← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 66

Sashe 45

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

_SUNADA KABBASA TA TURARA KAYA DA KASAKEN TURARUKAN WUTA NA KARFE DANA KASA DAMA NA ZAMANI YAN WAJE._

*_YERWA INCENSE AND MORE_*

_YERWA INCENSE AND MORE_

_YERWA INCENSE AND MORE_

_MASARAUTAR KAMSHI KENAN. KAYAN SU NA AKAN FARASHIN SARI DA SAYA DAYA DAYA.. SUNA YIWA AMARE HADI DA UWAYEN GIDAH DAMA YAMMATA. SUNAYIN NA TARON SHAGULGULAN BIKI DUK AKAN FARASHI MAI RAHUSA_

_BA'ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNA DA TARIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA RAHUSA HADI DA INGANCIN DA ALKALUMA SUNYI KADAN WAJEN BAYYANA MUKU._

_SUNA TURA KAYAYYAKIN SU FADIN NAJERIYA DA KETARE BAKI DAYA._

_ADIRESHIN SU. SUNA GARIN KANO DAURA DA TITIN DA ZAI SADAKA DA GARIN MAIDUGURI_

_SUNA KAN MANHAJOJIN SU DAKE KAFAFE DA DAMA KAMAR:_

_INSTAGRAM: @yerwaincense_and_more_

_FACEBOOK:yerwacollection_

_WHATSAPP: 08095215215/09044191709_

_A YANZU HAKA KAMFANIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE SUNA SALES DIN KAYAN SU NA 250ML NA TURAREN WUTA DA KUMA 240 DA 190ML NA KHUMRAHS_

_IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE AKWAI RAGIN KUDI DA HADI NA MUSANMAN DA ZAA YIWA DUKKANIN KAYAN DA KUKA SAYA._

_KYAU!! INGANCI! RAHUSA!! KAMA JIKI DA GIDAH!! AIKI!! ADADE ANA MOREWA SAI KAYAYYAKIN TURARUKAN KAMFANIN:*YERWA INCENSE AND MORE*_

_____
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: 38_

_ZAFAFA BIYAR 2023_

*Yana* mai kiran sunan ta wani bayan wani...

"Madeeha, Madeeha.... Madeeha"

Bata amsa shi ba. Ta sake karkatar da kanta gefe kawai ta shige cikin faculty dinsu da sauri . Ya bi bayanta tamkar zai zama zararre.

"Madeeha... Madeeha please." Nan ma shiru taki amsa shi.

Ta nufi corridor zata hau bene ya cimmata da sauri har yana haki.

"Meya faru ne.?"

Ta kawar da kanta gefe... Maganganun mahaifiyar sa na dada kururuwa acikin kunnuwan ta.

"Madeeha please."

"Rayyan... Please let me be... Dan Allah ka kyale ni."

Idanuwan sa ya zazzaro. Tamkar zai zube mata a kàsa ya sake matsawa hannuwan sa har suna rawa.

"Na rabu da ke fa kikace...I'm going insane... No I can't.. it can't be. This can't be happening Madeeha please. Kinsan me kike cewa kuwa?"

"Ni kwa na san me nake cewa. Ka saurara kaji da kyau. Ruwa ba sa'an kwando bane. Ni ba tsarar kulawar ka bace.. Rayyan. Kai din ka fito daga tsatson masu kudi mu kuwa talakawa ne talak. Gidan da muke ciki ma temaka mana akayi aka bamu aro. Karatun da nake yi scholarship ne. Gaba da baya kunfi mu komai .. ku"

"Please Madeeha . Kaman bakya cikin hayyacin ki. Madeeha me ya kawo wannan maganganun? Madeeha na gaya miki ni ke daya nake kauna ba wani abu daya shafe ki ba. Kudi da talauci haka Allah yake tsara komai. Madeeha dan Allah ki fitar da wadannan waswasin daga cikin zuciyar ki,You’re irreplaceable, non-returnable, and priceless to me. Never change.... Madeeha Since we met, I cry a little less, smile a lot more, and know that with you here with me– I’m living in a happier world. Thank you for that. You’ll never know how much I love you.... I love you more than life itself..."

