Sashe 89
Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Yarinyar da tun tana qanqanuwarta aka nuna mata ta ginu ta kafu kan raina talaka,dukkan wanda bai da shi bai da qima baida daraja a idanuwanta,kai hasalima bata masa kallon cikakken mutum mai 'yanci,yarinya ce mai yawan izza da jin kanta,yarinyar da bata mu'amala da dukkan mutumin da bai fisu arziqi ba,matuqar kina so ko kana so kuyi qawance ka tabbatar ka fito daga gidan da yafi nasu arziqi ko kake dai dai da ita,ta dauki kanta da girma,ta ajjiye kanta can nesa sama qololuwa,komai nata high class ne,komi da zata mallaka sai ta tabbatar yasha banban da na kowa,bata taba yadda wani ya fita ko ya shalle mata,bata lamunci kallon banza ba bare ka furta mata maganar banza,taku take iya qarfinta,jin kanta take tamkar diyar DONALTRUMPH ko kuma BILLGATE,kallon da takewa mutane ma dabanne,duban farko ga mai hankali zai fuskanci kallo ne na qasqanci da ganin kowa bai isa ba face ita din nan dai,masu hidimawa gidansu kallonsu take tamkar bayi da suka siyesu,babu wanda baifi qarfin ta takashi ba matuqar arziqinka ya gaza nasu,wayewarta ta wuce iyaka,ta wuce tunaninka,duk wani abu da baturiya zatayi shi a matsayinta na farar fata wadda bata da cikakken addini bare kunya shi su'adah zata yi ba,babu uban wanda take jin kunya,abu guda ne bata taba yiba bada mutuncinta,saboda ta riga ta sanyawa ranta bata da miji daya wuce mustpha,har yau batayi katari da namiji kamar mustaphan ba,duk wanda ta kalla sai taga mustaphan ya masa fintikau,tamkar yadda sama ta yiwa qasa nisa,bugu da qari ta tabbatar ta jewa mustapha a fanko babu abinda zaya hana wulaqanta duniyarta,babu abinda zai hana yayi fatali da dukkan wata qauna da take masa ya hukuntata mafi tsananin hukunci,tana yarfa tare da wulaqanta maza da yawa,kama daga hausawa har zuwa turawan,idan har kaga ta tsaya ta kulaka tofa ka tabbatar babanka an sanshi ya san wani shima,sunansa ya zama tambari a duk qasar da kuke da zama,su'adah bata san sanya atamfa ba balle daurin zani,dankwali kuwa saidai ta gani a kan wasu,yadda americans ke shigarsu itama haka yake,ta sanya rigarta da wando,ta fito da gashi ta fice abinta haka,a da har ra tsiri saka mini skert,mustapha yaci ubanta ya taka mata birki,tana qwafa tana kumburi bayan fitarsa tana ba zata daina ba,kaulat da take kira mom ta mata fada,ta fuskanci sam a cikin kaso dari na rashin nutuncin su'adah itakam ko arba'in bata yi ba,dama wai ance sai mai koyo yafi qwararre qwarewa
"Ke da kike son aurensa,ta yaya zaki qi yin abinda yake so,idan dai baso kike ki jawo mana asara ba,jira nake kawai ki gama secondry na qyasawa babanku maganar,don kada ma ya hango wata ya jawo mana asara" kan haka ya sanya ta daina sanyawa,ta kuma nemi dankwali take sanyawa akanta don dole wanda data fice yawonta zata figeshi sai kuma idan zata dawo gida.
