← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 66

Sashe 41

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rayyan ya daga kansa ya sauke akan CCTV dake a wajen a makale. Takaici ya sa ya juyar da kansa gefe.

Ba dadewa kuwa sai ga shi an bude kofar. Sanye ta futo cikin doguwar riga kirar Egypt. Bata yafa mayafin rigar ba. Ta dai daure shi akanta tamkar dan kwali. Fara ce mai matsakaicin haske.

"Shigo.. Rayaan" Ta fadi sunan nasa a yangance hadi da saka hannu ta yi masa nuni da cikin gidan.

Mai gadin ya dashare mata baki yana mata jinjina da hannun sa.

"Ga irin taki uwar daki na."

"Godia na ke... Rayaan ka shigo."

Rayyan ya juya ya kalli me gadin da shi dinma kallon sa yake. Ya shiga cikin gidan bayan ya tsaya ya zare kafarsa. Mai dauke da bakar safa daga cikin takalmin .

"Oh my goodness....Ai kafi kyau a fili Rayaan."

Rayyan ya dan yamutsa fuska. Yadda take bata masa suna tamkar ya zazzabga mata mari. Ya dai danne zuciyar sa kafin yace,

"Sunana Rayyan. Ray-Yan. Rayyan." Ya fada mata yana rarraba sunan nasa harafi bayan harafi.

"Na sani ni de na zabi ce maka Rayaan din saboda na banbanta da sauran ko?"

Bai ce komai ba. Ya bi bayan ta suka shiga wani parlor. Sai karkada jiki take tana turo baki gaba. Hakan da take ba karamin sake bakanta ransa yake ba. Dan dai ba yadda zai yi ne yaki yiwa mahaifiyar sa biyayya, Amman ba ta inda suka dace shi da yarinyar. Kai dama sauran yan matan da ta hahhada shi da su.

"Ka zauna." Ta fada tana mai masa nuni da kujera me cin mutum daya.

Kada kai yayi. Ya nemi waje ya zauna.

Ta zauna a kujerar kusa da shi ta juya sosai ta fuskance shi tamkar zata hadiye shi.

"Sunana Hafsat... Ana ce da ni Amsa ko Hafsy.. Kai fa?"

"Sunana Rayyan. Haka ake gaya mun."

"Ko Mr Ray ba?" Ta karasa fada tana murmushi

Shima kakaro murmushin yayi kamar zai yi kuka. Ya shiga hada hannuwan sa yana dan kallon tv da ke nuna tashar zee tv.

"Me zaka sha? Don Simon, Malt? Lemonade ? Fura? Yoghurt ko...

"Kakki damu a koshe na ke."

"Ni de dan Allah fa nace .."

"Aban ruwa to."

Mikewa tayi tanata karkada jiki ta nufi fridge ta dakko ruwan roba daya da wani tray me dauke da cup a saman sa. Ta ajiye agaban Rayyan

"Bismillah."

"Alright .. Thank you."

Daukae ruwan yayi. Yayi basmala ya sha ya ajiye agaban sa.

"Kana Birmingham uni ko?"

"Eh.. " Ya amsata kansa akan ruwan daya ajiye .

"Level nawa?"

"3... " Ya sake amsa ta

"Wane course?"

"Architecture."

"Wow... Ni ba zaka tambaya ni ba?"

"Kiyi hakuri. "

"Well ni ina Newton university. Level 4. Ina karantar sociology."

"Ma shaa Allah.."

"Sannan ina.......

Dif ya lula duniyar tunani. Sam bai cigaba da sauraran maganganun da take fada ba. Tanata zubar magana tamkar 'yayan kanya.

Babu ta inda suka hadu. Komai nasu yayi bam bam dana juna. Acikin tunanin ya sake daga kai ya sauke akanta. Ta saka hannu tana nuna masa wani frame da ke dauke da hotanta ta gama secondary school da alama zayyane masa bayani take akai.

"Ni na fi kowa kyau da kokari ajin mu. Duk kuwa da inada suruta gaskiya. Ba zaka tambaye ni akan salis ba?"

Sai a sannan ya dawo dai dai ya saurari maganganun ta na karshe. Wanda baki daya Bai san maganar me take akai ba.

"Na'am.?"

