← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 66

Sashe 30

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

_KAMSHIN TURAREN KAYA, TURAREN GIDA, TURAREN JIKI, TURRARN GASHI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN WANKA, TURAREN WANKI, TURAREN MOPPING, TURAREN BANDAKI, TURAREN LABULAYE DA ZANNUWAN GADO, AIR FRESHENER DA TURAREN AKWATUNA DA DRAWER DA MOTA... KAI HAR MA DA TURAREN DA KE CIRE BACIN RAI YA MUSANYA DA FARIN CIKI SABODA TSANANIN SANYAYAWAR SA DA YAYE DUHU DA DAMUWA_

_BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA NAU'IKAN TURARUKA NA KHUMRAH KALA KALA. SUNADA TURAREN RUWA NA FESAWA DANA MAIKO. SUNADA KAYAN GYARAN JIKI.._

_SUNADA KULACCA DA SAURAN BODY BUTTERS MASU YAYE WARI KODA KUWA AN YI KWANAKI BA WANKA BARE WANKI._

_SUNADA KABBASA TA TURARA KAYA DA KASAKEN TURARUKAN WUTA NA KARFE DANA KASA DAMA NA ZAMANI YAN WAJE._

*_YERWA INCENSE AND MORE_*

_YERWA INCENSE AND MORE_

_YERWA INCENSE AND MORE_

_MASARAUTAR KAMSHI KENAN. KAYAN SU NA AKAN FARASHIN SARI DA SAYA DAYA DAYA.. SUNA YIWA AMARE HADI DA UWAYEN GIDAH DAMA YAMMATA. SUNAYIN NA TARON SHAGULGULAN BIKI DUK AKAN FARASHI MAI RAHUSA_

_BA'ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNA DA TARIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA RAHUSA HADI DA INGANCIN DA ALKALUMA SUNYI KADAN WAJEN BAYYANA MUKU._

_SUNA TURA KAYAYYAKIN SU FADIN NAJERIYA DA KETARE BAKI DAYA._

_ADIRESHIN SU. SUNA GARIN KANO DAURA DA TITIN DA ZAI SADAKA DA GARIN MAIDUGURI_

_SUNA KAN MANHAJOJIN SU DAKE KAFAFE DA DAMA KAMAR:_

_INSTAGRAM: @yerwaincense_and_more_

_FACEBOOK:yerwacollection_

_WHATSAPP: 08095215215/09044191709_

_A YANZU HAKA KAMFANIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE SUNA SALES DIN KAYAN SU NA 250ML NA TURAREN WUTA DA KUMA 240 DA 190ML NA KHUMRAHS_

_IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE AKWAI RAGIN KUDI DA HADI NA MUSANMAN DA ZAA YIWA DUKKANIN KAYAN DA KUKA SAYA._

_KYAU!! INGANCI! RAHUSA!! KAMA JIKI DA GIDAH!! AIKI!! ADADE ANA MOREWA SAI KAYAYYAKIN TURARUKAN KAMFANIN:*YERWA INCENSE AND MORE*_

_____
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼:26_

_ZAFAFA BIYAR 2023_

_

*Hajiya* Bintu na parlorn sama ta jiyo alamun motsin an bude kofar kasa an shigo.

Rage muryar karar talabijin din da ke nuna faifan bidiyon labaran CNN tayi. Ta mike daga parlorn ta sauka zuwa kasan..

A kujerar dake cin mutane uku ta hange shi a zaune. Bayan kujerar ake gani ba gabanta ba. Don haka ta bayan ta gano shine.

Ta bude baki zata kira sunan sa kenan. Nabeelah 'yar ta ta karshe ta karasa parlorn tana kiran sunan Rayyan din.

"Hamma Rayyan..."

"Na'am baby sis.... Ya kike?"

"Lafiya kalau hamma. Ya su Amaal?"

"Duk suna nan kalau. Na baro ta zasuje excursion."

"Allah sarki."

Murmushi ne ya fadada a fuskar Hajia Bintun.Na ganin yadda suke ta hirar su kamar ko da yaushe idan ya waiwayo su.  Ta karasa cikin parlorn tana cewa,

"Rayyan..."

