← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 178 OF 226

Sashe 178

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ta tura qofan dakin baccinsa dake sama cikin nutsuwa,idanunshi cikin nata bayan muryar su'ad da ta soma dukan dodon kunnenta,shike fuskantar qofa su'ad ta juya baya,magana take cikin bacin rai harda qwallarta a idanu,yayin da ya zuba hannunshi cikin aljihun wandon shaddarsa yana dubanta,tuni ya cire babbar rigar sai 'yar sama da dogon wando,baya ta koma a hankali da niyyar komawa tunda ta fuskanci wata magana suke wadda wala'alla abune da su'ad din bazata so taji ba,a hankali ya motsa baki har yau bai daina kallonta ba,ta masa kyau matuqa,komai nata mai nutsuwa ne da shiga cikin zuciya cikin wani irin sanyi
"Zo nan" ya kirata yana ci gaba da kafeta da idanu,maganan da yayi ya sanya su'ad yin shiru daga rattabo maganar da take yi,ta waiwaya a hankali idanunta kan sumayyan,bawinciki ya sake ninka mata fiye da na dazu,har wani canjin kwalliya take,ita har a nuna mata ado,gabanshi ta qaraso,kafin tace wani abu ya bata umarni
"Rage kayan jikina ki hadakin ruwa,ina sin yin wanka" idanu ta dan fiddo,ta yaya hakan zai kasance ga su'ad wajen na tsaye,yadda ya kafeta da idanu tasan zata jama kanta wani abunne hakan ya sanya ta nufeshi ta soma balle masa botiran gaban rigarshi cikin taushi da sanyi,idanunsa ya dauke daga kan sumayyan ya mayar kan su'ad
"Uhmmmm,ci gaba ina jinki,na taho da jama'a na jira na" kai ta kada tana yunqurin danne hawayenta don kada sumayya ta ganta bare ta rainata,ta sani sarai tunda har ranshi ya baci sai ya horata,koda zata ciyo kansa to sai ya hukuntata,wanda bai iya hukunci ta dadin rai ba,idan ya maka sai kaji babu dadi
"Ka barshi kawai,idan ka dawo mayi maganar"
"Ke kika tada maganan yanzu kk?,bayan na gaya miki cewa ki barta sai na nutsu,ki qarasa kawai idan ba gaka ba daga wannan muhallin banson na sake jin komai daga gareki,idan na dawo zan ganku ne kawai baki daya ina fata kin fahimta" ita kanta tasan indai har zaman lafiya take so da mustaphan to ta bar maganan,ta yarda ya gabatar da su wa juna,idan yaso ta ruwan sanyi zata dafa yarinyar,zata ga barikanvi,zata ganar da ita rainin america ba irin na nijeria bane,zata nuna mata akwai banbanci,za kuma ta nuna mata almustapha nata ne iya daya da ita kadai ya dace.

Busy busy,need ur prayers,we shall meet tomorrow in sha Allah.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

9⃣0⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*YA UBANGIJI KADA KA JARRABEMU DA AZZALUMAN SHUGABANNI SABIDA ZUNUBANMU KAJI QANMU,YA ALLAH DUK MAI NEMAMMU KO NUFINMU DA SHARRI ALLAH KA MAIDA MASA DUK ABINDA YA YI TANADI A KAN KANSA YA KOMA MASA*
____________________________________

