← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 213 OF 226

Sashe 213

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Washegari suka dunguma gidan halima,baki daya harda yaran yaya abbakar nabila da yusuf da anty meena mamansu,almustapha ya bar mata mota da driver,wanda zai dinga kaita duk inda taje da buqatar zuwa,sanda suka je gidan 'yan barka nata shiga da fita,'yan uwan abdur rahamn,wasu ta sansu musamman na bangaren babanshi tunda sun hadu da mukhtar ta nan wajen,wasu kuma bata sansu ba,duk wanda ya santa a sanda take gidan mukhtar a yanzu da ya ganta sai ya kalleta ya sake juyawa ya dubeta,munagukan da a da suka cusguna mata baki daya jikinsu a sanyaye yake,baki daya sun kasa zama kusa da ita,kunya da kuma ganin yadda sumayyan ta sauya ta zama wata babbar mace duk ta cikasu,itakam bata dauki komai ba,tamkar basuyi mata komai ba haka ta sake musu fuska,abu daya ta sani shine an rige an wuce wajen,yanzu kam rayuwa ta baiwa kowanne certificate din abinda ya aikata,a gidan ta tadda zainab wadda shigowarta kenan,itama tana ta fama cikinta ya shiga wata na tara,sumayya ce nata keda wata bakwai da satittika,dukkansu suna zagaye da 'yar uwarsu,fuskarsu qunshe da farinciki,yaron yana saman cinyar sumayyan tana kallon tsantsar kama tsakanin yaron da babanshi abdurrahman,wato duk bawan da bai yarda da QADDARAR ubangiji ba lallai zai ci wuya cikin lamuranshi,matar mutun kabarinsa,yau ga yaron abdur rahman da halima saman cinyarta,sannan gata dauke da cikin almustapha,mutumin da ko a mafarki bata taba saninsa ba,sanda qaddara ta gindaya kuma ta sanshi din bata taba koda hasashen zama irin na auratayya zai hadasu ba,hira suke sosai gwanin sha'awa,wadda ke nuna zallar hadin kai da fahintar juna dake tsakaninsu,abdallah baya nan yana tahfiz sai azahar zai dawo.

        Sanda taga abdallah masha Allah,wani baragen girma gareshi,ya fara zama wani babba,ga wani hankali da nutsuwa tattare da shi,kana gani kasan ya samu isashshiyar tarbiyya,girma yake abdallan sosai,sanda ya ganta fuskarshi washe da fara'a ya iso gefan cinyarta bayan ya gaida duk wanda ya taras cikin falon yana fadin
"Ammi....ashe kinzo baki gaya min ba?"murmushu ta saki ranta fes,tana sake ganin girma da qimar abdur rahman har da ma haliman
"to ai gashi yanzu ka ganni ko?"
"Ammi kinga munyi sabon baby ko?,wai abba yace da ni yake kama?" Ya fada yana wasa da 'yan hannun jaririn dake cikin safar hannu,murmushi sumayya ta saki
"Sosai ma,kama kai" murmushi ya saki cikin jin dadi,nan ya soma bata labarin makaranta,kai kawai take kadawa tana murmushi,ganin abun take kaman mafarki,kaman ba ita ta haifi abdallah,qaunar yaron nata da tausayinshi suka dinga ratsata,ta kasa daurewa har sai data dora hannunta saman kanshi sanda ya kawo mata ruwa mai sanyi ya ajjiye mata yace tasha ta shafa a hankali ta furta
"Allah ya yi maka albarka kai da sabon qaninka mai kama da kai"
"Amin ammi na", basu suka bar gidan ba sai dare,don sai data jiraci dawowar abdur rahman tayi masa barka,yaji dadin zuwan nata sosai,yayi zaune abinsa a cikisu,sun dan taba hira,wanda yawanci kam abdallah ne,yanayin baiwar da Allah yayi masq,akwai basira da hazaqar karatu qwarai da gaske,wanda hakan ya sanya ake masa tsallaken aji,a hasashensu bazai wuce shekara goma ba zai shiga j.s,kayan barka ta yiwa babyn masu yawa kyau da tsada,akwati guda,sannan ta yiwa halima atamfofi biyu lave biyu,mayafi takalmi da jaka,ta mata godiya itama,saidai bataso godiyan ba,don bata ga abinda zata samu nak duniya 'yan uwanta basu mora ba,sai wajen takwas suka koma gida bayan sun sauke zainab har qofar gidanta suka taho da abdallah,tace bata yafe zuwan ha itama sai anzo mata har gida,tayi murmushi ta amsa mata,ranta fes ta koma gida,baki daya 'yan uwan nata suna cikin rayuwarsu cikin wadata da walwala,ba wata maiatsala a cikinsu,ci sha sutura da muhalli mai kyau kowacce bakin gwargwado ta mallaka.

