← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 226

Sashe 129

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

        Wanka ta fara yi sannan tayi sallolinta,anty dije tace mata ga abinci tace sai anjima,duka abinda take hankalinta bai wajen yana wajen abdallah,ina yake?,ina ya kai mata shi,tun tana kasa kunne da ido har ta kwanta saidai shiru kake ji,kasa haquri tayi ta miqe da hijabin sallarta ta qwanqwasa dakin anty dije ta mata izinin shiga,kwalliya ta tadda ta tanayi
"Uhm,ya akai amara qirjin biki" murmushi ta danyi wanda yafi kama da yaqe
"Anty wannan yayansu amiran ya amshi abdallah tun dazun,har yanzu ban ganshi ba bashi ba abdallahn" cikin ko in kula tace
"Wa?,wai musty,kada ki damu kisa a ranki kamar kina tare da abdallah ne,ai mayen yara ne,indai mustapha ne a rina" hankalinta ya dan kwanta da jin hakan,sai ta koma daki tayi shirin kwanciya,don ita kadai take da buqata a yanzh,tun tana sauraren ta ina abdallahn zai shigo har bacci ya sureta.

         Washe gari sam bata shiga gidan ba ma sai da yammaci tayi aka soma shirin tafiya dinner,nan ka bata ga abdallan ba,ba kuma wanda ya mata maganarsa,haka taci gaba da daurewa har sanda anty maamaa ta dan tsokaneta
"Abdallah kam anyi wuyar gani anyi sabon daddy" murmushi kawai ta danyi ta basar.

       Wani qayataccen event center suka kama,hmmm masu abu da abinsu,kada kaso kaga yadda gun ya qawatu yayi matuqar tsaru,ranar sumayya anyi abun gani,ita ta zauna mazaunin babbar qawar amarya,tayi komai yadda zata faranta ran amiran duk da a takure take matuqa,idanuwan maza bisa kanta sunyi yawa,kai har ma wasu daga cikin matan,sai da guri ya gama tumbatsa sannan su'adah ta iso,a nan tayi burgar data saba,tsakiyan abokan ango cikin dinkim riga da skert na wani shegen leshi mai azabar tsada wanda aka ci mutuncin tsadar tasa aka yi masa dinki na ganin dama,tsagar skert din har kusan gwiwarta,dinkin ya kamata dam,banda dankwalin da aka tsarawa dauri babu komai a kanta,don ko tuna sunan mayafi bata yi ba,liqi ta shiga yi da 'yan dubu dubu sabni kar wanda ita kanta bata san nawa ta barar ba,abin nema ya samu ta dauki idanuwan jama'a,ta kuma qona zukatan 'yan baqinciki wadanda bas son tarayyarta da mustapha,to su gani ya tsaya mata,sai data yi mai isarta sannan ta sauka daga step din ta koma mazauninta.

Sai sha daya na dare aka tashi kowa ya koma inda ya fito.

*******    *******    ******

        Tun qarfe goma na safe layin nasu ya tumbatsa ya dinke da jama'a kasancewar goma da rabi ne daurin auren,bacci ranar tayi sosai dakin anty dije,bata tashi farkawa ba sai qarfe tara da rabi na safe,tarin missed call ta taras duka na amira,da hanzari ta miqe ta fada toilet tayi wanka,a gurguje ta fito ta shirya cikim shaddar da sukayi anko wadda tayi masifar haduwa,kamar yadda dinkin doguwar rigar ya dace da jikinta,komai da tayi amfani da shi kalar zaren da akayi aikin shaddar da shi ne,ta fito fes mashaAllah,daidai sanda laila ta shigo,baki ta sake tana kallon sumayyan,ta qaraso dakin ta samu bakin gado ta zauna
"Wai dama don Allah anty sumayya haka kike da kyau" dariya yarinyar ta bata saboda bihaqqi ta fada
"Sai an tambayo" ta fadi hankalinta ka can gidan baba,saboda hayaniyar data dinga jiyowa na tashi ta tabbatar layin yayi tumbatsar da babu damar ta fita,valcony din saman benan anty dije ta bude ta fita ciki,layin ya shaqara da mutane ya cika masha Allah,kai ta dinga kadawa don tasan dole ta haqura har sai an ragu.

