← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 66

Sashe 46

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya janye idanunsa masu nauyi daga kan motar tata data yi U-turn ta fita daga cikin unguwar. Da kanta kuma take tuka motar ba direba ke janta ba. Kuma idan har taja mota da kanta to fa lalle koma menene tanaso taje da kanta ne ta cika shi.

Ba jimawa sai ga dawowar Madeeha. Dan adaidaita sahu ne ya dawo da ita har kofar gidan. Ta sauka ta shige ciki da sauri.

Ya kasa janye idanunsa daga kanta har sai da ya kule ganin ta. Zuciyar sa na dada tafarfasa. Gangar jikin sa na ingiza shi. Baki dayan foundation din da yayi akan alakar su da Madeeha su mama da saj-jeeda sun ruguza shi.

Ya bude bakin sa. Hadi da furtawa da labban sa da suke amsa nauyi yace,

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Allahumma ajirni fi musibati....

..
_INA JAMA'AR TA MU? KU MARMATSO KUSA . GA TAGOMASHIN ARZIKI. SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI. MUN GWADA DOLE MU BADA SHEDA_

_INA AMARE, UWAYEN GIDA, YAMMATA? IYAYE MAZA DA KE SON FARANTA RAYUKAN MATAN SU DA YAYAN SU DA MA KANNEN SU?_

_ALBISHIRIN KU. GA GORO. DOMIN WANNAN DADDADAN LABARI DOLE MU BAKU ALBISHIR DA ALHERIN GORO. GORON MA FARI KAL KAL_

_WAI AKACE KAMSHI RAHAMA NE... KAMSHIN MA MUSANMAN ME SANYAYA ZUCIYA DA RATSA MAGUDANAR JINI DA TSOKA._

_INA MASU NEMAN KAMSHIN TURAREN SAUDI ARABIA? T'CHAD DA MAIDUGURI? IRE IREN KAMSHIN DA BAYA BIN ISKA YANA KAMA WAJE YA RIKE GIDAH..._

_KAMSHIN TURAREN KAYA, TURAREN GIDA, TURAREN JIKI, TURRARN GASHI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN WANKA, TURAREN WANKI, TURAREN MOPPING, TURAREN BANDAKI, TURAREN LABULAYE DA ZANNUWAN GADO, AIR FRESHENER DA TURAREN AKWATUNA DA DRAWER DA MOTA... KAI HAR MA DA TURAREN DA KE CIRE BACIN RAI YA MUSANYA DA FARIN CIKI SABODA TSANANIN SANYAYAWAR SA DA YAYE DUHU DA DAMUWA_

_BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA NAU'IKAN TURARUKA NA KHUMRAH KALA KALA. SUNADA TURAREN RUWA NA FESAWA DANA MAIKO. SUNADA KAYAN GYARAN JIKI.._

_SUNADA KULACCA DA SAURAN BODY BUTTERS MASU YAYE WARI KODA KUWA AN YI KWANAKI BA WANKA BARE WANKI._

_SUNADA KABBASA TA TURARA KAYA DA KASAKEN TURARUKAN WUTA NA KARFE DANA KASA DAMA NA ZAMANI YAN WAJE._

*_YERWA INCENSE AND MORE_*

_YERWA INCENSE AND MORE_

_YERWA INCENSE AND MORE_

_MASARAUTAR KAMSHI KENAN. KAYAN SU NA AKAN FARASHIN SARI DA SAYA DAYA DAYA.. SUNA YIWA AMARE HADI DA UWAYEN GIDAH DAMA YAMMATA. SUNAYIN NA TARON SHAGULGULAN BIKI DUK AKAN FARASHI MAI RAHUSA_

_BA'ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNA DA TARIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA RAHUSA HADI DA INGANCIN DA ALKALUMA SUNYI KADAN WAJEN BAYYANA MUKU._

_SUNA TURA KAYAYYAKIN SU FADIN NAJERIYA DA KETARE BAKI DAYA._

_ADIRESHIN SU. SUNA GARIN KANO DAURA DA TITIN DA ZAI SADAKA DA GARIN MAIDUGURI_

_SUNA KAN MANHAJOJIN SU DAKE KAFAFE DA DAMA KAMAR:_

_INSTAGRAM: @yerwaincense_and_more_

_FACEBOOK:yerwacollection_

_WHATSAPP: 08095215215/09044191709_

_A YANZU HAKA KAMFANIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE SUNA SALES DIN KAYAN SU NA 250ML NA TURAREN WUTA DA KUMA 240 DA 190ML NA KHUMRAHS_

_IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE AKWAI RAGIN KUDI DA HADI NA MUSANMAN DA ZAA YIWA DUKKANIN KAYAN DA KUKA SAYA._

_KYAU!! INGANCI! RAHUSA!! KAMA JIKI DA GIDAH!! AIKI!! ADADE ANA MOREWA SAI KAYAYYAKIN TURARUKAN KAMFANIN:*YERWA INCENSE AND MORE*_

_____
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: 39_

_ZAFAFA BIYAR 2023_

   *Ji* yake baki daya gabobin jikin sa na rawa. Ya yinda labban sa suka yi masa nauyi. Wasu hawaye masu dumi suka fara zuba daga idanuwan sa.

Yasan halin Hajiya Bintu ba zata yi musu ta dadi ba. Ya dora kan sa akan sitiyari yana sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Ya yin da idanuwan sa suka fara yi masa nauyi. Taa ke wata jijiya ta fito radau a wajen goshin sa. Kansa na masa ciwo sosai

Wani zazzabi ya rufe shi sosai. Ba zai iya mayar da kansa gida ba. Hannun sa na rawa ya janyo wayar sa. Ya danna number Na'eem ya kira shi . Danma Allah ya temaka yasan number Na'eem din akan sa.

Na'eem: "Hello Mr Ray. Ka kira ni kuma kayi shiru."

Rayyan din ya dan matse idanu. Hannun sa akan saitin kirjin sa yace,

"Na'eem kana ina?"

"Ina gidah. Banda de da dawowa ba ai. Wait mun futo daga elective courses din da muke nake tambayan su T-Boy kana ina? Sukace ka bar cikin makaranta. Fatan komai kalau dai ko? Saboda sautin muryar ka ma ya canza.."

"Fito ka kai ni gidah please. Ina cikin mota."

"SubhanAllahi! Kana ina yanzun?"

"Ina area din ku."

"Okay gani nan fitowa."

Rayyan ya dan yi baya da kujerar sa ya kwantar da kansa. Ya yin da ya shiga lumshe idanuwan sa. Cikin zuciyar sa kuwa abubuwa yake ta sakawa yana warwarewa.

Ba jimawa kuwa Na'eem ya fito saqale da waya a kunnen sa yana kiran Rayyan. Tana shiga ya hango motar Rayyan din ma sai ya katse kiran ya karasa wajen sa.

Ya bude mazaunin direba yana mai bin Rayyan din da kallo.

"SubhanAllahi... Ko malaria kake yi ne?"

Rayyan ya girgiza masa kai alamun a'a kawai. Ya mike dakyar ya fita daga mazaunin direba ya koma dayan kujerar ya zauna..

Na'eem ya shiga ya tayar da motar da addua dauke a bakin sa. Ya juya yana mai bin Rayyan din da kallon tausayi.

"Sannu."

"Yauwa... Nagode"

"Wai meke faruwa ne? Na'eem din ya sake tambayar Rayyan yana juya kan motar zuwa hawa kan babban titi..

"Mami ce again da saj-jeedah."

"SubhanAllahi. Kar dai kace mun saj-jeedah ta samu Madeeha ta mata rashin mutunci?"

"Wallahi ta same ta .. Mami ma harda gorin kudi. I'm in severe pains."

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Abu beyi dadi ba. Wayyo Allah na"

"Kai dai bari kawai .. Na rasa abunda ke mun dadi Na'eem. Shikenan ni haka zan cigaba da rayuwa banida damar na KULA wadda nake so sai an shiga tsakanin mu? Na'eem ba zan iya rayuwa ba Madeeha ba. Yadda nake jin yarinyar nan a zuciya ta. Har cikin raina wallahi. I love her with every fiber of my being. Na'eem.. Ina kaunar Madeeha . Ta zamar mun MALLAKIN ZUCIYAH. Kuma zan iya sadaukar da farin ciki na domin na mallake ta. "

Na'eem ya girgiza kai kawai. Shi kansa ya rasa abun cewa. Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yana tallabe habar sa.

"Gaskia abunnan ya wuce mizanin hankali. Yanzu ya kake ganin za'ai?"

