← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 226

Sashe 69

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

      Ga mamakinta suna fitowa ta tadda abdur rahman tsaye qofar gidan,qofa bude yana kallonta,ta fuskanci me yake nufi saboda haka babu musu ta shiga,zainab ma ta bude gidan baya ta shiga,sau daya rufe sannan taga ya shiga gidan,baifi mintina biyar ba ya fito suka tafi,har suka je gida baice uffan ba,ya saukesu ta masa godiya ta wuce,tana shirin kwanciya saqonshi ya shigo wayarta,saqo ne dake dauje da kalamai masu nuna tsantsar qauna,da nuna ba za'a rabu da abinda ake so ba,tana gama karantawa ta goge ta kwanta,tana ayyana ta kusa nesa da dukkan wadan nan rudanin.

  ******   *********   *****

   *BAYAN KWANA BIYAR*

   Anty dije suka iso kano ita da yaran da mai gidan baki daya,gidansu na da anan suke masauki duk sanda suka zo din,bata samu zuwa gidansu sumayyan ba sai bayan kwana biyu da zuwan nata.

       Sha daya da rabi na rana suka iso baki dayansu,sun sauya baki daya daga anty dijen duka sunyi kyau da wata irin gogewa,kana ganinsu kasan kwanciyar hankali da hutu sun samu wajen zama,duk suna falon mama,maman da anty dije suna hirarsu ta zumunci,yaran duka sun kewaye sumayya suna ta bata labari,mutuniyar tata minar na zaune dare dare kan cinyarta,laila ce ta soma tambayar Abdallah wanda hakan ya janyo hankalin anty dije
"Nima fa ban ganshi ba" injita,murmushi mama tayi
"Mu zai nunawa 'yan ubanci ai,tunda yahanasu ta daukeshi kinga yaqi dawowa,uwar ma taje da kanta yaqi biyota" haba anty dijen ta riqe tana dariya
"Yanzun haka zamu tafi ki barshi a kano?" Tayi maganar ta sigar tambaya tana duban sumayya,dariya sumayya tayi
"Wai da gaske anty sai na bikin?,to idan naje ma kwana nawa ne zan dawo ai ba dadewa zanyi ba" dubanta anty dijen tayi cikin mamaki
"Wai meke damunki da baki son abuja ne kamar ana gutsurarki" tabe fuska tayi kamar qaramar yarinya
"Garin ne ni banjin dadinsa anty haka kurum" kanta ta dauke daga kan sumayyan tana cewa
"Sai kiyi kuma,mu me ya cimu?,"
"Yaya asama'u(sunan mama na asali)Allah yasa dai malam na gari,don tun yau nakeson sanar masa da sumayyan zan tafi,na lura kamar ku din a nan bata samun kwamciyar hankali da nutsuwar data dace,dama can baya kun yimim alqawarin bani ita kuma aure ya fado mata da wuri,kinga yanzu sai a cikamun alqawari na"dariya mama tayi tana cewa
"Malam yana nan ya fita ne taron bude wani sabon masallacin juma'a da aka gina,amma nan da biyar ko shida na yammaci zai dawo"
"To Allah ya dawo dashi lpy,ina nan har ya dawo"
"Amin" inji mama.
"Momy,wai anty da ita zamu tafi?" Khalipha ya fada cikin murna da doki yana dora hannunsa hannunshi kan cinyar anty dije
"In sha Allahu" ta bashi amsa,
"Yeeeeeyyyyyy" yaran suka sanya ihu baki daya har suka sanya sumayyan ta tuntsire da dariya duk da yadda jikinta yayi sanyi da zancan tafiyar tata.

Anty dije ko bata tafu din ba har sai da malam ya dawo,sanda ta tuna masa tsohon alqawarin da suka mata dariya ya saka sosai,don shi sam ya manta da maganar ma baki daya,shi kansa cikin yaransa yana son sumayya,tana da baiwa da wasu halaye na daban da ba kowa ke da su ba,amma babu yadda ya iya,tilas ya cika alqawarin da ya dauka duk da cewa tsoho ne,yace ya basu sumayya halak malak indai suna so,da yake gaban alhj farouq akayi shima yaji dadi sosai,har da shi a godiya,don shima yasan halayen sumayyan,ya tabbata ko zama tayi cikin yaransa zasu qaru da ita,hakanan zata taimaka ma matarsa zasu dinga ganin nasu na gida a kusa da su saji dadi.

Sanda labari ya iske sumayyan sai jikinta yayi sanyi saidai a fuska bata nuna komai ba ko don darajar yaran dake ta munnar zata koma gidansu,ya zata iya rabuwa da mahaifarta?,inda ta taso tayi wayo ta gabatar da rayuwarta baki daya?,inda anan dukkan wani tarihi na rayuwarta ya samo asali ya kuma kafu?,zata bi anty dije amma bata jin zata iya zama a garin din din din,zainab ce ta zungureta tana fadin
"Wai nikam wacce iri ce ke yaya sumayya don Allah,ina ma nice anty dihe tace zan koma gurinta,wallahi da kinga yadda ake abu" harara ta watsa mata
"Yanzun ma ki gayawa Abdulmalik kin fasa aurensa sai kizo ayi musaya da ni ke ki bita ni na zauna" dariya ta tuntsire da ita,tana son taga yaya sumayyan tata na masifa,sai tayi mata wani iri saboda bata saba ba ba al'adarta bace
"Bazan iya ba wallahi,ni da abdul malik jini da hanta ne"
"Madalla" ta fada taba juyawa taci gaba da abinda take cikim zuciyarta tana musu kyakkyawan addu'a da fatan dacewa da rayuwar aure mai inganci ba irin tata ba data kasance farkonta zaqi,qarshenta madaci wanda har yau take fama da taunarsa dacin bai bar bakinta ba,har yau duk farincikin da take ji idan ta tuna mukhtar sai ya gushe,duk sukunin da take ciki idan ta tunashi sai ya tarwatse,ko a yanzun data yi wannan tunani sai da hawaye suka biyo kuncinta.

