← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 66

Sashe 48

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bayan rasuwar sa ne. Aka raba gado kakata ta gaji nata gadon da na dan ta daya da suka haifa tare wanda nake agidan sa yanzu ni da ita. Wato Bappah Harith... Daga baya Bappah Harith din ya sayarwa Bappah na gidan ya sa yi wani a wata unguwar daban. Nafu kaunar kakata fiye da iyaye na saboda awajen ta na tashi itace ta zamar mun uwa ta kuma zamar mun uba. Kuma mahaifiya ta tabbas itace wadda tazo ta same ki a makarantar nan ta kuma je gidan ku. Saj-jeedah itace wadda ta fadamun mahaifiya ta ta miki gori akan kudi da sauran su. Sannan
Itama saj-jeedah din ta gaggaya miki magana. Da idona biyu lokacin na biyo ta gidan ku don ganin ki idanuwana suka ganemun fuskar motar mahaifiyata da ita acikin motar take tukawa ta fito daga gidan ku.

"To gundarin abunda na ke son sanar miki anan shi ne. Ba wai akan ki suka fara fadan maganganu ba marasa dadi. Mace ta farko da na fara kauna a duniya yar gidan kanwar mahaifiya ta ce. Uwassu daya uban su daya. Sunan ta Nana Firdausi. Ana ce mata Nana. Ni kuma Ina kiran ta da Nanatah. Madeeha bansan so ba sai akan Nana Allah ya jikan ta da rahama... Na so ta na kaunace ta fiye yadda labbana zasu furta Madeeha. Kinga dai da uwata da uwarta uwar su daya uban su daya ko? Wallahi mahaifiya ta bata kaunar ta kiri kiri tafuto tace wallahi ba zan auri Nana ba. Me zanyi da yar talakawa yar kauyen kwantakwaran da ke cikin Katsina,

"Nace mata ni da Ina kaunar ta a haka. Ban damu da kauyen cin ta ba ko karamin karfi da suke da shi. Nace ita din dai na keso ba wani abu daya dangance ta ba. Wallahi Madeeha sam sam mahaifiya ta taki yarda sam taki amincewa. Ta kuma sata sabamun idan har na gayawa mahafi na ko kakata Hajiya Fadila... Ke akan alakar ta da Nanatah wallahi Madeeha mahaifiya ta sai ta yanke zumuncin su da kanwar tata fa da suke uwa daya uba daya. Tace mata babu ita babu ita har duniya ta tashi.

"Na samu mahaifi na da zancen Nanatah. Mahaifin nawa ya tsawatar wa mahafiyata. Yace ta kyaleni mu cigaba da mu'amalar. Ya kuma ja kunne na da na cigaba da karatu na samu hankalin kai na sosai sannan ayi auren mu da nana. Wallahi Madeeha dake Allah qadirun ne ma ala manyasha'u. Shi ya barwa kansa sanin kowa da komai. Sai Nanatah ta fara ciwo a tsaitsaye. Daga karshe ma sai Allah ya karbi ran abar sa..

"Bayan rasuwar Nanatah. Na cire duk wata alaka ta soyayya da kaunar wata macen arai na. Allah ne nafi sani na dena shiga harkar kowa da komai idan aka dauke Hajia ta da mahafina . Amman ko mahaifiyata gaisuwa ce kawai take hada mu. Na dena mayar da hankali akan kowa da komai. Na dena shiga harkar dik wani abu da zai tarwatsa mun lissafi. An kai ni kasashen waje donyin karatu gaba daya na ki mayar da hankali. Haka suka gaji aka dawo dani gidah. Mahaifiya ta bata hakura ba tacigaba da hadani da yaran kawayen ta. Duk adalikin wai nayi aure na karbi ragamar kasuwancin mahaifina kamar babban wa na. Tafu so mu iya yaran sa mazan mu karbi ragamar kasuwancin ba tare da ya saka wasu daban ba. Mu uku ne kawai Allah ya azurta iyayen mu. Babban wa na Muhammad muna krian sa da moha. Sai ni Rayyan. Sai kuma kanwar mu nabeelah. Babana yanada kamfanin aluminium . Yanada kamfanin ruwan roba. Yana da kamfanin yin robobi . Yana kuma da manyan shaguna a kasuwar singa da sauran malls masu suna Hammads Marts. Sai travelling agency na fita kasashen waje da sauran su. Amman dik kanin kasuwancin nan nasa ko kadan bana ra'ayin su. Mahaifiya ta ta yi nayi naki yi. , Ta shiga hadani da 'yayan kawayen ta ko kannen su da sauran wanda take sa acigita. Kowacce ta hadani da ita basu mun ba. Duk naki yarda naki amincewa da hadin da ake mun... Madeeha na tsani komai,