"Nave baka tambaye ni akan salis ba. Kaga duk dai abunda na fada ya danganci salis. "

Wani abune ya tokare masa a wuyan sa. Irin halin tsaka me wuya daya shiga. Bayaso ya nuna mata bai saurari komai ba sai zancenta na karshe. Don ba zataji dadi ba. Don haka ya maze kawai ya kakaro murmushi,

"Ai kokarin ki ne ya burgeni sosai. Salis Allah sarki. Yana ina yanzu?" Yaci magani irin gaskiyar gasken nan.

Hafsat ta sake muskutawa ta shiga zayyano masa bayani ta karkare da,

"Iyaye na ba zasu bari na aure shi ba. Saboda gaskiya gidan su ba irin masu kudin nan ba ne. Suna de da dan kudin su haka dai. So long story shot aka raba soyayyar da ke tsakanin mu. Anata hadani da maza ni gaskia duk ba sanda yamun. Toh luckily enough sai ga mom dinka ta wa mamana magana. Sukayi exchanging pictures din mu. Naga ka mun . Nace eh a hada mu....Kasan yanzu auren kwarya tabi kwarya ake. Wa ke son auren wahala? So ni dai kamun 100 percent. Wa zai iya hulda da yaran talakawa? Captial NO! Kana saurara na kuwa Rayaan?"

Rayyan yayi shiru. Maganganun ta na dada nanatuwa a kofofin kunnuwan sa. Gaba daya dama bata yi masa ba. Sannan maganganun da ta yiyyi sun sake futar da ita daga ran sa...

Ya dubi agogon dake daure a wutsiyar hannun sa. Tara saura kwata. Ya mike batare da yace da ita komai ba yayi hanyar fita

"Rayaan.."

Bai ce da ita komai ba ya cigaba da tafiya zai fita ta babbar kofar gidan tayi sauri ta riko hannun sa....

_
_INA JAMA'AR TA MU? KU MARMATSO KUSA . GA TAGOMASHIN ARZIKI. SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI. MUN GWADA DOLE MU BADA SHEDA_

_INA AMARE, UWAYEN GIDA, YAMMATA? IYAYE MAZA DA KE SON FARANTA RAYUKAN MATAN SU DA YAYAN SU DA MA KANNEN SU?_

_ALBISHIRIN KU. GA GORO. DOMIN WANNAN DADDADAN LABARI DOLE MU BAKU ALBISHIR DA ALHERIN GORO. GORON MA FARI KAL KAL_

_WAI AKACE KAMSHI RAHAMA NE... KAMSHIN MA MUSANMAN ME SANYAYA ZUCIYA DA RATSA MAGUDANAR JINI DA TSOKA._

_INA MASU NEMAN KAMSHIN TURAREN SAUDI ARABIA? T'CHAD DA MAIDUGURI? IRE IREN KAMSHIN DA BAYA BIN ISKA YANA KAMA WAJE YA RIKE GIDAH..._

_KAMSHIN TURAREN KAYA, TURAREN GIDA, TURAREN JIKI, TURRARN GASHI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN WANKA, TURAREN WANKI, TURAREN MOPPING, TURAREN BANDAKI, TURAREN LABULAYE DA ZANNUWAN GADO, AIR FRESHENER DA TURAREN AKWATUNA DA DRAWER DA MOTA... KAI HAR MA DA TURAREN DA KE CIRE BACIN RAI YA MUSANYA DA FARIN CIKI SABODA TSANANIN SANYAYAWAR SA DA YAYE DUHU DA DAMUWA_

_BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA NAU'IKAN TURARUKA NA KHUMRAH KALA KALA. SUNADA TURAREN RUWA NA FESAWA DANA MAIKO. SUNADA KAYAN GYARAN JIKI.._

_SUNADA KULACCA DA SAURAN BODY BUTTERS MASU YAYE WARI KODA KUWA AN YI KWANAKI BA WANKA BARE WANKI._

_SUNADA KABBASA TA TURARA KAYA DA KASAKEN TURARUKAN WUTA NA KARFE DANA KASA DAMA NA ZAMANI YAN WAJE._

*_YERWA INCENSE AND MORE_*

_YERWA INCENSE AND MORE_

_YERWA INCENSE AND MORE_

_MASARAUTAR KAMSHI KENAN. KAYAN SU NA AKAN FARASHIN SARI DA SAYA DAYA DAYA.. SUNA YIWA AMARE HADI DA UWAYEN GIDAH DAMA YAMMATA. SUNAYIN NA TARON SHAGULGULAN BIKI DUK AKAN FARASHI MAI RAHUSA_

