← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 66

Sashe 31

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kaunar ta na ke T-Boy. Kauna irin wadda bata yankewa a zuciya. Kauna irin wadda ke sanyaya ruhi da magudanan jini. Kauna ce wadda ta kere a kwatanta tah..."

"Amman dai ka sani kai ma. Ko da tana kaunar ka auren ku ba zai tabayiwu wa ba... Ita din ba kowa ba ce. Makarantar nan ma ta scholarship akace ta shigo right?she's nobody.

"Bandamu ba guy... Tunda na fara dora idanu na akanta a kallon farko. Na kamu da kaunar ta a zuciya tah...Kai bari na gaya maka. Zan iya sadaukar da kowa da kuma komai akan kaunar ta."

"Gatacan da nata saurayin kana nan kana wahalar banza..."

Rayyan na daga kansa ya hango tana dashare wa wani saurayi kyakkyawan hakoran ta. Sai murmushi take faman yi.

wani abu ya taso ya dunkule masa a zuciya. Zai mike tsaye kenan. Baby -Saj ta zo wajen na su tana karkada mukullin motar ta..

.
_INA JAMA'AR TA MU? KU MARMATSO KUSA . GA TAGOMASHIN ARZIKI. SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI. MUN GWADA DOLE MU BADA SHEDA_

_INA AMARE, UWAYEN GIDA, YAMMATA? IYAYE MAZA DA KE SON FARANTA RAYUKAN MATAN SU DA YAYAN SU DA MA KANNEN SU?_

_ALBISHIRIN KU. GA GORO. DOMIN WANNAN DADDADAN LABARI DOLE MU BAKU ALBISHIR DA ALHERIN GORO. GORON MA FARI KAL KAL_

_WAI AKACE KAMSHI RAHAMA NE... KAMSHIN MA MUSANMAN ME SANYAYA ZUCIYA DA RATSA MAGUDANAR JINI DA TSOKA._

_INA MASU NEMAN KAMSHIN TURAREN SAUDI ARABIA? T'CHAD DA MAIDUGURI? IRE IREN KAMSHIN DA BAYA BIN ISKA YANA KAMA WAJE YA RIKE GIDAH..._

_KAMSHIN TURAREN KAYA, TURAREN GIDA, TURAREN JIKI, TURRARN GASHI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN WANKA, TURAREN WANKI, TURAREN MOPPING, TURAREN BANDAKI, TURAREN LABULAYE DA ZANNUWAN GADO, AIR FRESHENER DA TURAREN AKWATUNA DA DRAWER DA MOTA... KAI HAR MA DA TURAREN DA KE CIRE BACIN RAI YA MUSANYA DA FARIN CIKI SABODA TSANANIN SANYAYAWAR SA DA YAYE DUHU DA DAMUWA_

_BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA NAU'IKAN TURARUKA NA KHUMRAH KALA KALA. SUNADA TURAREN RUWA NA FESAWA DANA MAIKO. SUNADA KAYAN GYARAN JIKI.._

_SUNADA KULACCA DA SAURAN BODY BUTTERS MASU YAYE WARI KODA KUWA AN YI KWANAKI BA WANKA BARE WANKI._

_SUNADA KABBASA TA TURARA KAYA DA KASAKEN TURARUKAN WUTA NA KARFE DANA KASA DAMA NA ZAMANI YAN WAJE._

*_YERWA INCENSE AND MORE_*

_YERWA INCENSE AND MORE_

_YERWA INCENSE AND MORE_

_MASARAUTAR KAMSHI KENAN. KAYAN SU NA AKAN FARASHIN SARI DA SAYA DAYA DAYA.. SUNA YIWA AMARE HADI DA UWAYEN GIDAH DAMA YAMMATA. SUNAYIN NA TARON SHAGULGULAN BIKI DUK AKAN FARASHI MAI RAHUSA_

_BA'ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNA DA TARIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA RAHUSA HADI DA INGANCIN DA ALKALUMA SUNYI KADAN WAJEN BAYYANA MUKU._

