← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 210 OF 226

Sashe 210

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Ta gefan hajiya su'ad kuwa baki daya ta gama karance takun almustapha tsaf ta gane komai,son haihuwr yake kaman ya jawo randa yaron zai fito duniya,cikin qanqanin lokaci jikinta yayi sanyi ya mutu baki daya,a hankali ta soma tunanin me yasa bata fahimvi yana son yara ba?,me yasa bata gane ba?,tun daga sanda yace zaya bude gidan marayu da yanda yake nacin zuwa yaci ace ta karanci cewa shi din mutum me mai son yara da son mu'amala da su,kullum kwanan duniya ta kwanta tunaninta shine yadda zata gyara kurenta,ta yaya zata ganta da ciki?,ta yaya zata haihu?,har yau abinda ke sakadar zuciyarta kenan,batasan da wa zata yi shawara ba,anty kubra ce,saidai ta tabbatar cewa fada zata sha kafin daga bisani tace ita din ba ruwanta,da mamarta kawai zata shawarta,saidai maman sunyi tafiya da babanta basa samun zama,lokaci kawai take jira na dawowarta ta zauna susan yadda zasu gyara lamarin.

  ******  *******    ********

       A hankali take tako lallausan carfet dake dakin zuwa inda yake zaune shirye cikin jallabiya ta maza dark brown,ya dora hirami akanshi wanda ya dace da jallabiyar,hannunshi daure da baqin agogo,system ce gabanshi yana rage wasu ayyuka yayin da yake tsumayin fitowarta,zasu je siyayyan kayan baby ne,duk da cewa yana daga gida zai iya fadin duk abinda yake so a hado masa daga dukkan kamfanin da yakeso cikin fadin duniya,saidai yana so su fita su shiga kanti da kanta don sumayyan ta tattaka da qafafunta tayi zagaye saboda lafiyarta.

