← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 226

Sashe 39

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        Ta bangaren yaya yahansu kuwa sanda taji labarin sakin,sosai na zainab ya faranta mata,sai a lokacin ta dinga tuna abinda zainab din ra dinga yi musu,ta tabbatar har su ta hada ta asirce shi ya sanya suka gaza tabuka komai,jikinta kuma yayi sanyi da sakin sumayya,ita kanta ta dunga tunanin anya abinda mukhtar ya gaya mata ya faru ba tuggun zainab din bane?,tilas ta bar batun tunda abinda ake gudu ya riga da ya faru,amma lokacin da ya sake dawo mata da batun cikin na nan wani farinciki taji ya mamayeta,tana da muradin zuwa taga sumayyan amman kunya ta hanata,tana ganin kowa yasan gallazawar sa ta yiwa sumayya,da wanne ido 'yan uwanta zasu dubeta?,sai a yanzun take sake tausayin dan uwan nata ganin yadda ya sauya kamar ba muntarinsu ba.

    ****      ******    *****

      Hakanan yau ya tashi da muradin ganin cikinsa,amma ya kasa tantance cikin yake son gani ko sumayyar duk da zuciyarsa tafi afuwa ga cikin yake son gani,don rabonsa da ganinta tun randa malam ya gaya masa zancan cikin na nan a falonsa.

         Saura kusan kwanaki bakwai lokacin da yake mata siyayyar ya cika,amma duk da haka da yammacin ranar ya shiga store din da ya saba siyayyar,shugaban gurin na ganinsa ya san me dame yake buqata,shi ya sanya aka hada masa komai sannan akayi total ya biya ya karba ya fice.

         Qarfe biyar a qofar gidan tayi masa,yana sanye da wani yadi mai qarancin kauri ruwan bula mai haske wanda aka yiwa aiki da ruwan bula mai turuwa,duk da sauyawar yanayinsa da rama amma hakan bai hanashi kyau ba,sam rayuwar gidan bata masa dadi saboda a yanzun shikewa kansa komai,hakan ya sanya ya nemi wani saurayi wanda ke zuwa ya masa share share.

         Halima ce ta soma ganinsa,ta yiwa mamansu magana aka bashi izini ya shiga,duk da yaran yanzun basa sakewa da shi kamar da,hakan baya masa dadi sam don baiga abinda su ya shiga tsakaninsu ba.

        Cikin girmamawa ya gaida maman ta tambayeshi su yahanasun ya amsa mata duk lafiya qalau shi kuma ya tambayi masu jiki(wato sumayya),ba wata hira dama tun da can ke shiga tsakaninsu ba daya wuce gaisuwar,hakan ne ya sanyashi ya miqe bayan an gama shigo da kayan ya musu sallama ya fice.

        Sai ya kasa tafiya ya tsaya a soron,yana da muradin ganin cikinsa gashi ko gilmawarta bai gani ba bare yaji muryarta,hakan babu wanda ya masa zancanta,jingina yayi da bangon soron hannunsa harde a qirjinsa yana tunanin ta yadda zai ganta din,cikin ikon Allah sai ga zainab ta fito tana sanya hijabinta zata shagon kusa da gidansu ta karbo klien zata wanke kwanukan da suka kammala abincin dare da su
"Yauwa zainab,don Allah taimaka min ki fito min da yayarki mu gaisa" ya fada yana gyara tsaiwarsa,mamaki ya cikata,kamar tace wani abun kuma sai ta fasa ta juya ta koma ciki.

         A dakin sumayyan ta tarad da maman tsaye kanta tana mata fadan rashin fitowa su gaisa da mukhtar,tundanko banza dai ai uban d'anta ne,abinda ya faru kuma babu wanda ya ruga ya gogeshi cikin KUNDIN QADARARTA,hawaye ta soma gogewa abinda maman bata so kenan
"Amma mama meye amfanin fitar tawa mu gaisa,tunda dai lafiya qalau nake"
"Na san da wannan,ko banza ai ko baya ta taki zai so ya tabbatar da lafiyar abinda ke cikinki ko" maman ta fadi
"Shikenan kiyi haquri mama zan dinga gasheshi" tausayinta ya kamata,tana shirin yin magana zainab din ta shigo ta fada mata abinda mukhtar din ya buqata
"Kin gani ai,sai kije ku gaisa" ta fada ta juya tana ficewa,hajibinta ta janyi dake rataye jikin sif ta zura sannan tayo waje.