Da sauri ta kawar da kanta gefe. Saboda yadda kalaman sa suka kusan sanya ta tace ta hakura. Ta sauke zuciya kawai tana mai girgiza kanta kawai.

"Madeeha.... Lefin me nayi ni. ?Look wallahi bansan lefin me na miki ba. Daga lectures na fito. Saboda ke na shiryu ina halartar duk wasu lakcoci. Bana wasa da karatu. Abubwa da yawa na gyara su saboda ke Madeeha. Idan na maki lefi knowingly ko unknowingly..Ina mai neman gafarar ki. Kinji?"

Madeeha ta sake runtse idanu. Ta daga kafarta zata wuce ta gefen sa ya hanata ta hanyar sake komawa inda ta juya,

"Ka matsa na wuce..."

"No.."

"Rayyan ka matsa na wuce..."

"Na 'ki... Har sai kin gayamun dalilin da ya saka kike fushi da ni."

"Rayyan please ka matsa."

"I can't... I won't... Madeeha ki gaya mun abunda na miki na baki hakuri. Mu wuce wajen. Bakiji yadda zuciya ta ke mun zugi ba. Raina na tafarfasa da rashin kula ni da kike. Gabobin jikina na sarawa abisa yadda kike dauke mun kai... Madeeha ki kalli cikin idanu na ki gayamun lefin da na miki."

Ta sunkuya ta kásan sa ya wuce ta fara hawa mattakalar bene. Yabi bayanta da sauri.

"Allah idan baki tsaya ba zan fara magana da karfi kowa sai yaji..."

Tsayawa tayi chak sanin zai yi fiye da haka.

Ya rage sautin muryar sa yana kokarin jefe idanuwan sa cikin nata ta hana shi. Ta hanyar janye nata idanun da sauri ta runtse shi.

"Please Madeeha.."

"Dan Allah ka kyale ni ."

"Madeeha!! Taya zan jyake ki?. Banida wani abu mafi soyuwa da kusanci fiye da kaunar da nake miki fache ke Madeeha. Idan wani abun na maki dan Allah ki sassauta mun. Ki agaza ki dena fushi da ni."

Yana magana muryar sa na rawa sosai. Ta dubi agogon da ke wutsiyar hannun ta kafin tace da shi,

"Sauri na ke. "

"Ba saurin da kike ai saura awa daya ku shiga wata lecture din kakki manta inafa da time table dinku."

Ta yamutsa fuskar ta hadi da juyawa gefe kawai.

"Madeeha please. "

Madeehan ta sake kawar da kanta gefe cikin kasa da murya tace,

"Kamar dai yadda na gaya maka. Kafi karfi na. Kaje ke nemi wacce kuke dede ruwa dede tsakin bani Madeeha ba.. marainiya da gaba da bayanta talakawa ne talak. "

"What nonsense. Madeeha yau wani abun ya faru ne daban da bansani ba? Saboda lafiya kalau mukaa rabu da ke madeeha. Banason kina fadan maganganu irin haka wallahi. Bakiji zuciya ta ba."

"Ni de na gaya maka babu ni babu kai. Inda na godewa Allah ma dede da kwayar zarra bana maka kaunar soyayya a zuciya ta. Allah kuma yasa rabuwar mu itace tafu alkhairi. Mutane har biyu ne suka nemi ni dana dena KULA ka. Domin kai din 'dan babban gidah ne masu farcinan susa. Ni kuma ba yar gidan kowan kowa bace.

"Ki gaya mun su wanene please.?"

"Nide na gama magana.... Akan ka har cinikin kudi aka mun. Cewar ni yar talakawa da ke neman abincin cin yau dana gobe... Akan ka aka kira ni da kaskantattun kalamai wadanda babu dan Adam daya cancanci a gayawa. Sai dai hakan ni ba damuna yayi ba. Domin ba kudi bane farin cikin rayuwa. Wani kudin har sun masa yawa amman bayada farin ciki a rayuwar sa dede da kwayar zarra. Alhamdulillahi Allah ya wadaata mu da wadatar zuciya. Ina kuma fatan yau itace rana ta karshe da wata magana zata hadamu ko ta fatar baki. " Tana karasa fada tayi gaba abunta ba ta sake bi takan sa ba. Ta bar shi a tsaye tamkar sandar ba'are.

