← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 199 OF 226

Sashe 199

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

      Dukkaninsu suna da kyau  abinsu,faran faran da mutane,nan suka hadu suna hira abinsu,irin hiran farkon haduwa ba sakin jiki can da yawa,eesha na gefe tana hura hanci,ta dora qafa daya kan daya,ta san asm'u,duk da wuce asm'un da aji daya,hakan ya sanya ko ayanzun ka take jin ta fita,gidan 'yan uwansu take,bugu da qari ita dangin miji ce,su dinma da yake kowacce ta iya takunta daga gaisuwa basu damu da me take ba,a haka ummi tazo ta taddasu,hakan ya mata dadi qwarai,ta kuma yaba da tanadin da sumayya tasa aka musu,hatta da anty maamaa sai data ji dadi,duk da alkunya data yi tace baqin ummi ne dama,sunje dai sun gaisa da ita sannan suka dawo suka ci gaba da sabgoginsu.

         Basu tafi ba sai yamma liqis bayan sunyi musayar lambobin waya,cikin motar mus'ab duka zasu koma,sun tafi suna yabawa da sumayya,cikin qanqanin lokaci suka saba da hirarta suka a baki suka isa gida.

        Tunda suka tafin eesha ta dawo falon qasa ta zauna bayan data tabbatar ta gama shirya duk wani abu data tanada,rana saka ran cewa wani dalili ya sauko da ita daga dakinta zuwa kitchen din,hakan ya sanya ta kasa ta tsare ta zauna a falon,tana danne danne waya tare da kallon wani film a MBC action amma rabin hankalinta ja matattakala zuwa qofar kitchen din,duk wani ma'aiki da zai buqaci shiga kitchen din ta sallameshi tun yamma,ummi dama ita ke da girki taga fitarta zuwa sassan baba prof.

         Sajida ce ta sauko da sauri sauri,sannan da hazarinta irin mai tattare da quruciya ta nufi kitchen din,cikin hanzari ta dakawa sajidan wata iriyar tsawa data sanyata tsayawa cak
"Uban me zaki shiga ciki kiyi kanki na rawa?" Kaman zata saki kuka tace
"Anty amira ce tace na dauko ovaltine zata hadamin wani abu" sosai abin yayi mata dadi,da alama haqanta zai cimma ruwa,sai ta sake kaurara murya tana zare mata ido
"To koma kije kice mata nace ba zaki shiga ba,idan ta matsu ta sauko da kanta ta diba" tsayawa sajida tayi tana dubanta,don a ganinta ita kanta eeshan ta yiwa sumayya rashin kunya,bugu da qari ma gidan ba wanda akewa get na amfani da wani abu tunda basu gaji rowa ba,kowa na gaban kanshi je ciki kuwa harda ita eeshan
"Ba zaki wuce ba kika tsareni da ido ko sai na qaraso nan na babballaki na zubar" ganin hargagin da take mata ya sanya ta dole komawa saman da sauri.

        Sumayyan na zaune riqe da qaramin qur'ani tana karanta falaq da nasi da ikhlas tana qarashe addu'anta sajida ta dawo,maganan da eeshan ta gaya mata ta daure mata kai,bata ce komai ba ta gama addu'ar ta shafa,sannan ta miqe da hijabin jikinta tace da sajida
"Zauna,bari na debo miki"
"To" sajidan ta fada sumayya ta fice,dadi ne ya dinga ratsa eesha sanda taga sumayya ta shige kitchen din,tuni ta ajjiye wayar gefe ta miqe tsaye tana shirin ko ta kwana murmushi na fita a fuskarta.

