← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 66

Sashe 42

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

B-junior: "ka rigani gaya masa. Mr Ray yau kai ne anan da dare haka?"

Ya dube su ya tabe fuska. Kafin yace,

"Garin ne sai a slow." Yana rufe baki wayar sa ta fara kara.

Mahaifiyar sa ce ke kiran sa. Ya dubi screen din wayar kafin ya dauka dakyar ya kara a kunnen sa.

Shiru shiru bai yi magana ba. Can yace,

"Bata gaya muku abunda ita ta fada ba? To kiyi hakuri amman gaskiya ni bata kwanta mun ba. Kiyi hakuri .... "

Cikin fushi ta kashe masa wayar. Ya zare wayar daga kunnensa yana mai duba screen din ko network ne yasa baya ji. Ashe kuwa da gaske katse kiran tayi.

Kansa ne ya fara sara masa. Ya mike daga zaman da yayi kawai.

"Ba dai har zaka tafi ba "

"Eh tafiya zan. Kai na ne yake ciwo ga tashin safe da zanyi zuwa zan na kwanta. "

"Okay sai da safe."

"Sai da safe."

"Yauwa Allah ya tashe mu lafiya." Ya fada yana mai sake basu hannu sukayi sallama

Ya shiga mota ya bar majalisar zuwa gidan su. Yana tafe yana saaqa da warwararewa. Haka ya karasa gidan ransa na sosawa.

Kansa da hafsat ta chaza masa ga maganganu marasa dadi da mahaifiyar sa ta gaya masa na bacin ran abunda yayiwa hafsat din. Don tuni har ta kira waya ta gaya mata.

Daki ya shige ya watsa ruwa hadi da dauro alwala . Kan gado ya hau ya kwanta bayan ya saka wayar sa a silent.

Ya daga kansa sama yana tunani. Ya jima kafin bacci ya dauke shi. Cike da mafarkai kala kala.

______
     Da safe bayan wayewar gari. Hajiya ya dauka zuwa asibitin kunne da yake kai ta. Duk wata. Likita ya bata magunganu suka tsaya suka saya. Kai ta gidah yayi shi kuma ya wuce gidan su B-junior.

Sañnu ahankali haka kwanakin hutun su ya wuce . Suka dawo makaranta . Dawowar su hutun ba karamin dadi yayiwa Rayyan ba. Kasancewar yayi kewar muradin ran sa Madeeha.

Haka dai yayita nacin KULA ta. Bini bini yana biye da ita tamkar rakumi da akala. Duk inda ta saka kafa yana biye da ita

Haka zai ta nacin yi mata magana. Sai ta dau lokaci kafin ta bashi amsa. Hakan da suke ba karamin bakan ta ran baby Saj yake ba. Ita tanata wahala akan ya karbi soyayyar ta yaki. Kwata kwata ma yi mata yake tamkar ita din kanwar sa ce da suke jini daya.

Kamar ko da yaushe. Ranar ta ke Monday sun gama presentations dinsu na wani lecture.

Fitowa tayi ta zauna akan kujerun da suke a farfajiyar wajen faculty. Tana zaune tana danna yar wayarta me cocilan da yazed ya saya musu ita da Fareeha kowa daya.

Wata motace ta zo ta faka awajen da Madeeha ke a zaune. Wajen number an rufeta da wani bakin yadi bake dake nuni da privacy.

Kallo daya Madeeha tayiwa motar ta juyar da kanta gefe. Befu tsawon mintina biyar zuwa shida ba aka fito daga cikin motar.

Sanye saj-jeedah take cikin kayan riga da skirt na atamfa. Ta dora mayafi a gefen kafadar ta kalar kayan.

Takun takalmanta ne suka saka Madeeha juyawa baya. Hango ta tayi tana tafe tana karkada mukullin motar ta ahannun ta na dama.

Ta isa ga Madeeha ta tsaya kerere akan Madeeha tana taunar cingam( chewing gum).

"Sannu ko." Ta fada hadi da komawa gaban ta ta tsaya.

"Yauwa sannu." Madeeha ta amsa mata. Hadi da janye yar jakarta dake gefen ta ko zama zatayi ita baby Saj din.

