Sashe 33
Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar ta shako shi haka take ji. Kamar zata yi magana sai kuma ta zagaye shi zata bar gurin ya kuma kai hannunsa ya riko hijab dinta. Cak ta tsaya zuciyarta na zillo tana sake bin wajan da kallo ko akwai masu kallansu, aikuwa taga wasu zazzaune sun zuba musu ido, cikin fushi ta juyo tare da fincike hijab din tana masa kallan tsana tace.
"Karka sake rike wani abu da ya shafeni, idan kuna yiwa sauran matan University suna kyaleku ni bazan dauki wannan rainin hankalin ba. Kaine ka bata min lokaci dazu da fari ban zagaye ta baya ba har na rasa attendance na kuma rasa sauraran lecture, karka sake KULA NI idan kuma ba haka ba zaka sha mamaki."
Ta juya tana tafiya ya bita cikin sassanyar muryarsa taji yace mata.
"Sorry naji haushi da baki samu shiga lectures ba, amma nayi miki attendance."
Zaro ido tayi jin maganar shi ta karshe, lallai gayen nan akwai rainin hankali wai ya yi mata individual attendance din da ake yi, to ta ya? Har zata juyo ta sake yi masa magana sai kuma ta fasa saboda ta gane cewa shi din mugun dan rainin wayo ne.
"Dan Allah KI KULANI."
Taji ya fada cikin murya mai rauni. A fusace ta juyo tana yi masa kallan sama da kasa tace.
"Nima dan Allah ka kyale ni, rainin hankalin ka ya fara isa ta."
"Naji amma dan Allah ki dinga KULA NI idan na miki magana, kefa musulma ce kinsan hukuncin mai wulakanta dan Adam. Sam baki kama da masu irin wannan dabi'ar ba."
Sake wurga masa wani mugun kallo tayi, gabaki daya zuciyarta tafasa kawai takeyi. Cikin bacin rai tace.
"Bana kula mazan da bansan su ba. Mazan ma kuma ire iren ka da kowa yasan me kuke girbawa. Dan haka kaci gaba da hakuri ka kuma kyaleni."
Tana gama maganar ta nufi inda gurin zama yake ta zauna. Rayyan ganin ta zauna yasa shima ya karasa wajan ya samu guri ya zauna. Su T.boy suna ta kiransa ganin suma sun kusa shiga lecture amma yaki zuwa, ganin sun takura da kiransa ne yasa shi dagawa ba tare da yayi magana ba.
"Kana ina ne gashi har mun shigo hall.?"
"Menene?" Rayyan ya tambaya murya babu walwala.
"Ka taho kafin a fara lecture." T.boy ya gaya masa hakan.
"Bazan yi attending wannan lecture din ba."
"Kai..! Kasan halin shi bashi da mutunci duk takamar mutum." Cewar T.boy cikin tunawa Rayyan halin lecturer din.
"Eh bazan yi attending ba ko da zai hana nayi passing exam." Yana kaiwa nan ya katse kiran yana ci gaba da danna wayar.
Madeedah ta saci kallonsa tana mamakinsa, ita tana nan bakin cikin shiga lecture ya dameta. Shi kuma taji yana cewa bazai shiga ba koda bazai ci exam ba, meye amfanin karatun ka kasa bada abinda ake so.? Muryarsa taji yana cewa ba tare da ya dena danna wayar ba.
"Shikenan na rama miki rashin shiga daukar darasi ko? Kuma nace miki nayi miki attendance baki da matsala."
Madeedah ta kasa jure tambayoyin da suke cunkushe a zuciyarta tace masa.
"Ka rama min taya? Ta hanyar cutar da kanka kome? Tukunna ma kana ta cewa kayi min attendance how? Kuma kasan full suna na ko kuma da naka sunan kayi min amfani.?"
Habawa Rayyan sai yaji kamar an bude masa kofofin da suke toshe a cikin jikinsa. Wannan maganganun da kuma damar yin magana dashi da ta bashi sun bala'in yaye masa wani bakin ciki da yake damunsa a zuciyarsa. Sai da ya gyara zama ya maida wayarsa cikin aljihu sannan ya kalleta tayi saurin dauke fuska ya saki wani murmushi tare da sanya hannu yana sosa kyakkyawar sumar kansa yake cewa.
"Ba cutar da kai bane ba, a guri na indai zan rama miki bacin ran da na sanya ki to komai zai sameni ba zai zama cutarwa ba."
Madeeha ta tabe baki ta fara tunanin ko Rayyan din yana da matsalar hankali dan ita kam in banda tsautsayi babu abinda zai sa tayi irin wannan gangancin da yayi na kin shiga lecture. Muryarsa ta sake katse mata tunanin da ta shiga inda taji yana cewa.
"Naga yadda lecturer din yake muku, naga yadda kuke gudun samun matsala daga course din shi. Ina zaune naga ya shiga kuma naga ke baki zo ba . Hakan yasa nayi saurin shiga na rubuta sunanki Madeeha Sufyan Zubair. Reg number dinki ends with 98."
Agigice ta dago kai ta zuba masa kyawawan fararen idanunta jin ya fadi sunanta gaba daya. Murmushi ya sake yi idanunshi akan fuskarta yace.
"Registration number din ki ta zame min tamkar phone number dina ko ba itace....."
Ya shiga karanto mata reg number din ta gaba daya. Cikin sauri Madeehah ta mike tsaye tana zaro ido tare da girgiza kai bakin ta yana rawa tace.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un kai waye?"
Shima Rayyan mikewa yai yana zuba hannayensa cikin aljihun wandonsa, ya dan tako gab da ita tayi saurin matsawa ya sake girgiza kai yana cewa.
