← Book details Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 226

Sashe 32

Kundin Qaddarata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

       Kamar daga sama ta dinga jiyo sallamar zainab qanwarta,daurewa tayi ta miqe ta dawo bakin qofar dakinta don ta sanar mata tana ciki kada zainab tayi qaryar bata nan,sai data tabbata zainab din taji sannan ta koma bakin gadonta ta zauna har ta shigo. Kallo daya ta yiwa sumayyan tace
"Lafiya kike kuwa anty" qoqarin qaqalo murmushi tayi sannan ta dan ja tsaki
"Qalau nake,yau ne kinga na tashi bana jin dadin jikina da bakina gaba daya"
"Yaya kamar fa kuka naga kinyi" sai ta basar ta hanyar fadin
"Barni kawai,nida mukhtar ne ya matsan sai da nasha magani,ni kuma kinsan bana son qwayoyi" sai zainab din ta gamsu da maganarta ta zauna tana fadin
"Kamar kuwa mamanmu ta sani kinga tace sai na tsaya tayi dambu mutuminki na kawo miki",ba jira kuwa ta sanya hannu ta janyo flask din ta bude ta soma ci. Sosai taji dadinsa cikin bakinta,sai data ci fiye da rabi sannan ta ajjiye.

      Bata sake fitowa daga dakin ba ranar,kusan yini sukayi ita da zainab tana mata 'yan gyare gyare cikin dakin,koda ta yunqura don sama mata abinci sai tace azumi ma takeyi,a nan take gaya mata mama tace taje ta yiwa anty dije sallama zasu koma abuja ita da mai gidanta,gwamnatin tarayya ta qara masa matsayi,duk sai jikinta yayi sanyi,bata son rabuwa da anty dijen,idan ta tafi bata da gun wanda zata je su shawarta matsalarta kenan,anty dije zata tafi ta barta a sanda alamu ke nuna matsalolinta qara qarfi suke. Sai taji zuciyarta na neman raurawa amma sai ta aro dakiya da juriya ta yafa wa kanta gudun kada zainab din ta fahimci wani abu.

          Sai yamma lis zainab ta tafi ko banza ta debe mata kewa sosai kuwa,a ranar ta sanar da mukhtar tana so taje wajen anty dijen washegari,saboda jibi zasu tafi,Allah ya dorata a kansa ranar tambotsan nasa da sauqi,don a dakinsa ma ta kwana duk da zaman kurame sukeyi.

     ****      ****      ****

      Tun goma na safe ta kammala shirinta tsaf cikin shadd ja wadda aka yiwa adon stone work baqi,ita kanta sai data tsaya ta kalli kanta,duk damuwar da take ciki amma sai taga ramarta bata fito kamar baya ba,mamakin yadda ta qara haske da cika takeyi,haka ta yafa baqin mayafi a kanta ta saqala baqar jaka ta fito.

          A harabar gidan sukayi clashing da su kasancewar harabar ba mai girma bace,tilas idan zata wuce din su ganta,yana zaune cikin mota zainab na tsaye riqe da murfim mota,kudade ta yanka masa zai bata shine ta biyoshi amsa,tana karba ta juya tayi ciki abinta,zuwa lokacin sumayyan ma har takai ga ficewa daga gidan.

         A hankali yake bin bayanta,sosai ya rage gudun motar yana tafiya a hankali don baison ya wuceta,tafiya take cikin nutsuwa,idan ka kalleta sai ka rantse da Allah bata taba aure ba,sosai shaddar ta haska jar fatarta,ga komai nata yayi mata cif a jikinta duk da da shigarta babu inda ta bayyana tsiraici,a haka har suka kai bakin titi,yana so yace ta shigo ya kaita amma kamar an masa shamaki da ita haka yakeji,haka ya karya kan motarsa ya wuceta ya hau kwalta sosai. Itakam sai a lokacin ne ma ta lura da shi,da idanu ta rakashi sannan daga bisani ta dauke kanta tana hadiye wani abu mai d'aci.

