Sashe 56
Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Sannu da kokari dan nan... Allah yayi maka albarka kaji? Mungode kwarai Allah ya saka muku da alkhairi... Amin" Hajiya Fadila ta fada tana murmushi...Kafin ta sake cewa
"Zo Madeeha da Fareeha ku zuzzuba mana.."
"Toh" suka hada baki
Kafin daga bisani su shiga zuzzuba musu furar a kofunan suna mika musu.
Hajiya Fadila sai binsu ta ke da kallo cikin kauna marar gauraye. Idan ta kalli Hadiyyah (Ummy) ganinta take yar karama kamar a baya ..
Ta sauke zuciya katuwa kafin tace,
"Allah yayiwa mahaifin ku rasuwa Hadiyyah.. ya rasu shekaru inaji biyu da rabi ko Hydar?"
"Eh hakane Hajiya..."
"Ladiyo matar sa kuma .... Ta hadu da babbar lalura da su Hammadu suka je gano kauyen na ku rannan.. Suka dauke ta suka kai ta asibiti aka babbata magunguna.."
"Allah ya jikan sa da rahama.... Allah ya gafarta ma sa. Ita kuma Allah ya bata lafiya."
"Aamin " suka amsa baki daya .
Gwaggo ta matsa kunnen Innarajo tana mai nanata mata iyayen hadiza (Hadiyyah) sun bayyana..
Innarajo ta kada kai.... Hawaye daya na bin daya ta shiga yi musu addu'oi hadi da nuna barka da kuma farin cikin sake ganawa da sukayi da yar su hadiyyah bayan shekara da shekaru.. Tana daga kwancen idanun ta a rufe na makantar tace,
"Ba zan manta ba.... Da rana haka .. Anyi ruwa gari yayi sanyi na damuna... Muna bikin kanwata gata nan a zaune Haire (Gwaggo) Zamu tafi kai amarya daga Maiduguri zuwa Yobe Amman ba motar mu daya da su ba.....Ni da wasu yakumbon mu su uku muke da yarana guda biyu Fanta da kuma Borkindo gashi can...Sai motar mu ta lalace. Direban motar ya taro wata ya saka mu aciki daga jihar Maiduguri zuwa jihar yobe.... Anan muka hadu da ita yar uwa ga yarinya hadiza (ummy) data tashi a wurin mu da wasu sauran mata. sunanta Fatsuma idan ban maanta ba.."
"Tabbas haka sunan ta yake.... Fatsuma kanwa ce ga mahaifin su malam haladu mai rasuwa..."cewar Hajiya Fadila mahaifiya ga su Hadiyyah..
Su ummy suka tsaya suna bin Innarajo da kallo suna kuma sauraron ta yadda take bada labari tiryan turyan ranar ba surutai da take yi...
"Yauwa... Da wannan yarinya Hadiza akan cinyar ta.. Munata hira ana tafiya. Ashe wai direban motar tamu bacci ya kwashe shi.. Motar ta kwache masa... Nide naga motar na tagal tagal. Masu salati nayi, masu addua nayi da masu kurma ihu... Daga nan bansake sanin meya faru ba.. kawai naga duhu ba haske kwata kwata shikenan ban sake sanin meya faru ba....Naji dai sanda ake tambayar yaran waye wannan su biyu mace da namiji? Nace 'ya'ya na ne.. Ashe abunda bansani ba... 'Fanta macen ta ra su. Borkindo ne kawai namijin yayi rai. Sai wannan yarinya Hadiza sune yaran da ake cewa sun yi rai..... Dukkanin yan motan sun rasu ciki harda yan uwana da muke tare.. Sai wata mata da ita aka nufi asibiti da ita ranga ranga.... " Tana kawowa nan ta fashe da kuka... Hawaye daya na bin daya suka shiga reto a fuskar ta.
