← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 66

Sashe 51

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ummy na zaune a parlor tana kallon tv da ke nuna faifan shirin film din sangaya..

"Ummy."

"Naam Fareeha.."

"Wai Yaya Yazed ne ya kirani yanzu a waya kan na gaya miki zan masa rakiya."

Ummy ta danyi jim. Kafin ta daga kai tace,

"Shikenan ki je. Ki tsare mutuncin kan ki kinji ko?"

"In shaa Allah ummy."

"Yauwa to sai kun dawo."

"Toh."

Fitowa tayi wajen ahankali take tafiya har ta karasa inda yake. Yana tsaye a jikin motar sa ya jingina da ita ya wani harde kafafu. Ya yinda idanuwan sa ke zube akanta yana lumshe su Ji yake ina ma itan MALLAKIN sa ce....

Tana karasawa inda yake ya saka hannu ya bude mata gidan gaba na motar yana murmushi..

"Mu je ko? Ran ki ya dade .....

XOXO WRITES✓

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: 43_

   *Dan* jim tayi... Kafin daga bisani ta shige ciki tana mai dauke da madaukakin mamakin kalaman da suka fito daga bakin na Yazed.

Zagayawa yayi mazaunin direba ya zauna . Ya zura mukullin motar bakinsa dauke da adduar hawa abun hawa.

Ya tashi motar suka fita daga cikin gidan. Zuciyar sa na saka masa yadda zai fada mata kalaman da ke cikin zuciyar sa.

Ita kuwa Fareeha a nata bangaren... Tunani ne dankare a ranta. Na ganin ga kannen sa nan ya dauke su su raka shi mana duk inda zashi. Sai dai ita?

Ta juya ta dube shi. Kansa na kan tuki yana yi. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Yayinda shima ya sauke tasa. Suka karasa saki a tare.

"Fareeha...." Ya kira sunan nata ahanhaki cikin lafazi me dadi.

"Naam" ta amsa shi kanta a window tana bin yadda suke wuce wurare da kallo.

"Bari dai na bari mu karasa...." Ya fada yana mai karya kwanar U-turn zuwa wani eatery da ke gefen titi.

Ga tukubar me kajin hausa yana gasawa. Gefen sa kuma wata special fura ake hadawa..

"Fareeha.." ya sake kiran ta a karo na biyu.

"Naam ya Yazed." Ta amsa shi tana mai matsa yatsun hannuwan ta.

Sai jujjuya kalaman yake a fatar bakin sa.. Amman ya kasa furta mata.
Ta daga kai ta sake saukewa a kansa . Kafin cikin dan daga sautin muryar ta yadda zai iya jiyota tace,

"Ciki zamu shiga ne?"

Ya dan saka hannu ya sosa girar sa yana girgiza kai. Tamkar mai koyan magana yace,

"Ba ciki zamu shiga ba.... Zan saya nama ne da fura... Amma kafin sannan ina zuwa dai "

Da sauri ya bude kofar motar ya fita. Gaban sa na tsananta bugawa. Ya saka hannu saitin zuciyar sa ya dafe. Ya shiga sauke numfarfashi yana mai nanata abubuwan da zai gaya mata...

Kasa tabuka komai yayi. Ya hanzarta ya nufi wajen tukubar me nama ya bashi kudi. Hadi da yo masa bayani me naman ya shiga gasawa yana mai yayyanka naman. Ya zuba a ledoji uku. Ya sake karasawa wajen me fura shima ya saya a robobi

Ya nufi motar yabude gidan baya ya zura su akan seat. Sannan ya shiga mazaunin direba ya zauna.

Fareeha de nata matsa yan yatzu. Tunda ya gama su tafi mana...Ta shiga dan sossosa kasan leben ta.

Yazed ya yi shiru. Can yayi gyaran murya kafin yace,

"Fareeha..."

"Naam.."

"Abubuwan da zan fara yanzu wallahi babu kalmar dana kakaro ko wadda zan fada da bata shafi kaunar da nake maki ba...."

