Sashe 9
Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
🌹Zaku Sami Product guda daya Kyauta da kungiyoyin suka tanadar Muku don Gyaran jiki da magance matsalolin Infection da saukar da niima ( Maganin Herbal ne 100%Natural )
🌹 Yiwa Business din ku CAC Register kyauta
🌹 Yadda zaku Sami Rancen Kudi,ko nawa mutum ke bukata ku juya kuyi business ku maidawa kungiya kudin ta ( da yawa suna da ideas na business amma Babu Jari..don haka wannan babbar dama ce ayi amfani da ita don dogaro da Kai)
🌹 Kadan Kenan daga cikin Abinda program din ya kunsa mu kasance cikin group don samun Sauran bayanan Masu yawan gaske
💲ayi Sharing Link din don sauran Mata su amfana da wannan Shirin
______
Tun bayan fara wayewar gari su Madeeha basu koma bacci ba . Tamkar ko da yaushe. Janyo ruwa sukayi a rijiya suka zuzzuba a ma'adanan ajiyar su.
Daga nan suka wuce famfon bakin masallaci suka ebo sawu biyu. Bokiti daya na ruwan shan da suke zuba wa a randa. Yayinda dayan kuma suka raba zasuyi wanka da shi.
Da sauri Madeeha ta karasa dan wajen zagayen da suke abinci. Wuta ta hada nan da nan ta dora tukunya ta zuba ruwa cikin ta. Idan yayi zafi sai su raba suyi wanka..
"Salamu alaikum... Salamu alaikum."
A ka shiga doko sallama daga kofar waje.
"Wa'alaykm Salam.. Waye?"
Fareeha ta amsa. Hadi da gyara zaman hijabin ummy dake jikin ta. Wajen ta fita tana kara amsa sallamar,
"Wa'alaykm Salam.."
"Ke ina mai gidan?"
"Yana..u."
"Yana ina? "
"Inaga yana ciki."
"Oh kina ga nema baki ma sani ba. Gafara." Ya bata amsa cikin hasalewa .
Kawu Ashiru dake jiyo su. Yayi hanzarin komawa baya. Ya shiga kokarin daka tsalle ya haura ta katangar dakin da ke da yar kofa ta baya..
Mutumin ya ja tsaki tamkar zai buge Fareeha da bugu haka ya mangajeta ya wuce kai tsaye cikin gidan. Dai dai lokacin da kawu Ashiru ya cabe katanga zai haura.
Da sauri mutumin yayi ta maza ya riko bayan kawu Ashiru ya sauke shi kasa yana huci tamkar matashin zaki
"Auwali "
"Ba wannan maganar... Kai... Ina kudade na? Na rantse da kadaitar ubangiji sai ka biyani kudi na a yau. Dubun ka ta cika. Shege barawo. Ka dauka ni ma su mudi ne da suka yi shiru suka kyale ka? Wallahi tunda ka ci kudi na ka tabo tsuliyar dodo. Dan iska maras mutunci."
"Baba ga dumamen an du."
"Dumamen kan gyatumar ki? Zaki matsa ko sai na shatale ki?" Kawu Ashiru ya bawa yar sa khairiyyah amsa.
"Ke ina dumamen?" Mutumin ya juya ya tambayeta.
"Gashi."
"Kawo."
Karba yayi ya riko dantsen kawu Ashiru ya zube shi agaban sa. Kafin ya tattare hannun rigar sa ya shiga ci hannu baka hannu kwarya. Kawu Ashiru sai hadiyar miyau yake. Ga azabar yunwar da yake ji ga karin kumallon sa Wani kato na cinye shi agaban sa. Ba kuma yadda ya iya.
"Ke ...." Mutumin ya kwalawa khairiyyah kira.
Ta zaburo da sauri ta tsaya agaban sa.
"Ga ni "
"Je ki ce a karo... Sannan a barbada gishiri a miyar nan salam. "
Jikinta na rawa ta saka ta hannu ta karbi kwanan ta nufi wajen Rahila mahaifiyar su
"Umma ga shi .... Wai a karo "
Ta taga Rahila ta leka ta hangi basamuden mutumin ya tsare mai gidan nata Ashiru agaban sa. Tamkar malamin makarantar allo da almajirin sa yana karbar hadda.