"So nake na dan samu nutsuwa kawai. Amman gaskia Allah shine mafi sani. Yadda nake kaunar yarjyar nan ba zan iya bari su mama da saj-jeeda su raba mu ba."

"Yarinyar nan ai kasurgumar munafuka ce. Wallahi wallahi na tsane ta"

"Ga mama ta kasa dena raba ni da mutane Na'eem. Wacce iriyar rayuwa ce wannan? " Ya karasa fada hadi da girgiza kai kawai ya juyar da shi gefe

"Mama Bintu ce. Ni bansan ma me zance ba. Amma abu daya dana sani dai saj-jeedah ce zataje ta sake hura maka wuta. Yarinyar nan ai kana ganin ta gaka crook ce."

"Ba zan iya rabuwa da madeeha ba abunda na sani kawai kenan. Dole nayi fighting na dawo da Madeeha cikin rayuwa ta Na'eem. "

"In shaa Allah.. Khair... Zaku dawo ku cigaba da mu'amalar ku. Har ta kai ga zamowa matar ka."

"In shaa Allah...Aamin.! Na'eem ."

Haka dai suka karasa. Na'eem ya shiga motar gurin adana motocin gidan. Ta kofar baya Rayyan ya shiga sashen su.  Ya shige dakin sa da sauri . Bandaki ya fada ya rage cikin sa ya yo wanka hadi da dauro alwala.

Na'eem ya masa sallama ya biya wajen su Hajia Fadila suka gaysa sannan ya wuce gidah.

Ranar Rayyan ko abinci bai samu yaci ba. Yana idar da salla ya koma ya kwanta saboda wani gagarumin zazzabi da ya sake lullube shi har yana kakkarwar sanyi. Dakyar bacci ya dauke shi. Cike da mafarkai na muradin ran sa Madeeha.

     ✓✓✓ ✓✓✓✓✓.      ✓✓✓✓ ✓✓✓✓.

      Dakyar ta iya jan kafafunta ta shiga cikin gidah a lokacin da mai adaidaita sahu ya sauketa a kofar gidah.

Da Fareeha taci karo a sashen boys squatter din su tana tattare wajen da tsintsiya.

Da sauri ta saki tsintsiyar hannun ta ta karasa wajen madeehan da sauri. Domin suna gane wa idan dayan su na cikin damuwa ko akasin haka.

"Rabin rai tah."

"Na'am.." Madeeha ta amsa ta. Sai kuma ta fashe da kuka.

Fareeha ta rungume ta itama tana mai zubar da hawayen.. hadi da bubbuga bayan Madeeha cikin lallashi.

"Bar kuka Madeeha... Dan Allah ki dena zubar mun da hawayen ki.."

"Fareeha., Fareeha yau... F"

"Shhh! Bari cewa komai. Ai mahaifiyar sa bata dade da fita ba kika shigo."

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.... Dan Allah? Har gidah tabiyo ni bayan wanda tamun a makaranta.?"

"Hmm babu komai rayuwa ce. Allah ze mkli sakayya in shaa Allahu."

Wasu tafarfasun hawaye ne suka shiga sake kwaranyo mata a fuskar ta. Fareeha tayita bata baki kafin daga bisani taja hannun ta su shiga cikin sashen na su.

Ummy na zaune akan kujera tana jin rediyo. Suka shiga bakin su dauke da sallama. Ta amsa hadi da daga idanu ta dora su akan yan biyun nata.

"Ummy." Madeeha ta fada ranta duk ba dadi

"Naam Madeeha. Kin dawo?"

"Na dawo ummy "

"Toh sannu da dawowa. Fareeha dakko mata abincin ta a kitchen."

"Tohm ummy."

Fareeha take ta dauko Maya abincin a kitchen ta ajiye agaban ta. Hadi da janyo ledar pure water ta curo daya shima ta ajiye agaban ta.

"A koshe ma na ke ummy "

"Daure dai ki ci"

Madeeha ta ce to hadi da janyo abincin ta shiga ci tana korawa da ruwa . Cikin ta duk ya cunkushe

Ta cinye dakyar ta mayar kitchen ta kurkure bakin ta.

Jikin ta du ba dadi tayi hanyar daki zata shiga ummy ta kira ta.

"Madeeha."
Chapter 46 · 0% Book details