← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 66

Sashe 44

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni ba tsarar taraiyyar ka bace Rayyan..Ni din ba yar gidan kowann kowa bace. Hasalima makarantar nan ta scholarship na shigo ba tare da iyaye na sun biya kudin makarantar ba. Bamu da shi idan kaf danginmu zasu hadu ba zasu taba iya..

"Shhhh madeeha say no more... Kin dauka kaunar da nake maki ta danganci kudi ko mulki ko sarauta ne? Noo Madeeha ni ke nake kauna ba wani abu da ya dangance ki ba. Ina kaunar ki fuye da yadda labbana suke furtawa. ...Madeeha ki dubeni ki mun sassauci ki amshi rokon da nake miki kinji?"

Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya kanta na gefe tace,

"A yanzu dai kayi hakuri. Karatu ne agabana. "

"Zan iya jiran ki ai .. Matukar zaki amince da ni."

Kasan leben ta ta kamo ta ciza. Yar wayarta dake hannun ta ce ta fara kara ta dauka ta kara a kunnenta.

"Okay yazo! Alright gani nan." Ta mike da sauri tana gyara zaman hijabin jikin ta.

"Ina zuwa?"

"Lecturer din ya dhjgo zan shiga lectures din ne."

"Okay Allah ya bada sa'a My baby... Ina kaunar ki sosai."

Dan dariya tayi. Ta girgiza kai kawai hadi da yin sauri ta shige faculty dinsu . Ba dadewa kuwa malamin na su ya fara musu darasin da zai dauke su.

       ✓✓✓✓.        ,✓✓✓✓.       ✓✓✓✓. 

  Ranar jumu'ah ita kadai ce ta shirya zuwa makaranta kasancewar su Fareeha malamar tasu ba zata samu halartar darasin da zatayi musu ba.

Yazed ne ya dauki Madeeha suka wuce makarantar ya sauketa a department dinsu ya wuce.

Saura wajen mintina 30 kafin a fara lectures din. Gashi mutane tsirari ne suka isa. Su nour basu ma karasa ba.

Hakan yasa Madeeha ta koma wajen wani benchi ta zauna tana duba handout din da ke hannun ta.

Wata yar ajin su ce ta karasa wajen Madeeha .

"Madeeha *

"Na'am ya kike?"

"Lafiya kalau.. Ana neman ki ."

"Toh fa daga Ina?"

" Awaccen motar,." Ta fada tana mai mata nuni da motar

"Waye aciki mace ko namiji ?"

"Mace ce. Babbar macece."

"Okay zanje ." Ta mike tana karkade bayan ta. Don ta dauka yarinya ce don da tabbas Saj-jeedah zata ce.

Karasawa yayi wajen motar tanata auna mai neman ta da sanyin safiyar nan

Da takalman ta kirar mango designer ta fara cin karon sakamakon zuro kafafun ta da tayi awaje. Sanye cikin doguwar riga samfarin Lebanon

Kana ganinta kasan babar macece wacca ake damawa da ita a rukunin masu kudi ko mulki da sarauta.

"Ina wuni... au kwana?" ta dukusa tana gayshe da ita.

Matar ta murtuke fuska tana jujjuya kai

'daga dubu dari biyar zuwa million biyu zan iya baki su batare da na motsa daga nan ba."

Madeeha ta daga kai ta dube ta. Kafin ta mayar kasa.

"bangane ba Hajiya.,"

"Ni din mahaifiyar Rayyan ce. Na fito miki ta mutum ... Inason ki raba tsakanin ki da dana Rayyan. Ke kanki kinsan ke din ba kya cikin matan da Rayyan zae kula . Yanzu dai inason ki rabu da dana Rayyan. Ki futa harkar sa baki daya. Ki kuma fadi adadin kudin da kikeso zan baki. Kawai so nake ki dena shiga harkar yaro na. Idan kuma kin musanta haka to hukuma zata shiga tsakanin mu.,"

Madeeha ta danyi murmushi kawai. Kafin tace,.

