← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 66

Sashe 27

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lamarin na ki ne Fareeha ya fara wuce gona da iri. Muna ta rokon Allah ya yi mana canji a rayuwar mu. Allah ya karba addu'oin mu ya mana canji da dawowa nan gidan. Me muke anan din? Har wani aikin wahala mu ke anan.? Kar dai kiwa Allah butulci. Lokacin da muna unguwar gyada iya ebo ruwa kadai sai muyi sawu goma. "

"Kiji ki da wata baudaddiyar magana ke kuma... "

"Matsalar ki ce."

"Matsalar ki ce dai...."

Nan suka fara kokawar wasa. Kafin su fashe da dariya . Fareeha ta mike ta shiga bandaki ta wanko bakinta ta fara nata aikin . Madeeha ta tattare dakin sannan ta shiga bandaki tayi wanka.

Bayan sun kammala dukkanin aiyukan da zasu yi. Dakin ummy suka nufa suka gyare tas. Ummyn ta futo daga bandaki ta dawo parlor. Junaid ma ya shiga parlorn ya zauna. Bayan ya zube a kàsa ya gayshe da mahaifiyar ta su cikin girmamawa. Su Madeeha ma suka fara gayshe da shi

"Yaya Ina kwana...?"

"Yaya barka da safiya.."

"Barkan mu dai Fareeha da Madeeha.. Fatan kun tashi lafiya?"

"Alhamdulillahi Yaya."

"Lafiya Alhamdulillahi Yayan mu."

"Ummy ina kwana mu sake gaysawa."

"Ummyn mu ina kwana?"

"Lafiya Alhamdulillahi biyu kyautar Allah.. Madeeha janyo kofunan can ko ku harhada shayin."

"Tohm ummy."

"Ke kuma Fareeha dakko biredi yana kan durowar kitchen."

"Tohm ummy."

Junaid ya gyara zaman sa. Kansa akan hannun sa da yake murzawa yace,

"Ummy ..."

"Na'am Yayan su"

"Daman yazed ne dazu bayan mun dawo daga masallacin sallar asubah.."

"Eh ina sauraron ka Yayan su "

"Yauwa to shi ne yake cewa wai dame dame ne suka kare a kayan abinci da kayan shayin mu? Za'a kawo."

"Allah sarki Yazed. Su dai basa gajiyawa. Kyale shi Yayan su. Muna da sauran kayan abinci da kayan shayi. Kaga har rafin kanya na tafi da wasu daga ciki na kai wa su Innarajo."

"Wallahi basa gajiyawa. Sunada kyawawan zukata. Sai fatan Allah ya saka musu da mafificin alkhairi."

"Wallahi kuwa. Allahumma Aamin"

"Aamin Yaa Rabbi..."

Su Fareeha suka dakko kayan hadin karin safe. Nan da nan ummy ta harhada musu komai suka fara yin karin kumallon.

Intercom din su ce ta fara kara. Lokacin har sun kammala karyawar abincin da suka ci. Fareeha ta dauka da sauri ta saka a kunnenta.

Daga cikin gidan ne suke kiran su tanan duk kanin lokacin da suke bukatar wani abun . Ko neman wani daga cikin su

"Hello... Hibba! A'ah Fareeha ce. Eh mun tashi. Eh mun ci abinci. Okay toh"

Ta ajiye intercom din bayan ta amsa kiran. Suka zuba idanu suke bun ta da kallon karin bayani.

"Hibba ce ta kira wai mun tashi ne? nace eh!. Mun ci abincin safe? nace eh. Tace wacece ke magana Madeeha? Nace mata Fareeha ce. Wai to gata nan zuwa. "

Bata karasa rufe baki ba kuwa Hibba ta doka sallama ta shiga parlorn na su. Junaid ya fice waje bayan ya tsaya sun gaysa da Hibba.

Kaya ne dauke a hannun ta. Da wasu kayan a hannun wata mai aikin su da ke musu jeka ka dawo.

Zube kayan tayi akan kujera. Yayinda me aikin ma ta dora su akan na hibban data ajiye.

"Je ki Lantana."

"Toh."

"Ummy ina kwana?"

"Lafiya kalau hibbatullah. Kin tashi kalau?"

"Alhamdulillahi ummy."

"Hajiyan na gidah?"

"Eh."

"Toh bari naje mu gaysa."

