Sashe 7
Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta fito daga cikin bandakin ta sauya kayanta sauran ta zuba su acikin dan kwandon kayan wankin ta.
Ta shafa mai hadi da zizara kwalli. Tabi jikinta lungu da sako ta feshe da turare kasancewar ta ma'abociyar kamshi.
Hijabi ta zura hannunta da carbi. Ta shiga dogara yar sandar ta har ta karasa fita daga dakin zuwa babban parlorn gidan.
A daidai corridor din da zai saadaka da dakin ta ja ta tsaya jin kamar ana yar hayaniya. Muryar Hajia Hindu ce.
"Zamanta ki ke wai ko zamana? Eh? Tambayar ki na ke..."
Mai aikin ta tsugunna har kasa tana jujjiya kai. Idanuwan ta sun kawo ruwa.
"Dan Allah kiyi hakuri Hajiya.. Wai gani nayi tana son shan kunnun ne da kosan shiya sa ka nace idan na kammala na ta sai n..."
"Sai me? Sai ki dawo kan nawa umarnin ko? Ni ce matar gidan ko ita?"
"Ke., Ke ce Hajiya"
"To wallahi daga rana irin ta yau. Idan har kika sake fara yin abincin ta kafin nawa wallahi kinbar gidan nan kenan daga yau..." Ta karasa fada hadi da buga mata harara da jan tsaki ta fice daga parlorn.
Fuuu kamar tashin guguwa ta fito daga parlorn saura kadan ta bangaje Hajian ta zunguro baki gaba. Cikin murya irin ta takura dinnan karshen makura tace,
"Ina kwana...?" Tayi gaba batare data jira amsar ta ba.
Hajian ta girgiza kai kawai tabi bayan Hindun da kallo. Kafin ta karasa parlorn. Mai aikin na zube a kàsa tana share hawayen ta.
"Bar kuka jika tah ... Tashi kije kinji? Duk na jiyo abunda kuke cewa. Na kuma gode da irin kaunar da kike nuna mun. Allah ya miki albarka kinji?"
Ta daga kanta. Kafin cikin share hawayen ta tace,
"Na ji... "
"Yauwa... Kamar yadda ta umurce ki din. Ki dinga kammala duk aiyukan da ta sakaki kinji ko? "
"Tohm ... Insha Allahu"
"Yauwa... Allah ya miki albarka. Allah ya shiga lamuran ki. Ya temaka miki Amin. Tashi kije."
"Amin Hajia... Nagode sosai "
Mikewa tayi ta tafi zuciyar ta nata kambama rashin daraja irin ta Hajia Hindu.. Mahaifiyar mijin ki kike tozartawa haka? Ba ranar dazata fito ta koma ga mahaliccin sa Hajia Hindu bata muzanta mahaifiyar mjintata ba. Ko meye ribar hakan? oho... Ta bawa kanta amsa kafin ta karasa shigewa cikin kitchen din ta shiga yanka plantain.
Ko da mai aikin ta tafi. Hajia Fadila ta sauke ajiyar zuciya kawai . Dai dai lokacin da dan nata ya sakko daga mattakalar bene. Yana hangota ya washe hakoran sa . Idanuwan sa fes akan mahaifiyar ta sa. Ya karasa wajenta cikin kulawa da girmamawa ,
"Hajian mu barka da safiya... An tashi kalau? Ya jiki jikin? To Allah ya kara miki lapiya da nisan kwana mai amfani. "
"Da imanin Allah...."
"Yauwa da imanin Allah Hajian mu ."
"Allah yayi muku albarka ... Allah ya shiga lamuran ku. Ya yi riko da hannayen ku."
"Amin Hajia... Kin dai ci abinci ko?"
"Banda de da fitowa ba ai... Yanzu za'a karasa, Ba kuma na jin yunwa . Wajen aiki zaka tafi?"
Da sauri ya juya ya zubawa Hajia Hindu idanun tambaya. Da ke biye da shi tamkar zata koma cikin sa.
"Yanzu za'a karasa."