       Tunda ta fito ya zuba mata ido yake kallonta,sosai wannan karon cikin ya fito fiye da waccan karon,hatta tafiyarta ta soma sauyawa,kanta ma qasa din bata son hada ido da shi har ta qaraso,daga can gefe guda ta tsaya sannan tace
"Ina yini" ba tare data daga kai ta dubeshi ba
"Lafiya lau,ya jikin naki"
"Alhamdulillah" ta fada cikin sanyi,sai shiru ya biyo baya kowa da abinda ke saqawa cikin zuciyarsa,tsaiwar ta fara mata tsauri har ya lura da haka,sai ya waiwaya ya gangaro mata wani dutse da suke tokare qofa da shi ya furta
"Ga guri zauna" bata musa ba ta zauna din don tana da buqatar hakan
"Me yasa sumayya?,why?,kinga ayanzun kin zama silar da zamu raini yaronmu a mabanbanta gurare abinda ko a mafarki ban taba hasashen faruwarsa ba"ya furta wani daci na zagaya harshensa,idanuwansa na sauya launi,da sauri ta daga kai ta watsa masa fararen idanuwanta,take wani bacin rai ya soma bijiro mata,wato har yanzun zarginta yake kenan?,dama abinda yake son gaya mata kenan da har ya fiddo ta tana zaman zamanta tana lallaba rayuwarta.

       Qin tankawa tayi sai ma yunqurin miqewa da ta soma yi saboda bata ga alfanun ci gaba da tsaiwa a gabansa ba,ganin tana niyyar wucewa ba tare da ya gaya mata abinda zaya fadi ba yace
" idan nayi lissafi dai dai cikin ya kusa shiga wata na tara,zuwa yanzu ya kamata ace anyi siyayya,ki rubuta duk abinda kike da buqata jibi zan dawo na karba in sha Allah"
"Ka kawo duk abinda kake ganin zaka iya" ta fada tana mai shigewa gidan ba tare da ko ta waiwayoshi ba zuciyarta na suya,idanunta na zafi.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ KUNDIN QADDARATA✍
📖📖📖📖📖

NA
SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

WATTPAD:HUGUMA

HASKE WRITERS ASSO
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

3⃣3⃣

Zuwa ga marubuciyya safiyya abdullahi musa huguma mujin shuru kwana muna ta xuba ido mu masoyanki Allah yasa dai lafiya dan Allah ki taimaka ki cigaba da post muna jin dadi littafin sosai.
Na gode daga masoyarki.
Aysha M Adam ( maman muneepha)

Dan Allah duk wanda ya gani ya tura gaba har ya isah garaita plx.
👏🏻👏🏻👏🏻👏🏻
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

3⃣4⃣
______________________________

*Bismillahir rahmnair rahim*

*tsarki ya tabbata ga Allah wanda mulki ke hannunsa kuma mai iko ne akan komai,wanda shi ya halicci rayuwa da mutuwa,ya halicci cuta da lafiya*

*haqiqa kalmomin bakina sunyi qaranci wajen nuna tsantsar godiya ta ga ubangiji bisa alfarmar samun lafiya da yayi min,bani da abun cewa face roqonsa ya bani ikon morarta ta hanyar bauta masa da yi masa biyayya*

*godiya ga iyaye na,babu shakka soyayya irin ta mahaifa babu kamarta duk fadin duniya,naga zallar ta a idanuwa da ayyukansu,ban da abin biyansu,saidai bazan gaza ba wajen yi musu addu'ar ubangiji ya musu kyautar Aljanna madaukakiya,ya musu kyakkyawan qarshe,yasa su cika da kalmar shahada,ya jiqan magabatansu,ya cika musu burikansu duniya da lahira,ya cika rayuwarsu da farinciki lafiya wadata da kwanciyar hankali*

