← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 66

Sashe 40

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Da fari zan soma baki hakuri Hajian mu. Hakika shekaru sun ja. Bamuda tabbacin har yanzu hadiyya na raye ko akasin haka. Amman dai Yusha'u da ga Malama Asabe (me kosai) ya ce mun wasu fulani da ke kauyen rafin kanya sun je har kauyen . Yusha'u ya shedamun da ya dawo daga aikin da sukaje nema na kamfanin dandano da ke Lagos zamu je ni da shi zuwa kauyen rafin kanya. Wai matar da ake da tabbacin itace wadda ta rayu acikin hatsarin motar da sukayi yaranta biyu mace da namiji. To wai macen tata sai ta rasu a take awajen yayinda namiji dan ta daya da ita Hadiyyan sune sukayi rai. Amman ita matar sai ta samu rauni a idanun ta sakamon karfen motar daya fado akanta. Ruwan idanun ta suka tsiyaye ta makance. A takee alokacin ta makance. Ba idanun da zata sheda hadiyya ba yarta bace. Mutane sun tambayeta yaran biyu mace da namiji nata ne? Tace eh. Sakamakon ba idanun da zata sheda musu hadiyya ba yarta bace. .... "Ya karasa fada yana sauke gwauruwar ajiyar zuciya.

Hajiya Fadila ta jinjina kai. Kafin ta ce,

"Inaji ajiki na Hadiyyan tana raye in shaa Allah... Allah ya bamu saa Amin."

"Amin hajiya. Duk tsawon shekarun nan bamu da masaniyar hakan sai watan daya shude ko Hajiya?"

"Tabbas hakane.. Shima dalilin hakan da muka sani Asabe ce sila. Wannan baiwar Allah Asabe tayi kokari. Its tashiga ta fita ta jiyo abunda ke faruwa. Wai Ladiyo (kishiyar ta a baya) duk shudewar shekarun nan ba ta sauya hali ba. Kasan zuwan farko wai da yan kauyen sukaje don neman inda iyayen Hadiyyan suke ko eanda yasan danginta. Ashe ladiyon ce tace basu san wata Hadiyyah ba."

"Wannan mata ai ba zatai sanyi ba."

"Babu komai taje don kanta. Ai gashi nan sannu ahankali tana girban abunda ta shuka.."

"Wallahi Hajiya ai nake gayawa Hammadu nace masa ni fa tsabar saka Hadiyya a rai Allah har ta fara mun gizo da wata mata da ke makotan mu. "

"Allah sraki dan uwa me dadi. Allah ya bayyanata Amin."

"Amin hajjajun mu"

"Nagode muku dukkanin ku... Allah yasanya albarka acikin rayuwar ku. Allah ya kara muku dankon zumunci da kaunar juna. Allah ya bayyana yar uwar ku idan har tana raye Amin.."

"Amin Hajia.."

"Amin hajiyan mu"

"Aamin summa Aamin"

Haka dai suka amsa adduar mahaifiyar ta su. Kafin daga bisani suyi mata sallama. Kowanne ya nufi inda za shi.

Hajiya Fadila bayan futar su ta sake sauke zuciya hadi da sake kallon hotan su hadiyya tana mai runtse idanun ta...

Ya yinda labbanta ke ta doka adduoin samun nasara akan abunda suka saka agaba. ....

..
_INA JAMA'AR TA MU? KU MARMATSO KUSA . GA TAGOMASHIN ARZIKI. SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI. MUN GWADA DOLE MU BADA SHEDA_

_INA AMARE, UWAYEN GIDA, YAMMATA? IYAYE MAZA DA KE SON FARANTA RAYUKAN MATAN SU DA YAYAN SU DA MA KANNEN SU?_

_ALBISHIRIN KU. GA GORO. DOMIN WANNAN DADDADAN LABARI DOLE MU BAKU ALBISHIR DA ALHERIN GORO. GORON MA FARI KAL KAL_

_WAI AKACE KAMSHI RAHAMA NE... KAMSHIN MA MUSANMAN ME SANYAYA ZUCIYA DA RATSA MAGUDANAR JINI DA TSOKA._

_INA MASU NEMAN KAMSHIN TURAREN SAUDI ARABIA? T'CHAD DA MAIDUGURI? IRE IREN KAMSHIN DA BAYA BIN ISKA YANA KAMA WAJE YA RIKE GIDAH..._