A irin zaman hostel da sukeyi idan jarabawa ta kusa,suna zaune su shidan bayan kowanne yayi karatu ya gaji,sai kuma suka barke da hira,mustapha dake kashingide gefansu yana duba handout,shi kadai ne bai ajjiye tasa ba,sun riga kusan da sun saba da irin wannan halayya tasa,yadda yake na daban komai nashi dabanne,bai gajiya sam da karatu,iskar gun nayi mishi dadi qwarai,saboda wadatar shuke shuken dake wajen,a hankali suka gangaro kan hamza,shi sukewa tsiya kan yaci baya,ya rasa wadda zaya aura sai 'yar afrika,afrikan ma nijeria,nijeria ma yarinyar da kwalin secondry school kadai gareta,ra'ayinsa ne,don duk cikinsu ya fisu sassauqan ra'ayi,baiga dalilin da zai daukarwa kansa jangwam ba,yana mamakin yadda 'yammatan da idanunsa ke bude tarwai suke burgeshi,shikam ya sheqa yaga babu qwaya gwara ya auri local ya wayar da abunsa,kusan mustapha yafi kowa jin baqincikin batun,shi gaba daya atsarinsa ma baijin zai iya auren matar da bata da kwalin degree zuwa sama,matar da tasan abinda take yi,yana jinsu suna ta kumfar baki,daga bisani da yaji sun fara cikashi ya miqe zai bar gun,don kada ma ranshi ya baci kan lamarin,bai son cewa komai,haka ya kwashe litattafansa ya sauya gu yana ganin baiken hamza,tare da mamakin meye amfanin wayewa da karatunsa da zai dauki irin wadan nan yaran a matsayin matar aure,wadda babu wayewa tattare da su,a ganinsa saidai kawai kasha kayan haushi,babu wata kulawa da zallar soyayya mai maqalewa zuciya da zasu iya yi ma,a yadda yake din nan mayen soyayya ne,mutum ne shi mai burin samun macen da zasu baje kolin soyayya,ta soshi tamkar ranta,ta kula da shi kamar sabon jinjiri,ta shagwabashi kamar dan auta,ta bawa lamuransa muhimmanci ta fifitashi fiye da kowa ina zaya samu wannan ga irin wadancan matan?.
Lokacin da mustaphan ya gama karatunsa baki daya har ya samu aiki a wani babban asibiti dake garin,wanda da gudu suka daukeshi,sun jima dama suna bibiyar irin qwazonsa,don a daliban da jami'ar ta yaye a shekarar banu dalibin da ya kai qwazonsa,ranar baabaa prof yayi farinciki da samun d'a kamar shi,ya runa kalaman mahaifinsa muhammadu,ba shakka suna ganin abinda malam ya gaya musu zahiri,mustaphan daban yake tun daga haihuwarsa zuwa yau,haka ma ummee don baki daya suka rankayo harda anty maamaa suka zo bikin yaye su din.
familyn tun a lokacin family ne mai ban sha'awa da burgewa,cike yake da qaunar juna da hadin kai,dukkansu daga ummee har anty maamaa sun tsarkake zukatansu,kowacce ta riqe 'yar uwarta fusabilillab,sai Allah ya shiga lamarinsu ya kade musu dukkanin abun qi.
Ana ya gobe su baabaa prof din zasu koma uncle abdus samad ya sanarwa baabaan niyyarsu ta hada auren mustapha da su'adah,ba qaramin farinciki baban yayi ba,yana ganin lokaci ne na qara danqon aminci da zumuncin dake tsakaninsu,ko a lokacin sai da ya tuna da sulenshi,inama ace diyar sulenshi ce zai aurawa mustapha?,kowa yayi na'am da batun sabanin mustapha daya shiga tashin hankali da bacin rai,tunda shi kam babu wata alaqa ta soyayya data taba shiga tsakaninsa da yarinyar sam,hasalima bata cika sharadan da yake so ba,don candy kadai tayi,kawai dai ya dauketa ne matsayin qanwarsa,amma da batun yaje kunnen abokan nasa su suka kwantar masa da hankali,a ganinsu babu komai,a daura auren taci gaba da karatunta,shima yaci gaba da aikinsa,idan yaso sai yayi rainonta har takai matakin da yake so ta kai,ya dorata kan dukkanin tsarinsa,tunda babe din ta hadu,abinda basu sani ba dukkansu shine su'adan ta girmi tunaninsu,shi sam shawarar ma bata yi masa ba,abu guda da ya sanyashi amincewa shine ranar wata lahadi da ya jiyo muryar kaulat na kururuwa,su'adah din ya dirki guba saboda ta lura mustaphan baya sonta,abun ya tsoratashi,ta dauki halayen yahudawa baki daya na rashin yadda da qaddara,ko data farfado cewa tayi zata kashe kanta,roqon sa da uncle din ke masa kan ya aureta shi ya masa nauyi,ba tare da bata lokaci ba ya amincewa aurenta,yana tunanin yayi amfani da shawarar abokansa kawai.
