← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 66

Sashe 61

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dukkan su an daura auren na su ne akan sadaki mafi daraja .. Bayan an daura aka yi luntsumemiyar reception na maza yan daurin aure a farfajiyar gidan Bappah Harith...

MX WRITES✓✓
_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: 51_

_ZAFAFA BIYAR 2023_

**Tare suke baki dayan su a dakin Mami matar Alhaji Harith. Ciki harda Hibba data dawo gidan tun ana'i washe gari za'a fara biki...

Sanye suke cikin wasu laces hadaddu da suka kawaatu da dinkuna da mayafai da suka matukar sake dago tsaruwa da kayan sukayi musu.. Gefe daya yan biyun sun sake fito da kwalliyar kayan cikin kyawun su da Allah ya albarkance su da shi.

Beelanah beauty (08034697302) itace me makeup din da tazo gidan tayiwa amaren kwalliya. Kasancewar su din ba su taba makeup ba sai wani irin kyawu marar fasaltawa ya wanzu a fuskokin su dama sauran jikin su baki daya... Ga me kwalliyar ta iya kwalliya sosai..

"Yauwa to an gama..."

"Ma shaa Allah! Har kin kammala beelanah?"

"Na gama Hibba ."

"Wow gaskiya sun yi kyau sosai."

"Ma shaa Allah..."

"Nima na gama kabbasar kayan su... "

"Habawa ai ke dik turaruwan ki babu na yar wa ... Su ke sayar da kan su kayan ki ai... Saboda ingancin su."

"Gaskiya duk turarukan wuta da khumrahs da sauran kayan kamshi na kamfanin yerwa incense and more (08095215215) babu na asarar kudi. .."

Me turaren tayi murmushi .. Hadi da tattare komai da ta curo ta mayar cikin jakarta.

"Wai tun yanzu zaki tafi Madame yerwa ?"

"Sauri nake zan yi gyaran jikin wata amarya zan kuma turara kayan amaryar."

"Ma shaa Allah Allah ya temaka."

"Aamin Aamin.."

"Dan tsaya mu tafi please... Zanje gidah na shirya ni sai na dawo ."

"Okay Beelanah beauty... Gaskiya kin fito mana da amaren mu gasunan reras achan achan da su."

Sukayi dariya baki dayan su... Hibba ta raka su me turarem da me kwalliyar har bakin motar da za'a mayar da su gidajen su kasancewar home service ne.

Rayyan ne daga can gefe a zaune yana latsa wayar sa da ke hannun sa .. Wata folder ya shiga da take acike taf da hotunan Madeeha..

Daya bayan daya ya shiga kallon su yana sake zooming fuskar ta. Sai murmushi yake kamar sabon mahaukaci.

Na'eem ya isa wajen sa yana murmushi ya bashi hannu suka gaysa.

"An daura... Angon Madeeha bada kan ka asare." Na'eem ya bashi hannu suka tafa yana mai gaya masa haka..

Yana karasa fada Rayyan ya dubi gabas yayi sujjada yana mai godewa Allah abisa cika masa burin sa da yayi na MALLAKar Madeeha da yake dakwan kaunar ta a ZUCIYAr sa ... Tun tana kin KULA shi har dai ta fara kadan kadan... Tsabar farin ciki sai da hawaye ziri daya daya suka zuraro daga idanun sa...

"Alhamdulillah... Alhamdulillah... Alhamdulillah.." ya daga hannuwa ta fada hadi da shafawa a fuskar sa.

"Muje mu buga ps."

"PS zaka buga da wa kenan?"

"Da kai mana."

"Ni? A ranar da aka dauramun aure da macen data fi kowa kyau awaje na.. Babban burin da Allah ya cikata mun yau. Zaka ce na bika muyi game... Bayan haka kuma yanzu na shiga jerin me iyali ni ba saurayi bane irin ka." Yana karasa fada ya jefa masa harara.

Na'eem ya tuntsire da dariya har yana rike da cikin sa

"Kai dai mutumin wofi ne... Daga auren ka yau zaka fara gayawa mutane magana."