Fucewa ummy tayi zuwa cikin gidan. Ta basu wuri. Hibba ta gyara zaman ta tana danna wayar da ke hannun ta. Kafin ta ajiye a gefe ta dube su tana cewa,

"Gobe za'a fara orientation/matriculation din mu. So duk yau ake zuwa adau elective courses din da ake so da sauran cike ciken abubuwa daya danganci makarantar da bangaren da mu ka dauka na makaranta."

"Tohm... Idan na gane nufin ki... Kina maganar mu shirya kenan mu tafi makarantar.?" Cewar Madeeha

"Eh haka nake nufi."

"Wadannan kayan fa?" Fareeha ta tambayi Hibba tana mai nuna kayan da yatsan ta daya

Madeeha ta juya ta dubi Fareeha. Ta Kona mata rai da tambayar da tayi wa Hibba. Fareehan taki kallon ta. Hakan yasa Madeeha sake tsura mata idanu. Tana juyawa ta zabga mata harara.

"Kayan ku ne.... Bana bukatar su. Bansani ba ko..Kuna so?"

"Mungode Allah ya saka da alkhairi." Madeeha ta fada tana gyara zaman kayan

"So kai... Ire iren su daman na ke bukata. Dan idan kayanmu na ainihi zamu sa ka ba Wanda zai jera da mu."

Takaicin kalaman Fareeha. Yasa Madeeha mikewa zata bar wajen.

"Ina zaki madee babe..?" Hibba ta tambaye ta.

"Zan gyara ne. Ba kin ce zamu je makarantar ba?"

"Eh haka na fada. Ni ma bari na je na shirya sai mu hadi a wajen mota." Fareeha ta raka Hibba har bakin kofa

Tukun sannan ta koma ciki tanata murna. Dai dai da dawowar ummy daga cikin gidah.

"Ke kuma rawar me kike?"

"Ba zaki gane ba ummy. Kinga tagomashin arzikin da Hibba ta mana?" Ta shiga daga kayan tana mai wa ummy nu ni

"Ah ah ah... Rangadi. Allah ya saka mata da alkhairin sa. Su dai basa gajiya da temakawa."

"Amin wallahi kuwa."

"Wai ina Madeeha ne?"

"Ta shiga daki. Rabun rai. Kizo inji ummy."ta yi hanyar dakin tana kiran madeehan

Alokacin Madeeha ta gama sauya kayan ta zuwa wata atamfa kalar hoda mai torches baki. Ta yafa wadataccen mayafin ta baki.

"Kai dan Allah cire wannan kayan ki saka...."

"Ba zan saka kowanne ba. Matsa na wuce."

"Wai fushin me kike ne?"

"Tambaya ta kike fushin me nake Fareeha?"

"Eh tambayar ki nake... Saboda na kasa gane meyasa kike fushi da ni. Dan Allah mena miki?"

"Ba abunda kika mun Fareeha. Kawai dai kin fara sauya halayen da na san ki da shi.."

"Sauyin halaye kuma Madeeha? Meyasa kikace haka?"

"Bar zancen nan kawai... Ki sauri ki shirya mu tafi."

Bata sake ce da ita kanzil ba ta hade kayan credentials dinta original da photocopy takardu ta zuba a jaka ta fita.

"Ummy kin dawo?"

"Eh na dawo Madeeha.... Ai nace kina ina ashe har kin shirya."

"Eh wallahi ummy "

'ubangiji Allah yasa albarka acikin karatun nan da zaku fara. Allahumma Amin"

"Amin Aamin ummy.",

Fareeha ta futo daga cikin daki dauke da daurin zani zatayi wanka.

"Raba mana kayan Madeeha."

"Ke rike ni ba son su nake ba."

'ummy kinji abunda take fada?"

"Ke Madeeha meyasa kikace haka?"

"Bakomi ummy kawai dai bana son kayan ne. "

Fareeha da ummy suka bude bakunan su cike da madaukakin mamakin kalaman na Madeeha ......