Juyawa yayi ya dubeta . Tamkar zai tashi da gudu yabar parlorn. Sai kuma ya danne kawai. Ya kakaro murmushi , saboda idan yana kallon ta. Rayuwar baya ce kawai ke dawo masa. Yana kuma sake ganin baqin ta. Don haka ya daure kawai tare da fada mata,

"Ina kwana?"

"Lafiya Lau Rayyan...Yau ka waiwayo mu kenan ko?"

Harshen sa ya dan zaro wajen lips din sa ya ciza hadi da furzar da wata iska mai dumi yace,

"Yanzu ma makaranta zan wuce. Agayshe da Bappah."

"Ba zaka zauna ya dawo ba ? Eh Rayyan?"

"Sauri na ke ne... Amman maybe na dawo tanan mu gaysa ko da ba yau ba."

"Yauwa to ..Dan Allah ka temaka kaji?"

"In'shaa Allahu.."

"Yaya ka fara zuwa Birmingham uni ko?"

"Eh baby sis.."

"Nima idan result dinmu ya futo Nan nake son shiga."

"Allah yabada sa'ar sakamako mekyau"

"Aamin Yaya.. Amin"

Har waje ta raka shi suna ta yar hirar su. Ya yin da Hajia Bintu ke leken su ta window.

Komawa tayi sama ta saki labulen jikin ta sanyaye. Ganin dik tsawon shekarun nan har yanzu yaki sakin jiki da ita.

×BIRMINGHAM UNIVERSITY NIGERIA ×

Sannu ahankali ya karasa makarantar daga gidan su. Yana driving a slow ne. Saboda ko zai gano wulgawar ta

Yana driving yana kallon side mirror. Ya dade awajen gate ba ita ba alamar ta. Har dai ya hakura ya shiga gate din da motar sa

Bai parking a faculty dinsu ba. Wajen student affairs yayi parking din motar tasa. Ya futo ya jingina da murfin motar.

Wayar sa ce tayi kara ya dauka ganin B-junior ne.

"Ina cikin makaranta ma a yanzu haka... Saboda me zan maka karya? Wallahi ina cikin makaranta. Alright sai kun karaso.."

Ko da B-junior ya katse kiran tsayawa yayi yana bin wayar sa da kallo. Yau Mr Ray ne ya riga su shiga school.

Da sauri shima ya tashi ya fada bandaki ya wanko jikin sa ya sauya zuwa wasu kaya da sukayi matukar masa kyau.

Yana ta tsaye a student affairs . Tamkar ance daga idanun ka. Dagowar da zeyi kenan ya sauke kyawawan dara daran idanuwan sa akan ta.

Tana tafe sanye cikin doguwar riga purple and white color ta atamfa. Ta yane kanta da wadataccen mayafin fari.

Da idanuwan sa ya shiga kare mata kallo. Ya yinda bugun zuciyar sa ya tsananta ana jiyo karar bugun.

Bangaren social sciences ta nufa . Yana biye da ita ta baya. Tamkar rakumi da Akala.

Ganin ta yayi ta tsaya agaban bulletin tana jotting wani rubutu a littafin da ke dauke a hannun ta.

Wani twin theatre ta nufa. Da alamun anan za'ai musu lectures din. Student sun dan fara taruwa.

Komawa yayi gaban bulletin din ya dauka a wayar sa. Yana tsaye ya rasa abunyi

Wasu maza sunzo wucewa sunata hira da alamar yan ajin ne. Kuma class rep ne da yan uwan sa dalibai. Saboda yadda yajiyo su suna maka masa kira.

Rayyan ya kasa samun nutsuwa sai da ya je wajen class rep din ya masa yan tambayoyin daya danganci ajin.

Malamar da zata dauke su course din ba zata samu damar zuwa ba. Amman tayi grouping dinsu ta aikawa da class rep ya kira suna da reg number duk wanda ke acikin list din yayi signing attendance.

Rayyan ya shiga ajin ya zauna. Daya bayan daya ana ta kiran sunayen su har Allah yasa akazo kanta . Aka fadi sunan ta da registration number dinta,

"Sms/16/Irs/00098657 !! Madeeha Sufyan zubair.."