"Shi yasa nake ta so KI KULA NI amma kinki bare ki saurareni. Abinda na sani kawai shine. Ke din MALLAKIN ZUCIYA ta ce. Ina jinki a can cikin raina ta yadda baki na bazai iya misalta tarin muhimmancinki a rai na ba."
Ya karasa fada yana mai runtse idanun sa. Kalaman da yayi sun matukar bashi mamaki. Wai yau shine me yiwa mace naci akan ta karbu kaunar sa. Ko a mafarki bai taba zata rana irin ta yau zata zo masa haka ba. Shi daya ajiye soyayya ya rufeta da babun karshe...
Madeeha ta dan daga kai ta dube shi... Kafin ta saukar kasa da sauri.
Ikon Allah yau ta hadu da jarababben mutum sai faman ta kulashi yake yi kamar wanda ya bata ajiyar wani abun. Ta sake jujjuyawa tana bin mutane da kallo, so take tayi masa abinda zai hanashi kulata amma ta rasa.
"Me kace sunanka?" Kafin ya gaya mata ta sake cewa.
"Koma dai wanene sunanka ni bansan abinda kake nema a waje na ba, ka rabu dani ka kyaleni inji da bakin cikin lecture din dana rasa."
Ga mamakinta sai taji yace.
"Meye abin damuwa dan baki samu lecture ba? Karatun duniya ne fa ba dashi zamu mutu ba. Please ki dena damuwa dan Allah bana jin dadi."
Wani irin kallo tayi masa wanda yasa ranta ya kuma sosuwa.
"Nagode." Kawai ta fada tana sake zama ta dauke kai gefe dan taga shi ko a jikinsa rashin shiga lecture din sa. Da kuma gaggaya masa magana da take ta faman yi. Amman qyas yaki fushi tamkar an tsunkuli kakkausa..
"Karfe nawa zaku tafi gida?" Rayyan ya tambayeta cike da tsantsar kulawa.
"Sai dare." Ta bashi amsa cike da takaici dan ya isheta da magana.
"Well bayan magriba ko isha'i?" Ya sake tambayarta iya gaskiyarsa.
Wani haushi ya sake mamaye Madeedah.
"Kamar sha biyun dare."
Wannan lokacin sai da ya bude ido can kuma ya yi murmushi saboda ya gane magana ta gwabza masa. Rayyan ya shafa sumar kansa, haka kawai yake jin dadi da kulashi da takeyi duk da ba maganar dadi take masa ba yana jin wani farin ciki a ransa.
Suna zaune a wajan tana rike da wata jotter tana dubawa aka fito daga lecture din. Cikin sauri ta mike dan tun dazu take so a fito tabar wajan nan. Su Nawal da Nour ne suka hangota, mamaki ya kama su ganin Rayyan a wajan Madeedah da ke ta faman hade rai. Suna karasawa wajan Nawal ke cewa.
"Ya akai muka rigaki shiga? Kinsa Allah na dauka tare muka shiga kawai sai naga kinzo ya hanaki shiga."
Madeedah ta juya tare da zabgawa Rayyan wata banzar harara alamar duk shi yaja mata.
"Yayi test fa Madeedah, wallahi munso yi miki amma mugun ya karba individually babu damar wani yai wa wani kinsan shi da salo-salo na mugunta." Cewar Nour cike da jimami.
"Na shiga uku test? Wayyo Allah na." Madeedah tayi maganar cikin rawar murya idanunta kamar zatai kuka dan ba karamin rashin dadi taji ba.
"Bari naje na bashi hakuri ko zai bani dama nayi ni kadai." Ta juya da sauri zata tafi Rayyan ya tare gabanta, cikin fushi ta dago zata masa magana taga ya dora yatsa a saman lips din shi alamar karta ce komai.
"Kibari naje na roke shi idan ya bani sai nayi da sunanki. Kinsan malaman nan wasu ba kirki gare su ba musamman irin wadannan karkije yayi miki rashin mutunci bazan yafewa kaina ba."
Bai jira tayi magana ba ya juya yana yiwa Farhan magana cewar yazo ya rakashi office din lecturen. Baki bude Madeeha ke bin su har suka bacewa ganinta. Ganin ba magana yake da Farhan din ba
Nawal ta saki murmushi tana dafa kafadar Madeedah cike da zolaya take cewa.
"Guy din can ya fola Madee." Wani tsaki ta saki tare da hura iska daga bakinta tana cewa.
"Dan wahala ne kawai ni ba soyayya ta kawoni makarantar nan ba. Wallahi ya bani haushi wai saboda ban shiga lecture ba shima yaki shiga tasu saboda shirme."
Nour ta tafa hannu cikin shauki take cewa.
"Madee wallahi kin caba kut, kiga fa yanzu ya tafi ya yi miki test. Wow gaskiya har kun burgeni wallahi."
"Kema baki da aikin yi." Cewar Madeeda tana juyawa ta koma inda ta taso ta zauna. Suma bin ta suka yi suna ta yi mata tsiya tun tana ramawa harta share su.
Rayyan yana zuwa ya samu lecturen a office, Farhan tuni ya tsaya a waje sai dai ya kasa kunne yana jiyo su.
"Sir please kayi hakuri kayi test bana nan nayi late wajan kai sister na hospital ta kone. Please sir ka taimaka yanzu anan ka bani question nayi." Wani kallo yayi masa yana bubbude wasu files yake cewa.
"Yayi daidai kaga sai ka koma kaci gaba da jinyarta Allah ya bata lafiya." Rayyan ya kalle shi cike da haushi har zai gaya masa rashin kunya sai kuma ya tuna cewa Madeedah batai test ba saboda shi. Sumar kansa ya shafa yana sake yin kasa da murya.
"Sir ka takaimaka dan Allah." Cikin bacin rai yace da Rayyan.