← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 66

Sashe 14

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

_WAI AKACE KAMSHI RAHAMA NE... KAMSHIN MA MUSANMAN ME SANYAYA ZUCIYA DA RATSA MAGUDANAR JINI DA TSOKA._

_INA MASU NEMAN KAMSHIN TURAREN SAUDI ARABIA? T'CHAD DA MAIDUGURI? IRE IREN KAMSHIN DA BAYA BIN ISKA YANA KAMA WAJE YA RIKE GIDAH..._

_KAMSHIN TURAREN KAYA, TURAREN GIDA, TURAREN JIKI, TURRARN GASHI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN WANKA, TURAREN WANKI, TURAREN MOPPING, TURAREN BANDAKI, TURAREN LABULAYE DA ZANNUWAN GADO, AIR FRESHENER DA TURAREN AKWATUNA DA DRAWER DA MOTA... KAI HAR MA DA TURAREN DA KE CIRE BACIN RAI YA MUSANYA DA FARIN CIKI SABODA TSANANIN SANYAYAWAR SA DA YAYE DUHU DA DAMUWA_

_BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA NAU'IKAN TURARUKA NA KHUMRAH KALA KALA. SUNADA TURAREN RUWA NA FESAWA DANA MAIKO. SUNADA KAYAN GYARAN JIKI.._

_SUNADA KULACCA DA SAURAN BODY BUTTERS MASU YAYE WARI KODA KUWA AN YI KWANAKI BA WANKA BARE WANKI._

_SUNADA KABBASA TA TURARA KAYA DA KASAKEN TURARUKAN WUTA NA KARFE DANA KASA DAMA NA ZAMANI YAN WAJE._

*_YERWA INCENSE AND MORE_*

_YERWA INCENSE AND MORE_

_YERWA INCENSE AND MORE_

_MASARAUTAR KAMSHI KENAN. KAYAN SU NA AKAN FARASHIN SARI DA SAYA DAYA DAYA.. SUNA YIWA AMARE HADI DA UWAYEN GIDAH DAMA YAMMATA. SUNAYIN NA TARON SHAGULGULAN BIKI DUK AKAN FARASHI MAI RAHUSA_

_BA'ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNA DA TARIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA RAHUSA HADI DA INGANCIN DA ALKALUMA SUNYI KADAN WAJEN BAYYANA MUKU._

_SUNA TURA KAYAYYAKIN SU FADIN NAJERIYA DA KETARE BAKI DAYA._

_ADIRESHIN SU. SUNA GARIN KANO DAURA DA TITIN DA ZAI SADAKA DA GARIN MAIDUGURI_

_SUNA KAN MANHAJOJIN SU DAKE KAFAFE DA DAMA KAMAR:_

_INSTAGRAM: @yerwaincense_and_more_

_FACEBOOK:yerwacollection_

_WHATSAPP: 08095215215/09044191709_

_A YANZU HAKA KAMFANIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE SUNA SALES DIN KAYAN SU NA 250ML NA TURAREN WUTA DA KUMA 240 DA 190ML NA KHUMRAHS_

_IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE AKWAI RAGIN KUDI DA HADI NA MUSANMAN DA ZAA YIWA DUKKANIN KAYAN DA KUKA SAYA._

_KYAU!! INGANCI! RAHUSA!! KAMA JIKI DA GIDAH!! AIKI!! ADADE ANA MOREWA SAI KAYAYYAKIN TURARUKAN KAMFANIN:*YERWA INCENSE AND MORE*_

_____
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼:12_

__

    Gaba daya su Madeeha sun shagala da kalle kallen unguwar da suke kan titin ta Yazed yana tuka su.

Junaid ne agaba kusa da mazaunin direba. Ya yinda ummy ke baya itada Madeeha da Fareeha.

Tsayawa bayyana adadin yadda unguwar ke kawaace da gidaje masu dauke da shuke shuke da jijjigaggun gates bata lokaci ne.

Komai yaji a unguwar nan. Sai kukan kanaru ne da na saurayen tsuntsaye. Gefe daya kuma wasu gidajen haushin karnuka ne ke tashi.

Sai manya manyan motoci suma an faffaka a wasu kofofin gidajen. Ya yinda masu gadi kowanne ke kofar gidan aikin sa. Wasu gidajen ma harda karin yan sanda da mopols.

