← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 226

Sashe 104

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Tuni maman ta rigata yin gaba saboda hill shoes din dake qafarta wanda ya sake sauya yanayin tafiyarta,sannu a hankali take takawa,sai ka dauka wani salon tafiya ce ta daban,koko tsabar yanga ce da iyayi ga wanda baisan takalmin ne ya takurata ba,baqar rantsatstsiyar mota ce wadda har sheqi take da daukan ido saboda tsabar sabunta da kyau,ita daya ta rage tsaye a wajen,da alamu dukka an tafi,baya anty mamaan ta bude ta shiga,yayi kyau cikin farin qal din trouser da lallausar short sleeve t.shirt baqa mai adon fari a jiki,wadda ta fidda sirrin hannunshi na tarin gargasa wadda ta kwanta har saman tafin hannunshi,da wani sashi na murdadden dantsensa wanda kana gani kasan ya saba daga qarfe,daya daga cikin abinda ya sanya kenan bai fiya saka kaya masu gajeran hannu ba,black hight top snickers ne a qafarsa,tsintsiyar hannunshi daure da agogon fata na kamfanin gucci mai matuqar tsada da kyau,yadda jikinsa ke fidda wani sihirtaccen qamshin wani turare da mawuyacine ka gane wani iri ne haka motar ki fidda sanyayyan qamshin freshner,komai nasa mai kyau tsafta da aji ne,jin yana niyyar tayarwa ya sanya tace
"Tsaya,akwai mutum daya" a kasalance ya kashe motar,ka kadan baison tuqi da kanshi idan ba kamawa tayi ba kamar irin hakan,qarasowa tayi tana niyyar bude bayan anty maamaa tace
"Koma gaba amira" don tasan halinshi sarai,ya tsani ya dauko mutane su shiga baya baki dayansu,yana alaqanta hakan da sai driver,jin an ambaci sunan amira ya sanyashi juyowa,daidai sanda take daidaita zamanta gaban motar suka hada idanu,idanuwanta suka fada cikin nashi,tashin farko kowanne ya janye idanunshi,qirjinta na bugawa,qamshin turarenshi na ratsa qofofin hancinta,idanunta ta ragewa girma tana duban gaban motar,tana ji kamar ta zura da gudu ta bar motar,wani dabaibayi taji na daureta,kwarjininsa ya mata yawa,tana jin zamanta a bigiren bai dace ba,a kasalance ta sanya hannu zata rufe murfin motar taji kamar muryar laila na kiran sunanta,itace tafe riqe da hannun abdallah da yayi kyau cikin baqaqen suit na yara,sai baqin sau ciki na yara da baqar safa baki daya,suka qaraso bakin motar inda take zaune
"Anty,mami tace na kawo miki shi,kuka ya soma yaqi zama" dubanshi tayi cikin sigar lallashi
"Abdallah,ina cewa na gaya maka tun dazun bazanje da kai ba,ka koma gida ka zauna da su laila,yanzu zan dawo bazan jima ba" qafafunshi ya sa bubbugawa yana sakin kuka sosai kamar wanda ake yanka yana fadin
"Allah ni sai naje" ranta ya baci ganin yadda yake tsala kuka kamar tayi mishi wata uwa,sake lallaminshi tayi baiji na,maimakon haka ma sai ya buge hannun laila ya taho inda take ya shigo sit din da take,abinda bai taba yi ba kenan,yana qarasowa kuwa ta daga hannu ta kai masa mari,ta kuwa sameshi gefan fuskarshi,kafin anty maama ta furta maganar daga bude baki zata yi wata tsawa ta karade motar,tuni laila ta ja baya a tsorace,hannunshi ya miqo inda suke ya janyo abdallah wanda ke sakin kuka cikim jim zafin marin ya dorashi kan cinyarshi yana shafa inda ta mareshin
"U r very stupid,how dare you zaki mari qaramin yaro har haka?,saboda bakisan ciwonshi ba?,bakisan ciwon haihuwa ba?,idan baki iya riqeshi mai ya sanya ba zaki sa a maidashi wajen mamarshi ba,fice min a mota!" ya fada cikin bacin rai da zafin rai,bata ankara ba taji hawaye sun soma layi bisa kuncinta,ji take kamar mukhtar ke mata fadan,me ya fusata ta ta mari abdallah itama bata sani ba,hannunta ta sanya kan mabudin motar ta tura da niyyar fita anty maamaa ta dakatar da ita
"A'ah zauna,kuyi haquri mutapha,baki kyauta ba amiran umman khalipha,saurin hannu wa yaro bai kamata ba,ki kiyaye gaba"
"To maamaa" ta fada ba don taso ba ta koma ta zauna,so tayi ta qyaleta ta fita,wani nauyi taji zuciyarta tayi,tana jin hucin numfashinsu su biyun.