_SUNA TURA KAYAYYAKIN SU FADIN NAJERIYA DA KETARE BAKI DAYA._

_ADIRESHIN SU. SUNA GARIN KANO DAURA DA TITIN DA ZAI SADAKA DA GARIN MAIDUGURI_

_SUNA KAN MANHAJOJIN SU DAKE KAFAFE DA DAMA KAMAR:_

_INSTAGRAM: @yerwaincense_and_more_

_FACEBOOK:yerwacollection_

_WHATSAPP: 08095215215/09044191709_

_A YANZU HAKA KAMFANIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE SUNA SALES DIN KAYAN SU NA 250ML NA TURAREN WUTA DA KUMA 240 DA 190ML NA KHUMRAHS_

_IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE AKWAI RAGIN KUDI DA HADI NA MUSANMAN DA ZAA YIWA DUKKANIN KAYAN DA KUKA SAYA._

_KYAU!! INGANCI! RAHUSA!! KAMA JIKI DA GIDAH!! AIKI!! ADADE ANA MOREWA SAI KAYAYYAKIN TURARUKAN KAMFANIN:*YERWA INCENSE AND MORE*_

_____
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼:27_

_ZAFAFA BIYAR 2023_

_

   *Tsayawa* tayi kerere akan su... Sanye cikin abaya kalar purple data ji stones ta koshi.

"Barkan ku dai ..."

"Barkan mu Baby Saj ."

B-junior da ke gefen kujera ya muskuta yana gyara zaman sa.

"Zo ga waje ki zauna.."

Girgiza kai kawai tayi alamun a'ah. Ta koma bangaren da Rayyan ya ke .

Shi kuma alokacin Madeeha ya zubawa idanuwa yana bin ta da kallo ita da wanda suka tsaya a tare

Haka kawai yaji zuciyar sa na masa zugi da radadin ganin Madeeha da yayi da wani saurayin. Fararen hakoran ta tanata murmusa masa su.

Abu ya taso ya tokare masa a maqoshi. Gashi shi ya kasa zuwa ya yi mata sallama don ta KULA shi. Tabbas kaunar da yake mata ta gama zamar masa MALLAKIN ZUCIYAH..

"Ray...." Sa-jeedah ta kira sunan sa tana ta murmushi tamkar zata yage bakin ta.

Ya dan kakaro murmushin yaken shima,

"Saj-jeedah... Ya kike?"

"Lafiya kalau Mr. Ray na mu. Meya faru ne?"

"Ma shaa Allah.."

"Nace wani abun ne ya faru da kai?"

Bai bata amsa ba. Sai ma sake dage kansa da yayi kamar zanqala qoki. Gano Madeeha da yayi ita da wannan saurayin sun samu wajen zama sun zauna. Wata yarinya ma da alamar kawar madeehan ce ta nufi wajen su ta zauna. Suna ta hirarrakin su.

Da sun hada idanu sai ta zabga masa harara. Gashi har hararartata kyau take kara mata a idanun sa.

Saj-jeedah wani abu ya taso ya tokare mata. Takaicin su ya ishe ta. Ta daga hannu ta karkada shi alamun waving a dan gaba da fuskar sa.

"Snap out of it... Meke damun ka ne Rayyan?" Ta sake tambayar sa cike da son sanin mayatar kallon da yake bin wasu kucakai da su aganin ta.

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke. Kafin ya dan dube ta,

"A'ina?"

"Wadancan kucakan da kake kallo mana..."

"Okay yanzu kallo ma ban isa nayi ba ?" Ya tambayeta yana dan matsa hannuwan sa daya harde waje daya..

Turo baki tayi gaba cike da shagwaba. Girgiza kai kawai yayi. Ya zaro wayar sa aljihu. Kasa kasa yana video din Madeeha yana sake zooming dede fuskar ta. Dama wayar tasa privacy screen ce. Don haka su B-junior basa ganin komai...

Yana tsaka da video dinne wani saurayi da wata budurwa suka je wajen zaman su Madeeha suka zazzauna. Sunata hirar su

Yana daga kai. Idanuwan su suka sarke dana juna. Madeeha ta cuno baki gaba.

"Wai wancen mutumin wane jrin mayataccen kallo yake da shi ne? Wallahi haushin sa nake ji. Ya cika kallo. Dan sa'ido kawai.."

Ta fada tana mai nunawa kawayen ta Nour da nawaal ... Rayyan .

Habeeb daya daga cikin samarin biyu da ke tare da su Madeeha ya tabo dayan da ke da suna Farhan.