"Allah hajja sede kimun tsakani da shi. Dai dai da kwaryar zarra bantaba shiga shirgin sa ba shi ke bina dik inda nayi. Na kuma ji maganar ki insha Allahu ba zan sake kula shi ba. Duk kuwa da shine ke nace mun... Kullum yayi ta mun magana kamar dole."

"Rike .." Ta wulla mata bandir din yan dubu daya guda daya . Hadi da sake cewa

"Gashi nan ba yawa..Kiyi kudin mota kafin mu sake haduwa..Ina son kiyi shawara da zuciyar ki kudin da kika yanke zaki karba ... Ki kuna yi gaggawar fita daga harkar da na Rayyan daga rana irin ta yau. Karfe...

Ta fada tana mai duba agogon hannun ta.

Madeeha nan da nan hawaye suka shjga Malala a fuskar ta. Ta mike tsaye kawai ta wuce tabar wajen

Hawayen zuci da hawayen fili Madeeha ta shiga yi. Daya na bin daya. Ta tsugunna bakin wani dutse ta kunshe kanta acikin cinyoyin tah.

Bata shjga lectures ba, saboda ko ta shiga ba zata fuskanci komai ba sakamakon ranta da ke a bace.

Hawaye ta shiga yi sosai. Ta mike a sanyaye ta shiga masallacin da ke cikin faculty din su. Nan da nan kanta ya fara ciwo sosai. Jijiyoyin gaban goshin ta suka tashi suka yi rudurudu.

Jikin ta ya dau zafi rau, Haka ta kudundune a durkushe tana mai rera kukanta ahankali.

_____________

Ko da su Rayyan suka fito daga lectures . Kai tsaye ya wuce department din su Madeeha.

Duk ya dudduba lecture halls din babu ita ba alamar ta. Ya fita daga ciki yana dube duben inda zai hango ta

Sam bai ganta ba. Ya dan zagaya bayan department din ya hango taron wasu mata su hudu. Ya hango Nour kawarta .

Karasawa yayi yanata auna yadda zai tambaye su inda take. Don ba shida magana ko kule kule.. Madeeha kadai yake iya yiwa magana. Sai Kuma baby Saj da ya santa tun tuni. Amman idan ka tsame su biyun nan baya KULA wasu daban.

Ya tsaya daga dan gefen su yana jan kasan leben sa ta gefe . Ya musu sallama cikin muryar sa mai dadin sauraro.

"Salamu alaikum."

"Wa'alaykm salam."

"Sannun ku."

"Yauwa sannu" suka amsa shi suna duban sa.

Nawal tayi murmushi hadi da mikewa tsaye tana kallon sa.

"Madeeha ko?"

Ya daga kansa yana mai saka hannu ya soso kasan keyar sa.

"Eh." Ya amsa Nawal din

"Bamu ganta ba gaskia. Saboda bamu dade da fitowa ba muma daga lectures din. Bata zo lectures ba ai yau."

Rayyan ya bude baki cike da mamakin kalaman ta na karshe,

"Bangane ba tazo ba.."

"Eh gaskia bata shigo lectures ba. Kaga ba tazo school ba kenan. "

Bai ce mata komai ba ya bar wajen da sauri yana danno number Na'eemah cousin dinsa a wayar sa.

Ringing biyu ta dauka ya kara a kunnen sa, ita kanta tayi mamakin kiran. Sam domin basu taba waya ba sai dai idan wani uzuri ya biyo ta kanta daya danganci yan uwan su.

Rayyan!: Hello Na'eemah "

Na'eemah: Hey! Ya Ray.. Ina kwana?"

Rayyan: Lafiya kalau ... Nace kun shigo school ne yau?"

Na'eemah: A'a yau dama lecture daya muke da kuma me daukar namu ba zata samu zuwa ba. "

Rayyan: Oh okay...Uhmmm . Twin sis din Madeeha course mate dinki ce ko?"

Na'eemah: Eh.. Fareeha ba"

Rayyan : Ma shaa Allah. Ko zaki tambayeta yau Madeeha ta zo school ? Please. Saboda nide kamar ita nagani amman friends dinta sunce bata zo school ba."

Na'eemah: Alright Lemme ask her."

Katse kiran tayi. Ya dubi screen din yana tsaki da kananun mita

_kaji yarinya kaman ance ki kashe. Mtcew_

Bata dau lokaci sosai ba ta kira shi.