          Sosai ta lula tunani tsaye a bakin titin wanda hakan ya sanya ta kasa ankara da horn din da yake ta zabga mata,murmushi tayi ta qaraso gaban motar bayan ya sauke glass din
"Wa nake gani kamar abdur rahman cikin mota?"ta fada tana duban motar samfurin *vibe* fara qal da ita,sosai motar ta mata kyau
Murmushi yayi yana fadin
"Eh mana,ya son ranki?" Cikin dariya tace
"Fes wallahi"
"Ina zuwa haka da safe?"
"Zani gidan anty dije ne zamuyi sallama suna shirin bar mana kano su gudu abuja"
"Shigo ciki ma qarasa maganar ai hanya ta ce indai gidan da take har yanzu shine" ya fada yana bude mata mazaunin gaba
"Rufan asiri nan ai na qanwata ne,nan ma ya isa" ta fada tana shiga baya
"Yayarki dai,kina nufin nidin ban girme miki da wajen shekara uku ko hudu ba?"
"Jimin mutum da shegen son girma,shekara hudu kakar wata shekara arba'in,kai uku ne ma"
"Ko second daya ne dai na fiki ko?" Ya fada yana dariya,don sun saba da wannan caftar indai shi da sumayyan ne,itama dariya ta saki sannan suka shiga gaisawa a mutunce,ta tambayeshi mutanan gidan da kawunsa wanda qani ne ga mahaifin mukhtar.

"Kinsan tun ranar nan naso kawowa yaya mukhtar mota ta ya gani da kuma takardar zanen filin da zamu fara gina islamic clinic to ban samu dama ba"
"Da kyau masha Allah abdhr rahman,Allah ya sanya alkhairi ya kade fitina,kace yanzu sai bude asibiti"
"In sha Allah duk da aikin ginin ba qaramin abu bane,har kwantarwa nake sa ran zamu dinga yi,zamuyi amfani da likitancin musulunci da kuma na'urorin bature"
"Kace mun kusa fara kiranka alhaji abdur rahman"
"Da ba alhajin bane?,mijinki zaki cewa haka,gashi har yau ya kasa zuwa ko ina,ya zama sai a hankali wallahi" sai ta danyi shiru tana sauke boyayyar ajiyar zuciya don ha taba mata inda yake mata qaiqayi
"Ina fata kina ci gaba da addh'o'inki ko?"
"Babu abinda na fasa abdur rahman,sauqin ne sai a hankali"
"Haka ne,kada ki gaji,kinsan ita cuta farad daya take shiga sauqi kuma samuwarsa sai a hankali,Allah ya yaye ma dukkan musulmi baki daya"
"Amin abdur rahman,na gode" haka suka ci gaba da hira jifa jifa yana kwasarta da tsokana,har qofar gidan anty dije ya sauketa sanna ya mata kyautar dubu uku,da fari taqi karba sai da ya bata rai sannan ta amsa tayi godiya tare da bashi saaon gaisuwa gun qanwarsa bahijja da mamarsu.

Anty dije taji dadin ganinta sosai,nan suka wuni suna hira,ta tayata hada ragowar kayayyakin da bata kammala hada kansu ba,tuni yaranta sunyi gaba don su qarasa kammale gidan kafin isowar maman tasu. Suna hada kayan tana mata nasiha mai ratsa jiki,idanun sumayyan ya hada qwalla har ta kai ga gangarowa,ta share qwallar tana fadin
"Yanzu shikenan anty?,gurin wa zan dinga zuwa" sosai ta bata tausayi,yarinyar da dududu bata wuce shekara sha tara ba amma ta hadu da kaidin kishiyoyi kala kala,sai ta saki abinda take ta koma gefanta ta zauna
"Kina da Allah sumayya,baya ga haka akwai waya hannunki,duk abinda ya shige miki duhu ki kirani ki tambayeni,koda babu kudi a ciki kimin plashing zan kiraki da yardar Allah,ki ninka haqurinki kawai,domin duk wata mace da kika ga ta zama wata gidan mijinta ki tambayeta wanne irin haquri ta hadiya kafin ta kai ga cimma wannan matakin"
"To anty na gode"
"Babu godiya,ke diyata ce kamar su yasmin kike a gurina.....amma sumayya yanayin jikinki kamar ya sauya?,ko baki kula ba?" Ta fada tana kallonta
"Me kika gani anty?"
"Bakya jin wani sauyi a jikinki?"
"Babu abinda nake ji" ta fada tana kallon anty,shiru ta danyi sannan tace
"Shikenan.....koyaya kika ji wani abu kada ki zauna,kije asibiti"duk da bata fahimci abinda take nufi ba amma ta amsa mata da to.