       Sanye take da abaya peach mai adon duwatsu masu qyalli,peach mai turuwa da mai haske,tayi rolling da wani wadataccen mayafi  dark peach,plate shoes ne a qafarta shima kalar rigar,sosai cikinta ya fito kai kace yau ko gobe ne haihuwar,wanda alokacin baki daya bai wuce wata bakwai da sati biyu ba,a jikinsa yaji fitowarta ya daga kai a hankali yana kallonta,baisan sanda murmushi ya subu ce masa ba,aduk sanda kake da buqatar ganin fara'a qarara kan fuskarshi to yayi tozali da sumayya tana takowa zuwa gareshi dauke da cikinsa,duk duniya shine abu na farko dake faranta masa rai a duk yanayi ko matakin da ya tsinci kanshi,sau tari yakan ayyana me zata haifa cikin ranshi,jikinsa na bashi cewa twince ne musamman idan yana mata awo,saidai bai taba sha'awar duba meye acikinta ba,yace koma meye yana marhaban da zuwanshi,miqeww yayi tsaye ha cimmata a inda take kafin ta qaraso,ya bude tafin hannunshi ya sanya nata yana murmushi
"Wai wannan cikin naki anya babe?"
"Mene?" Ta tambayeshi tana daga gira,tattausan murmushi ya sake mata yana kada kai
"Shikenan.....muga qafar taki,ina fata ba kumburi ko?" Silifa din ta zame tana tayashi duba qafar tare da cewa
"Eh yanzu kam babu,tun jiya bai sake yi ba" gabanta ya durqusa yana mammatsa qafar kafin ya miqe yana cewa
"Masha Allah,Allah ya raba lafiya" dariya ta qwace mata ta dubeshi yanayin yadda ya furta maganar kaman mace
"Amin abu abdallah"
"Ummu abdallah...da zarar kin haihu fa za'a sauyan suna,saboda na zama daddyn yara da yawa,zan koma ABUL AULAD ke kuma UMMUL AULAD" idanu ta lumshe tana jifanshi da wani kallo,sosai sunan yayi mata,tana mamaki idan taju yana larabci,duk da hakan bai rasa nasana da zamanshi cikinsu,kai take gyadawa cike da gamsuwa
"Hakan yayi,amma har yara nawa zamu haifa da suka zama AULAD?" idanunshi yadan zaro yana kallonta
"Ko dozen haka ai sunyi ko?" Dariya ta tuntsire da ita shina yana tayata
"Eh lallai kayi dariya mana,bakusan yadda ake ji ba,a haifa muku kawai" qugunta ya kama suka fara takawa yana bata amsa
"Da gaske wallahi Allah nake miki,ina son naga wannan ya dane min wuya,wannan ya zauna acinya,wancan ya kaman kunne,wannan yana jamim hanci,wannan yamin fitsari wancan yamin bayan gida" dariya sosai ta kamata yadda ya taqarqare yana zuba bayani,har sai sata dafe cikinta tare da dakatawa da tafiya tana dubanshi
"Kace nanny zaka koma kenan cikin gidan?" Giranshi ya dage mata
"Laifi ne?,bakisan ma'aiki yana taya matanshi ayyukan gida ba?,sunnah ne fa" murmushi taci gaba da yi,sai yayi bala'in burgeta ba kadan ba,haqiqa kyawawan halayensa basa rasa nasaba da iliminsa
"Haka ne,Allah yasa mu dace"
"Amin beauty" ya fada yana jan hancinta wanda ya bude ya sake girma,sai ta kwabe fuska tana dubanshi shi kuma yama boye dariyarsa
"Kawai kace mummuna mana ha'an?" Dariyar ta qwace masa baki daya,yasa hannu yana toshe bakinsa,sai ta soma kukan qarya tana buga qafa daya don babu damar yin rigima sosai,riqe hannayenta yayi sosai yana bata haquri kafin yace
"Ba wani yanayi da zaizo wanda zai sanya na kasa ganin kyanki,ko yaushe ke mai kyau ce a wajena,ko da kuwa duka duniya basa gani,bare ma ha wannan ba,matuqar dabi'unki na tattare da ke ko kece sarauniyar munana na duniya haka nakeson abata,kinsan me?" Sai ta kada kai tana sauraronshi
"Dabi'a furuci lafazi da mu'amala sune abu na farko dake tallata dan adam,sune abubuwa dake jefa soyayyar mutum cikin zukatan kowanne bil'adam,koda mutane basu shirya sonka ba,sai kyawawan dabi'unka su rinjayesu su soka,haka kika mamayeni babe,sonki ya cika qirjina" murmushi tayi ta sadda kai,shima fuskarsa dauke da murmushin ya saka hannunshi ya daga kanta
"Ita kunya daure take da imani,idan aka dauke daya dole daya ya tashi haka annabi S A W yace,kenan,duk wajen da kaga babu kunya to tabbas babu imani a wajen,haka wajen da babu imani to kunya tayi qaura,duka kin hada my summy,don haka kin cancanci duk wanu nau'in so da kulawa" yatsunshu uku ta riqe tana dubanshi
"Ummm ummmm,daina fasamin kai"
"Kin taba ji ko ganin na miki qarya" kai ta kada alamar a'a,don bai taba yi matan ba,koda gaskiyar da zai fada zata qona mata rai bai fasa fada din
"Na gode,ubangiji yaci gaba da shiga cikin lamarinmu" sai da yayi kissing goshinta sannan ya amsa da amin
"Muje ki kira su'ad mu wuce ko?"
"To....." Sautin bai gama fita ba suka ji anja tsaki,suka waiwaya suna dubanta sanda take daga labule tana ficewa,ranshi ya baci sosai,me ya kawota har cikin falon sumayyan?,bayan can ba shigowa take ba?,bama wannan ba,tunda suke tsaye tana wajen tana kallonsu,da wani abu suke kuma na daban fa?,ba sallama ba neman izini?,sumayya bata ce komai ba haka shima,sai yayi gaba ta tako a hankali ta biyo bayanshi,
"Shiga kice mata ta fito" ya fadi yana gyara agigon hannunsa
"To" ta fada tana takawa da irin tafiyar masu ciki,ya bita da kallo da idanunshi har ta shiga.

