← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 226

Sashe 11

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

         Miqewa yayi ya dauki jakarsa zai fice sumayyan ta sha gabansa
"Ya mukhtar,bai kamata ka fita cikin wannan halin da kake ba" sai ya tsura mata ido yana kallon yadda ta langabe kamar zata yi kuka,haka kawai ana son shiga tsakaninsu da farincikinsu kam wani dalili can maras tushe,kan wani abu da basu isa su yiwa kansu shi ba sai Allah ya ga dama,sai ya saki murmushi don ya kwantar mata da hankali,ya sanya hannunshi ya shafi gefan fuskarta
"Kada ki damu sumayya,ina gane komai" yayi kissing goshinta yana fadin
"Sai na dawo" ya juya ya fita a gaggauce don bai son ma yaya yahanasu ta kuma tsaidashi.

         Kai ta kada sannan ta fito daga dakin ta ja ta kulle masa ta tafi da key din dakinta,cikin falonta tayi zamanta bayan ta kunna redio tana sauraran labaran rana freedom.

          Tana kammala jin labaran ta shiga kitchen ta dora abincin rana,cikin kitchen din ta zauna har ta kammala saboda jallop din shinkafa ta musu,ta zuba cikin cooler ta ajjiye cikin kitchen din kana ta nufi dakin fa'izar,ita daya ta taras da alama yaya yahanasun ta tafi wanda ita sam batasan ta tafin ba
"Ga abinci can cikin kitchen na gama" ta fada ta juya ta fice ba tare da ta jira amsarta ba,bata zaci ta ci ba sai da ta shiga dora sanwar dare taga babu komai cikin cooler din tas,mamaki ya kamata saboda batayi tsammamin zata iya cinyewa duka ba,don har da yaya yahanasu ta dafa,ta kada kai ta shiga sabgar dora abincin dare.

          Sau biyu suna kacibus da fa'izan na fitowa a kitchen din sanda take tsaka da girkin,tuwon semo tayi miyar kuka wadda ta wadata da man shanu da nama,ta kammala ta jere komai cikin kitchen sannan ta nufi famfo ta tara ruwan wanka tana jira botikin ya cika.

          Da sauri taga ta fito daga dakinta ta suri silifas ta fada bandakin ta bame qofa,sai ta bita da ido kana ta dauke kai,tana tsammamin matsuwa fa'izan tayi har haka?,ta kashe fanfon ta koma gefan rijiya ta zauna tana tsumayin fitowarta.

      Wasa wasa har ba fa'iza ba alamunta,abun har ya dan bawa sumayyan tsoro,sai ta miqe ta isa ga bakin bandakin ta qwanqwasa qofar,gyaran muryar da taji tayi mata ya tabbatar mata komai lafiya,sai ta koma bakin riniyar ta zauna tana ci gaba da dakon fitowarta.

        Ba ita ta fito ba sai da taji shigowar mukhtar gidan,a qalla awa daya kenan ta kwashe cikin makewayin,sumayyan ta miqe tana masa sannu da zhwa tare da jin nauyin zuwa ya taddata babu kwalliya saboda ta riga da ta saba al'adarta ce daya dawo ya sameta tsaf.

        Ta miqa hannu zata karbi ledar hannunta taji anyi wuf an karbe,da mamaki ta waiwayo fa'iza ce wadda batasan sanda ta fito daga bayin ba ke tsaye tana ta faman doka masa murmushi tare da yi masa sannu da zuwa,a dake yake sa mata,sai sumayyan ta koma ta dauki botikinta zata shige wankan
"Ai wlh ni da ke ne cikin gidan nan,indai ina nan an daina wannan karuwar kwalliyar daren" ta fada bayan da taga mukhtar ya shige dakinsa,waiwayowa tayi ta dubeta sai ta saki murmushi sannan tace
"Ko?"cikin qufula da ganin yadda maganar bata da da ta da qasa yadda taso ba tace
" eh,ko kina musu ne?"kai ta gyada sannan a taqaice tace mata
"Zamu gani" ta shige bandakin abinta,yatsa ta ciza takaici ya kamata,wai dama can yarinyar ba tsoronta take ba basaja take mata ko kuma zugata aka soma yi?,qwafa ta ja domin bata da amsa ta shige dakin angon nata.

