← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 226

Sashe 37

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Ko kallon abincin bata yi bare ta kai ga ci,ko ruwa bata iya kurba a bakinta,ki da yaushe tana kwance idanunta rufe kamar mutum mutumi,sai da malam yazo shi daya ya shiga dakin sukayi magana ta tsawon mintina kusan ashirin shi da ita sannan aka fara samun salama,takan karbi duk abinda aka bata taci koda zata yi amansa,hakan ba um ba um um sai zubda hawaye tamkar qwayar idonta zai tsiyaye,kusan kowa tausaya mata yake tare da girgiza da al'amarin,duk da cewa har yau malam kawai ta iya yiwa bayanin abinda ya faru shi kuma ya sanar da abubakar da umma sadiya,sosai umma sadiyan ta fusata qwarai tace sam ba zasu yarda ba tilas su maka mukhtar a kotu shi da zainab din baki daya,baisan halin sumayyan bane?,yarinyar da kusan shi ya qarasa yi mata tarbiyya,malam ne ya hana yace sam hakan baida amfani,tunda koda sun aikata hakan ba zasu iya maida hannun agogo baya ba,ba zasu iya gyara lamarin ba tunda abinda zai faru ya riga da ya farun,da wannan zancan suka rufe batun suka maida hankali wajen kula da lafiyar sumayyan.

         Da wani yammaci sumayyan na zaune jingine da bango,bata jima da yin wanka ba tana sanye da atamfa,mamanta ne da zaina da halima sai khadija da hajara cousing dinta zauneba dakin suna dan taba hirarsu,sallama akayi suka kalli bakin qofar baki daya suna amsawa,haj salamatu ce wato umma mahaifiyar abdur rahman ita da qanwarsa bahijja,duk da quncin da zuciyarta ke ciki saida sumayyan ta washe haqora ta sake gyara zama tana mata sannu da zuwa.

      Cikin mutuntawa suka gaisa su halima suka gaidata tare da miqewa suka fice don zuwa karbo canjin ruwan da suka siya cikin shagon asibitin a dazu
"Sannu sumayya ya jiki?,ya kuma mukaji da wannan abu" umma ta fadi fuskarta dauke da alhini da tsantsar tausayi,qasa tayi da kanta hawaye na zirarar mata
"Alhamdulillahi umm" ta fada muryarta a karye
"Ki yi haquri kan haquri sumayya,duk da na sanki dama ke gwanar haqurin ce,haqiqa Allah ba azzalumin sarki bane,ni sam bansan meke faruwa ba,abdur rahman da bahijja dai sunje zasu miki sallama da yake zai sake koma wa jami'atu ummul quraa zai hado masters dinsa,to da suka dawo sai suka ce sun tadda gidan naku a kulle,babu wanda ya kawo komai don har mukhtar din ya kira ya masa sallama baice da shi komai ba,sai jiya da safe saiga mukhtar din yazo gaida kawun nasa,a nan yake gaya masa duk abinda ya faru,wallahi mama ina jin batun na tabbatar sharrin kishiya ne da asiri ke dawainiya da yaron,cikin kwana uku tal da faruwar lamarin kada kiso kiga yadda ya fige ya lalace,babban abun haushin ma duk yadda muka so tunatar da shi wace sumayyan wallahi yaqi fuskanta yaqi gane wacece ita,har yau da haushi da zargin abun a ransa,amma babu komai mai gaskiya yana tare da Allah,kuma in sha Allahu Allah zai miki KYAKKYAWAN SAKAMAKO".

       " babu komai ai umma,kowanne bawa da irin tasa QADDARAR,kuma shi aure rai ne da shi,da zarar zaman ya qare sai kiga ko babu sanadi an rabu".hawaye ne kawai ke ci gaba da tsiyaya idanun sumayya,tamkar ta zura a guje haka take ji,bata qaunar jin duk wani zance da ya danganci mukhtar din,tunda mukhtar ya yi mata haka a duniya yaqi bata dukkan yarda da amincinsa bayan yasan wace ita to babu wanda bazai iya cin zarafinta ya ha'inceta ya wulaqanta ta ba.

