← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 226

Sashe 35

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

         Tamkar guduma zainab ta sanya ta daki qahon zuciyarsa haka yaji,take maganar da yaya yahansu ta ta sha gaya masa shekarun baya suka bijiro mada suka cakudu da wannan sabon batun
" kai idan zaka farka gwara ka farka,matarka fa ba son haihuwa take ba,bata ma sha'awarta,tunda kuke ka taba gani ta sha wani magani don ta haihu ko ta taba maka maganar kuje asibiti a dubaku?,ina kyautata zatan ma ita tasha maganin da zata hana kanta haihuwa,banda haka yarinyar dake da quruciya mai zai hanata haihuwa a irin wannan lokacin?". Wani fushi da bacin rai mai tsanani ya sauko masa,sai kawai ya miqe,burinsa kawai yaje ya samu sumayya yanzun nan,da sauri ta riqeshi don ba yanzu take da muradin nakiyar ta fashe ba
" a'ah mukhtar ina kuma zaka?"
"Sakeni zainab,sakeni naje na sameta" wani mugun marairaicewa tayi sannan tace
"Shi yasa fa naqi gaya maka tun jiyan,yanzu me zakaje ka yiwa yarinyar mutane kana cikin fushi haka?,idan baka iya kama barawo ba sai shi barawo ya kamaka,zauna muyi magana akwai mafita" babu musu ya koma ya zauna yana maida numfashi
"Mukhtar,kada ka damu,ni mai qaunarka,ina son abinda kake so,idan baka manta ba nike kulawa da sumayya...to kada ka damu,zan sanya ido sosai a kanta,sannan zan hana duk wani abu faruwa har Allah yasa ta haihu lafiya na maka alqawari" hakanan yaji kalamanta sun kwanta masa a rai,sai ya sauke ajiyar zuciya
"Na gode zainab,don Allah na roqeki ki kula da ita,a duniya yanzu babu abinda nakeso sama da cikin nan don Allah" wani shegen kishi ya takore mata,cabdi,a haka zata bari sumayya ta fara haihuwa,ai ba zaya yiwu ba,a fili tace masa
"Na maka alqawari tare ma zamu dinga wuni insha Allahu kada ka damu" jikinsa a sanyaye ya gama shirin zuciyarsa na bugawa,mamaki da haushin sumayya ne fal cikin zuciyarsa,da kamar ya wuce abinsa ba tare da ya mata sallama ba zainab din ce ta tursasashi kan sai ya shiga din,koda ya shiga sumayyan sai taga yanayinsa ya sauya sosai,ba kamar yadda ya saba mata ba,gabanta ne ya dinga faduwa tana fatan ba halayensa na baya bane zasu dawo,don ko kusa bata da buqatar wannan yanayin.

       Har ya juya zai fita sai ya sake waiwayowa ya dubeta
"Ki kularmin da cikina,din bazan iya jurewa ko yafiya gareki ba ga duk wani abun qi da zaya samu cikin nan ba" dai ya juya ya fita,kanta ne ya daure sosai,me yake nufi kenan,ta jima tana qoqarin lalubo amsar,daga qarshe abinda qwaqwalwarta ta bata shine tsabar son cikin da mukhtar din keyi ne haka ta barwa ranta taci gaba da sabgoginta.

      ****     ****     ****

    Bata gushe ba tana ci gaba da cusawa mukhtar tunani kala kala kan zub da ciki sumayya ke qoqarin yi,amma ta nuna masa tana bala'in takatsantsan akan faruwar hakan,sosai ya shiga damuwa da tashin hankali,mamakin sumayyan yake yi,da ya matsanta kan sai ya mata magana yana son daukar mataki,bazai iya jura ba idan wani abun ya samu cikin sai ta masa alqawarin zata nuna masa da idanunsa zai gani saboda hukunci da hujja yafi.

*KUNDIN QADDARA*

*_BAQAR RANA_*

Tun da safe ta hada mata shayi kamar yadda ta sabarwa kanta,duka yana cikin qudurinta da tsarinta. Ranar kusan da wuri mukhtar ya fita,tana kwancan har ya fita din ko abin kari ma bata masa ba saboda mugun qudirinta data qulla aiwatarwa a yau din nan ko farkawa bata nuna tayi ba,hakan ya sanya data shiga da shayin ta zauna tana jan sumayyan da hira,bata bar dakin ba sai data tabbata ta kammala shan shayin,sannu a hankali ta soma hamma,zainab din ta dubeta fuskarta qunshe da murmushi wanda ke dauke da manufofi uku,manufar cimma nasara da manufar mugunta,sai kuma dadi daya kamata saboda tafuskanci magungunanta zasu soma aiki lokaci guda yadda take so
"Kwanta ki huta qanwata na fuskanci kamar bacci kike ji"
"Wallahi kuwa,duk jikina ya mutu" ta fada tana jan pillow ya yada kai saboda nauyi da taji kanta ya soma yi sakamakon bacci mai nuyi daya lullube idanunta. Leqa fuskarta tayi ta tabbata ta soma baccin sannan ta sake sakin murmushi,a nutse ta nufi drower din gefan gadon sumayyan ta fiddo magungunan da suke soke cikin rigar mamanta,magunguna ne har saches uku dukka na zub da ciki ne,saches daya aka balla guda gudu wanda ita tayi amfani da shi ta zubawa sumayyan cikin ruwan shayin data kammala sha yanzu,sai wata 'yar qalamar kwalba da wani saches din wanda duka maganin dake bugarwa ne da saka bacci wanda yawanci 'yan shaye shaye aka sani suna ta'ammali da shi. Dorasu duka tayi kan drower din sannan ta fice.

