Sashe 20
Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
*** Tun safe suke gyaran gidan baki dayan su. Saboda kiran da akayi musu a waya. Na su temaka su tattare gidan dukkuwa da an dakko ma'aikata na kamfani sun gyara gidan . Sun tsaftace shi.
Fareeha na sake goge goge drawer din da ke cikin dakin da suke. Daki ne da ya amsa sunan daki irin na masu matashin kai da kudi ake kuma damawa da su a gamayyar masu dukiya.
Ya yinda Madeeha ke malale gadon da wani hadadden zanin gado mai hade da bargwan kwanciya. Ya sha matashin kai (pillows) Komai na dakin samfurin royals ne qirar kasar Turkey.
Babban daki ne da ke dauke da kujeru na alfarma guda biyu da teburi karami a tsakiyar kujerun. Daka daga kai daga saman su kuma shirgegigar talabijin ce mai dauke da kayan kallo.
Sai karamin fridge da dispenser itama a gefe. Da wani dogon abu na ma'adanar takalma. Gefen sa kuma closet ne shake da kayan sawa acikin leda an rarrataye su. Komai dai a killace kuma a tsare.
Ummy ta futo daga cikin bandakin dake cikin dakin. Ta gama wanke shi. Wankewa ta biyu kenan bayan kamfani sunyi na su.
"Ummy sannu da aiki..."
"Sannun ku dai Fareeha da Madeeha. Allah ya muku albarka ."
"Amin Ummy."
"Aamin ummyn mu."
Fareeha ta matsa gaban drawer tana babbankada kayan ciki da ke sakale a hangers. Dogayen riguna ne da suka gaji da tsaruwa. Kana gani kasan kayan masu hali ne.
Sa hannu tayi ta zaro wata bakar riga da ke cikin ledar ta da hanger . Kara ta tayi ajikin ta tana mai kallon kanta ta cikin wani mudubi dogo dake bayyana dukkanin tsayi da jiki.
Madeeha ta juya ta kalleta. Hakama ummy da tausayin su ya kamata.
"Kudi suna inda suke...." Fareeha ta fada hadi da sake manna rigar a jikin ta da hannu daya. Ya yinda dayan hannun ta ke gyara hanger din rigar da ke sakale a jiki.
"Suna inda suke kam Fareeha."
"Kinyi kyau better half... Kyau marar misaltuwa. Danma ba a jikin ki take ba. " Madeeha ta ce da Fareeha ya yinda fuskar ta ke dada buda annurin kaunar da ta kewa tagwan ta ta Fareeha.
"Kun karasa ne?"
"Ni de na gama ummy. "Madeeha ta bawa mahaifiyar ta su amsa.
'kunga wasu turaruwa .." ta fada tana shinshina murafen kwalaben turare.
"Fareeha... Mai da hankali ki karasa musu. Ki kuma mayar da turarukan mutane yadda suke.. Sannan wannan rigar mayar musu da ita kinji?"
"Tohm ummy..." Gyaggyara rigar ta yi ta mayar da ita cikin drawer. Ta kuma gyara zaman turarukan dressing mirror din zuwa yadda su ke.
"Yanzu an dena kiwon dabba mutum ake. Sai kuga wannan yadda suka ajiye komai din hikima ce da kuma gwaji. Amman idan suka zo suna tarar da komai yadda suke da yadda suka killace din. To zakuga yarda da amincewa sun shiga tsakanin mu"
"Maganar ki haka ta ke Ummyn mu. Allah ya bamu wadatar zuciya.. Amin"
"Aameen Madeeha.. Aamin"
"Aamin" Fareeha ta fada a sanyaye itama..
"Ko ina an kammala ko?"
"Eh ummy."
"Turaren wutan da kuka sassaka sun cinye ko? Saboda gudun hadari."
"Sun cinye fa. Awa wajen nawa amman Allah kamshin har yanzu yanayi. "
"Gaskia turarukan sunada matukar kyau.. Sosai fa"
"Sosai kam... Bari mu ga sunan. YERWA INCENSE AND MORE (08095215215/09044191709) Gashi wai suna garin Kano. Suna turawa da kayan su ko'ina a fadin najeriya da ketare. Bisa sari ko sayi 'dai 'dai. .."
