Sashe 54
Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ji da ganin sa ne suka dauke na yan wasu dakikai.. Kafin ya sake bude idanun ya dora akanta tuni har motar taja sunbar wajen.
Mikewa yayi da sauri ya nufi inda yaga motar tayi ta sha kwana ta koma babban titi. Jikin sa har rawa yake. Ya matsa wajen masu gadin yana cewa,
"Dan Allah matar data shiga mota yanzu agidan nan take?"
"Eh ai itace mahaifiyar su Madeeha d...
Bai karasa ba daya mai gadin ya rafkawa dayan me maganar harara. Ya dubi Rayyan yace da shi,
"Kai din wanene? "
"Afuwan... Sunana Rayyan ..Makarantar mu daya da su Madeeha din.. Sannan nan gidan da ke jikin nan din da kuke gidan kanin mahaifina ne.. Ba macuci bane ni."
"Bance maka macuci ba ai.kasan duniyar ce yanzu ta baci."
"Hakane... Kuna da gaskiya ai..."
Jkkin sa ya shiga ingiza shi da tarin tambayoyin da suka kusan chaza masa kai.. maganganun Na'eem na baya nata dawo masa. Da hotan da ke agaban Hajia Fadila kakar su kwanakin baya...
Cikin tunane tunanen ne da maganganun ke dawo masa sai ga dawowar su Yazed. Lokacin Rayyan ya juya baya yana lalubo number bappan su.
Dai dai lokacin da wayar Junaid ta fara kara ummy ta kira shi tana ce masa suna wajen Ina? Ga mota Hajiya mahaifiyar su Yazed ta bayar akai su har kauyen...
Nan Junaid din ke fada mata ai suna tare da yazed ma yace zai kai su sunzo daukar ta da kayan su.
Fita yayi daga cikin moyar ya shiga cikin gidan da sauri ya dakko chazar sa da ya manta ta akan ta socket din da ke jikin window din dakin sa.
Yana saka kafa ya futa wajen gidan ... Rayyan ya nufe shi .. ya bashi hannu suka gaysa. Nan da nan yayiwa Junaid din bayanin wanene shi da abunda ya kawo shi. Junaid din ya kada kai yana kallon sa kawai... Domin su Fareeha sun sanar da shi komai... Ya yaaba kwarai da hankalin Rayyan din.. Don haka yace masa yanzu dai garin zasu bari sai wani lokacin.
Rayyan ya takura har sai da junaid din ya bashi number wayar sa.
"Dan Allah inason magana da Madeeha.."
"Sauri muke ne wallahi.. mahaifiyar mu tana jiran mu. "
"Ko minti daya?"
"Banason tauye dokar mahaifiyar mu ne.. Kabari idan komai ya wuce zaku cigaba da mu'amalar ku da Madeeha.. Kayi hakuri."
"Ganin ta kawai nake son yi."
Yadda ya saukar da kimar sa. Ga wani mutinci da kwarjini da Rayyan din yayiwa Junaid ... Hakan yasa Junaid din kada kai kawai...
Ya janyo wayar sa agaban aljihu ya danna kiran Madeeha. Dake gaban motar titi yake kallo sam basusan dawar garin ba..
"Hello...'Dan zo Madeeha." Yana gama fada ya katse kiran..
Madeeha ta fito daga cikin motar tana tafiya ahankali. Bayan su ta gano su biyu. Zuciyar ta na mata waswasin shine bata aminta ba.
Ai kuwa tana karasawa ta tabbatar Rayyan din ne...
"Madeeha..." Ya fada kasan makoshi yana narkar mata da manyan idanun sa tubarkAllah...
Batace komai ba ... Ta dai saukar da idanuwan ta kasa tana wasa da yatsun ta na dama...
Murmushi yayi kawai. Ya juya ya kalli Junaid.. ya sake bashi hannu sukayi sallama.
"Nagode aboki na.."
"Ni ne da godia.." cewar Junaid..
Rayyan ya juya yabar wajen yana mai waiwayen Madeeha...
Yana tafiya Junaid yace da ita,
"Ya nata hadank da Allah... Kallo kawai . Shi ya sa na kira ki "
"Ummu tace kar na sake kula shi."
