← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 226

Sashe 85

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

     Sumayyan ta ganeta tare hadimar amiran ce,tare suke shigowa,isa da qasaitar gidan baabaa prof kusan kowa dame masa aikinshi shi daya,gaida sumayya tayi saidai ta kasa amsawa ta maida mata gaisuwar suka gaida juna,kusan zata dan girme musu saidai ita din yare ce,sannan ta rusuna cikin girmamawa ta miqawa amira jakar mai kyau,amsa tayi sannan tace
"zaki iya tafiya,idan ummee ta tambaya kice ina gidan umman khalipha"
"To madam" ta amsa ta fice,miqawa sumayya jakar tayi tana fadin
"Ga tsarabarki ta saudiyya,babu yawa a karba da haquri" murmishi ta saki tasa hannu ta karba tana godiya tare da fadin
"Mai yawan kenan" tana fidda kayan ciki,turaruka ne designers masu kyau guda uku,agogo cikin dan akwakunsa,sai hijabai saqar qasar oman suma guda uku masu azabar kyau,sun burge sumayya qwarai har sai data fidda murmushi saman lebanta
"Naga kina sonshi ne sosai"
"Naji kuwa dadin kyautarsa fiye da komai cikin kayan nan"
"Ina fata kin yaba"
"Qwarai da gaske" suka sa dariya baki daya,a nan anty dije ta fito,gaisawa sukayi sumayya ta nuna mata kayan ta gani ta tayata godiya.

Wayar amiran ce ta dauki qara,dagawa tayi tana dubawa,idanu ta zaro,a fili ba tare da tasan ta fadi ba
"Na shiga uku ya man yau kuma?" Da hanzari ta daga kiran ta kara kunnenta
"Ok,to yaya" ta fada tana miqewa
"Amiran umman khalipha na wuce,ya man ya aikeni na kaiwa umme waya kada ya qara kira ban je ba,ya kira wayarta taqi shiga haka land line din part dinta"
"Ok,muje na taka miki" sumayya ta fada tana miqewa
"Na gode" ta fada tana murmushi,don haka nan Allah yasa mata qaunar sumayya,burgeta take sosai.

Jerawa sukayi suka fito,suna gab da kaiwa qofa amira tace
"Uhmmm,ko ki tambayi ma mutuminki ko?"
"Ayyah,ya mahmoud,ki gaidashi don Allah nayi laifi kam"
"Um um,ni ba ma shi nake nufi ba,ya mustapha mana" shiru ta danyi gabanta na duka tunda ta ambaci sunam nashi,da ido amiran ke karantarta ganin bata ce komai ba har tana shirin fita ya sanya ta bar zancan ta soko wani
"Yaushe zaki shigo gaida baabaa,yana ta maganan baiga mamanshi ba" dan qaramin murmushi ta saki,sai taji tayi kewar tsohon duk da ba sabawa sukayi ba,amma saidai ko kadan bata sha'awa ko marmarin sake shiga gidan,tun daga randa abun ya faru.
"Ki gaida min baabaa da kyau don Allah,zan shigo idan Allah ya yarda" ta fada da siga biyu don bata da niyyar zuwa din
"Allah yasa da gaske ne,saikin shigo din na gode"
"Nike da godiya,ki gaidamin su ummee ma"
"Zasuji" ta fada tana ficewa tare da jin dadin yadda sumayyan ta nuna kulawa ga ahalinta.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣4⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*haqiqa Allah yana son masu yawan tuba*
___________________________________

       Cikin sati guda suka kammala duk wani shiri nasu na tafiya,ya kama ranar lahadi zasu tashi zuwa uk,hafiz ne kadai abun tausayi,don su kansu su laila sun daina dariya da tsokana sai tausayinsa,ranar asabar da daddare abbanshi da anty dije suka kaishi gidan kakarshi sannan suka dawo.