       Washegari ya abbakar ya sake tareta suka sake lissafi kan dukiyar abdallah,abin ba'a cewa komai sai albarka Allah ke sawa dukiyar,ta nunku fiye da zatonsu,bayan sun gama ta fidda tsaraba cikin kwalaye wanda batasan da ita ba,almustapha ya tanada kawai taga ana sauke mata su,haka yake,mutum ne da idan zaiyi alkhairi bai fiya son a sani ba,zaiyi abunsa ne a boye,shi yasa ko zaman tsarabar bata san da shi ba,na mama daban na malam daban,har da yaya abbakar,saura yace ta baiwa wanda taga ya dace cikin 'yan uwa,sai yammaci ta sake shiryawa suka fice ita,abdallah,yusuf da nabila sai gidan anty yahanasu,ba qaramin murna tayi da ganinsu ba,duk da abdallah dama bai sati biyu abdur rahman bai kai mata shi ba,sun zauna hira nan taji duk abinda ke gudana,auren jamila da fatima Allah yayi za'a yi din,saidai kayan gado nason kawo tsaiko,don ma abdur rahman ya dauke nauyi duk abinda za'a ci ko a sha a bikin har a gama,kowa cikin dangi ya nade hannu,dama can danginsu ba masu riqe zumunci bane,hakan ya sanya ko sanda iyayensu suka mutu ita taci gaba da riqon mukhtar,sosai taji ba dadi,ta dauki nauyin kayan gadonsu jamilan da fatima,kunya da nauyinta suka ishesu,godiya suka dinga mata,itakam bata kula ba,iyalan mukhtar sunfi qarfin komai a wajenta,ko banza abdallah ya hada haduwar da babu rabuwa cikinta,data koma gida sukayi shawara da ya abbakar da malam,ta barwa yaya yahansu gidansu wanda suka zauna a qarshe ita da mukhtar kyauta,tunda yanzu dukiyar abdallah ba komai bane don su barwa yayan gidan,kuka kam haka ta dinga yinshi,har sai data saka sumayya qwalla,tace mata babu komai haka rayuwa dama take,nan yayan ta fara shiryen shiryen komawa,tunda fes yake akan shiha lokaci lokaci ayi gyara yaya abbakar bai barshi haka ha don kafa ya lalace,gidan da suke ciki kuma zasu saka 'yan haya,sumayya tace ta dinga amsar kudin tana buqatunta na yau da kullum da su.

      Suna suka sha hankali kwance,tayi kyau sumayyan sosai,duk wanda ya santa idan ya kalleta sai ya sake dubanta,kana kallon nata zaka san cewa nutsuwa da kwanciyar hankali sun samu muhalli cikin rayuwarta,a nan ta barsu drivanta ya dauketa ya maidata gida wajen mama,tafison ta ganta kusa da ita.

********    ******   ********

      Da safe suna zaune falon mama ita da abdallah,yusra da yusufa da maman suna karyawa,yaran na gabanta baki daya kowa na karyawa tana fama da su,gyarawa wancan kofi gyarawa wancan zama,kayan bacci je jikinta ko wanka bata yi ba,yunwar data ke ji ta sanyata zama karyawa,ya abbakar dake shirin fita shi ya shigo yana fadin
"Mama...ga surukinki zai shigo ki gaisa...da alama sauri yake halan ka wucewa zasuyi" sam bata gane wa ya abbakar din yake nufi ba,kafin ta farga har mama ta masa izini,sai muryarshi taji a bakin falon yana niyyar shigowa.