_BA'ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNA DA TARIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA RAHUSA HADI DA INGANCIN DA ALKALUMA SUNYI KADAN WAJEN BAYYANA MUKU._

_SUNA TURA KAYAYYAKIN SU FADIN NAJERIYA DA KETARE BAKI DAYA._

_ADIRESHIN SU. SUNA GARIN KANO DAURA DA TITIN DA ZAI SADAKA DA GARIN MAIDUGURI_

_SUNA KAN MANHAJOJIN SU DAKE KAFAFE DA DAMA KAMAR:_

_INSTAGRAM: @yerwaincense_and_more_

_FACEBOOK:yerwacollection_

_WHATSAPP: 08095215215/09044191709_

_A YANZU HAKA KAMFANIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE SUNA SALES DIN KAYAN SU NA 250ML NA TURAREN WUTA DA KUMA 240 DA 190ML NA KHUMRAHS_

_IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE AKWAI RAGIN KUDI DA HADI NA MUSANMAN DA ZAA YIWA DUKKANIN KAYAN DA KUKA SAYA._

_KYAU!! INGANCI! RAHUSA!! KAMA JIKI DA GIDAH!! AIKI!! ADADE ANA MOREWA SAI KAYAYYAKIN TURARUKAN KAMFANIN:*YERWA INCENSE AND MORE*_

_____
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: 35_

_ZAFAFA BIYAR 2023_

    *Juyawa* yayi da sauri ya fuzge hannun sa. Ya dube ta yace da ita,

"Haba Hafsat... Macen kwarai bata haka. Allah yasa ki gane." Ya fice da sauri.

Tanata kiran sa yaki juyawa. Tabi bayan sa da kallo tana kyakkyabe fuska. Kafin daga bisani ta saka yatsa a baki ta ciza.

Tayi cikin gidah da sauri tana kuka wiwiwi. Ko da Rayyan ya futa mota ya shige da sauri ya tada ita yabar cikin unguwar da sauri.

Hannun sa daya akan sitiyari ya yinda dayan ke kansa yana shafawa zuwa kwantaccen gashin da ke zagaye da habar sa, Ya zuwa sajensa na gefe da gefen fuskar sa.

Ya furzar da iskar bakin sa mai zafi yana jujjuya kai kawai. Maganganun ta na dada yi masa yawo acikin kai. Da hannun ta data saka ta riko nasa hannun. Ya rufe idanun sa.

Hadi da komawa gefen titi ya faka ya kwantar da kansa ta baya hadi da yin baya da kujerar. Ya tuno sanda Madeeha ta wanke fuskar sa da mari alokacin da ya riko jakarta kawai.

Ya tuno yadda take kokarin suturta jikin ta da mayafai ko hijabi. Hadi da kamewa da take da ita yalwacacciya. Ya sauke idanun sa akan kiran hafsan dake shigowa wayar sa.

Taa ke ya saka hannu ya kashe wayar gaba daya, ya shiga tunanin kala kalan yan matan da mahaifiyar ta sa take hada su da shi.

Ya sauke gwauron numfashi hadi da nannauyar ajiyar zuciya. Gaba daya ba shida sauran kuzari.

Ya saka hannu ya danno gidan CD da taa ke ta fara da sautin karatun suratul baqra bisa ga jogorancin muryar shekih Sudeis.

Wani sanyi ya fara sanyaya ransa da bin magudanar jinin sa. Ya dan jima awajen kafin ya tashi motar ya tafi. Alokacin da ya lura wasu masu gadi nata zarya. Dake duniyar ta zama abunda ta zama kowa yana tsoro. Ganin ko shi din da ya faka wani mugun abun qin zeyi.

Kai tsaye ya wuce majalisar su. Su kansu abokan sunyi mamakin zuwan sa awannan lokacin. Kasancewar shi din ba ya zaman majalisa idan har dare yayi. Da ranar ma bai cika zama ba.

T-Boy: "Maza yau an tuno mu kenan ko?"
Chapter 41 · 0% Book details