Cikin iya duniyanci da gogewa sannu a hankali ta soma jan ra'ayinsa,sai ya sakar mata ya zuba mata ido,cikin kaffa kaffa take lamuranta,don tasan halinshi sarai bai daukar wargi,a hankali ta soma bude wata qofa daga cikin zuciyarsa,wanda hakan ya sanya ya dan sakar mata kadan,a wannan bigiren sukayi aure.
Baki daya ta bata tsarinsa na yayi rainonta,abu guda ne ya dore ci gaba da karatu da tayi,don itama tana masifar son karatu,tana son tayi karatun da zata zama wata,watan da duniya zata dinga maganarta da kwatancenta,ta riqi karatunta da masifar muhimmanci,tana ganin shine tsanin mataki na biyu da zai sanya ta zama wata a duniya,bayan zamantowarta daya daga cikin iyalin PROFESSOR MUHAMMAD MUKHTAR MUHAMMAD ADAM GOMBE.
Rayuwar gidan aurensu rayuwa ce irin wadda suka ga mazauna qasar nayi,rayuwar 'yanci,kowa yana da right,har wani lokaci mace tafi namiji dama,saidai a wannan bangaren mustaphan ya riqe kambunsa,yayi riqo da bahaushiyar al'ada,ya bata damarta,saidai fa bata isa ta tsallake umarni qa'ida ko dokarsa ba,wannan kadai take gani ya takura ta,shike bata mata rai,to amma ba komai bane a gunta saboda masifaffen son da takewa mustaphan,tanaji a acikin ranta ko ummee da tayi naqudarsa bata kama qafar son da takewa mustaphan ba.
Tsakaninta da mustapha ya biya mata buqatarta,ta aure kota kudi,taci sa'a kuwa gwanin kyautatawa iyali ne,bata san cinsa ko shansa ba,batasan tsaftar muhalli data tufafinsa ba,suna da kuku suna da mai share share suna da mai wanki da guga,sam ita a rayuwarta ma baki dayanta bata taba shiga kitchen ba,shege ruwan zafi saidai ta ganshi kawai,rayuwa ce irin ta banasaren mutum zallah suke gudanarwa,shima bai damu ba,amma wani lokaci sai yayi mamaki idan yaje nijeria yaga yadda su umme ke dawainiya da majinsu,basu duba tsufansa ko girmansa ko kuma yawan ma'aikatan dake gidan,wanda duk abinda kake so daka fada ta cikin waya za'a gabatar maka da shi,sai ya watsar tare da dora hakan kan mizanin banbancin al'ada da dabi'a.
Yana tsaka da aikinsa wani babban asibitin kudi suka yi masa tayin aiki a asibitinsu,ya duba yanayin asibitin yaga yayi masa,akwai nisa sosai tsakanin jahar da suke da jahar da asibitin yake,hakan ya sanya ya duba gida mai kyau a can ya siya,bedroom biyu falo sai kitchen ya koma can da aiki,yayin da ya bar su'ada a nan tana ci gaba da karatunta,don cewa tayi ba zata bishi ba gaskiya taba tsaka da karatunta,shima bai wani damu ba yayi tafiyarsa,saidai sam baida lokacin zuwa inda suke,ita dince idan ta motsa mata zata kwashi kayanta ta bishi,tayi masa weekend ta dawo taci gaba da sabgoginta.