← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 66

Sashe 29

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

_MASARAUTAR KAMSHI KENAN. KAYAN SU NA AKAN FARASHIN SARI DA SAYA DAYA DAYA.. SUNA YIWA AMARE HADI DA UWAYEN GIDAH DAMA YAMMATA. SUNAYIN NA TARON SHAGULGULAN BIKI DUK AKAN FARASHI MAI RAHUSA_

_BA'ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNA DA TARIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA RAHUSA HADI DA INGANCIN DA ALKALUMA SUNYI KADAN WAJEN BAYYANA MUKU._

_SUNA TURA KAYAYYAKIN SU FADIN NAJERIYA DA KETARE BAKI DAYA._

_ADIRESHIN SU. SUNA GARIN KANO DAURA DA TITIN DA ZAI SADAKA DA GARIN MAIDUGURI_

_SUNA KAN MANHAJOJIN SU DAKE KAFAFE DA DAMA KAMAR:_

_INSTAGRAM: @yerwaincense_and_more_

_FACEBOOK:yerwacollection_

_WHATSAPP: 08095215215/09044191709_

_A YANZU HAKA KAMFANIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE SUNA SALES DIN KAYAN SU NA 250ML NA TURAREN WUTA DA KUMA 240 DA 190ML NA KHUMRAHS_

_IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE AKWAI RAGIN KUDI DA HADI NA MUSANMAN DA ZAA YIWA DUKKANIN KAYAN DA KUKA SAYA._

_KYAU!! INGANCI! RAHUSA!! KAMA JIKI DA GIDAH!! AIKI!! ADADE ANA MOREWA SAI KAYAYYAKIN TURARUKAN KAMFANIN:*YERWA INCENSE AND MORE*_

_____
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼:25_

   *Kalle kallen* inda zai bi ya shiga ya yi. Saboda hanyar ta rabu gida biyu. Da dama da hagu. Daya ta bangaren social sciences ce. Ya yinda dayar ta ke ta sciences wato ta faculty din su..

Hannun sa ya saka ya shafo kansa da kasan habar sa. Hadi da furzar da iskar bakin sa mai zafi. Ya bi bayan faculty dinsu. Dalibai na rututu sanye wasun su suke cikin matriculation gowns.

Ya dubi wani saurayi da ke zaune akan benchi yana karanta littafin da ke hannun sa.

Rayyan ya karasa wajen sa ya bashi hannu suka gaysa. Cikin jan kasan leban sa ya dubi shi yace,

"Dan Allah abokina tambaya na ke."

"Toh Allah yasa na sani."

Bakin sa yayi nauyi ya rasa ta ta inda zai fara tambayar sa. Sam bai taba shiga cikin yanayin nan ba. Wai yau shine ke neman zaucewa akan wata ya mace. Macen ma yarinya karama da yake tunanin ranar itace farkon shigar ta makarantar a matsayin fresher ta year one.

"Ina sauraron ka... Tambayar da ka ce." Saurayin ya fada yana binsa da kallon karin bayani.

Ya sake sauke katuwar bahaguwar ajiyar zuciya kafin yace da shi,

"Dan Allah tambaya na ke ko kaga wata haka yarinya ta wuce tana ta sauri?"

Saurayin ya sake duban sa. Ya dubi bataliyar mutanen da ke wucewa suna kai kawo.

"Ai abokina mutanen da suke hada hadar wucewa da dawowa suna da yawa. Kusan ince masu saurin ma sunfi yawa "

"Hakane ...Nagode."

"Yauwa..."

Ya sake bashi hannu sukai sallama ya juya ya koma wajen su T-Boy. Ran sa dik a jagule ba bu dadi.

Suna ganin sa suka nufe shi kowanne da tambayar da yake masa. Ya ja siririn tsaki yana kauda kai gefe.

"Ni banga abun dariya ba anan..."

"Wai mutumi na daga kalon da kayo mata kwaya daya shine har zuciyar ka ta ka mu?"

"Tambaya mana shi dai maza. Lamatin fa ya fara ban mamaki. Bantaba gamin Mr Ray ya shiga wani yanayi na kwatankwacin haka ba tunda na ke face yau..."

