?,ashe akwai rabon zata ga yaron kanta?,ashe ita ma din watan watarana zata zama uwa?,zata yi raino ta kuma bada tarbiyya?,lallai ubangiji babu wanda ya kaishi iyawa cikin mulki da kyauta,babu ko shakka ubangiji baya bacci,baya mantawa da duk wanda ya ambaceshi ya kuma nemi agajinsa.

        Barinsu likitan yayi suka gama murnarsu,don ya fahimci dukkansu ba'a cikin hayyacinsu suke ba sannan ya sanarwa mukhtar din jikin sumayyan ba qwari,zasu riqeta su sanya mata drip(ruwa)har zuwa safiya ko zata ji karsashi,sannan ya rubuta magungunan da zatayi amfani da su wadanda zasu taimaka mata ita da abinda ke cikinta,sannan ya jadda masa alfanun cina abinci mai kyau da gina jiki da qara kuzari a gareta,karba yayi saida ya tabbatar an gama komai an sanya mata drip din sannan ya fita siyo magungunan.

       Ya jima zaune cikin mota ya kasa tayar da ita,ina zaikai wannan kayan farincikin?,da wa ya kamata ya raba wannan farincikin kada ya masa yawa ya masa illa?,da sauri ya zaro wayarsa daga aljihu ya soma daddanna wasu lambobi kyakkyawan murmushi kwance a kan fuskarsa,jinsa yake cikin wata duniya mai dauke dimbin farincikin da ya jima bai jishi ba,jinsa yau yake wani na daban.

     ****      *****     ****

        Ji take idan ga zauna gu d'aya tamkar wani mummunan abu zai faru ne tare da ita,tana jin qwaqwalwarta ko zuciyarta daya daga ciki zai iya tarwatsewa,tunda take bata taba cin karo da mummunan labari da ya firgita duniyarta ba irin wannan labarin,idanunta basu taba mummunan gani ba irin na wadan nan kwanakin,sumayya kishiyarta da ciki?,ita kuwa tana me?,wanne shirme take?,wanne baccin asarar tayi har mukhtar ya yiwa sumayya ciki duk da uban takatsantsan din da take?,duk da raba tsakaninsu da tayi ya daina sha'awarta?,tabbas idan har ta bari sumayyan ta rigata haihuwa cikin gidan ta dibga babbar asara,hakazalika bata ci sunanta,gidan da take da buri a cikinsa,gidan da take so shi da mamallakin gidan duka su zama qarqashin ikonta shine wata zata riga ta fara ajjiye iri?,tun yanzu ta fara ganin manya manyan sauye sauye ina ga ta haihu?,tun yanzun mukhtar ya ruguza dukkan wani plan data yi cikin gidan,wani kukawa yake bawa sumayyan wanda hakan ke nuni da qiris ya rage sun koma su dinke kamar daa koma sufi daa dinkewa,abinda idan har ya faru ba zata taba gafartawa kanta ba,lallai ko zatayi yawo tsirara sai ta tabbatar ta kawar da duk wata barazana dake shirin tunkaro ta.

      Kamar mahaukaciya haka ta suri wayarta ta soma laluben lambar wayar aminiyarta qawarta,wadda bata aiwatar da komai sai da shawarat,zama tayi dabas gefan gadonta jin wayar ta shiga,cikin qananun sakanni mamallakiyar lambar ta daga,ko ta kan gaisuwar da take jefo mata bata bi ba ta soma zayyano mata abinda ke gudana cikin gidan.
Chapter 33 · 0% Book details