"Aganinna tunda na rasa Nanatah banida wani sauran gata. Aganinna rayuwata ta zama useless batada wani amfani. So duk wani abu me muhimmanci na tattare na ajiye a gefe na dena yi. Kwatsam sai Bappah na da mike a gidan sa ni da Hajia kakata wato Bappah harith ya sake nemo wata makaranta ta kasar ingila da suka yi reshen su anan garin na kano wato makarantar nan ta Birmingham. Ko da na shigo makarantar nan dan ba yadda zanyi ne Bappah Harith da Hajiya sun tasani agaba. Haka ma Mami matar Bappah Harith data dauke ni tamkar babban danta data haifa itama ta rikeni. Kan dana yi hakuri na fara karatu hadi da mayar da hankali sosai.

"Ko da na shigo makarantar nan ba zuwa nake ba. Asha ruwan tsuntsaye kawai nake. Bana mayarda hankali ba kuma na zuwa yadda ya kamata ni da su T-Boy. Madeeha. Wallahi Allah tun ranar matriculation dinku dana dora Ido na akan ki kun fito daga mota kin tsaya kina gyara mayafin jikin ki daya koma gefe tun daga nan ZUCIYA ta sai ta kamu da kaunar ki. Love at first sight ne madeeha. Na fara kaunar ki tun da idanuwan suka doru akan ki Madeeha I've never had a moment doubt . I love you ,I believe in you completely. You are my dearest one, my reason for life .. Madeeha I don't care how hard being together is. Nothing is worse than being apart.. Madeeha in a sea of people. My eyes will always be searching for you♥️No matter what has happened. No matter what you've done. No matter what you will do I will always love you . I swear it.., Ke ce sanadin sauyin kaddarar rayuwata Madeeha. Ke din KULA NI da kike yi shine mabudin daya inganta rayuwata madeeha. Kin zamar mun MALLAKIN ZUCIYAH... Rayyan ka bar kaza kayi kaza. Wallahil azim Madeeha na sauya hali na kamar yadda kike buri. Kullum Ina zuwa lectures. Weekends Ina sch library. Attendance. Weekly assignments . Open tests. Individual attendance. Presentations, Duk basa wuce ni Madeeha.... Dan Allah ki tausaya mun kar hannun agogo ya koma baya. Ki tausaya mun karki rabu da ni. Ki tausaya mun ki cigaba da KULA NI....

"Ke din MALLAKIN ZUCIYAH ta ce Madeeha. Rashin ki a rayuwata ba karamin asara zan ba. Madeeha ban taba kaunar wata mace a duniya sama da ke ba. Ko Nanatah Allah ya gafarta mata da rahama ban mata kwatankwacin kaunar da nake maki ba. Domin akan ki har a asibiti na kwanta Madeeha.. Narasa farin ciki na saboda ke Madeeha. Kalli yadda na rame saboda ke. Madeeha bakiji zuciyata yadda take cuwo ba saboda rashin ki. Idanuwan na begen ganin ki. Madeeha please ... Ki temake ni kiyi hakuri. Idan baki hakura ba zan kai karar mahaifiyata wajen mahafi na zan sanar masa komai. Sannan zan samu Hajiya kakata na gaya mata itama. Madeeha kasancewar mu ni da ke awajen nan sai da nayita rokon su nour tukun suka amince da sharadin ba zaki rasa sauran lectures din ba nace na yatda.... Ya kike so nayi? Dole na gayawa Bappah abunda mama ta aikata."