_KAMSHIN TURAREN KAYA, TURAREN GIDA, TURAREN JIKI, TURRARN GASHI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN WANKA, TURAREN WANKI, TURAREN MOPPING, TURAREN BANDAKI, TURAREN LABULAYE DA ZANNUWAN GADO, AIR FRESHENER DA TURAREN AKWATUNA DA DRAWER DA MOTA... KAI HAR MA DA TURAREN DA KE CIRE BACIN RAI YA MUSANYA DA FARIN CIKI SABODA TSANANIN SANYAYAWAR SA DA YAYE DUHU DA DAMUWA_

_BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA NAU'IKAN TURARUKA NA KHUMRAH KALA KALA. SUNADA TURAREN RUWA NA FESAWA DANA MAIKO. SUNADA KAYAN GYARAN JIKI.._

_SUNADA KULACCA DA SAURAN BODY BUTTERS MASU YAYE WARI KODA KUWA AN YI KWANAKI BA WANKA BARE WANKI._

_SUNADA KABBASA TA TURARA KAYA DA KASAKEN TURARUKAN WUTA NA KARFE DANA KASA DAMA NA ZAMANI YAN WAJE._

*_YERWA INCENSE AND MORE_*

_YERWA INCENSE AND MORE_

_YERWA INCENSE AND MORE_

_MASARAUTAR KAMSHI KENAN. KAYAN SU NA AKAN FARASHIN SARI DA SAYA DAYA DAYA.. SUNA YIWA AMARE HADI DA UWAYEN GIDAH DAMA YAMMATA. SUNAYIN NA TARON SHAGULGULAN BIKI DUK AKAN FARASHI MAI RAHUSA_

_BA'ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNA DA TARIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA RAHUSA HADI DA INGANCIN DA ALKALUMA SUNYI KADAN WAJEN BAYYANA MUKU._

_SUNA TURA KAYAYYAKIN SU FADIN NAJERIYA DA KETARE BAKI DAYA._

_ADIRESHIN SU. SUNA GARIN KANO DAURA DA TITIN DA ZAI SADAKA DA GARIN MAIDUGURI_

_SUNA KAN MANHAJOJIN SU DAKE KAFAFE DA DAMA KAMAR:_

_INSTAGRAM: @yerwaincense_and_more_

_FACEBOOK:yerwacollection_

_WHATSAPP: 08095215215/09044191709_

_A YANZU HAKA KAMFANIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE SUNA SALES DIN KAYAN SU NA 250ML NA TURAREN WUTA DA KUMA 240 DA 190ML NA KHUMRAHS_

_IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE AKWAI RAGIN KUDI DA HADI NA MUSANMAN DA ZAA YIWA DUKKANIN KAYAN DA KUKA SAYA._

_KYAU!! INGANCI! RAHUSA!! KAMA JIKI DA GIDAH!! AIKI!! ADADE ANA MOREWA SAI KAYAYYAKIN TURARUKAN KAMFANIN:*YERWA INCENSE AND MORE*_

_____
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: 34_

_ZAFAFA BIYAR 2023_

  *Yana* daga kwance akan gadon sa. Tun bayan da ya dawo daga masallaci sunyi sallar isha'i...

Wayar sa dake hannun sa na dama yana ta jujjuyata. Kansa a sama yayin da ya lula duniyar tunani.

Message dinta ne ya sake shigowa a wayar tasa a karo na uku.

"Rayyan... Shine kaki daukar dik kiran da nake maka ko? To idan har kana gudun bacin rai na kaje kaga yarinyar nan na gaya maka. Yar babban gidah ce Wanda ake damawa dasu a gwamnati... Dan Allah karka bani kunya..."

Yana karasa karanta sakon ya girgiza kai kawai. Hadi da mikewa tsaye ya shiga zarya daga bango zuwa bango na dakin na sa. Ya hade hannuwan sa biyu waje daya. Kana kallon sa kasan akwai tufka da warwarar da yake yi.

Chan dai ya sauke zuciya kawai. Ya dauki wayar sa da ke kan beside locker ya zura ta a aljihun gaban rigar sa.