Ta yamutsa fuska hadi da daga hannu sama ta sauke shi akan cinyar ta. Cikin kasa kasa da murya ta shiga kananun mita.
"Sarkin jaye jayen masifa da balai. Yau kuma abunda ka jajibo mana kenan da sanyin safiyar nan. Yanzu gashi nan an zuba maka abinci iya rabon ka ya cinye yace a dad'o. Kai Allah wadaran Ashiru .. " Ta karasa hadi da lailayo zagi ta sauke akan sunan Ashiru.
"Rike ke kuma." Ta nana mata kwanan me dauke da tuwo daya da miya.
"Yace a barbada gishiri Umma. "
"Ga gishirin nan agaban ki ai can daya yar nema kema."
Yarinyar ta barbada gishirin ta nufi wajen su da kwanon a hannun ta.
"Yauwa...." Karba yayi ya sake zura hannu aciki. Yana kai loma yana lashe hannun sa.
"Mai dakin ka ta iya girki. Matsalar ta daya bata san kan gishiri ba ne ko kuwa batan rana ce ta girki oho."
Kawu Ashiru ji yake tamkar ya mike ya zuba masa mari. Cikin sa sai kukan agajin yunwa ya ke.
"Ungo kareshi.... "
Mutumin ya mika masa kwanon. Yana lashe yatsun sa.
Kawu Ashiru da sauri ya mika hannu zai karba.
"Karashe miyar...,"
Ya karasa fada yana sakin wata katuwar gyatsa.
Hawayen zuci kawu Ashiru ya shiga yi. Yana tuno marka markan malamalan tuwon jiya . Da miyar kukar data sha daddawa da magi. Ya tuno yadda jiyan tuwo biyu yaci yace a ajiye masa sauran malmalan a dumamen safe. Bashi ya ciyo akayi tuwon ma. Gashi ko biya bai yi ba. Wannan tsautsayin yazo ya haura masa. Gaba daya kasonsa mutumin ya aune su a cikin sa.
"Na ce zaka lashe miyar?" Ya tura masa kwanon wajen bakin sa.
Kawu Ashiru ya girgiza kai kawai yana jan hancin sa.
"Debo mun ruwa a butar can na wanke hannu na... Kaji ko?"
Kawu Ashiru ya mike. Kunya duk ta dabaibaye shi da takaici. Agaban kowa na gidan. Ciki harda kaji da zakaru duk tsayawa sukayi suna kallon su.
Ya dubi gabas ya yankawa akuyar Ummy mahaifiyar su Fareeha harara. Tamkar akuyar tasan fushin me yake yi.
Ruwan ya janyo a rijiya ya kai gaban mutumin .
"Ga shi."
"Yauwa."
Karba yayi ya wanke hannun sa tas . Ya hada da bakin sa ya kuskure.
"Yauwa a'ina muka tsaya ne...? "
Shi dai kawu Ashirun bai ce komai ba. Sai ma gyara zaman gurfanen da ya yi. Yanata matse idanuwa.
"Yauwa..... Maganar kudi na. Yau itace rana ta karshe. Ba zan daga maka kafa ba wabillahi lazi. Magana daya ce. Daga ita ba zan sake ba. Dole ne dik yadda zakai ka biyani kudi na. "
Kawu Ashiru ya bude baki kenan zai yi magana sai ga shigar aqeel babban dan sa. Yana tafe yana waka.
"Eh eh... Doe mi a do yo. Men no ro rest.. men no ro rest" Da karfi yake yana wani jijjiga kai yana lumshe idanu irin wakar nan ta shige shi. Sam bai damu da ba daidai yake furtawa ba. Nishadi na dada ratsa shi
"Kai waye ya ke wake wake ne?" Auwali ga tambaya yana mai yamutse fuska hadi da juyawa ya sauke idanun sa akan Aqeel.
"Kai aqeelu ba zakai shiru ba wai?"
