← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 66

Sashe 36

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Madeeha." Ya sake kiran sunan ta. Sai kallon ta yake. Tayi masa kyau kwarai matuka kamar baby doll.

"Na'am." Ta amsa ranta a dan sake. Don ta gaji da takurar da yake mata

"Ina wuni...?" Ta gayshe da shi ciki ciki.

"Lafiya lau. Madeeha .." ya sake kiran sunan ta bayan ya amsa gaisuwar da tayi masa.

"Na'am..."

"Waye wancen daya sauke kin san shi ne?"

"Wacce irin magana ce wannan?" Ta fada bagatatan. Da alama ma batasan maganar da tayi ta fito ba.

"Kiyi hakuri... Ina son sanin menene alakar ki da shi?"

Karkada kai kawai tayi ta karasa shigewa ciki ba tare da ta sake bi takan sa ba. Shi kansa tamkar ya buge bakin sa saboda yadda yayi mata tambayar a hagun ce.

Jikin sa a sanyaye ya koma ya zauna a inda ya zauna da farko. Bai tashi ba.

Cikin haka sai ga zuwan su Fareeha da Hibba . Hibban ce ke driving. Ya yinda Fareeha ke agefen wajen zama.

Rayyan ya tsaya yana bin su da kallo. Musanman Fareeha da suke matukar kama da Madeeha. Hannun ta dauke da ruwan roba na kamfanin swan.

Shigar ta sanye take cikin doguwar riga mai gajeran hannu da karamun mayafi kalar kayan. Ta shafa jambaki daya karbi fatar dan karamin labbanta. Suna kama sosai da madeehan sa. Sai dai Madeeha ta fu fara'a tana kuma yafa duk mayafi akanta ba a kafada ba.

Waya ya ga ta zaro ta kara a kunnen ta . Ba dadewa sai ga Madeehan ta iso wajen su.

Yaga sun rungume juna suna ta murmushi suna hirar su. Tsayawa yayi yana bin su da kallo. Kana ganin su kasan akwai amintacciyar alaka a tsakanin su.

Sun dan jima suna hirar su a tsaye su ukun. Kafin daga bisani yaga sun mata sallama sun tafi.

Yana dai zaune bai bar wajen ba har su Madeeha suka fito daga lectures din su ta karshen ranar. Kuma itace lectures din su ta karshen semester. Sai semester break da zasu shiga ranar Monday. Har tsawon kwanaki goma sha hudu. Sati biyu kenan.

Yayyafi aka fara kadan kadan. Daliban nata wucewa suna tafiya gidajen su . Madeeha bata futo ba tana lecture hall dinsu tana kwafar notes da kawarta tayi jotting lokacin data zo makarantar dazu tayi latti so bata samu ta rubuta abubuwan da malamin na su ke fada ba.

Ruwa aka tsuge dashi tamkar da bakin kwarya. Sai jiyo zubar ruwan sukayi shaa ta windunan ajin na su

"Madee kinji ruwa." Cewar Nawal kawar Madeeha.

Madeeha ta juya ta dubi windon da ruwa keyin feshi kadan kadan. Ga ruwa anata tafkawa tamkar da bakin kwarya.

"Ma shaa Allah! Marka marka."

"Uhm... Ke dai yi sauri ki karasa jotting din ki tashi mu tafi."

"Yanzu kuwa "

Mikewa sukayi bayan Madeeha ta karasa rubutun suka sauka zuwa kasa don tafiya gidah.

Rayyan ya faka motar sa dai dai kofar faculty din. Yana tsaye a bakin kofar dayan bangaren ba ta inda direba yake zama ba. Ya seta kofar faculty din da kallo yana jiran fitowar ta.

Tasha madaukakin mamaki alokacin da sukayi tozali biyu da shi. Abunda ya matukar bata mamakin kuwa shine ganin nasa da tayi tsamo tsamo acikin ruwa na ta dukan sa. Bai tafi ba tun dazu. Don ta hango shi ma a zaune lokacin da su Fareeha suka zo wajen ta.

Sai kuma ya bata tausayi. Nawal ta matsa kusa da ita . Ta rada mata akunne,

"Ga super glue dinki fa. " Nawal ta rada mata tana ta dariya

Madeeha ta dankara mata harara. Rayyan ya tako har gaban su. Ruwa na 'diga daga kasan rigar sa. Sakamakon yadda ruwan ke zuba shaaaa.. Ma shaa Allah!