"Ga waje idan zama za ki."

"Ba zama ne ya kawo ni wajen ki ba."

"Oh okay! Allah sarki."

"Kina ji ko?"

"Ina sauraron ki"

"To ki sake bude kunnuwan ki da kyau...."

Madeeha ta sauke zuciya. Ta daga kai ta dubi saj-jeedah da ke cika tana batsewa.

"Baiwar Allah batan kai kika yi ne? Saboda tunda nake a rayuwa ta magana ta fatar baki bata taba hada mu ba. Bansan ki ba. Ba..."

"Ni na san ki. Sanayyar ce ma ta saka na zo don na gargade ki akan abu mafi soyuwa da ni. Zan iya rabuwa da komai akan sa"

Madeeha tayi murmushi . Ta ajiye littafin da ke kan cinyarta a gefe .

"Ina sauraron ki...."

"Yauwa na zo maki a mutum. Saboda inaso hakan ya zama na farko kuma na karshe. Don idan kika sake hukunci na biyu ba da hannu na zan dauka ba. Daga rana irin ta yau ki futa a harkar Rayyan Hammad. Rayyan Hammad MALLAKIN ZUCIYAH ta ne ni daya babu wata kuchaka. Ni kadai na isa na KULA Rayyan. Tun muna kanana muke tare da shi. Lokaci daya kinzo kin shiga tsakanin mu.... "Ta karasa fada tana huci.

Sosai maganganun saj-jeedah sun sanya Madeeha mamaki kwarai matuka da kuma dariya. Ta shiga babbaka dariya sosai harda rike ciki. Hawaye daya na bin daya saboda azabar dariya.

Saj-jeedah takai kololuwar karshe a maqura. Ji take tamkar ta janyo ta ta lallafta mata mari hagu da dama. Sai dai ta danne kawai ta sake duban Madeeha tacika tayi fam. Cikin bacin rai ta sake ce mata,

"Ki deebi ahankali. Ruwa ba sa'an kwando bane. Ke kanki kinsan Rayyan ba tsaran ki bane. Dangin ku rankatakaf ba masu kudi bane ba masu mulki ba ba kuma masu sarauta ba. yar gidan malam shehu ce ke na soro me dattin hula."

Madeeha na daukar maganganun a kwakwalwar ta suna shige wa bata kulawa. Amman karashen maganar ta ya kona mata rai. Ta da daga kai ta dube ta,

"Akan namiji kike fadan wadannan abubuwan? Na dauka kina cikin jerin matan da suke rike da karatu ko sana'a . Sai yanzun na tabbatarwa kai na kina cikin jerin wahalallu masu wahalar da rayuwar su akan namiji. To ki bude kunnuwan ki da kyau kiji. Shi wanda kike ta ikirarin fadan sa kina tada jijiyoyin wuya baya gabana. Dede da sakan daya be taba burgeni ba. Bantaba sashi acikin sahun mutanen da ke gabaana ba. Karatu ne ya kawo ni makarantar nan. Kokari na da hazaka ta ne yasa na ci karatu a makarantar nan kyauta. Kuma Alhamdulillah kullum cikin godiya ga Allah na ke da yasa muka tashi da wadatar zuciya agidan mu. Kudi, Mulki ko sarauta ire iren ku suka dama... Sai abu na karshe da zan maki gargadi akai ....

Ta fadi haka hadi da mikewa tsaye ta rataya jakarta a kafada. Tana mai kallon agogon yar wayar ta me cocilan dake hannun ta.

"Ina mai baki shawara. Da ki tsaya ki fuskanci karatun ki. Namiji bashida tabbas. Zaki yi ta wahal da kan ki ne . Shawara na baki kyauta. " Tana karasa fada ta ketare ta bayan ta ta wuce ta.

Dai dai zuwan Rayyan wajen. Ya bi bayan Madeeha da sauri yana kiran ta. Taki juyawa. Ganin zai tara mata mutane sai ta tsaya chak.

Ya karasa wajen ta yana sauke numfarfashi.

"Madeeha.....

