← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 66

Sashe 28

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Rabin rai kar muyi haka da ke." Fareeha ta fada tana kokarin kamo hannun madeeha.

Maheeda ta lura ummyn bata ji dadi ba. Don haka ta matsa wajen kayan ta dauki set uku.

"Gashi na dau wadannan sun ishe ni."

"Yauwa to kinga hakan shine yafi. Allah ya kara hada kan ku Amin"

"Aamin ummy. "

"Aamin"

Madeeha da ummy suka zauna a parlor suna hira ya yinda Fareeha ta shige bandaki ta yo wanka. Hadi da shiryawa cikin daya daga cikin dandatsesen lace din da Hibba ta basu. Ta yafe jikin ta da wani mayafi me kyau sosai.

"Yauwa na shirya ni ma."

"Ah iyye kashe kala tawaje na."

"Allah!!nayi kyau ?"

"Sosai ma kuwa."

"Ma shaa Allahu."

Fita sukayi zuwa sashen su Hibba. Suka gaishe da maman su hibban . Sun Dan dauki lokaci suna jiran Hibba. Kafin ta karasa shiryawa ta fito.

"Sannun ku. Ashe har kun shiryo."

"Eh"

"Kin fito ke ma ras. "

"To mu tafi ko? Wai ina Yayan ? "

"Yana waje ai"

"Tohm mun tafi mama."

"Toh shikenan. Sai kun dawo. Allah yabada sa'ar karatun"

"Aamin"

"Aamin Mama. "

Yazed ne ya shirya don kai su. Yana tsaye a jikin motar sa qirar glk data sha fenti kalar sararin samaniya.

"Kun fito yan kanne na?"

"Yaya barka da safiya."

"Yaya barkan mu."

"Yaya Yazed ina kwana?"

Suka shiga gayshe da shi daya bayan daya

"Lapia kalau. Yan kanne na. Kuce har kun shirya ko yau sai jami'a ko?"

"In shaa Allah yaya." Cewar Hibba.

Ya yinda su Madeeha suka murmusa kawai.

"Biyu kyautar Allah. Hibbatullah. Ku shiga mu tafi ko?"

"Eh Yaya..."

Shiga sukayi. Hibba ace agidan gaba. Ya yinda Madeeha da Fareeha ke a bayan mota.

Ya tashi motar da addua suka fice daga cikin gidan.

"Wacece zata karanci international relations ma?"

"Ni ce Yaya..." Madeeha ta fada tana matsa yan yatsun ta.

"Ke kuma wani course ne ma?" Ya juya yana kallon Hibba.

"Haba Yaya wai ka manta.? Irin na Nadia. Tare muke da Fareeha"

"Kinsan abubuwan se ahankali. Sai ke."

Ya saita mirror saitin Fareeha. Ta dan yamutsa fuska kafin tace,

"Mass communications..."

"Masha Allahu. Allah yasa albarka a karatun da zaku saka fara"

"Aamin ya Rabbi."

"Aamin Yaya."

"Aamin."

Yazed ya murza madannin dake jikin gidan CD. Nan da nan kuwa speaker motar ta fara tashin karatun suratul Yusuf. Yazed ya shiga bin karatun ahankali yana lumshe idanu....

✓✓✓✓✓

Rayyan ne da kansa ya kai su Hajiya Fadila da Bappah Hydar airport. Jirgin su zai tashi zuwa kasa mai tsarki .

Su hajiyan suka fita daga cikin motar tare da kayan su. Hajiyan ta rike hannuwan Rayyan tana ta masa addua.

"Dan Allah! Dan yaye karka yaada zuwa makarantar nan. Ka cigaba da zuwa kaji ko?"

"In shaa' Allah Hajiya "

"Yauwa Rayyanu nah. Karka manta da zuwa gidan bappanin naka kaji ko?"

"Tohm Hajia. Yadda kikace ai haka za'ai."

"Tohm Allah ya bada sa'ar karatu."

"Aamin Hajiya Allah ya kai ku lafiya. Ya kara miki lapia yaja kwanan ki "

"Da imanin Allah."

"In shaa' Allah da imanin Allah Hajjaju makkatun."

Sake tsugunnawa yayi ya musu sallama. Hajiyan da Bappah Harith da Bappah Hydar . Da Aunty Kulu matar Bappah Haydar .

Ya koma motar sa ya shige. Wayar sa ya janyo da screen dinta ke ta haske. Missed calls ne rututu na baby Saj. Don haka bai bi takai ba. Ya jefata acikin aljihun gaban rigar sa ya tashi motar yabar cikin airport din .