Rayyan ya juya ya masa daquwa,

"Oho dai.... Na fita daga layin gauraye.."

Yan uwa da abokan arziki nata chudadowa da yin dafifi wajen angwayen biyu.. Sunata basu hannu suna gaysawa hadi da tsayawa ayi musu hoto..

Daga nan wajen masallacin suka dunguma zuwa cikin gidan na Alhaji Harith don cin liyafar da aka hada ta ta reception..

Tsaye Na'eemah take agaban window yayinda ta dage window tana duban wajen farfajiyar gidan. Ganin shigowar mazan sunyi dafifi sunata shiga cikin gidan.. Hakan ya sanya Na'eemah daga hannu sama ta shafa a fuskar ta.

"Alhamdulillah!! An daura.... Kaga amaren Ya Rayyan da Ya Yazed...."

Dakin ya dau shewa da sauran kawayen su dake ciki. Mari ma budurwar Junaid tazo . Itama an saya nasu auren zuwa bayan sallah babba.

Haka dai yammatan sukaita tsokanar su Madeeha anata dariya ana shewa. Can sai ga shigar Hibba dakin da sauri,..

"Angwaye sun shigo... za'a dau hotuna."

Madeeha ta juyar da kai ta dora akan Fareeha da itama kallon nata take.. Fareeha ta saka hannu ta riko hannun madeeha suka tashi tsaye..

Sanye Madeeha take cikin lace blue da yasha duwatsu yellow suna ta kyalkyali. Yayin da mayafin ta kalar yellow ne shima hadi da takalmanta da ke kafarta shima yellow ne..

Fareeha kuma tana sanye ne cikin lace ash daya sha duwatsu silver ... Mayafin ta da takalmanta suma silver ne

Sai sarkoki da suka sassaka da abun hannu na awarwaro da kuma zobe ..

Ahankali kuma a nutse suke tafiya kawayen na su na agaba. Su kuma sune a karshe.

Suka nufi babban parlorn da angwaye da abokanan suke.

Na'eemah tayi sauri ta karasa tsakiyar parlorn tana cewa,

"Yauwa assalamu alaikum..."

"Wa'alaykm salam...." Suka amsa baki dayan su.

"Toh Alhamdulillah... Ba abunda zamu ce da Allah sai nuna godiyar mu a gare shi.. Allah ya karawa annabi daraja da karaama."

"Allahumma Aamin.." suka sake hada baki wajen amsa mata.

"Okay angwayen dai biyu ne kamar yadda kowa ya sani. Akwai Ya Rayyan da Ya Yazed.. amare kuma akwai Fareeha da Madeeha.. Gasunan a jere dai kungan su. To inason please ya yazeed da ya Rayyan kowa yazo ya nuna amaryar sa acikin ku."

Rayyan ya daga kai yana murmushi. Domin shi tunda ya shiga idanun sa ke akan Madeeha... Duk taron mutanen da ta shiha ba zai taba mancewa da fuskar ta ba. Fuskar tata data zamo masa maganin damuwar sa. Da kaunar ta yake kwana yake kuma tashi..

Lokaci yana tafiya angwaye... Idan kuma kun kasa gane su to ku fada."

Rayyan ya mike daga zaman da yayi. Cikin tafiyar sa mai takun takama da kasaita hadi da jini a jika na matashin gwarzon angon da ke tattare da nishadi mai dauke da madaukakin farin ciki marar misaltuwa..

Yana karasawa wajen ya dora idanun. Sa akan Fareeha yayi murmushi... Ya juya ya saka hannuwan sa ba biyu ya rungume Madeeha hadi da yi mata rumfa da jikin sa. Cikin kunnenta ya rada mata,

"Congratulations to us...Mrs Rayyan.. Allah yasa mun bude shafin farin cikin rayuwar mu kenan . Allah yabani ikon KULA da ke Madeeha. Ina kaunar ki, Ina kaunar ki, Ina kaunar ki kauna wadda ba zaa taba kimanta adadin ta ba.. I love you with every fiber of my being." Yana karasa fadawa ya sakar mata sumba a gefen kunnenta ya kuma sake sakar mata wani a saman goshin ta..

