← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 66

Sashe 6

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

_labarin ya zo da salo na daban. Ya taho da wani launi na kauna marar gauraye💕_

_who doesn't love a romantic college love story ? Don't afford to miss this chance.🤪 Love is considered to be both positive and negative, with its virtue representing human kindness, compassion, and affection, as "the unselfish loyal and benevolent concern for the good of another" and its vice representing human moral flaw..💕_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_

_
*RUMBUN K'AYA*🔥

*DAUDAR GORA*🔥

*IDON NERA*🔥

*A RUBUCE TAKE*🔥

*KI KULANI*🔥

*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊

*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*

*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*

*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️

*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*

*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*

*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*

Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

*_K I K U L A N I_*
_(MALLAKIN ZUCIYA)💕_

_N A N A H A F S A T_
_MSS XOXO_

_بِسْمِ اللهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ_
_Da sunan Allah mai rahama, Mai jin kai… Mamallakin kowa da komai!!_

*_PAID- P A G E :006_*

*_ZAFAFA BIYAR 2023 PAID NOVELS_*

_INA JAMA'AR TA MU? KU MARMATSO KUSA . GA TAGOMASHIN ARZIKI. SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI. MUN GWADA DOLE MU BADA SHEDA_

_INA AMARE, UWAYEN GIDA, YAMMATA? IYAYE MAZA DA KE SON FARANTA RAYUKAN MATAN SU DA YAYAN SU DA MA KANNEN SU?_

_ALBISHIRIN KU. GA GORO. DOMIN WANNAN DADDADAN LABARI DOLE MU BAKU ALBISHIR DA ALHERIN GORO. GORON MA FARI KAL KAL_

_WAI AKACE KAMSHI RAHAMA NE... KAMSHIN MA MUSANMAN ME SANYAYA ZUCIYA DA RATSA MAGUDANAR JINI DA TSOKA._

_INA MASU NEMAN KAMSHIN TURAREN SAUDI ARABIA? T'CHAD DA MAIDUGURI? IRE IREN KAMSHIN DA BAYA BIN ISKA YANA KAMA WAJE YA RIKE GIDAH..._

_KAMSHIN TURAREN KAYA, TURAREN GIDA, TURAREN JIKI, TURRARN GASHI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN WANKA, TURAREN WANKI, TURAREN MOPPING, TURAREN BANDAKI, TURAREN LABULAYE DA ZANNUWAN GADO, AIR FRESHENER DA TURAREN AKWATUNA DA DRAWER DA MOTA... KAI HAR MA DA TURAREN DA KE CIRE BACIN RAI YA MUSANYA DA FARIN CIKI SABODA TSANANIN SANYAYAWAR SA DA YAYE DUHU DA DAMUWA_

_BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA NAU'IKAN TURARUKA NA KHUMRAH KALA KALA. SUNADA TURAREN RUWA NA FESAWA DANA MAIKO. SUNADA KAYAN GYARAN JIKI.._

_SUNADA KULACCA DA SAURAN BODY BUTTERS MASU YAYE WARI KODA KUWA AN YI KWANAKI BA WANKA BARE WANKI._

_SUNADA KABBASA TA TURARA KAYA DA KASAKEN TURARUKAN WUTA NA KARFE DANA KASA DAMA NA ZAMANI YAN WAJE._

*_YERWA INCENSE AND MORE_*

_YERWA INCENSE AND MORE_

_YERWA INCENSE AND MORE_

_MASARAUTAR KAMSHI KENAN. KAYAN SU NA AKAN FARASHIN SARI DA SAYA DAYA DAYA.. SUNA YIWA AMARE HADI DA UWAYEN GIDAH DAMA YAMMATA. SUNAYIN NA TARON SHAGULGULAN BIKI DUK AKAN FARASHI MAI RAHUSA_

_BA'ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNA DA TARIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA RAHUSA HADI DA INGANCIN DA ALKALUMA SUNYI KADAN WAJEN BAYYANA MUKU._