       Almustapha ne sanye cikin shadda dinkin tazarce,riga da wando,kanshi babu hula sai sumarshi dake kwance tana zuba qyalli,yayi kyau maqura har taji gabanta na faduwa sanda suka hada ido,ko yaya suka danyi kesa da juna na kwanaki sai taji ya sake zame mata sabo,ta soma tattare kofunan yayin da ya shigo ya tsugunna gaban maman yana gaidata,cikin jin kunya irin na surukuta suka gaisa,yana yi yana satar kallonta,ta kasa daga kai ta dubeshi kaman ta nutse,su yusra suka gaidashi yayin da abdallah ya isa gabanshi ya durqusa yana murmushi ya gaidashi,hannu ya miqa masa sukayi musabaha shina fuskanshi dauke da murmushi,yana son yaron sosai cikin zuciyarshi,saidai tarihin sumayyan da yaji yasan bazasu bashi shi ba,saidai yana kan bakanshi ko nan gaba sai ya dauke yaron,yadda yaron ua sake nutsuwa da girma sai yaji dama danshi ne,dama jininshi ne,saidai ko a yanzun yana jinsa cikin jikinsa tunda akwai jinin sumayya tattare da shi
"Tashi kije mana sumayya" mama ta bata umarni sanda almustaphan ya gama gaisheta ua fita zuwa dakin saukar baqi,a kunyace ta amsa,ta koma daki ta zura hijabi ya sake feffesa turare,dui da cewa qamshi ya kama jikinta,ko daga bacci ta tashi baka rasa jin qamshi a jikinta,don sai ta shafe loko da saqo na jikinta da turare ko ba kwananta bane kuwa,ko da basu tare.

       Yana tare da abdallah hannunshi cikin nashi,da alama tambayoyi yake masa kan karatunshi,yana bashi amsa,kuma yana bashi amsa yadda ya kamata don akwai alamun gamsuwa tattare da shi,shigowarta ya sanya abdallan zame hannunshi ya fita ya basu waje,tsaye tayi suna duban juna,ya miqe ya isa gareta ya hadata da jikinsa
"Meye haka?,salon horo ne ko kuwa?,ni zakiyiwa qwalele?,kinsam bazan juri kallonki haka ba ko?" Murmushi ta saka tana ajiye boyayyar ajiyar zuciya,dududud satinsu guda basu ha juna ba amma tana jin kaman sun yi wasu watanni masu dama
"Tsoro nake ji ne?" Ta furta a hankali
"Tsoron me?"
"Ina tsoron ko kazo tafiya da nine ba tare da na shirya ba,in sake tafiya in bar mama" murmushi mai sauti ya subuce masa,sannan ya soma rada mata
"Hakan naso matata,saboda mi kadai nasan yadda nayi kewarki,saidai idan hakan bai miki ba...zan iya zama na jiraki har tsahon sanda zaki gama abinda kike yi,ba abinda bazan miki ba,kinsan saboda me?" Kai ta girgiza alamar a'ah,sai ya juyo da ita suna fuskantar juna idanunshi cikin nata
"Ke din macace ta musamman,mai fifita farincikin mijinta akan nata,mai fifita buqatarta akan tasa,ina sane da cewa,sau tari kikan dauki zabina ki bar naki,kikan gabatar da komai nawa gaban naki,kin maida kanki tamkar baiwa a gareni" sai ya saketa ya durqusa gabanta kan gwiwarsa
"Don me nima bazan zama bawa a wajenki ba?,wannan shine qarshen adalcin da zan miki,Allah ya halicci zuciya da son mai kyautata mata da qi da kuma gudun duk abinda zai munana mata" bata ankara ba qwallar zallar farinciki ta subuce mata cakude da murmushi,jin kanta take tana shawagi a sama,cikin wata duniya wadda take mata kwatankwanci da duniyar SARAUTAR MATA,sai ya miqe da hanzari ya rungumeta ta baya saboda cikinta ya masa shamaki ta gaba,sun jima a haka sannan ya janye yana dauke mata hawayen da yatsansa
"Ko a yanzun ma ka buqaci mu tafi ni mai biyayya ce a gareka" kai yake girgizawa cikin farinciki
"A'ah....kije ki gama shirinki a nutse" kai itama ta girgiza
"Um...um,bazan barka kana jira ba haka noor,kaje ka dawo"
"Na yadda,amma zaki rakani asibiti?,zanje na duba bayin Allah"
"Sam'an wa d'a atan noor" murmushi ya saki kalman ta masa dadi,kissing dinta yayi sosai,sannan yace mata zaya dawo da yammar su je.
Chapter 213 · 0% Book details