       Kai kawai ta kada ta juya ta fice daga dakin,bata so tayi wani abu da zai sanya almustapha yayi misbehaving dinta gaban sumayyar,don ta riga data sani ta bata masa rai qwarai,ta kaishi bango,hakanan fushinsa bai da kyau ko kadan,idanunsa ya dauke daga kanta bayan ta fice ya dubi sumayyan sanda ta gama,daga boxer sai singlet,da idanu ya nuna mata singlet din,a kunyace ta cire mishi,ya sake nuna mata boxer din,sai ta kauda kai tana turo baki,itakam ba zata iya ba,shi ko nauyin su'ad baiji ba zai wani ce ra cire masa kaya,zata juya kenan ya janyota jikinta,ya matseta cikin jikinshi yana goga fatar jikinsa jikin tata,tsigar jikinta ta zuba saboda yawan gargasar dake jikinsa
"Ina zaki baki gama ba?"
"Na gama mana,na bar baquwa ne a qasa"
"Idan ina nan kisa a ranki babu wani a gidan nan sai ni da ke,abidan ce baquwa?,ki tambayeta haka takewa hamza?" Shuru tayi murmushu na qwace mata,sakinta yayi ya nufi bandaki yana cewa
"Kayan nan akwai zafi,but akwai dadi da kyau kayan al'ada" kanta ta maida inda ya yasar da babbar rigar,kana kallonta kasan bata jima jikinsa ba,hakan yake ko a can din ma cireta yayi ya riqe a hannunshi,gefan gadon ta koma ta zauna,wayarshi ta soma ruri,musaddiq ke kira,ganin haka ya sanya ta daga ta shaida musu wanka yake
"Au shine ya zube mu a wannan da yake shine agwagwa sarkin wanka?,tell him muna jiranshi" murmushi kawai tayi ta datse kiran,abotarsu na burgeta,kawai sun dauki kansu daya ne baku daya su shidan,qaraso yayi ya miqa mata hannu sai ta dora wayan saman tafin hannunsa,ya fara shafawa yana tambayarta waye ta sanar masa,sai ya dan tsuke fuska
"Why you permit him yaji muryanki?"
"Afuwan" ta fada a sanyaye,sai ya dan saki fuska yana ajjiye wayar tare da takowa inda take zaune,gab da ita ya zauna har suna gugan juna
"Ina da kishi,matsanancin kishim da bansan ina da shi ba sai da muka kasance tare,please ki kiyaye"
"In sha Allah", mai ta dauko ta soma shafa masa bayan ta gama tsane masa jiki,duk inda ta zagaya ko ta gifta qamshinta na bibiye da ita tare da cika masa hanci,cikin wani cotton yadi fari qal mai adon ash ya shirya,ba qaramin kyau kayan suka masa ba,sai ta dinga satar kallonshi ba tare data sani ba,shigar na qawatar da ita,jikin bango ya rutsata tsaye,tana shirin yin qasa da kanta ya riqe fuskan
"gulma.....kema kin iya,me yasa ba zaki bude baki ki magana ba?" Murmushi ta saki,sai ta saka idanunta sosai cikin nashi ta juyasu tamkar mai yin faari,hakan ya rudashi,ya sanya tattausan lebbansa ya sumbaci idanun nata,qarar wayarshi ta katse masa abinda yake shirin yi,ummee ke kira,ta sanar masa baba na son ganin sumayya a falonshi,ya sauke wayar yana dubanta
"Baba ne ke kiranki,but bana so ki fita,a cike wajen yake,muje na rakaki"
"To" ta amsa ta juya da niyyar ficewa,har ta sanya qafarta waje yace
"Hey" juyowa tayi tana dubanshi,da hannu yake kwatanta mata
"Ina hijabinkin nan babba wanda ya sauko qasa?"kai ta gyada
" yauwa,shi zaki sanya"
"To" ta amsa tana ficewa,wayarshi ya ciro ya kira su lamin ya shaida musu yana zuwa zaije wajen baba ne ya dawo,a dakin ta tadda abida har ta soma gyangyadi abinta,tace tana zuwa
"Babu komai,gama uzurinki,ni wannan kwanciyar ta fimin komai dadi" murmushi tayi ta fice tana tausayin abidan,tayi nauyi qwarai,duka duka watanni kadan suka rage mata ta haihu,ba lallai ma tabi hamza a gida taje tunanin zama har sai ta haihu din.

