← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 226

Sashe 118

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

         Yau da gobe kayan Allah,sannu a hankali kwanaki ke mirginawa suna wawasar kwanukanmu a duniya,da kuma kwanakin dukkan wani abu da muka sanya masa lokaci,zuwa yanzu su sumayyan na da watanni takwas cikin qasar ta uk,ba qaramin karba qasar ta yiwa sumayyan ba,bugu da qari kuma ga nafisa daga gefe data kafe kai da fata zata sauya sumayyan malam din zuwa wata sumayyan ta daban,sumayyan uk,qudirinta kuwa ya karbu,a yanzu idan kaga sumayyan zaka sha mamaki,komai nata ya sauya,wani irin kyau da da can yake boye a yanzu ya soma bayyana kansa,hutu jin dadi da kwanciyar hankali suma na bada tasu gudun mawar,hatta da anty dije kan kalleta mafi yawancin lokuta,dadi take ji cikin ranta da ta sanadiyyarta sumayyan ta soma samun canjin rayuwa,ashe da can damuwa rashin kwanciyar hanakali da tension ita ta tasamma kassara sumayyan da gurgunta tunaninta,a yanzun kai baka ce sumayya bace wadda ta taba aure,'yar shekara ashirin da biyu har da yaro ba,sai kayi zaton tana cikin shekararta ta sha shida ne,tun da can Allah ya bata sanyin murya nutsuwa da iya magana,sai abun ya sake zame mata ado,zakayi zaton daga wani babban gida ta fito.

       Gefe daya karatun ta ya kankama haiqan,turanci ba damuwarta bane a yanzu bare hausa,mai gaba dayan larabci dama ya jima da zama kan harshenta tun tana qanqanuwarta,tana daya daga cikin zaqaquran ajinsu a yanzu,zaka yi mamakin yadda harshenta ya karye,tana karbar karatunta da kyau,tuni wata daya baya ta kammala makarantar koyon girki da mu'amalar yau da kullum,ta fita da cetificate mai kyau,a yanzu kusan anty dije ta zama 'yar kallo ta fannin kitchen,kowacce rana da kalar abincin qasar da sumayyan zata girka,uncle farouq da taya bera bari shike basu kudi suje suyi siyayyan kayan da za'a buqata a ranar tunda shi bai sansu ba,laila ce 'yar rakiya,kai na rawa zata bita suje,zuwa yanzu ta sake tana iya zuwa gurare wadanda ke kusa da su ba nisa can ba,idan kuma suka so yin nisan nafisa ce jagora,zata debesu guri guri da yake ita din tamkar 'yar gari ce a garin,ranar haka zasu wuni a waje,sau tari sumayya na noqewa saboda ganin yadda nafisan ke kisan kudi idan sun fita amma taqi bata dama,duk abinda ta siyawa kanta sai ta saiwa sumayyan duk tsadarshi,dole tayi surrender ta tabbatar Allah ne yayi wannan hadin tsakaninsu.

*******     ********    *******

     Kamar ko yaushe yau ma tafe suke su shida,nafisa,sumayya,laila,khalipha,sai minal da kuma khalid dake riqe a hannu,ganyayyakin abinci suka sayo daga can suka wuce suka sha coffe a wani gun shan coffee dake daura da gun,zasu hau bus nafisa ta hana,a qasa suka dinga takowa tana nuna musu gurare tana musu bayani,sosai yanayin ya yiwa sumayya dadi qwarai,murmushi kawai ke tashi a fuskarta,sanye take da dubai abaya wadda tayi mata cif a jiki,ja ce mai dan turuwa kadan,bata yi amfani da mayafin rigar ba saboda yayi mata qanqanta,sai ta yafa wani medium vail dark blue wanda ya lullube har kafadarta.

      Idan ka kalleta dole ta burgeka,murmushin dake tashi kan fuskarta kawai abun sha'awa ne,kayan sun haskata matuqa,khalipha da minal da laila sunyi gaba abinsu suna ta tsalle tsallensu laila na qoqarin saitasu,ita da nafisan ke ci gaba da takawa a hankali suna hira tana bata labarai.

       Maganar da nafisan ta fada ta sanyata juyawa tana kallonta dariya ta kubce mata,sam bata lura da gabanta ba ji tayi ta bangaji abu,taga taga tayi zata fadi murya a sama taji ance
"Hey!" Tare da riqo hannunta,tashin farko ta gigice,abubuwa biyu cikin lokaci daya suka hargitsa ta,walainiya idanuwanta suka shiga yi zuciyarta na bugawa,man ne,mustapha,sanye cikin three pieces slim fit suit navy blue wadanda sukayi matuqar yi masa kyau tare da fidda sigar kyawunsa,idanuwansa saye cikin sun glasses,ya kafeta da tsinin idanuwanshi duk da bata iya hangosu fes amma tana ganin alamunsu,jikinta ya soma rawa sanda ya saketa sai ta sake tafiya zata fadi nafisa ta tarota tana fadin sunanta,tsaye yake qyam yana dubanta,duba mai dauke da bacin rai,tuni baturen dake tare da shi ya kammala tsince wayoyinshi da suka zube qasa yana masa sannu cikin harshen nasara,dauke idanuwanshi yayi ya maida kan wata rantsatstsiyar baqar mota data faka a gabanshi,qaramin tsaki ya ja sannan ya juya cikin takunshi ya nufi inda motar take,da alama dama ita yake jira,baturen ya mara masa baya cikin hanzari ya bude masa mazaunin baya kafin shi kuma ya shiga gaba,jan nafisa ta soma yi jiki na rawa tana waiwaye har suka shige motar suka tayar suka bar wajen.