Kitchen ta shiga ta samo kofi cikin kayan sumayyan ta zuba ruwa ta dawo kusa da magungunan ta ajjuye,ta bude kwabar kayanta ta ciro hijabi ta ajjiye saman kanta sannam ta nufi ma'ajiyar takalmanta ta ciro ta sanya mata daya daga ciki a qafafunta,sai data qare mata kallo ta tabbatar komai ya kammala sannan ta saki dariya ta fice zuwa dakinta.

Tazarar mintina goma ta bada kamar yadda aka ce mata magungunan zasu fara aiki amma maganin baccin zai sa ba zasu tashi aikinsu gadan gadan ba sai bayan minti ashirin,dakin ta sake nufa ta leqata sai ta tarar har yanzu baccin take amma tana motsawa akai a kai,jinjina kai tayi ta sake komawa dakinta.

Kai tsaye ta dauki wayarta ta laluba lambar mukhtar,bugu uku ya daga tare da yin sallama,bata bi ta kan amsawa ba ta soma magana cikin yanayi na matuqar rudewa qwarai da gaske
"Wayyo Allah mukhtar mun shiga uku,mukhtar na kasa riqe amanar da ka bani" cikin wani mugun tashin hankali ya miqe tsaye daga inda yake zaune sannan ya fara tambayarta
"Lafiya zainab yi magana mene ne?"
"Kasan ka barni a daki ina kwance ina bacci,to ina tashi naga lokaci ya ja,sai na tuna sumayya na barta bata ci komai ba,da sauri na shiga kitchen na hada mata abun kari na nufi dakinta,ina shiga naga babu kowa na duba gidan baki daya ban ganta ba,ina falo ina taraddi ina ma shirin kiran wayarka ko kasam zata fita?,kawai sai gata ta dawo dauke da wata baqar leda ita da wannan 'yar uwar tata,da nayi mata magana ma kallon banza ta yimin tayi tsaki ta wuce daki,sai ma qyaleta sabida nasan masu ciki da fushi,sai daga baya na sake leqata sai na tarar tana shan wani magani,na mata zancan abinci tace ta qoshi bata buqata taci a waje,na qyaleta na dawo ina hidimar gida,bayan wajen minti talatin sai na fara jiyo ihunta tana wayyo cikina wayyo bayana inzo in taimaketa" sai ta fashe da kuka kamar gaske,ya gaji da dogon jawabi kawai jira yake azo gurin
"Ki gayan me ya faru?"
"Jini ma gani daga jikinta mukhtar yana fita wanda ke nuna kamar bari tayi"
"Me!" Ya fada da madaukakin sauti,kafin ta kai ga amsawar ta soma jiyo kumar sumayyan na kiran sunata,dadi ya kamata komai yazo a daidai kenan?,sai ta sake dububurcewa
"Tana kirana mukhtar don Allah kayi sauri kazo mu kaita asibiti kada mu rasa cikin nan" sai ta katse kiran kawai cikin gaggawa ta nufi dakin sumayya.

Murququsu ta cimmata tana yi da malelekuwa daga saman gadon har qasan carfet din dakin,tun daga kan gadon jini ne har qasan dakin,wata azaba ke ratsata ilahirin jikinta,duk da azabar da takeji bai hana hankalinta tashi ba,tasha jin ana cewa zubar jini hadari ne gun mace mai ciki tun daga shigar ciki zuwa haihuwarsa,tsoro fal da fargaba ke zaga zuciyarta,tsoron rasa cikin jikinta,tsorom rasa gudan jininta
"Ki taimaka kin don Allah amarya kada na rasa baby na" ta fada hawaye da gumi na hade mata saboda tsabar azabar radadin da mararta ke mata,ga tarin mamakinta sai taga zainab din ta sheqe da dariya
"Kadan kika gani,ci gaba da karbar gashin ciwon rasa d'a kafin ki rasa mijinki ma baki daya,nice sila ba zan iya taimaka miki da komai ba,burina nake so ya cika" sai ta sake takowa zuwa gabanta ta ranqwafo
"An fada miki akwai ranar da kishiya zata so kishiyarta ne?,an gaya miki ni sauna ce da zan dinga miki bauta?ko an fada miki wawiya ce ni bansan me nake ba?,lallai dukkan wanda ya riga ka kwana tilas ya rigaka tashi,wannan ya isheki ishara game da kaidin kishiya,ke yarinyace,bakisan komai ba sumayya,daga yau zaki shaidi kaidin kishiya" ta fada tana juyawa ta fice ta barta a dakin tare da komawa falo tayi zamanta.

Runtse idanunta tayi wani abu na dawafi kan qwaqwalwarta,babu shakka ayanzun maganganun da zainab ta furta mata sunfi mata ciwo fiye da ciwon dake nuqurqusarta,tana nufin ita ta mata silar abinda ke faruwa yanzun da ita?,me ta aikatama zainab din haka mai muni da zata zama silar rabata da abinda ta jima tana dakon isowarta gareta?,don kawai sun hada miji?,saboda kawai suna qarqashin inuwa daya?WANNAN ITACE KAWAI HUJJAR?dafe mararta tayi tana ci gaba da kallon yadda jini ke kwaranya yanabin qafafunta tare da bin lafiyar carfet dinta.
Chapter 35 · 0% Book details