     Maganganu masu sanyi umma ta dinga fada mata masu kwantar da rai wadanda suka sauke kaso mai yawa na bacin rai baqinciki da firgicin da take ciki,sosai taji sukuni cikin zuciyarta,sai wajejan la'asar sannan umma ta musu sallama ta tafi bayan ta ajjiyewa sumayyan dubu uku tace tasha lemo.

**** ***** ****

Cikin kwana biyar jikinta yayi sauqi sosai,hakan ya sanya likita ya bata sallama tare da gargadarta ta rage damuwa ta kuma kula da lafiyarta.

Sosai take samun kulawa daga dukkan wani da yake cikin gidan nasu,kowa haba haba yake da ita,dakinta daban wannan karon malam yasa aka ware mata don kada su takura mata,amma duk da hakan wani lokaci cikinsu haliman take kwana,ganin yadda kowa ke son farincikinta ya sanyata warewa,tayi qoqari qwarai wajen fidda damuwa daga ranta duk don saboda su,duk da abadini hakan ba mai yiwuwa bane gareta.

Watanta guda da komawa yayanta abubakar ya siya kata foam na wata makarantar koyon sana'o'in hannu na mata don rage mata kewa da dauke kaso mafi tsoka a cikin lokacinta wanda hakan zai taka rawa matuqa da gaske wajen hanata tunani ko damuwa,kama daga dinkin labulaye,zannuwan gado,suturu kayan sawa,carfet zuwa saqa,hadin su humra,sabulu,man shafawa man kitso da sauransu dukka suna koyawa,sosai take jin dadin makarantar hakanan ta maifa hankalinta sosai tana dauke duk wani abu da aka koya mata,har ya zuwa lokacin ba'a debo kayanta daga gidan mukhtar ba din baki daya ta tsane su ta tsani ganinsu,hakan ya sanya umna halima tace idan an tashi daukosun a wuce da su gun masu saida furniture a siyar kawai.

*ZAKARAN DA ALLAH YA NUFA DA CARA*

Kusan a yanzu ya zame mata al'adarta,takan kwashi lokaci mai tsawo kwance cikin nazarin da tunani kafin bacci ya samu nasarar daukarta.

Yauma kamar kullum tana kwance ruf da ciki,duk da cewa dakin babu hasken fitila amma idanunta a bude suke tar,kwanyarta na aikin sarrafa tunane tunanen dake bijiro mata daya bayan daya.

Zumbur ta miqe sakamakon motsin da take ji can qasan mararta,wanda wannan shine karo na barkatai da take jin hakan cikin wannan satin,sau tari takanyi kasaqe tana sauraran motsin har zuwa sanda zai lafa mata,hakan ce ta faru wannan karon,bayan motsin ya lafa sai ta koma ta kwanta rigingine tana mai lumshe idanunta,tana tunanin gobe zata sanarwa mama don tana zaton ba lafiya saboda bata taba jin irin hakan ba.

Qarfe takwas na safe tana tsakar gidan tana shara bayan ta kammala duk wani aiki na gidan qannanta sun wuce islamiyya wadda suke shiga tara zuwa biyat da rabi na yamma,tunda tazo ta koma al'adarta ta da,tun kafin tayi aure ita ke hidimar gidan duk da qarancin shekarunta a lokacin,sai abinda yafi qarfinta ne kawai wanda ba zata iya ba take barma maman nata shi,to hakan ce ta kasance wannan karon,duk da maman na hanata kai bama ita ba har su haliman idan suna nan basa yarda tayi komai,amma takan qiya saboda hakan na matuqar debe mata kewa da sata jin qwarin jikinta.