To sati daya anty dijen ke da niyyar yi,siyayya dama zasuyi kasancewar ba zasu sake dawowa kano ba sai bayan qaramar sallah,haka ta dinga zuwa tana daukan sumayyan suna shiga kasiwa siyayya,a kwanakin baki daya sumayya bata zama bata da sukuni,hakan ya sanya abdur rahman ko lukman babu mai sukunin ganinta,saidai kullum ta Allah saqonninsu na tafe ta ma'adanar saqonnin na wayarta,wani lokaci har da tarin misscall na kiran da bata daga ba,taso sumayyan ta dauki kayayyaki amma tace bata buqatar komai,data matsane ta yanki sababbin yadin hijabai da zasu kai mata har qasa ta bayar a dinka mata,anty dijen nata tsokanarta mai hijabai bqta ce komai ba ta dai yi dariya don ita a yanzun babu shigar dake mata dadi irin ta hijaban.

Ana ya jibi zasu tafi bayan sun dawo daga kasuwa,suba zaune falon anty dije sumayya na tayata hada kaya wayar anty dije daga hannunsu laila ta dauji ruri,da sauri lailan ta sauko saga kan kujera ta nufi anty dijen tana cewa
"Hajiya mama ce take kiranki"
"Kamar kuwa tasan suna raina" anty dijen ta fada tana karbat wayar,sumayya nata shirya kayan ita kuma na wayar har ta kammala tana fadin
"Komawa kasuwa ya kama mu fa gobe sumayya" tana zuge zif din jakar matafiya ta trolly ta dago kai ta dubeta
"Naji kamar dazu kince kin kammala siyayya ko kinyi mantuwa ne?,nikam ma gaji da shiga kasuwan nan wlh kinsan ban taba shiga kasuwa haka ba?"tana zama gefan kujera tace
"Nima kaina na gaji sumayya,amma hajiya mama ce tafi qarfin komai gunmu,ko abban laila sai da ya soma qorafi jiya wai kasuwannin kano zamy siye ne baki daya har yau bamu gama siyayya ba?" Ta qarashe tana dariya sumayya na tayata
"Amma idan nace masa hajiya mama ce nasan bazai hana ba,ki kwana nan kawai gobe sai muje,atamfofi take so supers zatayi barka"idanuwa sumayya ta zaro
"da super zatayi barka?"murmushi anty dije tayi
"hajiya mama ce fa?,akwai yin harkar girma" shiru sumayya tayi sai data gama ta ture jakar gabanta sannan tace
"Nikam bazan kwana a nan ba,ni da ku ganni sai randa zamu tafi ku biyo daukata,zanje na qarasa jin dumin tsohuwata" hararata anty dije tayi
"Kome zaki fada saidai ki fada an riga an bamu ke kuma kin badu,so kike kice zaki ji duminta kafin jibi mu rabaki da ita ko?" Dariya ta qyalqyale da ita
"Ni ba haka nake nufi ba anty"
"Koma hakanne gobe da yamma kizo muje"
"To" ta amsa tana dan miqewa saboda bayanta da ya qage,kiran abdur rahman ya katse mata hutun nata,da kamar ba zata daga ba sai kuma ta kasa
"Gimbiya sumayya,ni yanzu lallabawa nake,naga alama ganinki sai an cike foam"
"Baka fara cike foam din ba ka dai kusa ka fara cikewa" ta fada a zuciyarta,a fili kuwa sai tayi 'yar qaramar dariya data sanyashi lumshe iso saboda yadda sautin ya ratsashi
"Ko kadan,sabgogi ke sukayi yawa,ina tare da anty dije kasan jibi zata koma"
"Ayyah,amin gaisuwa gurinta don Allah,naso in shigo mu gaisa na fara kamun qafa saidai yanzun haka ina sokoto,baki ma sani ba saboda baki damu da ni ba" murmushi kawai tayi mishi,a ranar ta sake masa sun taba hira,hakan ya masa dadi sosai,itama sai ta danji dadi a ranta,saboda rabon tayi hira haka da wani har ta mance,sanda ta gama taga misscall din lukman kusan goma,bata bi ta kaiba ta kashe wayar,anty dije ce ta dinga tsokanarta kodai ta barta kanon kawai,murmushi tayi wanda baikai zuci ba,don har ga Allah bata son ayi mata maganar aure,sai magariba sannan ta koma gida.

IDAN NA SAMU LOKACI WATAQIL ANJIMA KU SAMU WANI,IDAN KUMA KUNJI SHIRU TO BAN SAMU DAMA BA.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

5⃣5⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wa lillahi Aaqibatul umur*

*qarshen al'amari mallakar Allah ne*

__________________________________

*WANNAN SHAFIN SADAUKARWA NE GAREKI*

*UMMU RAMLAT(meena slimzy novel group)*

Qarfe sha daya na safiya su Anty dije ta qaraso da motar su wadda drivern su ne zai ja motar kamar yadda suka zo,alhj farouq tuni shi ya riga su komawa saboda kira da ya samu daga wajen aikinsu.
Chapter 69 · 0% Book details