Aqeelu dake duke yana nannade kasan wandon sa.
"Kai baba ba wayis (wise) bane Yasin. Idan ka saka hakuri ma rage ciki na zan na fita na bar muku gidan. Wallahi shiysa crypto na fashewa dana sallame ku da daloli zan rushe gidan nan ya zama na zuba shara .. San,"
Bai karasa ba auwali da ke huci. Ji yake tamkar ya mike ya shako wuyan aqeel.
"Kai dallah malam gafara can. Ya isa haka nan. Haba."
Sai a sannan aqeel ya lura da auwali. Ya shafa keyar sa yana kakaro murmushi.
"Ah me gidah yau kai ne anan? Ina gaisuwa fa."
Auwali ya tabe baki kawai. Yana cigaba da huci. Ya cika yayi fam tamkar zai fashe.
Fareeha da Madeeha dake leken komai ta taga sai dada dage sukeyi suna kallon komai
Sun shirya tsaf jikin uniform dinsu maroon color. Mai dauke da hijabi milk.
"Ba zaku dawo ku zauna ba wai?" Ummy mahaifiyar su ta fada tana mai cigaba da jan carbin ta.
"Yasin ummy gashi can kinga yadda yake sake harzuqa kamar zai hau kawu da bugu." Madeeha ta fada tana mai kyalkyalewa da dariya.
"Shine ki ke dariya Madeeha. Mai yakwan ki zauna ki jimamin lamarin?""
Jin abunda ummy ta fada. Hakan ya sa madeeha da Fareeha suka sake fashewa da dariya.
"Wallahi idan baku zauna kun nutsu ba ni da ku ne. Allah yasa na karasa carbin nan naga kuna nan a tsaye. "
Ba shiri suka zazzauna. Ta juya ta dube su tana kada kai kafin ta cigaba da jan carbin da take.
Wasa wasa auwali sai da ya bata awa daya agidan nan. Wayar sake da ke aljihun gaban rigar sa ce ta shiga kara. Ya dauka ya kara a kunnen sa.
"Eh ina gidan... Kasan Allah idan bai biyani ko da kwata bane sai na sassara shi gunduwa gunduwa. Na gundule gaban fitsarin sa wallahi. Na nakasta dan iskan awuce wajen."
Jin abunda ya fada. Kawu Ashiru ya hadiye wani tokararren abu daya tsaya masa a wuyan sa. Ya dubi gabobin jikin sa yana zare idanu
"Kai dube ni..."
Kawu Ashiru ya daga idanu ya sauke akan auwali. Auwali ya daga kai ya saka kafar sa daya ya dora a yatsun kawu Ashiru ya murje yatsan. Don azaba sai da kawu Ashirun ya yi kara.
"Kaga yadda na murje yatsun ka? Wallahi idan ka bata lokaci wajen cikamun kudi na Allah haka zan murje gabobin jikin ka. Gaban ka kuma na yanke na gasawa karnuka suci. "
"Dad..dan dan Allah kayi hakuri." Kawu Ashiru ya shiga magiya.
Gumin azaba na tsattsago masa ta goshi.
Mikewa auwali yayi. Hannun sa zube cikin aljihun wandon sa ya dubi Ashiru kafin yace,
"Bani dubu ashirin. Jibi da yamma kuma zan dawo ko kudi na.. Ko gidan nan. "
Kawu ashiru ya shiga dube duben ko'ina. Tamkar zai haukace saboda kidimewa
Mikewa yayi da sauri,
"Ina zuwa .."
Dakin Rahila matar sa ya shiga. Suna tsaye ta taga suna kallon su itada sauran yaran su.
"Rahila."
"Naam" Ta amsa shi tana masa kallon tara saura kwata.
"Aramun dubu ashirin. Da girman Allah zan biya ki idan na samu kudi. Ko wata kadarar ce ban na sayar "
Uban tsaki ta debo ta ja shi sosai kafin ta dire tana yamutsa baki.
"Idan mafarki ka ke Ashiru ai gwara ka farka. Me nake da shi da har zan baka ka sayar ka biya bashi?"