← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 66

Sashe 59

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu ya saka ya shafo kasan keyar sa. Cike da kunya yace

"Eh...."

"Yar wacece?"

"Ba yar kowa bace Bappah... Mahaifin ta ma ya rasu. Makarantar mu daya amma ta scholarship ta shigo."

Alhaji Hammadu ya daga kai. Kenan Bintu bata dena halayyar ta ba na chusawa yaranta aqidar kiyayyar talakawa a zukatan su...

Su kayi shiru kowanne da abunda yake sakawa a zuciyar sa. Hajiya Fadila ta sauke kallon ta akan Rayyan kafin tace,

"Dan yaye yau fa yakumbon ta ku zata dawo nan gidan..."

Murmushi fadade a fuskar sa .... Daman duk an karade dangi da zancen Hadiyyah zata dawo... Wacce dai yagani a gidan da su Madeeha suke. Dake iyali biyu ne suke zaune acikin gidan da su Madeeha suke. Shi dai duk daukar sa dayan iyalin sune na su Madeeha. Dayan kuma shine na yakumbo Hadiyyah kanwar su Bappah.

"Allah ya kawo ta lafiya...." Ya fada yana sake yin murmushin.

"Aamin Rayyanu. Amman ba it'a kadai bace ai tanada iyali "

"Alah ya dawo da su lafiya."

"Aamin Aamin Rayyanu."

Alhaji Hammadu ya sake daga kansa ya sauke akan Rayyan ,

"Ka tabbatar kana kaunar ita yarinyar?"

"Eh..." Ya fada a kunyace.

"To shikenan manya zasu shiga cikin zancen bayan anyi bincike akan su."

Rayyan yayi shiru yana matsa yatsun sa.

"Ya akai Rayyan?"

"Bappah.... Mama ta..."

"Uhm.. Ina sauraron ka Mama tayi me?"

"Ta je... Makarantar wajen yarinyar ta gaggaya mata maganganu marasa dadi itada saj-jeedah yar gidan deputy."

"Hajiya kinji wata lukutar masifar ko?" Cewar alhaji Hammadu ya gayawa hajiya fadila.

"Ai na ma rasa abun cewa Hammadu... Dan yaye meyasa baka gaya mun ba.?"

Rayyan bai ce komai ba kan sa dai a kàsa. Alhaji Hammadu ya sake duban sa yana cewa,

"Yanzu kun cigaba da huldar ta ku?"

Ya girgiza masa kai alamun a'ah...

"To fa meyasa?"

Rayyan ya sake daga hannu ya soso kansa da kofar hancin sa daya.

"Ai Bappah.... Taje har gidan su yarinyar."

"Me?"

"Na ce taje har gidan su yarinyar... To maman yarinyar tace lalle ta dena KULA ni ta yanke hulda dani .. Ba ma magana ma yanzu haka."

"Hajiya kinji fa.."

"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun... Kai, Kai..Kai duniya..."

Suna ta jimamin abun... Aka fara knocking kofar sashen .lokacin Rayyan ya dauki kofi ya taro ruwa a dispenser yana sha

Ya nufi kofar da ruwan ahannun sa. Yana budewa suka fara shigowa. Alokacin ya juya baya ya dan zauna akan hannun kujera yana shan ruwan. Muryar ta ta doki kofar kunnen sa. Yana daga kai ya sauke akan ta.

Dai dai lokacin da mahaifin sa Alhaji Hammadu ya mike yana cewa,

"Ku zo nan ku zauna Fareeha... Madeeha kema ga waje."

Yana juyawa suka hada idanu. Ya sauke akanta ta sauke akan sa. Ji kake taratstse... Kofin hannun sa ya fadi kasa ya fashe...

"Madeeha..... "Ya fada cikin daga murya dan baj taba zato ko tsammanin wannan lamari ba na ban mamaki da daure kai. Ashe Madeeha yar uwar sa...?Ashe Madeeha jinin sa ce? Ashe Madeeha yar kanwar mahaifin sa ce? Ashe Madeeha first cousin dinsa ce? Ashe Madeeha da shi din yan uwan juna ne basu taba sani ba???