"N sani ai kuma baki kula shin ba. Kallon ki kawai yayi kamar yadda ya roka...Gayen nan fa bashine mai laifi ba. Ki daina azabtar da shi. Ko da yake maganar na gaba da ke kika bi kinyi gaskiya... Toh Allah ya shiga lamarin"
"Aamin.." Ta amsa shi jikin ta a sanyaye.
Mota suka koma... Alokacin Yazed da Fareeha sun dan yi yar soyayyar su. Yazed ya tashi motar suka bar wajen.
Kai tsaye suka wuce babban titi inda direba da ummy suke. Yazed yayita rokan ummy kan shi zai kai su.
Dakyar dai ummyn ta amince ganin kar ta bashi wahala. Aka ciro kayan aka mayar motar Yazed, suka dauki hanyar kauyen da zasu na...
*****RAFIN KANYA****
MX WRITES✓
_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_
_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_
_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: 46_
_ZAFAFA BIYAR 2023_
---
Cikin ikon Allah da buwayar sa su Madeeha suka shiga kauyen rafin kanya.. dandazon yan talle sukayi kan su suna talle,
"Sai soyayyiyar gyada.... Ga mayi... Ga awara da yaji... Ga rogo.." Kowacce ta shiga tallata yan kayayyakin da take sayarwa.
Yazed yayi murmushi ganin sunata zuro masa leda.. Ya zura hannu a aljihu ya dakko gudar nera dubu daya ya mika musu,
"Gashi nan ku raba.."
"Mungode alaji. Allah ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya .." cewar dandazon yan tallan.
"Aamin .." dukkanin su ka amsa..
Ahankali bisaga kwatance da nunen Junaid... Yazed ya kai su Madeeha har kofar gidan su Innarajo..
"Sannu da kokari dan albarka. Allah ya saka maka da alheri. Allah ya yalwata arzikin ku ya cigaba da shiga cikin lamuran ku ." Ummy ta shiga yiwa Yazed addua.
Shi kuwa sai lankwashe kai yake yana mai susa keyar sa cike da kunyar ta... Don a matsayin surukar sa yake kallon ta. Ba shida wani buri yanzu fyace na MALLAKar Fareeha...
Haka dai suka shiga cikin gidan bakin su dauke da sallama harda Yazed.
Sukayi kansu sunata musu maraba....
Aka dakko katuwar tabarma aka shimfida musu.. Suka zazzauna anata yan gayshe gayshe..
Gwaggo ta kawo musu katuwar kwarya cike da fura da nono da yan kofunan silver ta ajiye agaban su.
"Wannan ne ban sheda shi ba." Gwaggo ta nuna Yazed da yatsa tana murmushi.
"Shine wanda ta dalilin sa muka samu matsugunin da muke ciki. Ci da shan mu. Sutura, magani kai komai dai wallahi gwaggo sun dauke mana .. "
"Ma shaa Allahu. Allah ubangiji ya saka musu da alheri ya albarkaci zuriyar su."Gwaggo tayi addua .
"Aamin Aamin.... " Suka amsa Baki daya...
Suka shiga hirar yaushe gamo... Gefe daya kuma shinkafa da wake ne aka kawo musu. Borkindo yaje ya sayo soyayyen kifi a bakin kasuwa suka dora akan abinci suna ci. Suka kora da ruwan sanyi.
Bayan sun kammala ci ne Yazed ya tashi zai tafi. Alokacin innarajo ta farka daga baccin da take yi.. Gwaggo ta sanar mata da zuwan su Madeeha. Duk kuwa da bata ganin su saboda makantar da take da ita...
Ummy ta sanar mata da zuwan Yazed din da wanene shi... Innarajo tayi ta masa addua tana shi masa albarka.
Haka dai suka cika shi da kayan kauye da tsintsiyoyi. Da ya kai wa mahaifiyar su ...
Madeeha da Fareeha da Junaid ne suka raka shi har mota suka saka kayayyakin a booth. Daga nan Junaid ya bashi hannu sukayi sallama.. Madeeha ma ta masa sallama ta koma cikin gidah.