_SUNA TURA KAYAYYAKIN SU FADIN NAJERIYA DA KETARE BAKI DAYA._

_ADIRESHIN SU. SUNA GARIN KANO DAURA DA TITIN DA ZAI SADAKA DA GARIN MAIDUGURI_

_SUNA KAN MANHAJOJIN SU DAKE KAFAFE DA DAMA KAMAR:_

_INSTAGRAM: @yerwaincense_and_more_

_FACEBOOK:yerwacollection_

_WHATSAPP: 08095215215/09044191709_

_A YANZU HAKA KAMFANIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE SUNA SALES DIN KAYAN SU NA 250ML NA TURAREN WUTA DA KUMA 240 DA 190ML NA KHUMRAHS_

_IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE AKWAI RAGIN KUDI DA HADI NA MUSANMAN DA ZAA YIWA DUKKANIN KAYAN DA KUKA SAYA._

_KYAU!! INGANCI! RAHUSA!! KAMA JIKI DA GIDAH!! AIKI!! ADADE ANA MOREWA SAI KAYAYYAKIN TURARUKAN KAMFANIN:*YERWA INCENSE AND MORE*_
______

×××××
  Dakin ummy... Junaid ya wuce. Su madeeha na biye da shi a baya. Bakin sa dauke da sallama ya shiga. Suma sukayi. Ummy ta amsa. Hannunta dauke da carbi tana addu'a.

Tana karasawa ta mike ta ninke sallayar ta ajiye akan sif. Junaid ya sauka daga kan kwallar daya zauna. Cikin ladabi yace,

"Ummy barka da rana..."

"Barkan mu dai Yayan su... Ka dawo ina sallah. Ya makarantar ?"

"Lafiya kalau ummy."

"Masha Allah! To Allah ya temaka. Ya bada ilimi mai amfani Amin."

"Amin Ummy. "

"Yauwa ku zo ku tsugunna anan. Me ya hada ku kuma yau da kawu?"

Fareeha ta juya ta kalli madeeha. Madeeha sai jan kasan leben ta kawai ta ke. Taki yadda su hada idanu .

"Gayamun gaskiyar zance Fareeha... Kinji?"

"Tohm Yaya.."

"Yauwa ina sauraron ki...."

Sauke zuciya tayi. Cikin matsa yatsun hannayen ta ta ce,

"Ba ruwan madeeha aciki "

"Kamar ya ba ruwana aciki? Karya take Yaya. Laifi na ne. Itace ma ba ruwanta .."

"Aa Yaya karka yadda da zancen ta.... "

Tsaki Junaid yaja. Ya kalli ummy. Kafin ya sake mayar da kan sa kan su.

"Wace iriyar magana ce wannan? Kunsan na kafa ma ku sharudda akan irin wannan abubuwan da kuke yi. Wannan tace waccan ce. Waccan tace wannan ce.. Sai ka rasa waye me laifin aciki.. " Ya karasa fada hadi da sakin wani tsakin cike da takaicin su

Ummy da ke gefe ta danyi murmushi kafin tace,

"Ni dai ina zaune anan na hangi Fareeha na shanya kanzon tukunya. Ya akai ya akai oho. Sai ga zakaran kawun ku ya zo ya fara caccakar kanzon. Zuwan madeeha ke da wuya sai ta kora shi. To daga nan na tashi na shiga daki. Inda na fara jiyo dariyar su itada Fareeha suna magana kan zakaran ya fada yar kwatar can ta wajen shuri. Ita tana daga hagu madeeha nada ga dama. Yayin da zakaran ke tsakiyar su acikin kwata. Kafar sa ta shige me najiyo suna cewa ma?"

"Ya shiga cikin wani karfe na madara da bai karasa fafewa ba...." Madeeha ta fada tana dariya.

Fareeha ma ta shiga kyakyatawa...

"Meye abun dariya? Ku dai sakarkaru ne." Junaid ya fada hadi da sake sakin wani katon tsaki akaro na ba adadi..

Ya kalle su ya zabga musu harara mai dauke da jan kunnen ya ishe ku.

"Daman jikina yaban ke ce kika aikata Madeeha......"

"Aaa Kai Yaya. Allah ni fa ban masa targade ba. Da kansa ya fada kwatar kafarsa ta shiga karfen. Ni fa ceto rayuwar sa naje yi. Na dakko sa kenan zan wanke hannu na sai ga shigowar kawu. Shine fa ya na shigowa idanuwan sa ya sauke akan zakaran na sa. Gefen sa kuma Fareeha ce. Shine fa ya shiga rankwashin ta ya fara zaginta. Naje na janye ta nace laifi na ne. Shine fa ya cigaba da fadan sa. Ya sa muka shiga dakin sa ya janyo wayar wuta ya fara tsaula mana... Ka ji fa yadda akayi..."