Mamaki mai tattare da almara ya sauka akan fuskokin su.... Kallon ta yake cike da madaukakin mamaki ... Hakama jta kanta madeehan duk wasu kofofin tunanin kanta sun kulle. Rayyan dan uwanta ne? Zuciyoyin su suka shiga bugawa lokaci daya tamkar zasu fado kasa..

MX WRITES✓
_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: FIFTY(50)_

_ZAFAFA BIYAR 2023_

________
Rayyan ya kasa dauke idanun sa daga kan Madeeha... Sam bai kawo hakan ba ya mance... Kwakwalwar sa ta tariyo masa sanda yaje gidan da su Madeeha din take ranar da su Madeeha din zasu tafi kauyen rafin kanya..... Ya tuno daya daga cikin masu gadin da ya ce masa matar da yake tambayar wacece? Itace mahaifiyar su Madeeha..

Hannu ya saka ya shafo kansa cike da madaukakin mamaki. Wani dadi ne tamkar ana busa sarewa ya shiga zagaye ilahirin jikin sa da gauraye.

Gaba daya sai a lokacin yake tariyo baya... Da sanda Na'eem ke gaya masa akwai wata mata me kama da su Bappah a makotan su.

Ya sake daga idanu ya dora akan Yakumbo Hadiyyah da ke kusa da Hajiya Fadila. Ya juyar da shi ya daura akan Bappan sa.. Wallahi kamar su daya... Kamar an tsaga kara an karya.

Hajiya Fadila ta kira Fareeha da Madeeha ta rungume su tsam a jikin tah. Kaunar da take musu na dada ratsa jijiyoyin jikin ta baki daya tamkar yadda take kaunar sauran jikokin na tah...

"Rayyan..." Alhaji Hammadu ya kira sunan sa.

"Na'am Bappah.."

"Ungo mukullin mota ta kaje Faragai suya ka karbo kajin da nasa a gasa yanzu."

"Tom Bappah .." ya tsugunna ya karbi mukullin yana satar kallon Madeeha da tayi kicin kicin tamkar ba tasan yana wajen ba.

Bayan ya tashi ya tafi ne Fareeha ta daga kai ta sauke akan Madeeha . Kasa kasa tace da ita,.

"Dama Rayyan dan gidan Bappah Hammad ne?"

"Gashi nan kuwa kina gani."

"Allah da iko yake..... Kana ta rayuwa da mutum ba kasan dan uwan ka ba ne."

"Uhum..." Kawai Madeeha tace ta cigaba da matsawa Hajiya Fadila kafafun tah...

Sannu ahankali dangin suka fara hallara... Yaran alhaji Hydar da matar sa da shi kansa. Sai Nabeelah kanwar Rayyan da Yayan su Muhammad shi ma da matar sa. Sai na cikin gidah iyalan Bappah Harith...

A babban kawataccen parlorn sashen suka hallara. Rayyan ya dawo ya kai wa Alhaji Hammad ledojin gaban sa.

"Kash. Kai wa Mamin ku a saka a tray babba mana ko food flask. "

"Tohm Bappah..."

"Ga leda ka bari. Madeeha zo dauki ledar nan ki bishi kinji.?"

"Tohm Bappah."

Ledar ta dauka tabi bayan Rayyan. Tamkar ta kurma ihu haka take ji. Shi kuwa dadi ne ya cika shi ya gauraye shi ya kasa boyewa ya juya yana kallon ta.

"Madeeha...."

Bata ce da shi komai ba ta cigaba da tafiya..

"Ko ince cousin....."

Nan ma tayi shiru bata ce masa komai ba. Rayyan ya saki tattausan murmushi yana sake bin ta da kallo.

"Na gaya miki kaunar mu daga Allah ta ke. Kankat ma gashi da mahaifiyar ki da mahaifi na iwar su daya uban su daya Madeeha... Kinji yadda zuciyata ta kara samun nutsuwa Madeeha? Ki ce wani abu ma na.."

Nan ma batace uffan ba. Tayi gaba tanata sauri... Ya grigzia kai kawai yabi bayan ta.

Kwana yayi tabi bayan sa. Suka je wajen wata kofa ta saka hannu zata bude ya tokare kofar da kafar sa yana mai jefa mata wanu kalll.