         Ga mamakinsu suna shirin soma cin abincin dare sai ga fa'izan,tana wani murmushi ta raba gefan mukhtar din ta zauna
"Naga ya kamata nima adinga cin abincin da ni don qara donqon zumunci ko?" Ta fada tana wani kashe masa ido,ha fuskanci yau sai wani rawar kai take,amma idan batasan kan garin ba shi zai mata kyakkyawan kwatance,babu wanda ya tankata iyaka aka tura mata kulolin ta debi yadda taga zata iya.

      Ita da sumayyan kusan tare kowannensu ya sanya lomar farko a bakinsa,idanu sumayya ta zaro sakamakon wani dan banzan gishiri da ya cika harshenta har zhwa kwanyarta,take qwaqwalwar tata ta tafi tunanin ta yadda akayi hakan ya faru?,a iya saninta lafiyar Allah ta kammala komai ta gyatta shi,amma me ya kawo wannan sauyin?,ko dai harshenta ke shirin samun matsala?,.

        "Qundun uban nan" abinda fa'iza ta fada kenan wanda shi ya tsinke zaren tunanin sumayya,kallon mukhtar suke dukkansu kowanne da tasa manufar a zuciya,zaquwar mukhtar yayi magana ta samu filin baje hajarta da kuma mamakin yadda yaqi maida hankali ga kalamanta takeyi,cikinsu babu wadda ya kalla saici gaba da sambada lomarsa yake,yayin da sumayya tayi qas da kanta ta daure duk wani abu da take ji kan harshenta itama taci gaba da kai lomarta tamkar babu wata matsala dake waka na.

       Idanu fa'iza ta dinga binsu da shi,to ko dai harshenta ne kadai ke gaya mata tuggunta yayi dai dai?,ganin sunyi uwar watsi da ita ya sanya ta kasa shiru sai da ta magantu
"Wai muntari bakaji uban gishirin dake cikin abincin nan ba ne?" Bai amsa maga ba sai da ya sake wata lomar
"Wanne abinci fa?"
"Na gabanku mana" ta fada tana nuna kwanon da yatsa tare da qanqance idanu
"Hala kina da matsalar dan dano ko?" Kafeshi tayi da idanu tana tantama,sai kawai ta miqa hannu ta kwaso miyar gabansa ta kai bakinta,tabbas iri daya ce haka ma dandanon iri daya ne,to tsabar iya asiri ne na sumayya yasa bai fahimta ba ko sun tasamma raina mata wayo ne,fa'iza macace da sam bata da siyasar zamantakewa,hakan ne ya sa ta kasa boye fushinta ta tashi ta fice fuuuu ta bar dakin cike da baqinciki,so tayi yau ya ciwa sumayya mutunci sannan ya janyeshi kuma ta kwana da shi yau ta cusa mata baqinciki.

         Idanunta ta dora kan mukhtat fuskarta qunshe da tashin hankali,ta bude baki zatayi magana ya dora yatsansa kan lebansa
"Shshshshsh!,kada kice komai,ita ta zuba gishirin kan ido na bayan shigarki wanka,tana zaton bazanci ba,batasan ba maqaryacin so nake miki ba,zan iya cin wanda yafi haka ma,bare ma shekararmu nawa da sumayyaty na santa qwarai wajen iya sarrafa hatsi" yadda ya qare maganar ne ya bata dariya har sai da ta dara din,daga bisani ya wanke mata duk wani damuwa tata suka bige da hira,yace idan ba zata iyaci ba kada ta cuci kanta ta ajjiye ya sama mata wani abu shikam zai iya ci,tace sam tunda har ya iya ci itama sai ta ci,qarshe dai ramun muguntar gun fa'izar ya koma tunda ko banza ta tashi ciki babu komai.

         Yau din da kanshi ya mata sai da safe,kishi ya kamata sosai ta dinga rayawa cikin ranta wato zashi yaje yayi abinda anty yahanasun ta umarceshi kenan dazu da safe,ta dinga juyi saman gado ita daya da qyar bacci ya saceta.