Suka shiga bata baki ... Hajiya Fadila da itama hawayen take tace,
"Allah ya jikan su da rahama... Allah ya gafarta musu Amin.. Ai Fatsuma bayan ta dauki hadiyya ta tafi bamu sake ji daga gareta ba. Sai labarin rasuwar ne ya riskemu. Tabbas ance manya biyu ne da yara biyu sukayi rai. Amman duk yara biyun wai yaran mutum daya ne.. Dan ko gawar bamu gani ba ta Fatsuma ance baa ganewa ma... Munyi kuka don har ciwo muka kwanta ni da yarana duka..To bayan haka abubuwa da dama sun faru har ta kai ga rabuwar auren mu da mahaifin su .. Bayan nayi idda kuma Malama Asabe gata atare da mu. Itace wadda tayi silar aurena da mahaifin Harith.. Wanda kafin aure na da shi...Shine bawan Allah wanda yake sawa Malama Asabe idan tayi kosai da kunu ta dinga bawa marasa hali shi a sadaqah.. Allah ya hada aure na da shi...Shine zamana ya dawo Kano.. Ya rike mu duka ni da yara na biyu tamkar shine mahaifi a agare su. Dukkanin wasu hakkoki da uba kewa yaran sa marigayi Owais haka yakewa su Aliko Hydara. Har Allah ya azurta mu da samun Harith qani agare su. Bajimawa sosai kuma Allah ya karbi ran Owais.... Duk tsawon shekarun nan lungu da sako iya saninmu babu inda bamu kutsa ba don neman gaskiyar lamari akan hadiyyah... Labari yazo mana kan ai Hadiyyah ana kyautata zaton tana raye.. Amman inda take dinne baa sani ba..Muna ta addu'oi da kai kokenmu ga Allah sai kuma ga labari me dadi ya riske mu na sanin inda Hadiyyah ta tashi...Kafin sannan Aliko hydara gashi a zaune kwana ki can yake cewa damu Hadiyyah saboda maganar ta da akeyi ta fara masa gizo da wata mata da ke makwantaka da gidan sa. Da ya tambayi wacece ita? akace sunan ta Hadiza ... Sai kuma jikoki na ma su biyu sun ce sun ga mai kama da kanwar bappanin su a makotan gidan Aliko hydara.. Alhamdulillah! Alhamdulillahi! Alhamdulillahi! Dukkan yabo ya tabbatar ga Allah madaukakin sarki ... Sannan dole ne mu miko godiyar mu marar iyaka agare ku.. Mungode da riqon Hadiyyah da kukayi tamkar diyar da kuka haifa acikin ku. Tun tanada karancin shekarun ta ya zuwa girmanta har zuwa auren ta... Allah ya saka muku da mafificin alkhairin sa. Allahumma Aamin..."
Innarajo ta saka hannu tana goge nata bawayen. cikin rawar baki da jiki tace,
"Bansake sanin inda kai na yake ba... Ashe sai da na kwana na wuni kafin na farfado.. Bayan na farfado ake sanar mun da nayi hakuri na fawwalawa Allah lamurana... Domin baa gama yiwa dan Adam halitta har sai ya koma ga mahalliccin sa... Wani zai rasa hannu, Wani kafa, Wani gwiwa, wani barin jiki, Wani ma duka jikin... Daga karshe dai ake sanar mun nasamu makanta sakamakon hatsarin daya afku damu.sauran yakumbon duk sun rasu. Yata ma ta rasu sai borkindo... Ashe yarinyar da muka dakko ba ta mu bace... Mu tamun Allah ya karbi ran abun sa... Bayan na wartsake na dawo gidah ni da sauran yan uwana muka fara tambayar sunan yarinyar tace Ha... Wannan ya ma.?"
"Hadiyyah... "
"Yauwa Hadiyyah.... Zahirin gaskiya kuma ni da sauran yan kauyen ma baki daya bamu san sunan ba. Ba Kuma mu iya fada ba... Muka tambayeta garin su nanma bata sani ba. Tanadai ta kiran sunan Hydar din da shi..."
"Hammad."