Ana gab da sallar magariba ta koma gida,a gajiye ta koma,bandaki kawai ta fara shiga tayi wanka ya daura alwala,sai da ta kammala sallahr magariban sannan ta fita,cikin kitchen taji motsinta sai ta tura qofar ta shiga,tana tsaye tana hada food flask na abincin mukhtar,qarasawa tayi kusa da ita ta mata sallama,kai kawai ta daga ta dubeta ta maida kai taci gaba da abinda take ba tare data amsa ba,ita din ma bata damu data amsa ba kai tsaye ta jeho mata tambayar da ta fito da ita
"ina abincina zainab,banga flask dina ba"
Dagowa tayi sosai ta sake kallonta,sai ta saka wata dariya data sanya dole sumayyan ta tsaya tana kallonta cike da alamar tambaya,sai da ta tsagaita don kanta sannan tace
"Ince ko baki samu labarin baki da abinci a gidan nan ba" jin maganar tayi banbarakwai,ba kuma ta fahimci inda ta sa gaba ba,saboda haka taci gaba da kallonta,dauke kai tayi daga bisani sai ta nufi dan qaramin store din dake kitchen din da niyyar fiddo da ko indomie ce ta tafasa,sai ta tarad da store din a garqame da kwado,waiwayowa tayi ta sake duban zainab din
"Naga alamun baki fahimta ba,amma bari nayi miki bayani dalla dalla,mukhtar ya soke baki abincinsa,walau ni na dafa ko ke kika dafa kin fahimta ai yanzu ko?" Sosai maganar ta daketa,sai ta kasa furta komai baya ga wani abu da ya tokare maqoshinta,bata fahimci me hakan ke nufi,tilas ta jira dawowarsa tunda shi ya ajiyeta ba zainab ba,wannan maganar ba tata bace. Wuce zainab din tayi ta nufi sashenta ta dauki tukunya ta tari ruwa ta dora kan gas tare da jefa lipton,tilas ta sanya wani abu a cikinta ba don haka ba abinda take ji cikin zuciyarta bata jin wani abu mai suna abinci zai iya wucewa ta maqogoronta.

Hannayenta ta harde saman qirjinta tana jiran ruwan ya tafasa,tamkar zata fadi haka take ji,ga yunwa ga bacin rai,tana kammalawa ta juye a cup ta nufi daki,bata ko bi ta kan qananun habaicin da zainab keta jefawa cikin waqe,don yanzu bata ita take ba ta kanta take. Tea ta hada da kayan shayinta wanda dama a dakin suke.

Ko rabi bata sha ba ta soma yunqurin dawo da shi,sai data amayar da shi tas sannan ta dawo ta zube qasan carfet din dakin cikinta naci gaba da juyawa,rasa abinda ke mata dadi tayi,fashewa tayi da kuka tana kiran sunan Allah.

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

2⃣9⃣
_________________________

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Bismillahir rahmanir rahim*

*kullu man alaiha faan,wa yabqa wajhu rabbuka zuljalalu wal ikram*

_dukkan wani abu dake kanta(duniya)qararre ne,zatin ubangijinka mai girma da daukaka ne zai dawwama_
_________________________

*Na sadaukar da wannan page da dukkan wani makarancin littafin KUNDIN QAgDDARATA,haqiqa zan so ace ina da lokaci da zan iya binku daya bayan daya na amsa commenta naku,saidai ina fatan wannan shafi ya isar muku,na gode qwarai*

_masu qorafe qorafe kuyi haquri,ku karbi littafin a duk yadda yazo muku,da fatan kunyi duba da ayar da tazo a farkon shafin,ita kadai ta isa ku fahimci me nake nufi,godiya nake_
Chapter 32 · 0% Book details