"Ka bude please...." Zazzakar muryar ta ta doki kofofin kunnuwan sa. Ya lumshe idanu ya bude ..

"Ki ce Rayyan...."

Kasa fada tayi ta juyar da fuskar ta gefe. Yayi murmushi hadi da sake cewa,

"Ba zaki fada ba?"

"Rayyan..."

"Good... muje to "

Ya shige ciki ta bi bayan sa. Hajja Hindu nata sauri zata fita sai ga su.

"Yanzu nake shirin komawa da ina zaune nayi mantuwa na fito. Ah ah Madeeha ce ko Fareeha?" Ta dubi Madeeha tana murmushi

"Madeeha ce..." Madeeha ta amsa ta tana murmushin itama

"Ma shaa Allah ... tubarkAllah.... Yauwa kajin ne Rayyan?"

"Eh zune Mami."

Karba tayi daga hannun su ta zuba su akan wasu trays manya guda uku.

"Kuje kawai zan bayar a kawo."

"Okay Mami."

Ya saka hannu ya bude kofar da hannun sa. Madeeha ta sunkuya ta hannun nasa ta fice waje...

Ta shiga sauri tana hadawa da gudu. Don kada Rayyan din ya biyo ta. Tariga shi komawa parlron da suka taru. Ta samu waje acan kurya ta zauna ..

Rayyan ya shiga ya nemi waje saitin ta ya zauna. Ya kuma zubamata manyan idanun sa ko kiftawa bayayi sosai. kunya da takaici duk suka taru suka mata yawa..

Aka bude taron da addua... Alhaji Hammadu ne yafara tashi ya gabatar da kansa da gundarin abunda taron zai aiwatar. Bayan yayi Hajiya Fadila ma tayi. Bappah Harith da Bappah Hydar ma suka yi.

Duk maganganun da kowannen su ya tashi yayi magana ce akan rayuwar hadiyyah ta baya ya zuwa ranar irin ta yau. Sosai suka nuna karfin zumuncin su don yaran su su tashi da aqidar hakan...

Aka bawa Hadiyyah Ummy tayi magana ta gabatar da kanta. Daga nan Junaid yayi magana sai Fareeha da tayi tamikawa Madeeha lasifika tayi

Alhaji Hydar ya sake karbar abun maganar yana cewa,

MENE NE MA’ANAR YAN UWANTAKA:

"Wata alaka ce ta kud da kud wadda take shiga tsakanin mutum biyu ko fiye, suna kasancewa a karkashin inuwa guda saboda wani dalili da ya hada su, wato dai alakar tana iya zama ta hanyar dangantaka ta jini, unguwa, wajen aiki, gari, kabila ko addini. Sai dai kuma ‘yan uwantaka ta addini ta fi duk sauran karfi, saboda ita ta bambanta ta hanyar cewa ita alaka ce wacce take tsayuwa ta hanyar shari’a da son Allah, ta yadda dukkan musulmai a ko’ina suke a fadin duniya to ‘yan uwan juna ne, sabanin ‘yan uwantaka ta jini, gari ko kabila domin su a cikinsu za a iya samun sassabawa da adawa da bambance-bambance na addini a tsakanin juna.

MUHIMMANCIN YAN UWANTAKA DA KAUNAR JUNA A MUSULUNCI
"Yan uwantaka da kaunar juna a musulunci babbar ni’ima ce mai tarin muhimmanci kuma wata babbar hanya ce wacce take kiyaye al’umma daga dukkan nau’oi na cutarwa da rarrubuwa, domin za mu ga cewa ta hanyar ne a kan samu hadin kai mai karfi, kuma a kan kasance tare har a yi aiki domin bunkasa addini da warware matsaloli da bukatun al’umma, wanda hakan zai kara taimakawa al’umma su samu yalwatar arziki, dankon-zumunci da kyakkyawar alaka da tarbiyya, kuma su nisanta daga dukkan kaidin makiya na ciki da na waje. Kamar dai yadda za mu iya ganin haka a cikin nassosi na Qur’ani da hadisan Ma’asumai (as).
Chapter 59 · 0% Book details