       Tana gaba yana biye da ita kamar wani body guard,hakan ma yayi masa,tunda ko banza yana morewa kallonta,kasa control din kanta tayi sa'ar da taga malam da abdallah,da gudu yaron ya nufota ta duqa ta tarbeshi ya fada jikinta ta rungumeshi
"Ammi......ashe nan kika dawo kin bar gidan umman khalipha.....laaaaaa,daddy?" Ya katse maganar tasa ya dora da wannan sanda suka hada idanu da almustapha wanda ke tsaye hannayenshi harde a qirji,sosai abun ya masa,sai ya tuna sanda ya ganta da hijab cikin ranakun bikin amira,ta bude hannunta kamar haka yaran suka shige,kwadayin samun yaranshi ya taso masa ya kuma sake nunkuwa fiye da da,don a wannan lokacin haka kawai yaji yafison yara fiye da baya,yana jin dama ace abdallan nasa ne,yaron ya shiga zuciyarshi,amma tana nufin itace mamarshi?,Allah ne ya kiyaye bai kai mata bugu ba randa ta bugeshi kenan,sam bai sani ba,barin jikin sumayya yayi ya nufo almustapha,cak ya dagashi sama murmushi na subucewa daga fuskanshi,sama ya dinga juyashi abdallahn na dariya,yana son ayi masa hakan dalilin da yasa ya kasa manta almustapha kenan,dauke kanta tayi wani farinciki na ratsata ta isa gabansu baba ta duqa,cikin qauna ladabi da girmamawa take gaidasu,cikin kukawa baki daya suke amsawa kafin baba ya dora
"Haduwa tayi wuya mamana,tunda kuka dawo ban ganku ba" kai ta sadda qasa tan murmushi
"Ummee tace kaje jigawa ai sanda muka iso"
"Gaskiya ne kam,ina fatan komai lafiya?,ko da yake alamu sun nuna hakan,saidai muci gaba da binku da addu'a" murmushi taci gaba da yi ba tare data tanka ba,dai dai sanda almustapha ya qaraso ya durqusa gabansun kamar yadda sumayya tayi ya soma gaidasu suna amsawa,ta dan saci kallonshi sanda yake tambayar mama da yaya abubakar,baba ne yace a basu waje da sauri malam yace
"Haba muhtari,waye baqo cikinku,me zan gaya mata me zata gayan,ka daina min haka" dariya baba ya saki ya koma ya zauna,hira suka taba sama sama duk da sumayya ta kasa sakewa,daga bisani ta dauke abdallah ta basu waje,malam din ba sai ta kawo masa komai ba,idan ta aikata hakan ma kamar tayi rashin kunya kenan,don ita kanta ba zata iya qayyade yawan abincin dake gabanshi ba.

        Suna tafe abdallah na kafadarta duk nauyinsa,tana tambayarsa yana rattabo mata labarai kala kala
"Ummu abdallah" taji an ambata daga bayanta,almustapha ne,cikin kunya ta sauke abdallah,ya qaraso ya karbi hannunshi
"Don me zaki fito ki barni ni kadai,wuce sashenki" ya fada yana gyarawa abdallah hannun rigarshi,ba musu ta wuce ta barsu a nan.

        Wajen ummee ya wuce,kasancewar duka yau bai shiga ya gaidata ba,tana cikin baqi ta miqe ta bishi saman,ta samu daya daga cikin kujerun ya zauna,abinda ya burgesu yadda abdallan ya duqa har qasa ya gaida ummen,ji take da ana qwacen d'aa da ta qwace abdallah ta baiwa almustapha,saidai babu komai duka tushiya daya ce,tana fatan wadda ta samar da wannan ta samawa nata dan itama,cikin kulawa da juna suka gaisa sannan yace
"Su'ad fa ta shigo kun gaisa?"
"A'ah,amma wataqila ka ganta,ai ba tafiya zata yi ba yau din,ko zuwa gobe ma duka daya ne zamu gaisa" take ranshi ya baci har fuskarshi ta nuna hakan,dama ya zargi haka saboda baiji baba ya masa maganarta ba,duk yadda akayi shima baisan da zuwanta ba,ko zai lamunci komai amma banda bangaren iyayenshi,sun fiye masa kowa da komai a rayuwarshi,yana da azamar miqewa ta dakatar da shi
"Bance kaje kuyi bacin rai ba har hakan ya kai kunnen babanka gida cike da jama'a" ajiyar zuciya ya sauje,tafi kowa saurin karantarsa abinda yayi niyya kenan yaje ya sameta,ya dan jima wajen ummeen suna tattauna lamuranda suka jima basuyi hira akai ba kafin ya fita daga bangaren.
Chapter 178 · 0% Book details