"Gaskiya ba algus. Allah kamshin har cikin zuciya ta... "
"Wallahi jam. Kinga Fareeha kullo kofofin can. Ke kuma Madeeha datse musu dakunan ki bar makullan a jiki. Na gidan kuma ki kai wa babar su siddiqa.."
"Amman ummy yanzu sai mu basu makullin bayan ko tsinke ba su zo sun dauke ba?"
"Kar na sake na sake jin kin ce uffan... Abunda nace kenan. Don haka wuce ki je. " Ummy na karasa magana tayi gaba abunta.
Ya yinda Fareeha da Madeeha ke tsaye acikin parlorn. Sunyi curko curko.
"Wai ke meye ne jikin ki duk a sanyaye?" Cewar Madeeha.
"Ba komai" Fareeha ta fada tana jan kafafunta cikin sanyi.
"Karya kike yasin.... Dan Allah me yake damun ki?"
"Hmm..m"
"Ya da hmmm.? Ina sauraron ki."
Fareeha ta zauna akan hannun kujera. Ya yinda dayan hannunta ke jikin kujerar tana shafa ta.
Kirar royal chairs ne. Da suka gaji suka tumbatsa da haduwa. Sai sheki suke .
"Madeeha.."
"Na'am Fareeha.. Don Allah ki sanar mun komai. Kar ki ki fadamun. Kinji? Banason ki rage bacin rai ko yaya ne "
Kada kai Fareeha tayi. Da doriyar cewar,
"Tohm.." a kasan makoshin ta.
Cikin sanyin jiki da sanyin murya mai tattare da dimbin damuwa tace,
"Madeeha yanzu mu haka zamu karkare rayuwar mu? "
"Karkare rayuwa kamar ya ya kenan? Bangane inda zancen ki ya dosa ba Fareeha.. Ki gaya mun yadda zan gane. Kin jefa zuciyata cikin rudu."
Fareeha ta sake sauke dankararriyar ajiyar zuciya mai tafe da dimbin damuwa ta cigaba da cewa,
"Sai yaushe ne rayuwar mu zata sauyi? Sai yaushe ne zamu yi sallama da kuncin rayuwa? Sai yaushe ne zamu samu albarkacin arziki? Shin mu kenan haka zamu kare rayuwar mu da talauci hadi da zama a karkashin inuwar arzikin wasu? Yaushe ne zamu yi rayuwa kamar kowa? Yaushe ne...."
"Ya isa haka Fareeha... Ya isa... Bar cewa komai... Kuma kiyi gaggawa wajen neman gafarar ubangiji. Maganganu kikai cikin kidimewa mai tattare da dimbin rayuwa. Bakya cikin hayyacin ki... Yi sauri ki nemi gafarar mai duka."
"Allah ka yafe mun.." Fareeha ta fada. Kanta a kàsa.
"Yauwa rabin rai ta. Nasan tabbas zuciya batada kashi. Dan Adam ajizi ne tara yake bai cika goma ba. Sannan ki sani cewa dukkanin kowa da komai rubutacce ne daga mai duka. Domin Allah qadirun ne ala manyasha'u. Arziki ko rashin sa, Lapia da rashin ta. Samuwa ko asara. Mutuwa da haihuwa. Arziki ko talauci. Kinga duk yadda mike ganin muna cikin matsatsin nan? Wallahil azim munfi wasu samu a haka. Wasu suna nan na abinci ma nema suke. Amman du bi mu ga matsugunin zama an bamu. Muna cikin koshin lafiya, Mu ci mu sha, Mu kwanta mu farka me yafi wannan? Ga wadatar zuciya Allah ya azurta mu da ita. Ke wani kudin ma musiba ne. Masu kudi da yawa ba sa bacci saboda fargaba. Yan siyasa barin kasar suke saboda gudun hadari. Hakama yan kasuwa da ke gidaje masu tsaunika ... Duk dan tseratar da rayukan su ga halaka. Haba Fareeha bansan ki da wannan halin ba. Kuma nasan tabbas damuwa ce ta kawo hakan. In shaa Allah Allah zai shiga lamuran mu. Zai yalwata mana farin ciki marar misaltuwa. Zai azurta mu ya buda mana kofofin rahamar sa. In shaa Allah komai zai wuce. Allah baya dorawa bawa abunda ba zai iya dauka ba. Kinji ko rabin rai.?"