Junaid ya sauke zuciya. Daman yasan tabbas babu laifin su. Tsabar tsagwaran son mugunta ce kawai irinta kawun na su Ashiru.

"To Allah ya kyauta...." Ya fada yana girgiza kai kawai.

"Amin Yayan su..."

"Ku tashi ku je..."

Mikewa sukayi suka fice daga dakin. Junaid ya juya ya kallo mahaifiyar ta su. Dai dai lokacin data dauki ledar awarar gabanta ta saka guda daya a baki.

"Zo ku karba Fareeha... " Ta daga labulen dakin ta mika musu awarar.

Da sauri Fareeha ta karba suka shiga donar yaji suna ci.

"Ummy wannan abubuwan sunyi yawa wallahi..."

"Na me fa?"

Ya dartse kasan leben sa kafin ya fitar da hucin zafi daga bakin sa.

"Kawu Ashiru ma na ummy .. Haba cin zalin yayi yawa ummy. Kullu yaumin ba irin duka da cin zalin da yake mana shi da iyalan sa. Musanman akan yaran nan Fareeha da Madeeha ummy... Mata ne fa. Yadda yake dukan su ya wuce mizanin hankali ."

Ummy bata ce komai ba .. Ta kada kai kawai hadi da cewa 'uhum' a kasan makoshi ...

"Yadda yake wulakanta mu Allah ya wulakanta s..."

"Karka karasa Yayan su .... Ai na gargade ku.. Uba ne agare ku. Kar na kuskura na kara jin haka ya fito daga bakunan ku. Ka ji ko?"

"Toh... Ummy! Naji."

"Yauwa. Allah yayi muku albarka... "

"Amin Ummy.. Amin"

"Ga abincin ka can.. "

"Toh ummy."

Daukar abincin yayi ya fita waje zuwa dakin sa.

Fareeha da Madeeha na zaune a dan tsukukun harabar bangaren su suna wasan yar carafke.

"Yaya kaga Mari?" Madeeha ta tambaye shi tana kanne ido.

Biron jikin gaban aljihun rigar sa ya curo ya buga akan kan madeeha. Fareeha ta kyalkyale da dariya.

"Yarinyar nan ta mato akan ka Yaya . Allah kuwa "

Ya tabe baki hadi da rankwashin ta itama da kasan biron.

"Babu ruwan ta baiwar Allah... Matsa kafin nayi kutufo da wani acikin ku."

Kyalkyale wa da dariya sukayi. Shi ma ya murmusa kawai ya shige cikin dakin sa.

Ya bude kwanon abincin ... Taliya ce yar hausa da wake. Ta sha man ja da ke kamshin albasa. Da yajin tafarnuwa a gefe.

Ya debo ruwa a kofi ya ajiye. Yayi basmala. Yana ci yana kurbar ruwan har ya karasa cinyewa ya yi hamdala hadi da gyatsewa..

Yana karasawa ya kalli agogon da ke wayar sa me cocilan. Uku saura kwata. Don haka ya mike da sauri ya fice zuwa wajen rijiya ya janyo ruwa .

Ya kira Fareeha ta dakko masa kwandon soso da sabulu. Bandaki ya shige bayan yayi addu'a....

××LT 'O' AVENUE ××

Tashin ta kenan daga bacci bayan ta koma a lokacin da tayi sallar asubahi. Da salati ta mike tana murza idanun ta da ke zugi.

Ta mike dakyar tana mai fadin;

"Ya Rahmanu mun tashi da karfin ikon ka. Alhamdulillahi.." Ta janyo yar sandar ta tana mai dogara ta

A haka ta karasa bandaki. Ta ajiye yar sandar ta a gefe. Ta cika kwamun wankan da ruwa mai dumi kafin ta shiga ta chude ilahirin jikin ta da gauraye.

Bayan ta kammala ta daura alwala bayan tayi tsarki. Wannan al'adar tace ta zama cikin alwala a koda yaushe.
Chapter 6 · 0% Book details