Har ya fara atishawa. Ya ja face mask ya rufe fuskar sa. Gaba daya ya cika ta da tausayin sa. Ta daga idanu ta dube shi. Ita ba kowan kowa ba tanata mamakin yadda yake nuna kauna agare ta .

"Ga mota can ku shiga ko?"

Ta daga idanu ta dube shi. Kafin ta juya ta kalli Nawal data daga mata kai da eh. Har sun nufi motar . Muryar Farhan ta daki kofofin kunnuwan su

"Nawal... Madeeha."

Tsayawa sukayi. Suka karasa wajen na su bayan sun gaysa. Rayyan na daga gefe yana kallon su. Yana watsa musu wani kallo na takaicin dashare bakin da Madeeha take tana kula su.

Basu wani dade ba suka gama gaisawa da su Farhan . Madeeha nata raragefe saboda batasan shiga motar. Nawal ta riketa da karfin gaske suka karasa wajen.

Rayyan yanata murmushi dadi kashe sa. Ya bude kofar gaba nawal ta shigar da Madeeha ciki. Ita kuma ta koma baya ta zauna.

Wani dadi yaji yana mamaye ilahirin jikin sa. Ya bude motar ya shiga ciki da basmala da adduar hawa abun hawa. Suka hau kan titi. Yana tafiya a nutse ahankali.

Dai dai bakin titin kusa da gidan mai nawal tace anan zata sauka saboda gidan su na bakin titi. Rayyan ya faka motar ta fita.

Madeeha zata bi bayanta Nawal din ta hanata futa ta hanyar saka hannuwan ta ta tura ta cikin motar . Madeeha badan taso ba ta koma ta zauna tana matse fuska..

"Kiyi hakuri mu karasa... Kinji?" Ya fada mata cikin murya mai dadin sauraro.

Batace da shi uffan ba ya hau kan titi suka cigaba da tafiya,

"Wane unguwa ne?"

"Sultan road." Ta bashi amsa kanta na kan titi.

Ruwan ya tsaya. Rana ta dallare ko'ina.

"Zan sauka anan..."

"Madeeha please .. ki bari na sauke ki agidah."

Muryar sa da dadin sauraro a nutse a kuma hankali cikin lafazin rarrashi.

Suka cigaba da tafiya akan titi ya murda volume wakar Ed. S, yana bi ahankali... Wani dadi na sake mamaye shi yau ga shi ruhin sa Madeeha a mota daya..Kuma su kadai abun sha'awa, Kalaman da mawakin ke fada yana biye da shi. Sunyi dai dai da kalaman da zuciyar sa ke son sanarwa Madeeha. Don itan MALAKIN ZUCIYAr sa ce. Ga shi kuma.. Alhamdulillah burin sa ya cika tana KULA shi duk kuwa da kulawar bata dadin rai bace,

"I found a love, for me darling, just dive right in and follow my lead, Well, I found a girl, beautiful and sweet Oh, I never knew you were the someone waiting for me.. Darling, you look perfect tonight
Well, I found a woman, stronger than anyone I know she shares my dreams, I hope that someday I'll share her home. I found a lover, to carry more than just my secrets to carry love, to carry children of our own...." Yana bi ahankali yana tuki yana kuma juyawa yana kallon ta. Har wakar ta gamu wata ta reason ta shiga.

"Girl, you know I want your love, Your love was handmade for somebody like me. Come on now, follow my lead. I may be crazy, don't mind me... "

Haka suka karasa unguwar. Yazed ya dan juya ya kalleta,

"Meye house number?"

"Ka sauke ni anan..."

"Please... Madeeha.. Mu dena musu. Meye number gidan?"

"578fd"

"Wow... Akwai gidan uncle dina makotan ku ne maybe ma kunsan su. Su 577fd ne gidan."

"Bansan su ba.,... Ba gidan mu bane mu bamu dade da dawowa ba." Ta bashi amsar haka ba tare da damuwa ba.

Ya kasa gane me take nufi. . Don haka ya kyaleta kawai. Bai sake cewa da ita komai ba. Ya kaita har kofar gidan su ta fice da sauri bayan tace masa,

"Mungode "

Murmushi yayi kawatacce yana mai bin ta da kallo har ta karasa shigewa cikin gidan su ...