Fareeha ta danyi murmushin da hakoran ta suka bayyyana farare tas da su a jajjere.
"Na ji..."
"Ma shaa Allah! Ubangiji Allah ya cigaba da dafa mana. "
"Aamin Yaa Rabbi."
"Aamin Aamin."
Kullo windows sukayi da kofofin suka bar makullan ajiki. Babbar kofar da zata sadaa ka da cikin gidan itama sun datse ta sun cire mukullin.
Madeeha na kokarin sake murde handle din kofar dan tabbatarwa da kofar ta rufu ruf kenan. Masu gadin gidan suka tura jijjigaggan gate din daya gaji da kawatuwa a kuma dakeee
Zungura zungurar jifajifai har uku ne suka shiga harabar gidan. Bakake da su hakama maduban motar duk tinted glasses ne. Madeeha da Fareeha suka bi motocin da kallo. Musanman Fareeha da baki daya kacokan hankalin ta ya koma kan su.
Safiya mahaifiyar su siddiqa suka fito da sauri daga bangaren su. Zaninta sauran kadan ya kunce saboda saurin da ta ke yi.
Kofofin murafen motar ne suka budu. Dukkanin su suka shiga sauka daga cikin motocin.
Da sauri Safiya ta kwace mukullin da ke hannun Madeeha cikin karfin ta har tana mauje mata hannu. Lamarin ya ba wa Madeeha mamaki kwarai matuka. Musanman da kunnuwanta suka fara jiyo mata kararakin da safiyan ke fada,
"Sannun ku da zuwa hajjajun mu. Ashe mun kammala gyaran ko'ina a dede. Yanzun nan na koma ciki nace bari na watsa ruwa kafin ku iso. Mun sha aiki ne tun safe ba zama. Kai tsayuwar me kuke yi ne? Je kuce wa mahaifiyar ta ku babu sauran aiki tunda baku zo ba sai yanzun da mukaa karasa komai ni da siddiqa.. Sai yanzu itama take wanka.."
Madeeha bakinta ya kasa rufuwa saboda tsananin mamakin abubuwan da Safiya take fada. Baki daya ta juya zancen. Cikin takaici da tsantsar mamaki tace,
"Bangane muje ba. Ni da Fareeha da mahaifiyar mu ummy mu kadai ne muka gyara gidan nan muka share ko'ina muka wanke wurare hadi da saka turaruka na wuta. Narantse da girman Allah tsinke baku dauke ba. Banda yanzu wallahi baki daya yau banga fitowar ku ba ma. Mukulli kuma yanzun nan kika finkice sa a hannu na. Bacin mun gama aikin kenan ummyn mu taa koma gidah tace mu rufe ko'ina mu bar keys din a jikin kofofin..."
Nan da nan safiya ta fara salati tana sallallami hadi da tafa hannaye ta nana a cinyar ta. Ya yinda Haj Ruwaida matar gidan tayi murmushi kawai. Hakama sauran yaranta da suke tare. Ameer da Abdullahi da Hibba. Yazed da ke can gefe idanuwan sa zube akan su Fareeha. Tunda Madeeha ta fara magana yake binta da kallo har ta dire zancen ta. Kafin ya sake mayar da kansa kan Fareeha. Ya shiga yi musu wani kallo mai tattare da son gano wani abu game da su.
"Dukkanin ku mungode Allah ya saka da alkhairi Allah ya bar zumunci. Bari mu shiga ciki mun kwaso gajiya. "Haj Ruwaida na karssa fada tayi ciki. Ya yinda yaranta ke biye da ita a baya idan ka tsame Yazed
"Fareeha, Madeeha."
"Naam Yaya Yazed."
"Naam Ina wuni?"
"Duk lafiya kalau .. Ku gaysar mun da ummyn ku. Mungode da dawainiya. Zan shigo idan na dan watsa ruwa. "
"Toh shikenan "