      Luf abdallah yayi kan cinyar mustapha wanda ya zaunar da shi suna facing juna ya rungumeshi cikin jikinshi yana ci gaba da shafa inda tayi marin,ci gaba da kallonshi abdallahn yayi,a hankali ya furta
"Abba!" Sannan ya sake narkewa cikin jikinshi,wani nauyi zuciyarta ta sake yi,sai ta kasa daurewa ta sanya kanta a tsakiyar qafafunta,tausayin abdallahn yasake qara yawan hawayen dake fita a idanunta.

        Bubbuga bayan abdallahn yaci gaba dayi kadan kadan har sai da yaji alamun ya huce,hannun ya sanya gefanshi ya ciro gorar ruwan da ya dauko da niyyar sha ya bude mishi ya saka mai a baki,sai da yasha sosai sannan ya rufe ya maidata gurbinta,ya sake zaro wayarsa ya latso wasu lambobi ya kara a kunnenshi yayi magana a taqaice
"Eh,ka sameni gidan,ka tambaya adress din" ya katse kiran ya ajjiye,tada motar yayi sannan ya ya jata a sukwane abdallah na kwance jikinsa.

        Shiru ne ya ratsa motar ba wanda ya sake magana,sumayya na kife har yanzu kan cinyarta tana qoqarin control din hawayenta,ambaton sunayen Allah ta dinga yi daya bayan daya har ta samu hawayen suka tsaya saidai bata iya dagowa ba har suka isa wajem,anty maamaa ce ta soma fita,tuni tayi gaba saboda suna isowa taji ana nemanta ta lasifiqar dake cikin wajen taron.

       A hankali ta daga kanta ta gyara yafen mayafin dake kanta sannan ta bude murfin motar ta fice,ta gefan ido yake dubanta har ta bace a wajen,gajeran tsaki ya ja,yana jin bazai iya ci gaba da zama a wajen ba,daga yarin yayi ya dubeshi har ya soma bacci,sai yaji tausayinshi ya kamashu,haushinta ya sake qumeshi,cikin zuciyarshi ya dinga masifa shi kadai,bude motar yayi ya saba abdallah a kafadarsa suka koma sit din baya,kwantar da shi yayi sannan ya zauna gefansa.

       Tana tsaye bakin get din gidan jingine jikin motarta hannunta harde a qirjinta,sam wajen bai dace sa tsarinta ba kasancewar a gargajiyance suka tsara komai,bugu da qari ranta a jagule yake,yadda almustapha ke ninka nuna hakin ko in kula da lamuranta,shigowar motar yaso ya dan ja hankalinta kadan,saboda irin motar mustaphan da take mutuwar so,wadda a yau ita taso hawa amma yaqi bata hadin kai,dauke kai tayi daga kallon motar don kada ta zubda ajinta,a dauka 'yar matsiyata ce kamar yadda take rayawa a ranta,ganin fitowar anty maamaa daga ciki shi ya sake maida hankalinta kan motar
"Kada dai ace almustaphan ne?,yazo ya dauko maamaan a ciki amma ni ina matsayin matarsa ya watsan qasa a ido?" Take raya haka a ranta tana qarewa motar kallo,bata jin mustaphan ne,don tunda itama yaqi daukota ya kawota tabbas babu wanda zai kawo koda kuwa iyayenshi ne(a tunaninta),ita kanta motar bai taba hawanta ba sai yau,hakan yasa ta yin kwadayin ace ita ya fara dauka a ciki,mutum ce ita mai son taga tafi kowa,komai a gunta aka fara ganinsa,bata gama wannan tunanin ba sumayyan ta bude murfin motar itama ta fito cikin salon wata tafiya da zaka tsammaci ta yanga ce,saidai tsabar kasala quncin zuciya da tsinin takalminta ya haifarwa da mai kallonta ganin cewa yanga take kai tsaye,wani bala'i ne ya dirarwa zuciyarta,take ta tattara kallonta baki daya a wajen,ci gaba tayi da kallon sumayyan wadda sam hankalinta bai wajen taci gaba da yi har ta wuce,zuciyarta na tsaka da bata shawarar zuwa ta duba matuqin motar don tabbatar da cewa mustapha dinta ne cikin motar ko wani ne daban mai farcen susa ya yaci nasarar mallakar irin motar mijin mata,hutassheta akayi saboda fitowar da yayi ya koma gidan baya yana sabe da abdallah,ta gane yaron,yaron data cuccusawa zagi jiya da daddare saboda ya gyara mata gyaran alwalarta,huci ta soma fitarwa saboda wani zafi da taji qirjinta yana yi,me kenan?,me hakan ke nufi?,ba bata lokaci ta soma takawa zuwa bakin motar.