Ita dai Fareeha tayi shiru tana sauraron sa. Ya cigaba da cewa

"Kalmomi sunyi kadan wajen bayyana adadin yadda nake kaunar ki Fareeha... Ke din abar soyuwa ce aguri na... ke din masoyiyata ce, ina son na sanar da ke adadin yadda nake son ki a cikin zuciyata, sai dai kuma, na rasa samun kalaman da zan yi amfani da su wajen bayyana hakan a gare Ki. Ina son ki. Banda kamar ki Fareeha...Kalmomin da a kowane lokaci nake farin-cikin furta su gare ki su ne..... . Burina a kullum bai wuce na ganin na mallake ki ba har abada. Fareeha a duk lokacin dana daura idanu na akan ki...Na kan ji wani abu a cikin zuciyata, ba komai bane fyace fitila wadda ke kunnuwa a dukkan lokacin da na sanya idanuwana a cikin naki. Ina son Ki fiye da yadda alamun hakan ke bayyana a saman fuskata.

"Fareeha kin zamo cikin tunani na, kina daga cikin mutanen da ba zan taba mantawa da su ba a rayuwata. Kin zamo cikin tinanina. Bana fatan zuwan wani abu da zai zamo silar rabuwarmu, ko da a ce mutuwa ce. Ina kaunar ki sosai .. I love you more than words can say, and I want to spend the rest of my life loving you Fareeha I have been falling in love with you more and more each day, and I can't keep it a secret any longer.Fareeha.. I love you, and I want to spend the rest of my life with you.... Kiran ki da nayi kizo ki mun rakiya ba komai bane fyace bayyana maki kaunar ki da ke lullube acikin zuciya tah..Tun ranar dana fara dora idanu na akan ku. Tun bana banbance ku da Madeeha. Har Allah yasa nazo na gane dukkanin ku. Fareeha Allah ya dasamun bishiyar kaunar ki da ke yalwatuwa kullum acikin zuciyata. Kin zamo min MALLAKIN ZUCIYAH Tah. Fatana a yanzu bai wuce na rokan ki temaka KI KULA NI... Fareeha I love you beyond words..." Ya karasa maganar cikin rada rada hade da sake rage sautin muryar sa. Cikin kalamai na kauna mai tattare da kauna ga wanda ake nunawa kaunar.

Kasa cewa komai tayi. Dukkanin kalaman na sa da yayi suka dinga mata yawo acikin kan ta. Ya yinda zuciyar ta ke mamakin hakan. Ta daga kanta ta sauke kallon ta ga wajen kofa.

Yazed yayi shiru... Gabansa nata bugawa. Ya saka hannun sa daya ya shafo keyar sa. Ya tashi motar ahankali suka bar wajen

Tukin motar sa yake cikin tafiya ahanhaki kuma mai tattare da nutsuwa ...

"Fareeha..." Ya kira sunanta ahanhali a tausashe.

Fareeha ta sauke kallon ta akan sa.. kafin ta mayar kan yatsunta da take matsawa.

Ya sake marairace murya da yin rau rau da fuskar sa.

"Ba ki ce komai ba... My dearest cutie pie.. uhmmmm.. Fareeha tah..."

Mamakin kalaman sa ne suka cika mata zuciya ciki da gewayen ta. Mema zatace masa! Babu. Gaba daya ya gama nannade ta da kalaman sa da suka chusa mata kunyar sa .

'ba zamu koma gidah ba har sai kinyi magana..."

Ta daga kai da sauri ta kalle shi. Ya daga mata girar sa yana mai jijjiga kansa.

"I mean it...." Ya fada cikin karshen gaskiyar sa.

"Kayi hakuri." Ta fada ahankali.

"Ya kike so nayi da kaunar ki da ke dawainiya da ni kullu yaumin Fareeha? Haka zakj barni nayita wahala da jidalin kaunar ki?"

"Yaya Yazed...." Ta fada a rarrabe. Gaba daya ta rasa me ma zatace masa.