Har tayi hanyar lecture hall dinsu zata shiga ta fasa. Ta gyara zaman kayan jikin ta hadi da zaro niqabi a jakarta ta saka. . Wajen buses dinsu ta nufa Allah ya temaka ta motar ta zo.

Suka shisshiga itada sauran dalibai masu karamin karfi.

Ko da Rayyan ya bar wajenmm Kai tsaye ya koma wajen da ya baro su B-junior. Suna zazzaune sun tsayar da wani me gyaran takalmi yana polishing takalman B-junior.

Wajen saj-jeedah yaje tana tsaye tana gyara zaman daurin dankwalin kanta. Ya dubeta ya watsa mata wani kallo mai tattare da tuhuma,

"Saj-jeedah."

"Naam Ray."

"Me kika gayawa Madeeha ? Eh?" Ya karasa tambayarta yana mai daka mata tsawa.

"Bangane me na gayawa Madeeha. Ba."

"Guy meya faru haka?"

"Menene haka?"

Su T-Boy da su B-junior suka shiga tambayar sa. Bai KULA su ba. Ya sake yamutsa fuska yana kallon saj-jeedah

"Tambayar ki na ke me kika cewa Madeeha? Wallahi akan Madeeha zan iya miki abunda baki taba zata ba. Ke shikenan har abada bazan KULA mace ba sai kinje kin batani awajenta ko ki fadi maganganu marasa dadi. Wacece ke? Me kike takama da shi.. Mulki ko sarauta ko karfin mukami? Ba abunda ya dameni ki sani wallahi baki isa ki rabamu ba. Baki isa ki haramta soyayyar mu ba. Baki isa ki wargaza farin cikin mu ba. Baki isa ki tada husumar da zata haddasa tarzomar shiga tsakani na da Madeeha ba . Wallahi wallahi kinyi kadan saj-jeedah. "

"Wai neya faru ne?"

"Me tayi ne?"

"Tambayata kuke? Bata gaya muku ba? Abunda ta saba yi ne ashe bata dena ba. Taje ta samu Madeeha ta gaggaya mata magana. Har da su ko maganar kudi aciki. Ke da takamar ki kudi kudi kawai. Komai kudi. Mtcew"

"Kudi Kuma? Wallahi banu bace . "

"To waye idan bake bace.? Kar ki manta na san halayen ki tun kina kankanuwar ki da ke."

Su B-junior suka zuba mata idanu suna bin ta da kallo. Tayi kasa da idanu tana wasa da yatsun ta.

"Ni kawai nasan na ja kunnen ta.... Amma"

"Amma what? Eh?"

"Amma maganar kudi mama ce."

Bai jira ta sake cewa komai ba ya girgiza kai kawai. Ya nufi motar sa da sauri ya shiga bai tsaya ko'ina ba sai gidan su

Tun daga waje mai gadin ke sheda masa ai hajiyan bata nan. Bata dawowa tun fitar da tayi da safe.

Kai tsaye ya nufi unguwar su Na'eem dan uwan sa. So yake yaga ko da dawowar Madeeha ce. Baki daya lissafin kansa ya tarwatse .

Abunda ya sake matukar ruguza masa lissafi shine ganin motar mahaifiyar sa da yayi ta fito daga cikin gidan da yake a matsayin na su Madeeha.

Ya cika ya batse da mamakin ganin ta da yayi. Wanda har ya kasa tabuja komai. Ya hada traffic jam karami sakamakon motocin da suka tsattsaya a bayan motar sa suna masu jiran wucewar sa.

Dakyar ya iya gangarawa gefen titin unguwar ya faka motar sa. Ya kasa cewa komai. Gabansa na bugawa hadi da masa barazanar fadowa sakamakon gagarumin madaukakin mamakin daya shiga.
Chapter 45 · 0% Book details