Tana daga rumfarta zaune amma tana iya hango duk abinda ke faruwa cikin tsakar gidan kasancewar labulen falon a dage yake don ta samu iska ta shiga inda take,da idanu take bin duk wani motsi na sumayyar da kallo,tausayi da qaunar yarinyar tata na ratsata,sai kima wasu sauye sauye da take ci gaba da gani dangane da ita,har sai da ta kammala komai sannan ta shigo falon
"Wash" ta fada wanda hakan ya sanya maman juyawa ta kalleta
"Lafiya dai ko?"
"Lafiya lau,kawai gajiya nake ji da kasala mama" shiru ta danyi sannan ta sake dubanta,tunani ne fal cikin zuciyarta amma bata aminta da abinda zuciyarta ke kawo mata ba don bata jin hakan zai yiwu
"Bakijin komai a jikinki sai kasalar kawai?" Dan shiru tayi sannam tace
"Ummmm,wani lokaci inajin motsi mama har nace zan gaya miki ko zanje asibiti,sai kuma naji motsin ne kawai baya ko ciwo cikin nawa" ta fada cike da quruciya dake nuni da rashin sanin abinda ke faruwa da ita
"Tun wajen yaushe kike jin hakan?" Ta tambayeta tana dubanta da saka ran jin amsa
"Eh wajen kwana goma kenan"
"Lallai kuwa ya kamata mu koma asibiti" maman ta fada tana jinjina kai cikin qarafafawa wanda hakan ya bawa sumayyan tsoro,take hantar cikinta ya kada,kodai wani babban ciwo ke shirin samunta?,gaza yin shiru tayi saboda tsabar tsoro
"Mama!......bani da lafiya ko?" Ta fada kamar zata saki kuka,murmushi ta saki don kwantar mata da hanakali,bugu da qari itama bata da tabbas din abinda take zato kansa
"Lafiya lau kike,dauko min wayata na kira malam in sanar da shi idan yaso sa muje kiga likitan"
"To" ta fada jikinta a sanyaye qirjinta na bugawa duk da maman tace mata lafiyarta lau,dakin gadon maman ta shiga ta fiddo wayar ta dawo ta miqa mata sannan ta samu gefe ta koma ta zauna.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

3⃣2⃣
_________________________

*Bismillahir rahmanir rahim*

*wa iyyamsaskallu bi durrin fala khashifa lahu illa huw,wa iy yuridka bi khairin fala raadda li fadhlih,yusibu bihi man yasha'u min ibadihi wa hul azizul gafur*

_"idan Allah yaso ka da cuta(lalura,abubuwa marasa dadi)babu wanda zai yaye maka face shi,idan kuma ya soka da alkhairi babu wanda ya isa ya maida falalarsa,yana sowa ga wanda yaga dama cikin bayinsa,haqiqa shi madaukaki ne mai gafara"_
_____________________

       Cikin abinda duka bai wuce awanni biyu ba isar su asibitin da shiga dakin ganin likitan,umartar ta yayi da tahau wani dan gado wanda kusa da shi na'urar daukar hoton ciki ne.

       "Allahu akhbar" shine abinda likitan ke fadi yana jinjina kai tare da girmama iko na ubangiji,yaro ne kwance cikin mahaifarta ga motsi nan yana yi ga bugun zuciyarsa da komai,dukkansu ba wanda idonsa bai gani ba daga sumayya har mama,mamaki fal zukatansu tare da girmama lamarin buwayi gagara misali,sai da ya kammala komai har EDD sai da ya duba mata sannan yace ta sauko ya koma kan tebur dinsa ya soma rubuce rubuce.

       Magunguna ya rubuta mata wadanda zasu qara mata lafiya sannan ya bata wasu gwaje gwaje da ya kamata ace a wannam stage din da cikin ke da watanni hudu da sati uku tayi su
"Likita lafiyarsa qalau"furucin ya subuce ya fita daga bakinta jikinta a sanyaye,murmushi yayi yana dubanta
" lafiya qalau komai yake,babu wata damuwa tattare da shi"sai da ya bata amsar sannan kunya ta kamata ta sadda kai qasa,batasan cewa tana bala'in qaunar abinda ke cikin nata ba sai yanzu,wani qwarin gwiwa karsashi da soyayya take ji cikin ruhinta,banu shakka wannan karon tanajin zata iya yaqi kan cikinta a shirye take.

       Basu bar asibitin ba sai da suka kammala duk wani gwaji suka siyi magungunan suka nufi gida.
Chapter 37 · 0% Book details