"Yauwa da Hammad da Umma da Mama da su baba duka... Muna ta cikiya dai aka gano ai wadda ta rasun Fatsuma yar cikun garin na kano ce yankin bullere... Da tambaya aka kai su wani gidah na yankin dangin Bakar hula... Daga nan sukayi musu rakiya zusa gidan malam haladu da ake kyautata zaton shine mahaifi agare ta. To daii sukace wata mata da sukayi mata bayani tace ita basusan wata Hadiyyah ba. Kar wanda ya sake shigo musu gidah. Sau uku muna aikawa da sako zuwaga yan uwan Hadiyyah nanma shiru baa ce mana komai. Na yanke shawarar rike ta awaje na kawai sanda Allah yasa tanada rabon ganawa da iyayen ta sai su gana...
"Shekaru su kayi ta ja. Har girma, Hadiyyah ta isa aure. Mijina kafin Allah yayi masa rasuwa shi yayi waliyin auren ta da malam Sufyan da ke cikin garin Kano.. Allah ya azurta su da samun yara uku gasu nan... Sai kuma Allah ya karbi ran abunsa... Zamanta ya dawo tare da kanin sa Ashiru. Zama yaki dadi. Amman duk da haka haka Hadiyyah tacigaba da hakuri tana zaman yaranta. Ba bolar da baa zuba musu itada yaran ta. Karshe ma sunaji suna gani shi ashirun ya sayar da bangaren da suke ciki acikin gidan ya kuma basu wa'adin tashi suka bar masa gidan. Zaman su ya koma hannun wannan bayin Allah da suka basu matsugunin zama agidan su. Hadiza na da kawaici.tawakalli, tausayi,jin kai dakuna biyayya... Tunda nake da ita yi nayi bari na bari muke yi. Ba rashin kunya ba fada ba ganin ido wallahi. Ga kyauta. Duk kuwa da halin rashi da suke ciki wallahi bata taba zuwa hannu biyu wajen mu batare da ta kawo mana abuba... Zan iya cewa Allah ya dauki ran fanta ya azurta mu da hadiza.. Hadiza ta maye mana gurbin fanta. Na samu tarin alkhairai ta sanadiyyar hadiza. ... Wannan yarinya Hadiza da karfin iKon Allah rayuwar data sha ta wahala...Gaba zataji dadi in shaa Allah. Na kuma yi murna nayi farin ciki da samuwar iyayen Hadiza... Hadiza idan mun miki ba daidai ba akan sani ko rashin sa.. Dan Allah ki yafemana kinji?"
Ummy ta matsa wajen Innarajo ta rungumeta tsam a jikin ta tana mai zubar da hawayen itama
"Ba aabunda kukai mun Innarajo... Nima ki yafe ni. Allah ya yafe mu baki daya.."
"Aamin Aamin..." Dukkanin su suka fada..
Haka dai suka cigaba da tattaunawa akan rayuwar data shude a baya da wadda ake ciki ahalin yanzu
Su Madeeha fuskokin su dauke da tsantsar farin ciki marar misaltuwa...
Sun jima kafin daga bisani suyi haramar komawa gidah. Sun so Hadiyyah (ummy) ta bisu da yaran ta su tafj.. Ummyn tace musu zata dawo idan sukayi sati.
Hajiya Fadila kuwa tace itama zata zauna sai a biyota da kayanta. Hakan kuwa akayi su Bappah bydar suka koma da su Malama Asabe da aka cika su da tarin abubuwan arziki da kudi masu dimbin yawa kasancewar ta sanadiyyar su aka gano inda Hadiyyah Ummy ta ke..
Kaya cike da akwatuna biyu aka kai wa hajiya Fadila kauyen ita da ummy...a ranar kuma aka kawo sabon injin wuta da fankar tsaye da kayan abinci fal da sabon risho... Ruwa ma fal roba roba haka akaita saukewa da lemuka.. Da biredi me yanka yanka🤣
Ai kwa makota da sauran yankin kauyukan sukai ta dafifin zuwa ganin kwakwaf..
Alhaji Hydar , Alhaji Hammadu da Alhaji Harith. Dukkanin su suka shiga rokan alfarmar dawowar ummy da yaranta wajen sa.. Daga karshe dai bayan nacin da Alhaji Harith yayi ta yi.har da su shi ai bai taba sanin ta ba..Su ai sunyi zaman yarinta da ita... Su temaka su bar ummy da yaranta su dawo gidan sa. Idan yaso ta dinga zuwa tana ziyartar su...