Ficewa yayi daga dakin na sa kai tsaye yayi dakin kakar su Hajiya Fadila. Tana zaune agaban gado ya yinda hoton da zu ke agabanta. Hannun ta rike da charbi.

Tana ganin sa ta hau murmushi tana bin sa da kallo cike da zallar kaunar da take yi masa,

"Dan Yaye.."

"Naam Hajjaju makkatun tawa ni daya."

Zama yayi a gefen ta ya kai hannuwan sa kan kafafun ta ya fara matsa mata su.

"Allah dai ya maka albarka dan yaye"

"Aamin Hajjaju makkatun.. Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana.."

"Da imanin Allah..."

"Da imanin Allah. Allah ya saka miki da ma daukakin alkhairin sa . Ki ta samun cigaba a rayuwar ki baki daya"

"Aamin danyaye. Amin"

Agogon hannun sa ya kalla. Kafin ya mayar da duban sa ga Hajiya Fadila.

"Hajiya bari na dan fita na dawo."

"To dan yaye a dawo lafiya."

Har ya mike sai kuma ya dan sunkuya ya dau ki hotan dake gabanta.

Ya tsurawa hotan idanu yana bin dukkanin yaran ciki su uku da kallo. Kamar su daya babu abunda ya raba su. Sai dai ita macen nada yalwar gashi kuma gashin girar ta sun hade...

"Da dadewa na taba ganin hotan nan awajen Bappah.. "

"Eh ...." Hajiya Fadila ta fada tana mayar da hawayen da ke kokarin zuba daga idanun ta

"Allah ya shiga lamarin." Ya fada a sanyaye. Don yasan labarin da ya danganci hotan.

Ya mayar mata da hotan gaban ta. Ya nufi wajen fita da ga dakin yana cewa,

"Toh sai da safe Hajiya. "

"Allah ya tashe mu lafiya dan yaye."

"Aamin Hajia."

Ko da ya fita kai tsaye ya wuce address da din mahafiyar ta sa ta rubuta masa na inda zai gana da yarinyar nan da ta hada su.

Yana tafiya ne akan titi. Yayinda yake dan kallon map ta wayar sa da ke bashi direction na gidan su yarinyar.

Babu ma nisa sosai. Ko da yake tsayawa yayi da motar sa abakin kofar gidah. Ya dan jima yana zaune bai fito daga cikin motar sa ba.

Daya daga cikin masu gadin gidan ya nufe shi yana mai tambayar sa bayan sun gaysa da vdwat,

"Wani kake nema ne ranka ya dade?"

Rayyan ya daga kai ya dubi mutumin da a shekaru mutumin ya haifeshi. Da alama kuma me gadin gidan ne.

"Nan ne gidan su Hafsat?"

"Hafsat wacce daga ciki? Kaga gidan can ma me gate ruwan kasa akwai hafsat a gidan."

'inde ba wrong direction map yabanj ba nanne gidan. "

"Me kace yaro? Menene kuma roderekshon...(Wrong direction..)" Mai gadin ya tambaye shi fuskar sa lumshe da farin ciki da kuma karin bayani da ga Rayyan din da yake so ya ji.

"Ayyah baba ba damuwa... Hafsat Bulama .kaman haka sunan ya ke .

Baban ya daga kai alamar tabbatarwa yace,

"Kwarai inde yar gidah minista, Wato farfesa Bulama kake fada nan ne gidan.."

"Toh sbikenan... Nagode baba."

"Zo ga waje ka faka motar ta ka.."

"To baba.."

Samun waje yayi daga nesa da dan gidan kadan yayi parking motar sa. Ya fito daga ciki ya zura mukullin a aljihun sa. Yayin da ya zaro wayar sa dake kara a aljihu. Mahaifiyar sa ce ya dauka ya kara a kunnen sa.

"Na'am!! Ga ni ma fa na zo ina kofar gidan. Tohm" ya katse kiran bayan sunyi sallama .

"Bari na maka iso ko.?" Dattijon me gadin ya ce da Rayyan haka. Ya yin da yayi gaba Rayyan din na biye masa a baya

Suka shiga cikin harabar gidan. Gidah ne babba na masu hali da yaji komai ya koshi.

Me gadin ya saka hannun sa ya danna madannin kararrawar da ke nuna sanarwar anzo gidan.
Chapter 40 · 0% Book details