Kujeta ta ja ta zauna daga gefe yadda zata iya hango komai,ta bude wayarta ta soma lalubar lambar amira don ya bata uzurinta,hakanan taji yana yinta ya soma sauyawa kamar ba ita daya bace a gun,kamar fisgar mayen qarfe haka idanuwanta suka jata zuwa inda yake tsaye tsakiyan wasu zaratan samari kamarshi.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

7⃣2⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*ALLAH YANA GAFARTAWA WANDA YASO YA KUMA AZABTAR DA WANDA YASO*

YA ALLAH KA GAFARTA MANA
___________________________________

*TAB,BIGI SAI BIGI,BABBAN GORO SAI MAGOGIN QARFE,IDAN KAJI WANE BA BANZA BA,INA MA'ABOTA KARATUN LITATTAFAN HAUSA,KAMA DAGA NA QUNGIYAR HASKE HARMA WANDA BA NA HASKE BA,SHIN KUNA DA BUQATAR JIN WANI SABON KUNDI WANDA YA TATTARE LABARAI NAU'IN DABAN DABAN WADANDA SUKA SHAFI AL'AMURA NA ZAHIRI DAKE FARUWA CIKIN RAYUWARMU TA YAU DA KULLUM?.......TO MAZA KU GARZAYA KU NEMI LITTAFIN KUNDIN HASKE,WANDA KE QUNSHE DA LABARAI DAKE DAUKE DA NAU'IN RAYUWA IRI DABAN DABAN,LABARAI NE WANDA KE DAUKE DA DIMBIN DARUSSA MASU RATSA ZUKATA,DUMBIN ILIMI MAI JAWO HANKALIN DAN ADAM ZUWA SAKE LURA DA GYARAN RAYUWARSHI,MAZA KA/KI GARZAYA KADA A BAKI LABARI,BA SHAKKA ZA'A CI DA RABONKI MATAUQAR KIKA BARI YA WUCEKI,AKWAI SHI A WATSAPP DA APP DIN WATTPAD BAKI DAYA*

*SADAUKARWAR WANNAN SHAFIN GA:*

*SADIYA ZABURA*
*UMMU RAMLAT*
*MAMAN SAYYID*

*DA MARUBUCIYA*

*AYSHA DAN SABO*

*RABBI YA BAR QAUNA*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽😍😍😍

       Kyawawan idanuwanshi wanda suka wadatu da gashin idanu kamar yadda girarsa take masu kama da na wanda ke jin bacci suke kan ta,shi daya ne tak sanye cikin qananun kaya sabanin dukka sauran wadanda suke tsaye tare,baki dayansu shadda ce jikinsu dinkin tazarce kaloli daban daban,kusan tare suka janye idanuwansa,gabanta ya shiga faduwa,kasa zaman wajen tayi,batasan ana iya gajin mutum ba,gashi ko mayafi babu a jikinta,sai ta miqe jikinta na rawa gabanta na faduwa ta bar wajen,ta tura qofar ta kulle ta dawo cikin bedroom din anty dijen.

      Gefan gado ta kwanta rub da ciki tana sauke numfashi,maganganun baabaa suka soma dawo mata,har yau ta kasa gane me yake nufi,tana da buqatar qarin bayani,tana buqatar taimako wajen wanu ko zata fahimci me yake nufi,amma ta taimaka masa wajen gyara rayuwarsa kamar yaya kenan,wanu mummunan abu yake mara kyau yakeso ta saka baki?,amma ita a wa?,bata da wannaj power din,ganin qwaqwalwarta na neman daurewa yasa ta kada kai tare da yin watsi da maganar,maimakon ci gaba da tunani sai ta sake daukan wayarta ta lalubi zainab ta kirata,din jiya suna wajen dinner taga misscall dinta baya kuma samu ta bita ba.