Na'eemah : Hello Ya Rayyan. "

Rayyan; Naam dear sis."

Na'eemah: Na kira tace eh tazo school tun safe... Z"

Ai bai jira ta karasa ba ya kashe wayar . Da sauri yabar wajen yanata dokawa Madeeha kira a waya.

Lokacin Madeeha na masallaci kan nata ya fara sara mata sosai ta daga wayar tana kalon sa yana kira.

Maganganun mahaifiyar sa na dada ratsa ta. Ta girgiza kai kawai ta shiga cikin contacts ta goge number sa.

Tamkar zararre haka Rayyan ya zama. Ya cigaba da kiranta duk kuwa da bata dauka.

Samun waje yayi ya zauna ya shiga cikin text message ya fara zana mata sako ya tura mata

"SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina kaunar ki Madeeha, Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta.... Please ki dauki kira na. I love and miss you soo much♥️"

Ya tura mata sakon . Ya sunkuyar da kansa kasa . Yana tunanin mafita. Su T-Boy suka karasa inda yake suna kiran sunan sa.

Saj-jeedah sai murmushi take. Domin Hajia Bintu mahaifiyar Rayyan din ta sanar mata yadda sukayi da madeehan.

"Mr Ray ba kada lafiya ne?"

"Guy me ke faruwa ne?"

"Aboki na ba lafiya ne?"

Duk suka shiga jifan sa da tambayoyin damuwa. Ko daya bai amsa musu ba. Sai hange hange da ya shiga yi na inda zai hangota

Tamkar almara ya hango ta tafuto daga cikin masallaci. Dauke da littafan ta a hannu tana amsa waya. Alokacin Fareeha ce ta kira tana tambayar ko lafiya Rayyan ya kira Na'eemah ko taje school. Inda madeehan ke ce mata bakomai zai ta karasa gidah zasuyi magana.

Tamkar ya rungume ta ya lallashe ta haka yake ji. Da sauri har yana hadawa da gudu ya karasa wajen ta yana....

..
_INA JAMA'AR TA MU? KU MARMATSO KUSA . GA TAGOMASHIN ARZIKI. SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI. MUN GWADA DOLE MU BADA SHEDA_

_INA AMARE, UWAYEN GIDA, YAMMATA? IYAYE MAZA DA KE SON FARANTA RAYUKAN MATAN SU DA YAYAN SU DA MA KANNEN SU?_

_ALBISHIRIN KU. GA GORO. DOMIN WANNAN DADDADAN LABARI DOLE MU BAKU ALBISHIR DA ALHERIN GORO. GORON MA FARI KAL KAL_

_WAI AKACE KAMSHI RAHAMA NE... KAMSHIN MA MUSANMAN ME SANYAYA ZUCIYA DA RATSA MAGUDANAR JINI DA TSOKA._

_INA MASU NEMAN KAMSHIN TURAREN SAUDI ARABIA? T'CHAD DA MAIDUGURI? IRE IREN KAMSHIN DA BAYA BIN ISKA YANA KAMA WAJE YA RIKE GIDAH..._

_KAMSHIN TURAREN KAYA, TURAREN GIDA, TURAREN JIKI, TURRARN GASHI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN WANKA, TURAREN WANKI, TURAREN MOPPING, TURAREN BANDAKI, TURAREN LABULAYE DA ZANNUWAN GADO, AIR FRESHENER DA TURAREN AKWATUNA DA DRAWER DA MOTA... KAI HAR MA DA TURAREN DA KE CIRE BACIN RAI YA MUSANYA DA FARIN CIKI SABODA TSANANIN SANYAYAWAR SA DA YAYE DUHU DA DAMUWA_

_BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA NAU'IKAN TURARUKA NA KHUMRAH KALA KALA. SUNADA TURAREN RUWA NA FESAWA DANA MAIKO. SUNADA KAYAN GYARAN JIKI.._

_SUNADA KULACCA DA SAURAN BODY BUTTERS MASU YAYE WARI KODA KUWA AN YI KWANAKI BA WANKA BARE WANKI._
Chapter 44 · 0% Book details