"What nonsense .. Me nace miki akan kula da Hajia? Hatta abincin da zataci sanin kanki ne don ita na karo maaikata. Ya za'ai ki kalleni kice yanzu za'a karasa. A wannan lokacin? "
"Ya isa haka Hammadu ... Ya isa dan Allah. Yanzu za'a karasa . Dan Allah ka dena hawa doron zuciya. Suna kokari wallahi ."
Hajiya Hindu tayi kwafa tana kallon Hajia Fadila har ta karasa maganar ta buga mata harara. Sam taa tsani yadda mijin nata yake tarairayar mahaifiyar sa.
Abun tsayawa yake ya tokare mata a wuya ya hanata sakat. Ta tsani ta wayi gari taga Hajian na cikin farin ciki. Musanman ma idan farin cikin mijin nata ne yayiwa Hajian. A duniya kam taki jinin kauna da shakuwar da ke tsakanin su.
"Dan duba kiga idan sun kammala a kawowa Hajia please. " Ya fada yana mai kallon agogon hannun sa.
Hajiya Hindu tayi kwafa tana juya idanu. Dake bayan sa ya juya. Sai Hajia Fadila ce ke fuskantar ta. Shi yasa duk harara da zunde da gatsine gatsinen da take baya gani ..
"Yar iskar tsohuwa .. Allah ya kashe ki mu huta da ala'ka'kai.........' Ta fada cikin zuciyar ta tana sakin siririn tsaki a kasan makoshin tah.
ZAFAFA BIYAR 2023 PAID NOVELS✓
_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_
_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_
_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼:07_
_ZAFAFA BIYAR PAID BOOKS 2023_
✓✓✓✓✓. ✓✓✓✓✓
Kitchen din ta shiga ranta a matukar bace. Ta dubi mai aikin dake kada kwai zata soya. Ta wurga mata wata wulakantacciyar harara mai cike da tsantsar kiyayya.
"Sannu Hajia. "
"Idan kika sake cemun sannu sai na mauje ki wallahi. Sannun uban ki?! Munafuka annamimiya. Wuce ki karasa mata abincin na ta. Kuma wallahi daga yau idan kika sake katsalandan din fara gama hada breakfast dinta sai ranki ya baci.... Zaki wuce ki tafi ko sai na hada kan ki da tukunyar gaban ki?"
Kan yar aikin a kàsa ta girgiza kai,
"Kiyi hakuri Hajiya ba zan sake ba. "
"Ki ma sake din ki ka yadda ake hukunci. " Taja tsaki kafin ta wuce wajen warmers tana mai bubbada cikin su. "
"Plantain ma kawai ta soya sai dankali yar iska. " Ta karashe tana mai sakin tsaki.
Yar aikin ta shiga parlorn kanta a kàsa. Hajian na zaune da dan nata agaban ta. Tamkar zai koma cikin ta. Da tayi motsi zai fara tambayar me ke damun ta? Shin ko akwai abunda take so..?
"Yauwa ga abincin an kawo... Na zuba miki ko?"
Dan murmushi tayi kafin tace da shi,
"Ba zaka makara awajen aiki ba ne?"
Yayi saurin girgiza kai tamkar karamun yaro. Cikin kulawa da biyayya yace da ita,
"Ba zan makara ba.... Duk kuwa da ni ne shugaban kowa. Ina kokarin kamanta adalci da jagoranci nagari. Kusan koda yaushe ni ke riga kowa zuwa..." Ya karasa magana. Yana zuzzuba mata komai akan wani tray..
"Allah yayi muku albarka Amin. Allah ya kara muku daukaka da kamanta yin adalci ga maaikatan na ku Amin."
"Aamin Amin."
"Bismillah ko na kara?"
Dan murmushi kawai tayi masa. Ta yi bismillah ta shiga cin kosan bayan ta hada da biredi slice daya. Gefe daya kuma kunun ta ne sai kamshin kayan kamshi ya ke.
Sai da ya tabbatar ta kammala cin komai daya zuba mata. Sannan ya dakko roba da hand wash ya matsa mata ta wanke hannun ta.
"Nagode.. Allah yayi albarka Amin."
"Amin Amin..."