        Bayan sun gama gaisawa da mama ta musu Allah ya sanya alkhairi zainab ta karba,nan take gaya mata jiya aka kawo lefe sati uku kuma aka sanya,murmushu sumayya ta saki tana tsokanarta
"Kice mu fara shirin tahowa kano ko?"
"Wallahi yaya,kizo ayi tsare tsare masu kyau"
"Insha Allah,ina huce gajiyar wannan bikin zaki ganni,Allah ya nuna mana da rai da lafiya"
"Amin yaya,ina abdallah na"
"Uhmm,ni kaina bansan ina yake ba,yana gidan biki"
"Ki gaisheshi tunda ya manta da mu" dariya ta danyi
"Zaiji,ki gaidan halimaty,wayarta bata shiga"
"Zata ji" suka katse wayar.

       Tana sauke wayar ta jiyo muryar abdallah yana karadi daga qasa shi da sh hafiz,sauka tayi daga gadon ta sauko qasa,yayi masifar kyau cikin wata arniyar shadda ash wadda batasan inda ya samota ba,hulace kanshi zanna wanda sau faman zuba qyalli take,qafafunshi saye da takalmi sau ciki,abinka da uwa da da,yana ganinta ya tako da gudu ya daneta,murmushu tayi ta zube saman kujera yana faman zuba mata surutu da bata labari.

        Ganin sha daya tayi ga gidan babu kowa sai ita ya sanyata yin shahada ta yafa mayafinta ta fito,kamar zata nutse haka ta dinga ratsa mutane a darare tana wucewa har ta kai ga cikin gidan bayan ta kira humaida ta gaya mata inda suke,ko ina harabar gidan 'yan uwa da abokan arziqi ke kai kawo,kowa ka ganshi cikin kwalliya da walwala,daga gefe guda ta hango mahmoud da tarin abokansu ciki har da alqasim,suma sun ganta saboda haka ta qara sauri don kada su rusketa.

       Batayi aune ba sukayi karo kanta ya daki qirjinsa,tayi taga taga ta komo ta fada qirjinsa,zuciyarta kamar zata fito saboda tsoro,tayi yunqurin janyewa,ta samu nasara saidai hannunta na cikin nashi hannun yana duban qwayar idanuwanta,sai yanzu ya samu amsar inda ya samu qamshin da ya buwayeshi tun shekaran jiya,wanda har kuka su'adah tayi sabida jin qamshin,don ta tabbatar hadin humra ce ta mata ta musamman ba turaren namiji bane,gaba ta tusashu tana tambayarsa ina ya samu turaren,baki daya zuciyarta ta gama zayyana mata yana neman wata ne,idan banda haka ina zai samo turaren mace a hannunshi?baya ga haka ta lura wannan karon sam baya marmarinta,baya nemanta idan ba ita ta buqata ba,bayan a baya ta sani cewa duk sanda suka hadu har sai ta gaji ta hada kayanta ta gudu yake qyaleta,amma wannan karon sam ba haka bane,yana jinta yayi mata banza ya gama shirin baccinsa ya kwanta tare sa juya mata baya,don bashi da amsar bata,shi kansa yana jin qamshin cikin hancinsa amma baisan inda ya sameshi ba,baijin zai iya bata lokacinsa ya mata wannan bayanin tunda har tana zarginsa,to ta dauki duj hukuncin da take gani zata iya dauka,hakan ya sake hassala zuciyarta,itama ta shiga fushi da shi gadan gadan miqe ta fice ta sauya dakin kwana,bata san cewa ba shi ta yiwa ba kanta ta yiwa,tunda ba yau farau ba da yake kwana shi daya tamkar gauro,idan da sabo ai ya saba.
Chapter 129 · 0% Book details