"To gashi Nan dai wata tayi sa'ar sukurkuta mana shi."

Suka sake fashewa suna tuntsirewa da dariya irin mai kai mutum makura dinnan da sanya shi cikin takaici.

Ya sake jan wani tsakin a karo na ba adadi kafin ya juya ya bar musu wajen ya koma can wajen wasu kujeru ya zauna.

Wasu mata daga gefe nata bin sa da kallo kamar zasu hadiye shi. Hakan da sukayi ne yasa shi zaro gilashin sa ya zura a idanun sa.

✓✓

Tsaye ta ke agaban bulletin din na su tana mai rubuta yan abubuwan da ya shafi harkar bangaren karatun nata a jikin notepad.

Ya yinda Yazed ke daga can gefe da waya a sakale a kunnen sa yana amsawa.

Bayan ya karasa wayar ne ya matsa dan nesa da ita yana ce da ita,

"Kin dauki elective courses din? "

"Eh na dauka har da na mass communication me four credit loads."

"Ma shaa Allah. Kinga kuwa point dinki ze daga musanman idan kin samu A ko B. Allah yabada saa Amin."

"Aamin Yaya Yazed."

Haka dai Madeeha ta kammala komai daya shafi bangaren cike cike da rubuce rubucen da zata adana tare da temakwan Yazed .

Bayan sun karasa ne suka koma wajen su Fareeha da Hibba. Wadanda alokacin ma sun karasa kammala komai su ma.

Student affairs suka nufa suka karbi matriculation gowns suka sassaka. Kafin daga bisani su wuce princess Diana auditorium inda ake taron na matric.

Sannu ahankali haka suka karasa dukkanin komai da ya kasance zasuyi aranar. Yazed ya tsaya tsayin daka wajen gamin sun gama komai aranar.

Sai gab da magriba sannan suka fita daga cikin makarantar suka koma gidah.

   Ko da suka karasa gidah. A matukar gajiye suka sakko daga mota. Hibba ta wuce cikin gidah da sauri. Ya yinda su Fareeha ma suka shige na su bangaren da ke boys squatter.

Ko da suka yi sallama. Zubewa kowannen su yayi a kàsa . Madeeha har da mayar da numfarfashi.

"Karatu da dadi da wahala... Allah ya bamu ikon farawa kalau." Cewar Madeeha.

"Wato ummy yau munci gajiya wallahi." Fareeha ma ta fada tana bubbuga kafafunta da hannun ta na dama. Saboda tsananin ciwon da suke mata.

"Hakane dama ai. In'shaa Allahu alkhairi nan gaba karatun zai zame muku baki daya. Allah kuma yasa ku fara a sa'a. Allah ya sanya albarka Amin. "

"Aamin Ummy."

"Aamin ummyn mu."

Haka dai suka cigaba da hirarrakin su. Junaid ma ya dawo daga tasa makarantar. Ya samu degree aji na biyu a wata jami'a da ke garin na kano.

Labarta masa yadda yadda su kayi cike cike da komai da ya dangance su a makarantar sukayi. Wani labarin ya sa shi dariya wani ya tausaya musu.

A haka har lokacin baccin su yayi. Junaid ya tashi ya koma dakin sa. Kafin daga bisani ma Ummy tayi nata dakin.

Ko da suka koma nasu dakin hirar suka cigaba da yi iya su biyu. Fareeha tayi murmushi kafin ta cigaba da cewa,

"Kinga yan gayu a faculty dinnan namu? "

"Haba ..?"

"Wallahi Allah kuwa .. Kowanne yana ji da kansa. "

"Ni banma tsaya bi ta kan su ba. Na matukar gajiya."

"Gamu da ma acikin gidan yan gayu. Unguwar yan gayu..Mun zama yan gayu."

Madeeha ta daga kai ta dube ta. Kafin ta saukar da shi kawai tana girgiza kai,

"Meya faru rabin rai?"

"Fareeha har tambaya ta kike meya faru?"

"Eh saboda kina neman janye wa zuciyar ki da kwakwalwar ki inda kika fito da tsatson ki ma baki daya."

"Yanzu me nayi anan?"

"Ni de shawara na baki kada rudin duniya ya debe ki. Ki mance inda kika fito."