Guri ya zama daga Yazed sai Fareeha a tsaye a jikin motar sa. Ya gyara zaman hular kansa yana kallon ta kasa kasa.
"Sai yaushe zaku dawo?.... Na fara kewar ki."
Fareeha kunya duk ta kamata......Ta saka tafukan hannayen ta ta kare fuskar ta.
Ya sake lankwasar da kai yana duban ta ...
"Uhm.... My baby... Nace zan yi kewar ki sosai."
"Lokaci yana ja..." Ta fada ahankali tana lankwasa yan yatsun ta..
"Bana ganin komai banda ke... Kunnuwana basa jin komai sai zazzakar muryar ki mai dadin sauraro.."
"Uhum.."
"Fareeha.."
"Na'am..."
Ya furzar da iska daga bakin sa..Kansa akan agogon da ke daure a wutsiyar hannun sa yace,
"Bari na tafi...."
"Tohm Allah ya kiyaye hanya.."
"Ba 'dan kalamai... My baby... Babu?"
Shiru tayi. Ta kasa cewa komai..
"Tohm.. Na tafi kenan?"
Ta dan kalle shi ta kauda kai,
"Allah ya kai ka lafiya.."
"Aamin My baby... Kuma Allah ya dawo mana daku lafiya. Zanyi kewar ki sosai... Ke fa?"
Murmushi kawai tayi. Ba tace da shi komai ba. Yazed ya sake gyara tsayuwar sa.
"Shikenan ba abunda zaki ce?"
"Ni ma"
"Ke ma me?"
"Zanyi kewar ... K....a"
Ta fada a rarrabe tana saukar da kai da sauri.
Yazed yayi murmushi. Abunda yake son ji dama kenan.. Ya sake rankwafawa yace da ita,
"Allah ya kare mun ke... Ya tsare mun ke."
"Tare da kai..." Ta sake fada tana murmushi itama.
Bude kofar motar yayi ya shiga ya zauna ya tasheta...
"Kije ...Sai naga shigewar ki ciki zan tafi.."
Wani murmushin ta sake yi masa da ya kara mata kyawu akan kyawun da take da shi..
Tafiya tayi ta shige cikin gidah. Shi ma ya ja motar lokacin daya ga ta shiga ciki. Ya hau kan titi ya dauki hanyar komawa cikin garin na kano..
°°°°°. ,°°°°°. °°°°°.
Ko da ya bar kofar gidan na su... Titi ya nufa ya samu adaidaita sahu ya shige ciki. Dan adaidaita sahun ya kai shi har cikin makarantar ta Birmingham.
Rayyan ya shiga motar sa ya tayar bayan ya sallami me dan sahun. Yana tuki da wayar sa a handsfree ya kira Na'eem..
Bugu biyu ya dauka suka gaysa...
"Na'eem matar nan da kake gayamun makociyar ku yau na hadu da ita.."
"Allah sarki!! Na kwana biyu ma ni banganta ba. Dama sau biyu na taba ganin ta."
"Kai kamar har ta baci... Anya ba ita..
Kit kiran ya katse. Rayyan ya dauki wayar da niyyar sake kira kawai yaga wajen tambarin sunan layin waya na rubuce da manyan bakin 'no service..'
Ya saki siririn tsaki hadi da ajiye wayar a gefen kujera ya kara gudun da yake ya nufi gidan su..
Ko da ya isa gidan.. nabeelah ya tarar a parlor tana kallon drama din pretty little liars..
Ta gayshe shi ya amsa fuskar sa a sake. Kai tsaye ya shige dakin da mahaifiyar sa ke jinya.
Bakin sa dauke da sallama ya zauna... Ta dan juyar da fuskar ta gefen sa. Ya gayshe ta ta amsa dakyar saboda azabar ciwo.
Hannun ka baya rubewa ka yanke ka wullar. Haka ya shiga yi mata adduar samun lafiya da gafarar ubangiji. Tukun sannan ya nufi gidah kansa tsaye.
Yana shiga da motar sa. Ya hango babbar motar da suke tafiya da ita idan zasu wani garin duk yawan su.