Kai tsaye ya wuce gidan su. Wanka ya fyalla. Yayi shiga cikin jallabiyar sa baka sabuwa gadaqau da Hajiya ta kawo masa tsaraba a waccen tafiyar tata ta baya.

Ya bi jikin sa lungu da sako ya shafe da turare kamfanin giogio Armani da Hugo boss.

Ya zauna kenan yana kokarin janyo PSP zai buga... Muryar Hajiya ta shiga masa reto a cikin kwanyar kansa ta,

Dan Allah!Dan yaye karka yada zuwa makarantar nan. Ka cigaba da zuwa kaji ko?"

Sauke nannauyar ajiyar zuciya yayi ya mike da sauri . Kai tsaye yafi ce daga cikin dakin sa zuwa wajen harabar da ake adana motocin gidan. Shiga yayi cikin motar sa ya tashe ta yabar cikin gidan zuwa makaranta.

Ya zaro wayar sa ya kira B-junior ya danno T-Boy zuwa conference call .

"Kun shiga makaranta kuwa?"

B-junior : "Mr Ray lafiyar ka kuwa?"

T-Boy: Tambaya mana shi please.. Kunnuwa na ne ke jiye mun gaibu ko kuwa?"

Rayyan yayi murmushi tamkar suna ganin sa. Ya katse kiran . Direct ya wuce gidan su T-Boy. alokacin T-Boy din ma na malale akan gadon sa da ko tashi baiyi ba. Rayyan ya azalzale sa ya tashi.

"Wai meye matsalar ka da wani zuwanmu makaranta yau? Gaskia bacci bai isheni ba."

"Anqi a barka kayi baccin. Tashi mu tafi"

T-Boy na ta kananun mita ya mike ya shige bandaki yayi wanka yaci abinci tukun sannan suka wuce gidan su B-junior .

Kowanne na cikin motar sa. Motocin kuma rantsattsu na alfarma. Wanda suka tada kai da kudi suka koshi.

Kai tsaye suka wuce jami'ar ta su ta

*BIRMINGHAM UNIVERSITY NIGERIA*
(UNIVERSITY IN KANO)

TUNDA suka shiga cikin makarantar, Su Madeeha suka baza idanuwan su suna kallon ko'ina na makarantar. Harta Hibba da ta taso gidan masu kudi sai da ta raina ajinta ranar.

"Mun zo fa..." Yazed ya fada yna bin kowannen su da kallo.

"Yaya na rasa me zan fada ma. Lord! I'm outta words .. Makarantar nan ta hadu fiye da kalamai. Ta hadu beyond my wildest expectations." Hibba ta fada tana mai sake baza hanci

"Sai ma kun shiga ko'ina da ko'ina ma shaa Allahu."

Suka bubbude kofofin motar suka fito. Kowannen su yayi kyau kwarai matuka

"Ku biyu tunda department daya kuke kuje ku fara rage wasu abubuwan. Ina Madeeha ke kuma muje na yi miki rakiya." Ya nuna Fareeha bayan ya gama fadar abunda zai ce.

Fareeha tayi dariya tana nuna Madeeha da yatsa.

"Ga Madeeha nan."

Suka kyalkyale da dariya ya juya saitin Fareehan ya mata wani kallo mai dauke da tacacciyar kaunar da yake mata.. Amman ya kasa gaya mata duk tsawon shudewar lokuta.

"Mu je ko.., Madeeha?"

Madeeha tayi gaba yana biye da ita. Kafin su jera atare suna tafe suna hirar su.

Zuwan su kenan suka faka a kofar student affairs gate. B-junior nata jera tsaki. Gefe daya Kuma T-Boy ne ke ta kamo sunan Rayyan yana kananun mita.

Rayyan ya juya ya sakar musu tsaki.Dan shima mitar da suke masa ta ishe shi,

"Ya isa hakanan haba mana. Nace muku ni bansan yau ba lectures ba. Bansan da wani orientation/matriculation day na sababbun dalibai ba. Da ace na sani me ze kawo mu cikin makarantar.? Bayan lectures ma ba zuwa mike ba. "

Haka dai sukaita korafe korafen su suka dena. Takaicin su ya sashi matsawa can nesa da su wajen wani benchi ya zauna. Ya daga wayar sa saitin idanun sa yana dannawa.