        Sam sumayya bata lura ba har sai data dauko gwangwanin ovaltine din ta dauki hanyar fitowa,ji tayi ta tafi baki daya sululu zata kifa ta baki
"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ta furta,cikin wani irn hanzari ta saki gwangwanin ta dafe freezer dake daf da ita,duk da haka sai da qafarta ta amsa ta rintse ido tana sake kiran sunan Allah,da gudu taga shigowar eesha wanda hakan har yaso ya sake firgitata ta soma dudduba jikin sumayya tana cewa
"Innalillahi wa inna iliahi raji'un,me ya sameki?,kinji wani abu ne?,me ya samu jikinki?" Shigowar ummi cikin rudani wadda shigowarta falon kenan taga eesha ta runtumo kitchen din da gudu ta biyo bayanta,sumayya ta soma yu qurin tashi ummi ta nufeta,eesha ta dakatar da ita tana qarasawa wajen sunayya tana taka wajen cikin taka tsantsan ta kama sumayya tana dudduba qasan data fadj
"Ai babu ma abinda ya sameki" eeshan ta fada haushi na cikata,so tayi tazo ta ganta male male cikin jini,ta fadi kan cikinta tayi barin dan tayin dake cikinta,wani irin kallo sumayya ke bin eesha da shi wanda ita eeshan bata kula ba,baqincikin rashin cimma nasarar da bata yiba kadai ya cika mata qoqon zuciya,ta dora dukkan alamomin tambaya kan eeshan,zainab ce ta fara fado mata a cikin abdallah,take jikinta yayi sanyi,gabanta ya yanke ya fadi taci gaba da nazartar eeshan a fakaice,duk wasu abubuwa da take son gani ta samesu,tuni ta janye baya ta bar sumayya hannun ummi ummi na duban wajen
"Me ya kawo miyan kuka nan wajen har ya janyo miki faduwa,subhanallah" ummi ta fada tana janye sumayya daga wajen
"Ita tayi ta mai shegen warin daddawa" ta fada tana yatsine fuska,kai sumayya ta gyada
"Ni nayi,sai gata kuma ta taho har nan" ta ambata tana duban eesha,dauke kanta tayi ta juya ta fice daga kitchen din tana kumbura
"Bakijin dai komai a jinki ko?"
"Eh ummi,ba komai" ta bata amsa tana miqewa
"Bi a hankali,idan kina jin wani anu ki fada,don Allah nidai daga yau na yafe shigowa kitchen din nan" ummin ta fada cikin damuwa
"To ummi" ta fada tana nufar qofar kitchen din,zuciyarta cike fal da mamaki,me ta yiwa eesha,don tana son almustapha sai ta nemi rayuwar dan cikinta,d'an kuma wanda take iqirarin tana so,lallai dole ta sanya ido da takatsantsan da eeshan,don ba zata taba lamunta yaran da tun kafin ta haifesu su dinga shan wuya ba haka kawai ba tare da laifinsu ba,biyo bayanta ummin tayi,sai data sake tabbatarwa komai lafiya sannan hankalinta ya kwanta,saukowa qasa tayi,ta tara ma'aikatan dake kula da kitchen baki daya ta tsawatar musu,sannan taja kunnensu da kada ta kuma gani sun bar sumayyan ta shiga kitchen sannan ta sallamesu kowa ya koma muhallinsa bayan sun gyara gurin.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽

✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

9⃣9⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana cewa*

*duk wanda ya aikata daidai da qwayar zarra na alkhairi(komai qanqantarsa) zai gani(cikin littafin ayyukansa,zai ganshi a rubuce kuma za'a masa hisabi da hukunci a kansa),hakanan duk wanda ya aikata dai dai da qwayar zarra na sharri zai ganshi.
__________________________________________

          Tun daga lokacin sumayyan ta zubawa eesha ido cikin nutsuwa,tana kula da takatsantsan da duj wanu taku nata,a bangaren eesha kuwa ko daya bata sauya qudurinta ba,ko da yaushe tunaninta daya na yadda zata illatar da sumayyan ne.

   ******    ******    *******

      Qarfe goma da rabi ranan ta sauko bayan farkawarta daga bacci wanda kusan almustapha ne ya tasheta,sai data gama biye masa sannan ta shiga tayi wanka ta shirya ta sauko don ta karya,bata da damuwa tasan cewa komai na shirye,tun daga randa wancan abun ya faru bash sake barinta shiga kitchen ba.

        Tare suka sauko da sajida,ummi na sashen anty maamaa,sajida ta wuce dining don ta karya,ita kuma kiran halima da ya shigo wayarta ya sanya ta wuce saman kujerun falon ta zauna tana amsawa,qarar sajida data jiyo shi ya sanyata sakin wayar ta miqe,bata jin nauyin jikinta haka ta nufi sajida da tayi zaman 'yan bori saman step na dining area,wajen ta isa tana dagata gami da tambayarta
"Faduwa nayi anty" ta bata amsa tana shirin sakin kuka saboda qafarta ta bugu sosai,idanunta sumayya ta kai wajen sai taga ruwa ne ya zube wajen
"Ya akayi kika zubda ruwa haka sajida?"
"Bani bace nima haka naga wajen,kuma ban kula ba har sai da na fadi" wani tunani ne ya darsu ran sumayya,ta sanya hannun ta cikin ruwa sai taji yana santsi da qanshin klien,to waye ya zubda ruwa haka?,tasan cewa babu yadda za'ayi ma'aikatan su zubda ruwan su tafi ba tare da sun gyara ba,ummi bata nan sajida ba ita ta zubar ba
"Eesha" zuciyar sumayya ta raya mata,kai ta girgiza,batason ta zargeta bayan bata gani da idanunta ba,riqe sajidan tayi don dawo da ita saman kujera,tana juyowa suka hada idanu da eeeshan,sai ta juya ta shige dakinta,mamaki ya kama sumayyan,wai me eeshan ke nufi,take ranta ya baci,ta zaunar da sajida saman kujerar ta kama qafarta tana mammatsawa,gefe guda ke mata ciwo,sai ta isa bakin dispenser ta tari ruwan zafi ta dawo kusa da sajidan ta gasa mata qafar sosai,cikin ikon Allah wajen ya saki,ta shafa mata man zafi a wajen sannan taje da kanta ta goge wajen sannan ta hada mata abin break din taci ta kwanta.
Chapter 199 · 0% Book details