"Ni ba Yayan ki bane wallahi. Ki kuma dena ce mun wani Yaya... Yazed din yafi. Haka kawai ba zaa ki amsar soyayya ta ba da wani sunan Yaya. Na ki wayon.,"

Dariya sosai kalaman sa suka bata. Ta sake yin murmushi kawai kafin tace

"Dare fa yanayi...."

"Kinki ban amsa ta Fareeha.."

"Zanyi shawara ."

"Shawarar me kuma? Haba Fareeha. Kinsan tsawon lokacin dana dauka Ina jidalin kaunar ki kuwa Fareeha?"

"Zanyi shawara ai na ce."

"Indirectly dai kina nunamun shawarar da zaki fada itace amsar da zaki bani ta bakya kauna ta.... "

"Uhum."

"No ki bude baki kiyi magana Fareeha.. "

Ta dan ja kasan leben ta ta dartse. Sam batasan me zatace masa ba. Har ga Allah bata shirya karbar abunda zai ce ba kenan. Duk a tunanin ta maganar wani abun ce daban.

Ya ma zaai yanzu tace masa a'a bayan muhalli da ya basu ya kuma share musu hawayen su alakacin da aka musu tozarci suka bar gidan da mahaifin su ya barmusu na gado. Ga makarantu masu tsada da duk silar Yazed din suka shige su.

"Bakya so na ko Fareeha?"

Kasa cewa komai tayi. Ta juyar da kanta waje tana duban tsallaken titi kawai.

"Fareeha . Bakya so na ko? Kawai ki gaya mun. Ko zan dau rashin maganar ki a matsayin bakha kaunata ... Shikenan...."

Ta runtse idanun ta da sauri tana jijjiga kai.. ko dan halaccin da ya musu ai bata ki ba. Domin zuciya mai halacci bata manta alkhairi komai girman sharri.

"Ban tsane ka ba Yaya Yazed."

Fa sauri ya juya yana duban ta. Saura kadan ya doke wani mai sayar da gwanda da sauran kayan marmari.

"Is that a yes..? Kin amince da kokon barar soyaya ta Fareeha?"

Hannuwan ta biyu ta saka ta tufe fuskar ta. Ya saki atttausan murmushi yana dukan sitiyari da hannun sa daya. Zuciar sa fes. Ransa yayi haske . Gangar jikin sa ta tsumu. Gabobin jikin sa na nuna annushuwa da amsar da Fareeha ta ba shi.

Ya dan sunkuyar da kansa yana duban fuskar ta ta.

"Fareeha..."

"Uhm..."

"Banda humming... Ki bude mun fuskar ki na dan kalla mana.. kinji?"

Sam ta kasa cire tafukan hannuwan ta data rufe fuskar ta da su. Kunyar sa ta gama dabaibaye ta.

Yazed jinsa yake tamkar sabon jaririn da bashi da wata damuwa... Sai wani dadi yake ji yana lumshe idanuwa. A haka har suka karasa gidah
.

Suna karasawa ta fita daga cikin motar da sauri. Yazed ya bude motar shima ya fito yana kiran sunan ta don tuni ta shige zata bar wajen

"Fareeha.."

'naam."

"Ungo mana...." Ya mika mata ledar naman daya da wata leda da fura aciki."

Hannuwanta biyu ta saka ta karbu ledar ta masa godiya zata juya kenan ya riko gefen ledar ashe be saki ba.

Yayi taku uku ya cimmata yana murmushi. Kasa kasa yace mata

'haka zaki wuce ki tafi ba dan kalamai? Uhmmmm? "

Kunyar sa ta kara dabaibaye ta. Wai yau Yaya Yazed da ta duaka a matsayin yayanta shine ya cire kunya yake gaya maya kaunar ta yake. Kwata kwata ko kunya baya ji.

"To ki ce mun sai da safe mana..."

"Sai da safe Yaya Yazed.."

"Gaskia ki dena cemun Yaya Yazed... Banaso. "
Chapter 51 · 0% Book details