No 578FD shine lambar gidan da yazed ya danna hancin motar sa akai. Gida ne kawatacce daya amsa sunan gidah irin na masu farcinan susa. (Masu kudi) gidah ne babba na bene. Da yaji parking space da kuma boys squatter itama wadatacciya har kashi biyu daya na kallon daya.

Gidah ne dankararre. Cikin sa ya sha shuke shuke. Har da wajen buga kwallo ta ragar sama. Da kuma wajen swimming pool da karin wajen motsa jiki.

"Toh mun zo ..." Yazed ya fada hadi da zare mukullin motar daga wajen zura mukulli

"Wai wai wai.. Ummy kinga gidah?" Cewar Fareeha..

Ita kuwaa Madeeha baki daya ma. Ta kasa cewa komai. Sai bin ilahirin ko'ina na cikin gidan ta ke da kallo.

"Ummy masu kudi sunji dadin su." Madeeha ta fada tana mai cigaba da bawa idanunta abinci na kallon gidan.

"Nagani.. Allah ya azurta ku da shi. Ya baku inda zaku huta , Hankulan ku su kwanta. "Ummy ta gaya musu. Ya yinda fuskar ta ke qumshe da fara'a.

Yazed yayi gaba . Suna biye da shi a baya. Ya daga yatsa daya ya sauke akan tankamemen gidan daya sha fenti fari da ratsin sky blue.

"Nan inda muke nan ne baki dayan mu. Mahaifiyar mu da kanne na mata. B-q dincan kuma daya daga ciki nanne zaku zauna. Yana dauke da dakuna uku da bandaki daya. Da anan sashen na ke ni da wasu yàran kanwar mahaifinmu. Sai kuma bayan an gyara nan bangaren sai aka mana dakuna aciki muka dawo. Can inda muka baro din sai ya zamana idan wasu bakin sunzo maza. Sai a basu su dinga zama.. ...

Yana tafe agaban su yana nuna ko'ina yana musu bayani. Har suka karasa sashen da yake gaya musu.

"Nan bangaren akwai mutane.. Sunyi tafiya ne itada mai gidan nata. Babban direban mahaifina ne. Sun dade basuje kauyen su ba. Shine suka tafi jiya.... Sannan mu baa cikin gidan mu ke ba. Duk suna kasar Amsterdam mahaifiya ta da yan uwa na. Nima wani uzuri ne ya hanani tafiya...."

"Allah sarki.. Allah ubangiji ya saka muku da alkhairi."

"Aamin Maama. Kar kuji komai.. Da lamuncewar su... Dan su ne ma suka sake karfafa gwiwar dawowar ku nan din."

"Ma shaa Allah. Allah ya biyaku da alkhairin sa. Yadda kuka share mana hawayen mu. Ubangiji Allah ya jibanci lamuran ku. Aamin"

"Aamin Mama. Amin Amin. Tare da ku gaba daya."

Yayi gaba yana mai juya baya ya dora idanun sa akan yan biyun na Ummy. Musanman akan wadda zuciyar sa tafu karkata ga ita. Runtse idanun yayi ya bude. Ganin baki daya ya kasa gane wacece dazu yaji ya kamu da kaunar ta. Sosai kamar su ta tsunduma shi a waswasi.

Ganin zasu harbo shi. Sun tsaya suna binsa Suma da kallo. Da ke shine a gaba. Ya yinda su ke biye da shi abaya.

Juyawa yayi ya cigaba da tafiya su kuma suna binsa da kullin kayan su kowanne ya rike.

Har boys squatter din ya kai su. Tamkar gida karami dai haka madaidaici. Haka sashen ya ke. Yayinda wani irinsa ke kallon sa shima. Ginin ya sha fentin up white . Wajajen bugler din kuma red color ne mai turuwa.

Mukullin ya zaro a aljihun sa ya bude wajen. Tafkekiyar kofa ce dataci ta koshi itama .

Suna shiga sai wani daki a farko da bandakin sa agefe. Yazed ya bude dakin suka bishi. Dakin yanada dan girman sa ba lefi. Da fankar sama. Sai katifa madedeciya.