        Da daren ana ya gobe zasu tafi tana zuge jakar matafiyanta wayarta ta dauki qara,bata duba ba ta dauka ta kara kunnenta,sai taji muryar lukman,murya a sanyaye  bayan sun gaisa ya soma fadin
"Da gaske sumayya baki damy da ni ba baki damu da yaranki ba,kizo kano kiyi kwanaki har goma ki kasa gayan,bare kice zaki ki gaida hajiya,sumayya me muka yi miki haka?" Sai a lokacin ta tuna ma tace zata gaida hajiyan abdur rahman,baki daya ya mance,ta kuma san shima yana sane shiru kawai ya mata ya zuba mata na mujiya
"Kayi haquri,babu abinda kuka yimin,tunda naje ban zauna ba munata shiga kasuwa da sallamawa 'yan uwa da dangi?"
"Sallama wacce iri" dan jim tayi tana jin nauyin fada masa,saidai dole ne ya sani din yanzu
"Gobe in sha Allah zamu tashi zuwa uk,sai bayan shekara daya zamu dawo" baki daya jikinsa ya saki,jijiyoyinsa suka yi laushi,idanunsa ya lumshe wadanda ke masa zugi,ya budesu da qyar muryarsa kamar wanda zai saki kuka yace
"Da qyar ne idan ban rasaki ba sumayya,burinsu nuwajra na ki dawo musu bazai cika ba,na saddaqar sumayya kin subuce min" ya fadi yana kada kai tamkar yana gabanta,shuru tayi ba tare data ce komai ba,don batasan me zata ce din ba,itama sai ya kashe mata jiki baki daya,tausayin yaran ya taso mata,nannauyar ajiyar zuciya y saki
"Shikenan sumayya,ina miki fatan alkhairi,Allah ya tsare ya dawo daku lafiya,saidai hakan bai nuna na miqa wuyan rasaki,bazan fidda da rai da rasakin ba sai randa naga an daura miki aure da wanu wanda nake fatan wanin ya zamanto nine" ya qarashe muryarsa na dan rawa,sabida ba zaya taba mance kulawa da kwanciyar hankali da farincikin da ya samu a aurenta ba,duk da cewa baki daya zaqin da dadin na wasu taqaitattun watanni ne,amma hakan ba zai taba barin kwanyarsa ba har ya mutu,sumayya ba irin matan da kake saurin mancewa da rayuwar da kayi da su bane,tana da wata iriyar baiwa ta musamman mai tsayawa a wuya
"Na gode,a gaida yaran"
"Zasuji,da fatan zan samu number dinki ta can idan kun isa ko don ku dinga gaisawa da yara"
"In sha Allah" ta fada tana datse kiran,jikinta a sanyaye ta sauke wayar,tana mamakin yadda ta shiga rayuwar wasu mazaje,har suke iya bata muhimmanci mai yawa haka a rayuwarta,bayan ita din bata ga wani abu da take da shi ba wanda za'a kwadaitu wajen zama da ita,da wannan tunanin taci gaba da aikinta har ta kammala ta kwanta don ta huta.

     *RANA BATA QARYA*

     Dukkansu sun hallara cikin lafiyayyar zungureriyar motar data dauke kayansu baki daya,wanda baabaa prof shi ya bada ita yace a kaisu a cikinta,anty dije data shiga sallama da su ita da uncle farouq suke jira.

        Harara anty dije ta aika mata da ita bayan sun fito wadda batasan ta mece ba har sai data bude baki tayi magana
"Kinji dadi a ranki ko?,ai yanzu sai ki shiga ki musu sallamar tunda mai gidan da kansa ya nemeki" sosai taji kunya da har baabaa prof ya cigiyarta,bata son shiga gidan sam,haka ta sauko a hankali ta nufi gidan cikin shigar wata iriyar gown mai dogon hannu A shape,wadda anty dijen ce ta siyo musu tace ita zasu sanya,tayi rolling da dan madaidaicin mayafinta,kayan sun mata kyau matuqa,saidai baki daya jinta take a takure saboda rashin sabo,ta riga ta saba ta adana jikinta cikin hijabi.

        Gabanta na faduwa ta sanya kanta zuwa sashen baabaan
"Laaah ilah" taji an ambata a bayanta,da sauri ta juya,amira ce ke tsaye tana kallonta,fuskarta dauke da dariya hannunta riqe da mayafi
"Ai yanzun nake sauri naje rakiya kada ku tafi ki barni,na lura sam wlh amiran umman khalipha baki damu da ni ba,nike ta taki"
"Kiyi haquri don Allah kada kice haka,yimin jagora na yima baabaa sallama"bata amsa ba face gaba data soma yi wai ita taji haushi sumayyan tabi bayanta tana dariya,saidai kafin su qarasa din bakin amiran ya kasa shiru
" gaskiya dole amiran umman khalipha ki dinga boye jikinki cikin hijab,dama haka kike?,wannan idan muka jera ai sai ki kashe mana kasuwa,haka kika hade?"ta fada cikin sigar wasa da mamakin irin kyawun sumayyan,wani irin kyau me tsari da ban sha'awa,dariya sosai ta baiwa sumayya har ta kai mata duka ba tare data shirya ba,itakam babu wani kyau sam data gani daga gareta,ita amiran bata kalli kanta ba,kyau hutu wayewa da kwalliya duka,ta ina zata kashe mata kasuwa,ita bama neman kasuwar take ba don haka taci kasuwarta hankali kwance,ta qarashe sauran maganar a fili,dariya sosai ta baiwa amiran
"Wai kina nufin ba zaki sake aure ba?" Wani abu ne ya soki sumayya sai ta kasa amsawa,kai kawai ta kada mata ba tare da tace komai ba,ganin hakan ya sanya amiran jan bakinta tayi shiru,don dama ko can ita ba mai yawan bin qwaqwqwafi bace har suka isa sashen baban.

       Yana falonshi zaune kan kujerunsa na alfarma,idanunsa saye da gilashi yana kallon tashar VOA,gefansa jarida ce,daya barin kuma damammiyar furarsa ce da umme ta gama dama masa yanzun nan,don ko falon bata kai ga ficewa ba.
Chapter 85 · 0% Book details