      Bude murfin motar tayi sannan ta cusa kai cikin motar kai tsaye,hannunshi na saman kan abdallah yaji shigowarta,juyowa yayi ya dubeta sannan ya dauke kai yaci gaba da abinda yake kamar bai santa ba,ta sani sarai bazai tanka mata ba idan in zata shekara matuqar ba ita tayi magana ba,ko ita din tayi bata da tabbacin amsarsa
"Tsakani da Allah ka kyauta kenan man,naci burin hawa motar nan ka watsan qasa a ido amma sai naga ka kawo wasu,har wata banza can ka baiwa damar zama gefanka wanda ni kadai ke da wannan matsayin?" Ta fada cikin son dai daita fushinta don kada ta fita daga hanya ta jawa kanta wani sabon lamarin,ta san duk sabida zancan qarasa karatunta ya sake zame mata wani badadde,ilai kuwa shiru ne ya biyo baya,kishin sumayya data gani yaci gaba da mintsinin zuciyarta
"Wai shin ma meye alqarka da ita waccan yarinyar da har ta samu matsayin daukota cikin motar da koni ban taba shigarta ba,sannan ko kai kanka yau ka fara shigarta?" Bai da ko niyyan waiwayowa ya dubeta bare ta saka ran samun amsa,wayarsa ce tayi tsuwwa ya saka hannu inda ya ajjuyeta ya dauko yana dubawa tare da amsa kiran da ya shigo din
"Bude ka shigo a bude take" ya gayawa drivern nasa a taqaice,dama shi yake jira,sauke wayar yayi still bai dubeta ba yace
"Idan kin gama kina iya sauka ko?"wani abu ya tokare mata wuya,sai ta zuba ido tana kallonshi,sonshi kamar ta lasheshi,haushi kamar ta hafiyi zuciyarta,idanunta ya cika taf da qwalla,cikin rawar murya da son karya lagonsa da kuka ta soma cewa
" ni kake ma haka mustapha?"hannu yayi saurin daga mata wanda dole ta shanye sauran maganarta,sai ta bude murfin ya fice da hanzari,budewa drivan yayi ya shiga cikin girmamawa ya russuna bayan ya zauna ya gaidashi,a taqaice ya amsa mishi,sai da ya tayar da motar suka bar layin suka hau kwalta sosai sannan cikin girmamawa yace da shi
"Ranka ya dade ina zamuje?"
"Maitama" ya bashi amsa a taqaice,baice komai ba ya qara gudun motar suka lula titi.

         Sosai lunching din ya qayatar,ba qaramin qauna iyalin saifullahi suka nunawa amira ba,basu tashi ba sai qarfe bakwai na dare,wannan karon tare da su amiran suka koma,saidai ko kadan bata da walwala,a takure take jim zuciyarta baki daya,hatta da amiran ta lura,amma bata ce mata komai ba saboda ta tambayi anty mama abdallah taje gaya mata abinda ya faru,ana saukesu ta dubi amira
"Kimin afuwa zan wuce gida sai gobe,kaina ke mij ciwo sosai" ba qarya take ba da gaske kan nata ciwo yake mata,sai ta daga kai
"Na miki,Allah ya bada lafiya,ya tashemu lafiya" ta bude murfin motar ta fice.
Chapter 104 · 0% Book details