"Yauwa kai aboki na sai ka dinga kwana anan ko? " Ya fada yana wa Junaid murmushi

"Iyye su Yaya anyi sabon daki." Madeeha ta fada tana dariya.

"Ai kam dai Yaya congratulations." Fareeha ma ta fada tana dariya.

Junaid yayi murmushi . Hannun sa kan fentin jikin bangon dakin me maiko yana shafawa. Farin ciki ya gauraye zuciyar sa.

"Mungode... Allah ya saka muku da alkhairi." Junaid ya fada yana murmushi.

"Aamin tare da ku baki daya."

Suka fito daga cikin dakin. Gaban sa kadan sai wata kofa itama. Suka kutsa kai ciki suka shiga.

Kitchen ne mai dauke da kitchen cabinets masu kyau. Sai risho da dan karamin fridge.

"Mama nan kitchen ne. Ga store nan aciki."

Suka leka store din. Buhunhunan shinkafa karami ta tuwo data dafawa. Sai macaroni kwali daya da indomie carton daya. Sai jarkar mai karama data manja da su magi.

"Kai Allah ya saka da alkhairi. Wallahi baki na ya rasa ta cewa ma." Ummy ta karasa fada. Yayinda ambaliyar hawaye suka shiga reto a fuskar ta.

"Aamin Mama. Tare da ku."

Ya fita daga kitchen din suna biye da shi a baya. Ya murda wata kofa. Parlor ne karami mai dauke da kujera guda uku. Sai yar karamar tv da kayan kallo.

Sai kofofi guda biyu da ke ta cikin parlorn daya na kallon daya. Ya bude daya kofar suka shiga dukan su.

Daki ne mai dauke da katifa da shimfidar sa da bargo. Sai fanka ta tsaye.

"Mama ke nan ne dakin ki." Yazed ya karasa fada hadi da zura mukulln dakin ajikin kofar.

"Ma shaa Allahu... Ubangiji Allah ya biye muku da alkhairin sa. "

"Aamin Mama."

Su Fareeha ma duk suka shiga yin addua shide amsa musu kawai yake da Aamin.

Suka fito daga dakin suka shiga mai kallon sa. Daki ne sak irin na ummy.. Amman shi yana dauke ne da kananan katifu irin na yan boarding dinnan. Guda biyu. Kowanne an shimfida masa zanin gado da bargo. Sannan fankar sama ce sai gudu ta ke.

"Ga dakin ku... Yan biyu, Masu kama daya." Yazed ya fada yana murmushi. Hade da sake zube idanuwan sa akan su.

A tare sukayi murmushi. Suka kuma rungume junan su suna murna. Bakin su abude. Sun kasa rufewa. Kana kallon su kasan dukkanin su suna cikin tsantsar farin ciki marar misaltuwa.

Yazed ya samu kansa da yin murmushi shima. Yaji dadi kwarai da yadda sike yaba ko'ina.kuma suka nuna farin cikin su a kan hakan.

"Baki yayi kadan wajen furta adadin farin cikin da kuka saka acikin zukatan mu. Allah ya cigaba da buda muku. Allah ya biyaku da mafificin alkhairin sa. Allah ya tsare gaban ku da bayan ku.... Mungode, Mungode, Mungode." Ummy ta fada . Yayinda yar tissue paper din da ke hannunta ta jike da hawayen da take gogewa,

Yazed ya dan kalleta. Tausayin su ya sake kama shi.

"Dan Allah kibar kuka mama.. ai an zama daya. "

"Kukan farin ciki ne. Kukan jin dadi ne... Bar ni na zubar da hawaye. Na dadi ne"

Sukayi dariya baki daya. Fareeha da Madeeha kowanne ya zabi katifar sa. Sunata murna . Yazed dadi ya sake kama shi.

Yaja kasan leben sa ya ciza. Ko da zai bayyana wa daya daga cikin su tunda ya kasa gane wadda ya kamu da kaunar ta ta. Tabbas ba yanzun zai fada mata zuciyar sa ba. Sai Nan gaba idan ta kara shekaru. Don yanzun kam akwai karancin shekaru a tattare da su.

Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya. Wanda har sai da dukan su suka juya gare shi.
Chapter 14 · 0% Book details