MX✓

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: 36_

_ZAFAFA BIYAR 2023_

  Juyawa tayi ta dube shi. Saj-jeedah na tsaye daga inda take tana hangen su. Yayin da idanuwan ta suka cika taf da hawaye.

"Ina zaki?"

Ta dauke kanta daga duban sa tana mai kallon wani waje daban.

"Madeeha .. Nayi lefi ne?"

Ta girgiza masa kanta. Ya sake rage sautin muryar sa. Cikin murya tamkar ta rada rada ya sake cewa da ita,

"To waya taba mun ke? Uhmmmm?"

Ta daga kanta ta sauke akan saj-jeedah dake daga kai irin idan ta sake kula Rayyan to za ta ga hukunci

Wani murmushi madeeha tayi ta zare jakarta da ke gefen kafadar ta .

"Dan rike mun na gyara takalma na."

Rayyan ya dashare hakora. Yayi hanzarin karbar jakar ya rike mata yanata hangame baki yana murmushi.

"Ko zaki zauna a kujera ki gyara?"

"Alright...Mu je." 

Yana gaba tana biye da shi a baya. Ta juya sukai ido hudu da saj-jeedah tayi mata murmushi irin na kiyi abunda zaki yi dinnan..

Kololuwar takaici ta takure wa saj-jeedah a makoshi. Ta juya hawaye ya fara zuba a idanuwan ta. Ganin yadda Rayyan din ke rike da jakar Madeeha. Ita kuma madeehan ta sunkuya zaune akan kujera tana gyara zaman takalmin kafarta.

"Na gama " Ta mike tsaye hadi da mika hannu Rayyan ya bata jakarta.

Sai faman murmushi yake yau Madeeha na KULA shi.

"Nagode" Tace dashi bayan ta karbi jakarta ta. Hadi da sakar masa wani tattausan murmushin.

Har bakin lecture hall yayi mata rakiya suna tafe su biyu duk kwua da ba hira suke ba. Sun dace matuka da juna gwanin ban sha'awa ga duk wanda ya dora idanun sa akan su.

Saj-jeedah bata dai na kallon su ba. Har sai da Madeeha ta shiga lecture hall yayin da shi kuma Rayyan din ya mike ya tafi nasu department din.

Jikin ta a sanyaye ta juya ta bude motar ta ta shiga . Ta saka key hadi da dora kanta akan sitiyari. Ta rasa ma ina zata nufa.

Sam ba zata iya shiga class ha yanzu saboda ranta ya kai kololuwa a baci. Baki daya jinta take tamkar wata marar lafiya. Gabobin jikin ta duk sun saki.

Fita tayi daga cikin makarantar zuciyar ta na cigaba da sakawa da warwara. Ta shiha shawara da kanta tana neman mafita.

Kai tsaye ta yanke shawarar zuwa wajen mahaifiyar su Rayyan din don gaya mata halin da ake ciki.

Gidan su ta nufa ZUCIYAr ta na sake tunzura ta da ta fayyacewa mahaifiyar Rayyan din komai tun kafin lokaci ya kure mata.. kada nan gaba Rayyan din ya mata nisan kiwo.

Tana zuwa mai gadi ya bude mata kasancewar ya san ta. Ta shiga farfajiyar cikin gidan ta faka motar ta. Kanta tsaye ta shiga cikin parlorn gidan bakin ta dauke da sallama.

"Assalamu alaikum..."

"Wa'alaykm salam.."
Hajia Bintu ta amsa ta tana daaga zaune a kujera a parlorn kanta a sama.

"Mama.."

"Ah wa nake ji kamar Saj-jeedah."

Saj-jeedah tayi murmushi. Ta samu waje ta zauna,

"Ina wuni Mama.?"

"Ba gajiya saj-jeedah. Ya gidah?"

"Lafiya kalau Alhamdulillah."

"Ma shaa Allahu. Ya su Hajiyan?"

"Suna nan kalau."

"Ma shaa Allah Allah ya temaka. Ya karatun kuna ta yi ko?"

"Muna ta yi Mama."
Chapter 42 · 0% Book details