_INA JAMA'AR TA MU? KU MARMATSO KUSA . GA TAGOMASHIN ARZIKI. SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI. MUN GWADA DOLE MU BADA SHEDA_

_INA AMARE, UWAYEN GIDA, YAMMATA? IYAYE MAZA DA KE SON FARANTA RAYUKAN MATAN SU DA YAYAN SU DA MA KANNEN SU?_

_ALBISHIRIN KU. GA GORO. DOMIN WANNAN DADDADAN LABARI DOLE MU BAKU ALBISHIR DA ALHERIN GORO. GORON MA FARI KAL KAL_

_WAI AKACE KAMSHI RAHAMA NE... KAMSHIN MA MUSANMAN ME SANYAYA ZUCIYA DA RATSA MAGUDANAR JINI DA TSOKA._

_INA MASU NEMAN KAMSHIN TURAREN SAUDI ARABIA? T'CHAD DA MAIDUGURI? IRE IREN KAMSHIN DA BAYA BIN ISKA YANA KAMA WAJE YA RIKE GIDAH..._

_KAMSHIN TURAREN KAYA, TURAREN GIDA, TURAREN JIKI, TURRARN GASHI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN WANKA, TURAREN WANKI, TURAREN MOPPING, TURAREN BANDAKI, TURAREN LABULAYE DA ZANNUWAN GADO, AIR FRESHENER DA TURAREN AKWATUNA DA DRAWER DA MOTA... KAI HAR MA DA TURAREN DA KE CIRE BACIN RAI YA MUSANYA DA FARIN CIKI SABODA TSANANIN SANYAYAWAR SA DA YAYE DUHU DA DAMUWA_

_BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA NAU'IKAN TURARUKA NA KHUMRAH KALA KALA. SUNADA TURAREN RUWA NA FESAWA DANA MAIKO. SUNADA KAYAN GYARAN JIKI.._

_SUNADA KULACCA DA SAURAN BODY BUTTERS MASU YAYE WARI KODA KUWA AN YI KWANAKI BA WANKA BARE WANKI._

_SUNADA KABBASA TA TURARA KAYA DA KASAKEN TURARUKAN WUTA NA KARFE DANA KASA DAMA NA ZAMANI YAN WAJE._

*_YERWA INCENSE AND MORE_*

_YERWA INCENSE AND MORE_

_YERWA INCENSE AND MORE_

_MASARAUTAR KAMSHI KENAN. KAYAN SU NA AKAN FARASHIN SARI DA SAYA DAYA DAYA.. SUNA YIWA AMARE HADI DA UWAYEN GIDAH DAMA YAMMATA. SUNAYIN NA TARON SHAGULGULAN BIKI DUK AKAN FARASHI MAI RAHUSA_

_BA'ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNA DA TARIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA RAHUSA HADI DA INGANCIN DA ALKALUMA SUNYI KADAN WAJEN BAYYANA MUKU._

_SUNA TURA KAYAYYAKIN SU FADIN NAJERIYA DA KETARE BAKI DAYA._

_ADIRESHIN SU. SUNA GARIN KANO DAURA DA TITIN DA ZAI SADAKA DA GARIN MAIDUGURI_

_SUNA KAN MANHAJOJIN SU DAKE KAFAFE DA DAMA KAMAR:_

_INSTAGRAM: @yerwaincense_and_more_

_FACEBOOK:yerwacollection_

_WHATSAPP: 08095215215/09044191709_

_A YANZU HAKA KAMFANIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE SUNA SALES DIN KAYAN SU NA 250ML NA TURAREN WUTA DA KUMA 240 DA 190ML NA KHUMRAHS_

_IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE AKWAI RAGIN KUDI DA HADI NA MUSANMAN DA ZAA YIWA DUKKANIN KAYAN DA KUKA SAYA._

_KYAU!! INGANCI! RAHUSA!! KAMA JIKI DA GIDAH!! AIKI!! ADADE ANA MOREWA SAI KAYAYYAKIN TURARUKAN KAMFANIN:*YERWA INCENSE AND MORE*_

_____
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

*Thanks for choosing us*🔥

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼:24_

*Ummy* ta matsa kusa da kujera inda kayan suke. Ta daddaga su tana mai bubbuda su da kallon gaban su da bayan su

"Menene aibun su Madeeha. ?"

Madeeha ta danyi murmushi kafin tace,

"Wallahi ummy ba abunda sukayi. Kawai dai ni naji bana kaunar saka su. Idan na saka su dinne sai naga tamkar ba ni madeehan ba. Ina daukar kai na a wata daban... Ko kayan kwanaki data babbamu na kasa saka wasu daga cikin su. "

"To yanzu ai jami'a ku ka shiga Madeeha. Da munada hali. Ai har sabon dinkuna zamu muku na zuwa makarantar . Ni banga lefin kayan nan ba Madeeha "

Madeeha sai tayi shiru bata sake cewa komai ba. Ummy ta dubi Fareeha tace,

"Dauki duka ke. Tunda tace bata so."
Chapter 27 · 0% Book details