"Toh naji naji .."

"Allah ya baki hakuri."

"Kema Allah ya baki hakuri."

Murmushi suka yi wa junan su. Sannan suka rungume juna cike da zallar kaunar da suke wa junan su.

✓✓✓✓. ✓✓✓✓. ✓✓✓✓.

*BIRMINGHAM UNIVERSITY NIGERIA*
(UNIVERSITY IN KANO)

   Da wuri ya tashi ya gama dukkanin abubuwan da zai yi. Shi kansa yayi mamakin tashin na sa da wurwuri domin alarm din da ya seta ma bai buga ba. Ya riga alarm din tashi da awa daya da  mintina sha takwas.

Ya feshe jikin sa da turaruwa na ruwa da na fesawa. Kai tsaye ya fice daga dakin ya wuce parlorn da zai saadaka da kofar fita waje.

Hajia Hindu ce zaune akan kujera. Tana dauke da remote tana canza channels.

"Mami.."

"Na'am Mr Ray... Yau ni ma na 'dana ko?"

Dan murmushi yayi ya tsugunna,

"Ina kwana Mami?"

"Lafiya kalau Alhamdulillah.."

"Ina su Amaal ko sun tafi school ne?"

"Yanzu ta zo ta gayshe ni tatafi wanka kasan yau wai zasu excursion kasuwar singa "

"Allah sarki.... "

"Makarantar zaka tafi ne?"

"Eh in'shaa Allahu Mami.. zan biya na gayshe da su Mama kafin na wuce"

"Ai gwara ka dinga zuwa makarantar Rayyan. Allah ya temaka Amin "

"Aamin Mami. Aamin"

"Ka gayshe da su"

"In shaa Allahu zasu ji."

"Allah ya temaka Amin."

"Amin Amin ."

Ya mike tsaye yana cewa da ita,

"Na tafi."

"Tohm Rayyan.. Allah ya dawo da kai lafiya. Allah ya bada sa'ar karatu Amin"

"Aamin."

Ficewa yayi daga parlorn zuwa wajen motoci. Ya tashi motar sa da addua ya fuce daga gidan kai tsaye ya wuce...

×LT 'O' AVENUE×

Tun daga bakin kofar gate din gidan gaban sa ke faduwa.... Baya kaunar shiga ciki. Ya sanya hannun sa kan kirjin sa dake masa barazanar bugawa zai fado a kàsa...

Ya runtse idanun sa da ke masa nauyi ya danna kan horn. Mai gadi ya tashi daga ciki ya bude masa.

Shigewa yayi ciki bayan ya dan dakata ya tsaya sun gaysa da ma'aikatan gidan..

Da sallama a bakin sa ya shige wajen motoci ya faka motar. Kafin daga bisani ya fita daga cikin motar. Kafafun sa na masa rawa. Yayin da idanuwan sa ke masa barazanar rufuwa ruf. Kunnuwan sa na masa gizon muryar ta. Idanuwan sa na tariyo fuskar ta.

Hailala ya shiga yi yana cije kasan leben sa. Haka ya karasa shiga cikin gidan bakin sa dauke da sallama......
_INA JAMA'AR TA MU? KU MARMATSO KUSA . GA TAGOMASHIN ARZIKI. SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI. MUN GWADA DOLE MU BADA SHEDA_

_INA AMARE, UWAYEN GIDA, YAMMATA? IYAYE MAZA DA KE SON FARANTA RAYUKAN MATAN SU DA YAYAN SU DA MA KANNEN SU?_

_ALBISHIRIN KU. GA GORO. DOMIN WANNAN DADDADAN LABARI DOLE MU BAKU ALBISHIR DA ALHERIN GORO. GORON MA FARI KAL KAL_

_WAI AKACE KAMSHI RAHAMA NE... KAMSHIN MA MUSANMAN ME SANYAYA ZUCIYA DA RATSA MAGUDANAR JINI DA TSOKA._

_INA MASU NEMAN KAMSHIN TURAREN SAUDI ARABIA? T'CHAD DA MAIDUGURI? IRE IREN KAMSHIN DA BAYA BIN ISKA YANA KAMA WAJE YA RIKE GIDAH..._
Chapter 29 · 0% Book details