Dai dai lokacin da Madeeha da yazed suka tunkaro wajen. Yazed na bayan ta kadan yana waya.

Yayinda Madeeha ke agaba. Guguwar iskar da akeyi ta daga mayafin ta ya koma gefe daya. Ta saka hannu tana janyo mayafin don rufe jikin ta

Duk abinnan akan idanun Rayyan daya saki lebe da saleba yana binta da kallo tamkar zai mayar da ita cikin sa.

Kallo ne daya da yayi mata bisa qa'ida. Amman tundaga wannan kallon ZUCIYAR sa sai ta kamu da kaunar ta. Tamkar shigar iska haka kaunar ta ta shiga ilahirin duk wani sashe da rassa na jikin sa.

Madeeha ta juya tana jiran Yazed ya karaso. Yazed din ya mata alama da hannu da na zuwa. Ita kuma sai ta saki tattausan murmushi mai tafe da wanda ya kalla.

Har suka bullewa ganin sa. Rayyan bai fasa binta da kallo ba. Kallo ne kamar zai hadiyeta. Kallon ta yake tamkar zai mayar da ita cikin sa. Kallon ta yake tamkar ya dauke ta ya gudu. Kallon ta yake don tuni tamkar ta zamar masa MALLAKIN ZUCIYAH...

Yana can yana kallon hanyar da suka bacewa kallon sa. B-junior da T-Boy na tsaye kerere akan sa. Har sai da B-junior din ya dumama masa dundu a baya tukun sanan ya dawo daga duniyar kallon Madeeha daya lula.

"Kai meyee haka ne ? Lafiyar ka kuwa Mr Ray?"

'ina tayi?"

"Wa?"

"Wacece...Ina tayi? Ko gamo kayi? Yau kai ne da tambayar ina tayi? Mutum ko aljan?"

Rayyan ya ja kasan leben sa yana ciza. Hadi da fuzgar da zazzafar iska daga bakin sa.

Har ya tsaya yana tunanin ina mafita? Sai kuma ya bar wajen da sauri ya nufi hanyar daya ga tabi....

.
_INA JAMA'AR TA MU? KU MARMATSO KUSA . GA TAGOMASHIN ARZIKI. SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI. MUN GWADA DOLE MU BADA SHEDA_

_INA AMARE, UWAYEN GIDA, YAMMATA? IYAYE MAZA DA KE SON FARANTA RAYUKAN MATAN SU DA YAYAN SU DA MA KANNEN SU?_

_ALBISHIRIN KU. GA GORO. DOMIN WANNAN DADDADAN LABARI DOLE MU BAKU ALBISHIR DA ALHERIN GORO. GORON MA FARI KAL KAL_

_WAI AKACE KAMSHI RAHAMA NE... KAMSHIN MA MUSANMAN ME SANYAYA ZUCIYA DA RATSA MAGUDANAR JINI DA TSOKA._

_INA MASU NEMAN KAMSHIN TURAREN SAUDI ARABIA? T'CHAD DA MAIDUGURI? IRE IREN KAMSHIN DA BAYA BIN ISKA YANA KAMA WAJE YA RIKE GIDAH..._

_KAMSHIN TURAREN KAYA, TURAREN GIDA, TURAREN JIKI, TURRARN GASHI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN WANKA, TURAREN WANKI, TURAREN MOPPING, TURAREN BANDAKI, TURAREN LABULAYE DA ZANNUWAN GADO, AIR FRESHENER DA TURAREN AKWATUNA DA DRAWER DA MOTA... KAI HAR MA DA TURAREN DA KE CIRE BACIN RAI YA MUSANYA DA FARIN CIKI SABODA TSANANIN SANYAYAWAR SA DA YAYE DUHU DA DAMUWA_

_BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA NAU'IKAN TURARUKA NA KHUMRAH KALA KALA. SUNADA TURAREN RUWA NA FESAWA DANA MAIKO. SUNADA KAYAN GYARAN JIKI.._

_SUNADA KULACCA DA SAURAN BODY BUTTERS MASU YAYE WARI KODA KUWA AN YI KWANAKI BA WANKA BARE WANKI._

_SUNADA KABBASA TA TURARA KAYA DA KASAKEN TURARUKAN WUTA NA KARFE DANA KASA DAMA NA ZAMANI YAN WAJE._

*_YERWA INCENSE AND MORE_*

_YERWA INCENSE AND MORE_

_YERWA INCENSE AND MORE_
Chapter 28 · 0% Book details