"Ka gane wa take nufi?"

"A'ah.."

"Course mates dinmu mana.."

Juyawa Farhan yayi. Ya danyi murmushi kawai yana rufe baki.

"Su Mr Ray... T-Boy da B-junior da baby Saj."

"Su dai..."

"Su waye su din?" Madeeha ta tambaye su tana gatsine baki.

Farhan ya muskuta ya sake gyara zaman sa. Ya shiga yi musu bayani.

"Wancen na farkon da ke shan lemo a hannun sa sunan sa B-junior dan gidan ambassador dawud Bashir ne. )Sunan kakan sa Bashir ya ci. Shine ake ce da shi B-junior. Suna da matukar kudi mai wuyar fasaltawa. Mahaifin sa kafin ya zama ambassador ya rike mukamai da yawa na gwamnati.

"Na kusa da shi kuma T-Boy dincan. Sunan sa Tahir . Mahaifin sa shine mai Himma hotels and co...)Yan kasuwa ne dangin sa. Suna da kudi sosai. Ance baban na sa yanada hotels a wasu garuruwan ma da kamfanoni.

"Sai ita waccen macen sunan ta sa-jeedah. Ana kiran ta da baby Saj. Baban ta shine deputy governor na garin nan. His excellency Ismail Auwal Wadau..

"Sai shi Rayyan dincan family din su masu matukar kudi ne na bugawa a jarida. Suna da gidajen mai a fadin najeriya garuruwa da dama. Suna da kamfanoni da dama. Mahaifin sa Alhaji Hammadu oil mogul ne. A bangaren aluminum kuma ba shi da na biyu...

"Su kadai suke harkar su. Basa shiga shirgin kowa. Basa kula kowa. Su kadai suke rayuwar su. Inde harka ce ta kudi to gaskiya duk makarantar nan sun kere kowa ."

"Chab... To dan sunada kudi shikenan sai su dinga wannan izzar haka? Kuma ai kowanne da kudin da iyayen ku ke da shi. Ba scholarship kuka ci ba kamar ni." Cewar Madeeha.

"Ai su na su kudin ya zarce duk inda ake tunani "

"Ki dena cewa haka my best girl." Nour ta ce da Madeeha don karfafa mata gwiwa.

"Ai shine... Kuma ai gwara ace kokarin ka ne ya kawo ka ba kudin iyayen ka ba."

Haka dai suka cigaba da hirarrakin su. Daga karshe kuma lokaci yayi sukayi wa su Farhan sallama suka koma class.

Domin su Farhan din karatu suke koya wa su Madeeha. Su din ba yan year one bane. Ajin su daya da su Rayyan..

Rayyan ya sauke zuciya lokacin da Madeeha ta mike suka tafi . Yaji dadi a ransa da ta tafi tabar mazan da suke a tare. Ya kuma ji rashin jin dadi saboda bazai cigaba da kallon kyakkyawar fuskar ta ba.

Wasa wasa sai da su B-junior suka gano Rayyan. Duk kuwa da boye boyen da yake. Amman kaunar da yake nuna yana yi mata dole suka gano

Gashi ko ya kwatanta KULA ta. Bata sakar masa fuska. Zata bata rai ta wuce shi kawai.

Abun ya fara damun sa sosai. Har yazamto su B-junior sun gano halin da yake ciki.

CIKIN takun sa na kasaita mai tattare da zatin haiba da madaukakin kwarjini ya fara hawa mattakalar benen da zai sadaka ga dinning hall/cafeteria din makarantar.

Daga can karshen kuryar hall din ya hango abokan na sa su biyu. Kamar ko da yaushe babu dalibai awajen sosai. Sai wanda suka isa suke kuma gadara da kudin iyayen su.

Duk inda ya gifta sai dalibai yan uwan sa sun juya sun sake duban sa sosai. Saboda tsananin kyawun sa, Kasaitar sa da kuma gayun sa.

Sanye yake cikin kananun kaya. Samfurin designers riga Burberry da wando Dkny. Agogon sa kalar rigar jikin sa na Rolex, Sai azurfa a yatsan sa daya.

Ya karasa wajen abokan nasa ya zauna yana cije lebe.

"Geee..." Cewar T-Boy.

"Guy...Sup?"
Chapter 31 · 0% Book details