      A falom ta sameta tana tsaye,idanunta sun kada sunyi ja,tabbas kalaman da ta jiyo suna fita daga bakin almustaphan su suka sata shiga taji me yake gaya mata,kalamai ne masu nauyi dake fita daga ainihin qwaryar zuciya,tana zaton mawuyacine fa idan batayi kuskuren da zai hanata sukuni a rayuwarta ba
"Amm....anty yace ki fito zamu tafi"
"Kije kice masa ba zani ba,fitar min daga daki tun ban zagi uban ubanki ba"ta fada cikin tsawa da hargagi idanu ta daga ta dubeta kawai ta jiya a nutse ta fice,tabbas ba don tana tsoron abinda zai biyo baya ba da babu abinda zai hanata shaqo wuyan sumayyan tayita jibgarta kamar Allah ya aikota har sai taga ita da dan cikin nata sun daina motsi,amma ta tabbatar yin hakan dai dai yake da rasa komai cikin rayuwarta,ciki kuwa harda igiyar aurenta da almustaphan.

       A tsayen ta sake taddashi ya tsurawa qofar falon ido,ta iso inda yake ta bude bakinta zata roqeshi yaje yaji damuwar su'ad din sai ya daga mata hannu
"wuce mu tafi"kawai yace da ita yana dubanta,ba musu tayi gaba,duk sanda yake cikin fushi yakan koma mata almustaphan nan data sani a farkon rayuwarta,rufa mata baya yayi suka fice.

       Cikin katafaren shagon da sukayi fice wajen samar da kayan jarirai suke zagayawa,tana daukan duk abinda taga yayi mata shima yana tayata,fuskarshi a sakw kaman ba dazun ranshi ya baci ba,kayane masu kyau da tsada wanda jinsin mace ko namiji zai iya sanyawa(unisex).

         Daga gefansu kadan idanunta suka dinga mata gizo,kaman nuwaira take hangowa ita da wata mata suna zaban kayan yara maza,sai ta ajjiye rigar dake hannunta ta taka a hankali ta qarasa wajen
"Nuwaira" ta fada a hankali,da sauri ta juyo suka hada ido,take fuskarta ta washe da wani madaukakin murmushi,ba don tsinin cikin data gani jikin sumayya ba ba shakka rungumeta zatayi
"Anty sumayya?.....mama kinga anty sumayya,anty sumayyarmu,wayyo yau su basma zasu ji labari naga anty sumayya,yau ya hajiya zata ji saboda dadi" nuwaira keta jero wannan magana ba tsayawa,matar dake gefanta tana murmushi kawai,wanda duba daya zaka mata kaga tsantsar kaman dake tsakaninsu da nuwaira,kyakkyawar macace blcak beauty,wadda kallo daya zaka mata kasan nutsuwa ta ratsata,tana daukw da tsohon ciki wanda ke nuna alamar haihuwa yau ko gobe
"Oh nuwaira,nutsu mana ku gaisa ko tukunna" murmushi itama sumayyan take bakinta yaqi rufuwa suka soma gaisawa da matar sannan ta gabatar mata da kanta
"Ni sunana rumaisa,nice mamar nuwaira,ke kuwa nasan kece sumayya,matar da lukman ya taba aura haka ne?" Kai sumayya ta kada taba murmushi cikin mamaki
"Hakane,amma yaya akayi kika ganeni?" Murmushi itama tayi
"Dole na ganeki ai,mai gida mamarshi da duka yara kullum sai sunyi maganarki...ashe da rabon zamu hadu"
"wallahi kam" sumayya ta fada tana duban nuwaira
"Nuwaira,kinga yadda kika zama budurwa sosai,lallai aure nan kusa kenan" dariya ta saki cikin jin kunya tace
"Anty maman ce fa ta dawo gidan abba na" kai take gyadawa ko bata fada ba ta tsammaci haka
"Naga alama nuwaira masha Allah,Allah ya bada zama lafiya" hango almustapha tayi yana lalubenta da idanunshi don bai san tayi nan ba
"Ni zan wuce nuwaira ina kukayi masauki?"rumaisa ce tace
"nazo ganin likita ne amma nan da kwana hudu zamu koma,amman ki bani adresa dinki in sha Allah zamu zo har gida,nima naji dadin ganinki don naji dukkan wani qoqari da kikayi kan rayuwar diyata da kuma gidan baki daya,kin cancanci muzo mu gode miki" murmushi kawai tayi sukayi musayar lambar waya,ga rubuta adress din jikin qaramar takarda ta bata sannan sukayi sallama suka rabu.
Chapter 210 · 0% Book details