"Àa kar kai haka..." Tayi saurin fada bakin ta na rawa.

Rayyan yayi murmushi yana sake kada kai,

"Muryar ki ma azabtar dani kike akan ta madeeha kin saka numbers na a block list. Akan ki na sai layikan waya da yawa. Dukwnanda na kira ki da shi ko na turo miki sako seki goge kiyi blocking . Ya kike so nayi da rai na eh? Haba madeeham bakisan Ina kaunar ki bane madeeha?, "

Kasa magana tayi. Rayyan ya cigaba da tarairayar ta cikin maganganu masu dadin gaske masu dauke da kalamai masu ban tausayi da tura sakon kauna ga wanda ake gayawa.

Ya bude baki zai cigaba da magana kenan. Aka shiga bugo kofar ajin. Yayi mamaki kwarai matuka saboda yasan ajin renovating dinsa akeyi ba zaa fara lectures acikin sa ba sai an dawo sabuwar semester.

Yadda ake jijjiga kofar ne hadi da wullo duwatsu yasa Rayyan yin wajen kofar a fusace. Bayan inde su Nawal ne sun rigada sunyi magana da shi ba zasu hadu da Madeeha ba sai lectures din 4_6 hudu zuwa shida.

Fareeha ya hangi tanata cika tana batsewa.

"Malam bude ka fito mun da yar uwata... Rabun rai kina ina?"

Madeeha dake jingine da bango ta tafi da sauri ta riko kofar. Rayyan badan yaso ba ya bude ya juya yana bin Madeeha da kallo

"Kice wani abun Madeeha.. KI KULA NI madeeha.. ke din MALLAKIN ZUCIYAH ta ce.."

"Allah ya sutturu buqwi. Zo mu wuce madeeha." Ta riko hannun ta suka bar wajen.

Rayyan yabu bayan su Amma Ina.. kafin ya karasa tuni Fareeha ta tura Madeeha cikin motar Hibba suka bar cikin makarantar baki daya.

Jikin sa a sanyaye ya cigaba da kallon motar hae suka qure ganin sa. Ya bar wajen shima ransa duk a jagule. Zuciyar sa na ta kissima masa abubuwa da yawa...

.
_INA JAMA'AR TA MU? KU MARMATSO KUSA . GA TAGOMASHIN ARZIKI. SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI. MUN GWADA DOLE MU BADA SHEDA_

_INA AMARE, UWAYEN GIDA, YAMMATA? IYAYE MAZA DA KE SON FARANTA RAYUKAN MATAN SU DA YAYAN SU DA MA KANNEN SU?_

_ALBISHIRIN KU. GA GORO. DOMIN WANNAN DADDADAN LABARI DOLE MU BAKU ALBISHIR DA ALHERIN GORO. GORON MA FARI KAL KAL_

_WAI AKACE KAMSHI RAHAMA NE... KAMSHIN MA MUSANMAN ME SANYAYA ZUCIYA DA RATSA MAGUDANAR JINI DA TSOKA._

_INA MASU NEMAN KAMSHIN TURAREN SAUDI ARABIA? T'CHAD DA MAIDUGURI? IRE IREN KAMSHIN DA BAYA BIN ISKA YANA KAMA WAJE YA RIKE GIDAH..._

_KAMSHIN TURAREN KAYA, TURAREN GIDA, TURAREN JIKI, TURRARN GASHI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN WANKA, TURAREN WANKI, TURAREN MOPPING, TURAREN BANDAKI, TURAREN LABULAYE DA ZANNUWAN GADO, AIR FRESHENER DA TURAREN AKWATUNA DA DRAWER DA MOTA... KAI HAR MA DA TURAREN DA KE CIRE BACIN RAI YA MUSANYA DA FARIN CIKI SABODA TSANANIN SANYAYAWAR SA DA YAYE DUHU DA DAMUWA_
Chapter 48 · 0% Book details