Waiwayowa tayi inda nafisa ke tsaye bayan ta cikata,sai ta tsinci nafisan na kallonta
"Waye wannan sumayya?" Ta jefo mata tambayar ba tare da ta shirya ba,boyayyar ajiyar zuciya ta saki gabanta na bugawa,hakanan Allah ya dora mata wani tsoronsa
"Nima ban sanshi ba" ta fada tana ci gaba da jan nafisan don su bar wajen,batasan me zata ce mata din ba,saidai baki daya gwiwoyinta sun sare kamar an doke mata su,kamar qafarta ba zata iya kaita gida ba
"Taya zaki ce baki san ko waye ba bayan na shinshino alamun sanayya tattare da ke?"
"Kiwa Allah kada ki qara tambayata,don ban sanshi din ba"
"Ala kyauta" nafisan ta fada ba tare data sake tambayar tata ba,haka suka isa gida tamkar kurame.

Cikin sanyi jiki ranar baki daya ta wuni,girkin ma data fita ta sayo ingredient din bata iya yinshi ba,ta cewa anty dije bata jin dadi,sai ta koma daki ta kwanta kawai lamo,bata fadawa anty dije ga wanda ta gani,to tace mata me?,tace taga wa?,meye hadinta da su da zata sanar mata haduwarsu?,ta tabbata su laila basu ganshi ba tunda bata ji sunyi maganarsa ba.

******* ****** ********

Sannu sannu kwana nesa,yau da gobe kayan Allah,sai gasu sumayya sun fara hada komatsansu waje guda,wasu suna aikowa da su nijeria wasu kuma suna faka su waje daya,wata daya ne ya rage musu wa'adin zamansu a qasar ya qare,wato sati hudu zuwa biyar masu zuwa zasu bar qasar,tuni nafisa ta soma qaguwa suma su koma gida,ta fuskanci lallai idan su sumayyan suka barsu qasar sam ba zata ji dadin zama ba,zulaiha ce abar tausayi,wadda Allah ne yasan ranar komawarsu,zata yi kewa ba kadan ba,saidai tilas ta haqura.

Hutun sati guda uncle farouq suka samu,hakan ya sanya suka zauna sukayi dukkanin lissafinsu na abinda zasu saya wanda zai musu amfani,ranar da daddare suka shirya zuwa wani katafaren mall wanda ke saida dukkan wani abun buqata,kama daga mai qaramin kudi zuwa mai babban kudi,duk wani abu na amfanin dan adam,sutura zuwa abinci da abunsha suna saidawa a wajen,basa bude gurin sai qarfe shidda na magariba har zuwa tsakiyar dare.

Uncle farouq ya kira ya buqaci taxi da zata kaisu ya bada adress dinsa,cikin mintuna qalilan ta iso,shine zaune a gaba shi da minal,su kam suna baya,hira suke sosai cikin motar,wanda ita bata ma san me suke cewa ba saboda tana amsa wayar abdur rahman ne,bayan ta kammala ta maida wayar jaka,dubanta anty dije tayi cikin salon tsokana
"Nafa lura kwanaki biyun nan ana dasawa da abdur rahman,ko yaushe cikin waya,ko dai da shi za'ayi ne?" Kunya ta bata saboda uncle farouq dake cikin motar,sai ta kasa magana ta saki murmushi kawai,dariya ya danyi yana daga gaban motar yace
"Allah dai ya zaba abinda yafi alkhairi kurum"
"Amin" cewar anty dije.

Ta kai kimanin aqalla minti ashirin tana nemansu cikin katafaren shagon bata gansu ba,ta duba anty dije da uncle farouq babu su ba alamunsu,tuni ta soma tsurewa,ta ajjiye kwandon dake hannunta ta soma laluben hanyar fita nan ma ta kasa ganeta,qwalla ta cika idanuwanta jikinta ya soma rawa,ina yaran sukayi?,ina su anty dijen suke?,idan ta rasasu ta yaya zata iya komawa gida?,wannan tunanin ya sanyata qara sauri,data fita daga wannan bagaren saita fada wancan saidai ko qyallinsu bata gani ba.

Wani irin burki ta taka wanda ba don tayi saurin dakatawa ba babu abinda zai hana su yin karo da juna,dubanta yake kamar yadda take dubansa,kamar ko yaushe fuskar nan a murtuke babu walwala,kai kace bai taba dariya ba a duniya,gabanta ya shiga faduwa kamar kullum,ji take kawai tata ta qare,ta rasa da mutumin da zata hadu sai da wannan?,kamar yadda al'adarsa take,saye yake da suit qirar company dolce anda gabbana baqaqe,hannayensa saye cikin aljihunsa kai kace babu abinda yazo siya,daga ita har shi babu wanda ya motsa,ita bata wuce ba tana kallonshu,yayin da shi kuma ke duba turarukan dake jere reras yana karanta sunayensu daya bayan daya,tuni hawayen da take adanawa suka soma samun hanya da zuciyarta ta raya mata su anty dijen sun bace mata fa,wata qila ma sun bar mall din suna nemanta suma,tattaro ragowar qarfin ta tayi da niyyar rabewa ta wuce don yana tsaye ne tsakiyar hanyar,ya raba hanyar gida biyu.

Hannunta guda daya taji an riqo,wata zabura tayi ta waiwayo qirjinta kamar zau fado,taushi da laushin tafin hannun nashi na ratsa jiki da jijiyoyin jininta,bai ko dubeta ba ya soma jan hannun nata,bata da wani qwarin gwiwa da qarfin da zata qwace,ko wacce gaba ta jikinta an zare mata laka,abu daya zuciyarta ke raya mata,yau tata ta qare,don wannan mutumin babu alamu na imani ko tausayi tattare da shi,Allah ne kadai yasan me zai aikata,hawayenta suka qaru tana biye da shi tamkar raqumi da akala.
Chapter 118 · 0% Book details