Kasancewar unguwa daya suke da bappan sa Bappah Hydar. Gidan ma a manne suke da juna su number gidan 577fd ne. Don haka ya biya ta gidan suka gaysa kafin ya wuce unguwar su . Ransa fes. Tamkar an masa babbar bushara. Haka yake jinsa cikin wani irin madaukakin farin ciki marar misaltuwa...

Ranar kowa sai da ya gane Rayyan na cikin farin ciki. Saboda fara'ar da yayita yi yana hira da yan gidan su.

_
_INA JAMA'AR TA MU? KU MARMATSO KUSA . GA TAGOMASHIN ARZIKI. SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI. MUN GWADA DOLE MU BADA SHEDA_

_INA AMARE, UWAYEN GIDA, YAMMATA? IYAYE MAZA DA KE SON FARANTA RAYUKAN MATAN SU DA YAYAN SU DA MA KANNEN SU?_

_ALBISHIRIN KU. GA GORO. DOMIN WANNAN DADDADAN LABARI DOLE MU BAKU ALBISHIR DA ALHERIN GORO. GORON MA FARI KAL KAL_

_WAI AKACE KAMSHI RAHAMA NE... KAMSHIN MA MUSANMAN ME SANYAYA ZUCIYA DA RATSA MAGUDANAR JINI DA TSOKA._

_INA MASU NEMAN KAMSHIN TURAREN SAUDI ARABIA? T'CHAD DA MAIDUGURI? IRE IREN KAMSHIN DA BAYA BIN ISKA YANA KAMA WAJE YA RIKE GIDAH..._

_KAMSHIN TURAREN KAYA, TURAREN GIDA, TURAREN JIKI, TURRARN GASHI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN WANKA, TURAREN WANKI, TURAREN MOPPING, TURAREN BANDAKI, TURAREN LABULAYE DA ZANNUWAN GADO, AIR FRESHENER DA TURAREN AKWATUNA DA DRAWER DA MOTA... KAI HAR MA DA TURAREN DA KE CIRE BACIN RAI YA MUSANYA DA FARIN CIKI SABODA TSANANIN SANYAYAWAR SA DA YAYE DUHU DA DAMUWA_

_BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA NAU'IKAN TURARUKA NA KHUMRAH KALA KALA. SUNADA TURAREN RUWA NA FESAWA DANA MAIKO. SUNADA KAYAN GYARAN JIKI.._

_SUNADA KULACCA DA SAURAN BODY BUTTERS MASU YAYE WARI KODA KUWA AN YI KWANAKI BA WANKA BARE WANKI._

_SUNADA KABBASA TA TURARA KAYA DA KASAKEN TURARUKAN WUTA NA KARFE DANA KASA DAMA NA ZAMANI YAN WAJE._

*_YERWA INCENSE AND MORE_*

_YERWA INCENSE AND MORE_

_YERWA INCENSE AND MORE_

_MASARAUTAR KAMSHI KENAN. KAYAN SU NA AKAN FARASHIN SARI DA SAYA DAYA DAYA.. SUNA YIWA AMARE HADI DA UWAYEN GIDAH DAMA YAMMATA. SUNAYIN NA TARON SHAGULGULAN BIKI DUK AKAN FARASHI MAI RAHUSA_

_BA'ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNA DA TARIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA RAHUSA HADI DA INGANCIN DA ALKALUMA SUNYI KADAN WAJEN BAYYANA MUKU._

_SUNA TURA KAYAYYAKIN SU FADIN NAJERIYA DA KETARE BAKI DAYA._

_ADIRESHIN SU. SUNA GARIN KANO DAURA DA TITIN DA ZAI SADAKA DA GARIN MAIDUGURI_

_SUNA KAN MANHAJOJIN SU DAKE KAFAFE DA DAMA KAMAR:_

_INSTAGRAM: @yerwaincense_and_more_

_FACEBOOK:yerwacollection_

_WHATSAPP: 08095215215/09044191709_

_A YANZU HAKA KAMFANIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE SUNA SALES DIN KAYAN SU NA 250ML NA TURAREN WUTA DA KUMA 240 DA 190ML NA KHUMRAHS_
Chapter 36 · 0% Book details