Parlorn ya dauka da karar kawayen amare da abokanan ango.. Yazed ma ya matsa wajen Fareeha ya sanya hannu ya dakko nata ya runtse su waje daya yana jefa mata wani kallo mai tafiya da wanda akewa kallon .

"Dan Allah ku dan tsaya a dauke ku a hotunan." Cewar zaarah. Ng me hoto.. (08021481240)

Styles ta shiga basu na hotunan tana mai daukar su kala kala. Bayan kowanne yayi da matar sa sai aka fara yi da kawaye da na abokanan ango.

Rayyan bakin sa tamkar zai yage saboda yadda yake dashare shi yana rike kuma da hannun madeeha yaki cikata..

Sai da su Mami suka fara shigowa za'ayi hotan da su tukun sanan Madeeha ta mintsile shi ya saketa.

Haka dai yan uwa suka yi ta shiga anayin hotunan da su. Kafin daga bisani angwayen su fita.

Wuri ya zama sai amare da kawayen su. Aka kawo musu abinci kala kala suka cicci.

Bayan sunyi sallah ne sai suka fara shirye shiryen zuwa kai amaren Fareeha da Madeeha..

Bayan an shirya su cikin wasu lafayoyi masu dan karan kyau da tsada sashen ummy da Hajiya aka kai su..

Duk bappanin su na nan. Gefe daya kuma kawu Ashiru ne yanata hura hanci. Tunda yaji labarin yan uwan ummy nada maiko maiko (kudi) ya sab'aba ya dawo yana dandalar arzikin albarkacin yaran.

Da fari su Madeeha basu so hakan ba. Ummy ta tsawatar mu su hadi da cewa hannun ka baya rubewa kace zaka yanke ka wullar .

Fada sosai aka shiga yi musu na jan kunne abisa rayuwar da zasuyi agidajen auren su.

Ummy na daga gefe bata cewa komai . Sai dai idan anyi addua ta sunkuyar da kanta kasa ta amsa da Amin a kasan makoshi..

Sai daga karshe bayan dukkanin su sunyi musu fada idan aka cire ummy da bata cewa komai...

Sai bayan an kammala ne da zaa saka su a mota .. aka kai su wajen ummyn don suyi mata sallama.

A tsakiya suka sakata. Gefe Madeeha. Dayan gefen Fareeha. kuka sike harda wiwi. Kuka ne mai tsuma zuciyar duk wanda ya saurara..

Duk suka karyar da zukatan mutanen wajen.. duk dauriyar ummy sai data kasa hawayen itama suka shiga yar tsare a fuskar ta.

Ta yakice su da kyar tana goge hawayen da tissue din da ke hannun ta. Cikin murya marar sauti sosai tace,

"Allah ya sanya alkhairi da albarka', salaama, zaman lafiya, yalwar arzuka, wadatar zuciya, da rayuwa me inganci a rayuwar auren ku Fareeha da Madeeha... Allah ya muku albarka. Allah ya muku albarka , Allah ya muku albarka.. Allah ya kauda fitnah a tsakani. Allah yasa rai aka yiwa, Allah ya baku ikon kula da mazajen na ku..Su kuma su rike ku da amana, kuyi musu biyayya yi nayi bari na bari , sabuwar rayuwa ce zaku shiga ta daban... Allah yabada zuriya ta gari me yalwar albarka." Tana karasa fada ta juya da sauri ta shige cikin dakin ta ta turo kofar.

Sosai suka sake fashewa dawani kukan . Dakyar aka iya lallashin su. Aka janye su aka nufi motoci da su.

Gidan Fareeha aka fara zuwa aka kaita. Daga karshe kuma aka kai Madeeha nata gidan.

Yan kai amare suka juya zuwa gidah suna masu bin su da adduoin zaman lafiya a da yara masu tarin alkhairi da albarka.

Kawayen amare kuwa sai da sukayi siyan baki suka cancame kudaden su...
Chapter 61 · 0% Book details