         Bata jima da fara baccin ba ta dinga jin ihu sama sama cikin barcinta,a sannu ta bude idanunta tarwai,tabbas ba mafarki bane,ihu ne daga dakin fa'izan kuma muryarta ce cike da gunjin kuka,ta kasa kunne sosai ta dinga jin yadda take neman agaji da dauki,runtse idanunta tayi sai kuka ya subuce mata ta sanya hannunta ta toshe dukka kunnuwanta baccin da bata koma ba kenan.

         Kiran sallar farko na asuba taji an bude falonta,ta kasa kunne sai kuma taji shuru har akayi kiran sallah na biyu,ta sauko daga san gadon da idanunta wadanda sukayi luhu luhu saboda kuka,ta zira hijabinta ta fito daga dakin jiri da dibarta.

        A falon nata taga kamar mutum kwance,gabanta ya fadi da sauri ta koma da baya ta kunna makunni qwan lantarkin falon,haske ya qauraye ko ina,mukhtar ne kwance saman doguwar kujerarta tafin hannunsa dafe da goshinsa.

         Dauke kanta tayi tamfar ma bata ganshi ba yayin da shi kuma ya bita da ido har ta fice,sai da ta daura alwala ta dawo sannan ya tashi ya fice,tana kan abun sallarta har gari ya soma haske,sallamarsa taji yana shigowa ta runtse idanunta har ya qaraso gabanta,ya fuskanci me take nufi domin yana da tabbacin mawuyaci ne idan baya jiyo qarajin fa'iza a jiya ba,saboda shi kadai yasan ta'asar da ga tafka mata da gayya.

      Muryarsa a tausashe da irin salon dake kwantar da hankali da ratsa sassan jikinta yace
"Sumayya,kiyi haquri don Allah,wlh ban shiga dakin fa'iza a jiya don naci fuskarki ko na bata miki rai ba,kiyi haquri idan ranki ya baci,komai nayi nayi ne saboda koya mata saboda ta fice daga rayuwarmu....kiyi haqur....."
"Ya isa ya mukhtar" ta fada da sauri tana katseshi
"Ka daina bani haquri,matarka ce kamar yadda nake matarka,kuma adalcin kenan" ta fada duk da tana jin daci qasan zuciyarta amma hakan ba zaya hanata fadin gaskiya ba.

     Hannunta ya sake kamawa sosai,kana ganin fuskarsa kasan cikin bacin rai tsantsa yake
"Duk da haka nayi da na sanin kasancewa ta tare da ita,fa'iza......." Hannunta ta dora saman bakinsa qwalla da digar mata
"Matarka ce bana son jin komai,don Allah ka tafi ya mukhtar kaji,ka tafi bacci nakeji" da gaske take fadin maganar saboda haka ya saketa ya miqe a sanyaye ya fice,tun tana kukan bilhaqqi har ta koma yi qasa qasa,da haka bacci ya sureta.

        A firgice ta farka sakamakon hasken rana da ya dalle ta wanda ke alamta mata gari ya waye sarai,da sauri ta dubi agogo,har qarfe goma na safe,gabanta ya fadi data tuna cewa babu abinda yau tayi a gidan,a hankali ta miqe ta isa falo ta yaye labulen window dinta ta duba dakinsa,a kulle yake da muqulli tana jin mawuyaci ne idan fita kasuwa ba kenan,dawowa tayi uwar dakin ta tsaya gaban madubi don duba idanunta,bata so ta fita har fa'iza ga fuskanci tayi kuka ko ta fuskanci taji kishi ko ta gane abinda ya faru daren jiya cikin gidan har ta raina ta,hudubar anty dije ce boye duk wani abu da zai sa ta gane logonta,bare ta riqeshi ta dinga musguna mata da shi,fuskarta fayau haka ma idanun sun koma babu kumburin,saima haske da suka dada yi,hijabinta ta cire ta daura dankwali saman kanta ta fice tsakar gidan.
Chapter 11 · 0% Book details