Sai data karasa jan carbin hannun ta tukun sannan tace da shi,
"Yau idan Allah ya yarda zan koma gidah."
"Gidah Kuma? Hajiya Wani abun akayi miki anan din?" Ya fada muryar sa na kunshe da damuwa.
"Ko daya.... Kawai dai adadin kwanakin da na diba zanyi sun cika har sun haura ma."
Hajia Bintu da ke labe tana jinsu fuskar ta ta yaye da farin ciki jin Hajiyar zata bar gidan ta gama kwanakin ta. Daman zamanta akan kaya take. Tunda tazo bata samun sukuni da dadin rayuwa.
Ta sake kasa kunne a labe tana sauraron su. Yadda mai gidan nata yake sake durkushewa gaban mahaifiyar tasa yana lallaba ta ne ya sake sosa ran Hajia Bintu. Domin taki jinin kaunar da yake nunawa mahaifiyar ta sa. Aganin ta ta zarce tunani. Ta zarce shakuwa da so. Ta wuce kima ta wuce duk yadda zata fasalta
Ta saka hannu a baki ta gyatsa tana jijjiga kai cikin takaici.. Muryar mai gidan nata na dada bakanta duk wasu kofofin zuciyar ta dana rassan jikin ta.
"Haiiya idan wani abun muka miki akan sani ko na rashin sani..Dan Allah kiyi hakuri .... Kinji Hajiya? Ki cigaba da zama anan. Wallahi bakiji dadin da nakeji ba dan zaman nan da kikai."
Hajiya Fadila tayi murmushi kawai
"Ba abunda kuka mun. Allah kuma ya kara wadatar arziki da kwanciyar hankula. Allah ya maka albarka kai da sauran yan uwan ka ya sake dagaku Amin. Ai na dade anan din dan birni.. Tun da muka dawo daga kasa mai tsarki fa nake nan gidan. Ko jiya da su autah suka zo ma na so binsu kuma sai na kyale dai kawai."
Alhaji Hammadu ya fadada murmushin sa.
"Ahap Hajiya kawai ki ce Dan autan ki ke kewa zaki koma, Da shi da Rayyan... Ai ni daman nasan tunda jiyan nan ya sakaki agaba yana kuskus da zance nasan kalallame ki yake ki koma... To ai shikenan ya zamuyi. Abunda kikace ai shi zaai Hajiya.... Amman dai ba yanzu zaki tafi ba ko? Kibari nake office na dawo sai na kai ki da kai na gidan na sa ko kuwa?"
"Tohm shikenan Allah ya kai mu. Allah kuma ya bada sa'ar abunda zaa fita nema. Amin"
"Amin Hajjajin mu. Kema Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana mai amfani amin"
"Amin ya rabbi da imanin Allah."
"Eh da imanin Allah... To ni zan fita. Na bar ki lafiya.."
Durkusa wa yayi ya mata sai anjima ya fita ... Hajia Bintu dake labe tabi bayan sa don yi masa rakiya.
Ko dazai shiga mota ma sai da ya jaddada mata da ta kula da Hajia ta kuma dafawa Hajian abincin da take bukatar ci.
Wannan kalaman na sa ba karamin sake bakanta ran Hajia Bintu sukayi ba. Ta cije dai bata sauya fuska ba har dai direban sa yaja mota suka fita daga gidan.
Cikin gidan ta koma.. tana mita
"Wallahi bazan dafa ba. Ga ma'aikata nan sai ni zan dafa mata abinci saboda itace shafaffiya da mai ko? Ba zan ba wallahi .."
Ta bude kofar kitchen ta shiga. Ta tsaya tana kallon mai aikin dake dauraye kwanuka.
"Ke..."
"Na'am Hajiya.."
"Je ki tambaya tsohuwar can me takeso a dafa mata. Duk abunda tace to ki dafa mata. Amman karki kuskura kimun almubazzaranci da kayan abinci. Karki dauki kaza naman sa dinnan zaki dauki dauri daya na bakar roba. Kina ji na?"
"E Hajiya... " Bakinta na rawa da gangar jikinta ta sake cewa,
"Idan kuma tace tanaso da kaza fa Hajiya?"