Shine registeration number din Madeeha da sunan ta. Nan da nan kuwa Rayyan ya tariye sunan nata da registeration number din ta acikin kwakwalwar sa. Kafin daga baya ya tashi yafuce daga ajin.

Ya sake zuwa wajen time table din su Madeeha da ya tabbatar nasu ne sanan ya tafi. Zuciyar sa fara tas da ita. Ya samu abunda yake nema.

✓✓✓

Zuwan madeeha jami'ar. Ta sanyawa Rayyan wajibcin zuwa kullum ko da kuwa basuda lectures sai ya shigo dan Madeeha

Gashi bai taba mata magana ba. Amman dik wani abu da zatayi sai ya sani. Wata irin kauna yake mata marar algus.

Kauna wadda Allah kan dasawa dan Adam. Wacce batada iyaka akan wanda ake yiwa din.

Gashi lokaci ysna ta ja. Har sun saba da makarantar. Fateeha da Hibba department dinsu daya. Ya yinda ita kadai department dinta daban...

×××××××××××

Cikin nutsuwa su ke tafiya su biyu. Fareeha sanye cikin mayafi ja . Daya amshi kalar wasu torches da ke jikin material din jikin ta. Ya yinda Madeeha hijabi ta saka kalar sararin samaniya daya sha karin guga...

Madeeha ta dubi Fareeha,

"Kinsan cewa abunda kikayi baki kyauta ba ko?"

"Bangane abunda nayi ban kyauta ba. Me kike nufi Madeeha?"

"Hmm Fareeha kenan.. Kinsan shi zancen duniya ba ya boyuwa. Musanman zancen ma daya danganci wanin ka Fareeha... Ba'a canzawa tuwo suna.. Karki dore da sababbun halayen da kika tsira bazasu fissheki da komai ba sai da na sani agaba.."

Fareeha taja tunga ta tsaya a lokacin da kunnuwanta suka jiye mata abubuwan da Madeeha ke fada akan tah...

"Sharri zaki mun?"

"sharri kuma? Toh kinga ko furucin da kikai yanzu ba ya daya daga cikin halayen ki a baya Fareeha.."

Tsaki sosai taja. Da niyar ta sake dakatar da madeehan sai kuma wata mota ta tunkaro inda suke. Madeeha tayi gaba kawai bata sake bi ta kan ta ba. Tajiyo hucin tsayawar motar awajen Fareeha. Ta kuma jiyo maganar Fareehan suna gaysawa. Da kawayenta mata aciki.

Girgiza kai kawai tayi. Ta mike zuwa hanyar department dinsu

Kamar ko da yaushe yana zaune akan wasu kujeru na gini da ke kofar department din. Yayin da gaban sa robar ruwa ce ta nestle.

Ya daga idanu kanen.. Kallon su ya sauka akan juna. Ya yin da Madeeha ta chuno baki gaba. Hade da wulkita idanu zuwa na bacin rai ta wuce shi fuuu..Bayan ta dankara masa harara yar gaske...Domin cikin dan lokacin da suka dauka na mayatar kallon da yake mata. Ta aza hakan a matsayin takura da takaici.

Daman zuwan ta kawai ya ke jira. Kuma ya gani. Domin ita din ta zamar masa tamkar abincin da ke bawa idanun sa nutsuwa. Zuciyar sa ta karkata da ita. Tazamar masa MALLAKIN ZUCIYAH... Ba yada babban burin da ya wuce na ta waiwaya ta kalle shi. A kullum bakin sa na kaunar furta mata martanin da suka yi wa bakin na sa a koda yaushe nauyi

"KI KULA NI.... Ya furta ahankali cikin kasan zuciyar sa. Ya furzar da iskar bakin sa mai zafi... Tabbas ya kara tabbatarwa kansa ya kamu da kaunar wadda bata san yanayi ba. Wadda ta tsane shi fiye da kowa da komai. Wai yau shi Rayyan Hammad ke dauke da makauniyar kaddarar kaunar yar tahalikar yarinyar da ke kasan kasa da shi a komai na rayuwa... Madeeha Sufyan zubair.. Ya koma wajen su T-Boy dake wani kawataccen garden ya zauna.

Ya dubi T-Boy da ke candy crush a wayar sa. Yace da shi
Chapter 30 · 0% Book details