*fans ina matuqar godiya a gareku,'yan watpadd bani data cewa sai fatan Allah ya muku kyakkyawan qarshe,'yan watsapp bazan manta karamcinku a gareni ba,ubangiji ya hadamu cikin jannatul firdausi,addu'o'in alkhairinku gareni fans ina roqa muku ninkinsa wajen ubangiji*

*_wannan shafi sadaukarwa ne a gareku_*

*mariya SB*

*aysha abubakar(maman khalipha)*

*mariya yola(mamam shuraim)*

*mommy maimuna musa*

*Allah ya saka da alheri ya qara zumunci*

______________________________
Hakanan yau ya tashi da muradin ganin cikinsa,amma ya kasa tantance cikin yake son gani ko sumayyar duk da zuciyarsa tafi afuwa ga cikin yake son gani,don rabonsa da ganinta tun randa malam ya gaya masa zancan cikin na nan a falonsa.

         Saura kusan kwanaki bakwai lokacin da yake mata siyayyar ya cika,amma duk da haka da yammacin ranar ya shiga store din da ya saba siyayyar,shugaban gurin na ganinsa ya san me dame yake buqata,shi ya sanya aka hada masa komai sannan akayi total ya biya ya karba ya fice.

         Qarfe biyar a qofar gidan tayi masa,yana sanye da wani yadi mai qarancin kauri ruwan bula mai haske wanda aka yiwa aiki da ruwan bula mai turuwa,duk da sauyawar yanayinsa da rama amma hakan bai hanashi kyau ba,sam rayuwar gidan bata masa dadi saboda a yanzun shikewa kansa komai,hakan ya sanya ya nemi wani saurayi wanda ke zuwa ya masa share share.

         Halima ce ta soma ganinsa,ta yiwa mamansu magana aka bashi izini ya shiga,duk da yaran yanzun basa sakewa da shi kamar da,hakan baya masa dadi sam don baiga abinda su ya shiga tsakaninsu ba.

        Cikin girmamawa ya gaida maman ta tambayeshi su yahanasun ya amsa mata duk lafiya qalau shi kuma ya tambayi masu jiki(wato sumayya),ba wata hira dama tun da can ke shiga tsakaninsu ba daya wuce gaisuwar,hakan ne ya sanyashi ya miqe bayan an gama shigo da kayan ya musu sallama ya fice.

        Sai ya kasa tafiya ya tsaya a soron,yana da muradin ganin cikinsa gashi ko gilmawarta bai gani ba bare yaji muryarta,hakan babu wanda ya masa zancanta,jingina yayi da bangon soron hannunsa harde a qirjinsa yana tunanin ta yadda zai ganta din,cikin ikon Allah sai ga zainab ta fito tana sanya hijabinta zata shagon kusa da gidansu ta karbo klien zata wanke kwanukan da suka kammala abincin dare da su
"Yauwa zainab,don Allah taimaka min ki fito min da yayarki mu gaisa" ya fada yana gyara tsaiwarsa,mamaki ya cikata,kamar tace wani abun kuma sai ta fasa ta juya ta koma ciki.

         A dakin sumayyan ta tarad da maman tsaye kanta tana mata fadan rashin fitowa su gaisa da mukhtar,tundanko banza dai ai uban d'anta ne,abinda ya faru kuma babu wanda ya ruga ya gogeshi cikin KUNDIN QADARARTA,hawaye ta soma gogewa abinda maman bata so kenan
"Amma mama meye amfanin fitar tawa mu gaisa,tunda dai lafiya qalau nake"
"Na san da wannan,ko banza ai ko baya ta taki zai so ya tabbatar da lafiyar abinda ke cikinki ko" maman ta fadi
"Shikenan kiyi haquri mama zan dinga gasheshi" tausayinta ya kamata,tana shirin yin magana zainab din ta shigo ta fada mata abinda mukhtar din ya buqata
"Kin gani ai,sai kije ku gaisa" ta fada ta juya tana ficewa,hajibinta ta janyi dake rataye jikin sif ta zura sannan tayo waje.
Chapter 39 · 0% Book details