Sashe 50
Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ko da ya gama amsa wayar ya cika da mamaki kwarai matuka. Saboda sam bata sanar masa zata fita ba ma. Amman da mutanen suka kwatanta masa inda hatsarin ya wakana.
Ba nisa da area din gidan kanin sa Alhaji Hydar . Don haka a zaton sa can din taje.
Cikin rawar jiki ya nufi motar sa ya shiga. Bisaga jagorancin direban sa daya tukashi suka nufi wajen da hatsarin ya wakana.
Nan da nan ambulance tazo. Aka cirota dakyar aka sanyataa acikin mota me bada agajin hatsari.
Suka nufi asibiti da ita. Likitoci na bata agajin gaggawa....Ta jigaata kwarai matuka don sam bata hayyacin ta ma. Ta suma doguwar suma ta kuma farfado bayan temako da likitoci kala kala suka babbata...
Rayyan na gidah ransa duk ba dadi shima. Labari ya zo musu bisaga kiran wayoyin su da akayi akace Hajia Bintun na asibiti sakamakon hatsarin daya rutsa da ita. A kan babban titin da zai sadaka da unguwoyin da dama na cikin Nassarawa GRA. Wanda ke shataletalen titin unguwar sultan road...
_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_
_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_
_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: 42_
_ZAFAFA BIYAR 2023_
Tuni asibitin ya cika ya tumbatsa da yan uwa. Sai dafifin zuwa ake yi ganin jikin nata.
Dake hatsarin ya jefa zukata da yawa acikin rudu. Har kafafen yaa da labarai na jiha da na kasa baki daya anata nuna hotunan hatsarin a shafukan kafafen . Mutane nata tu'ajjabin hatsarin hadi da nema mata lafiya awajen rabbus samawati.
Ta samu kaaraya a kafafuwan ta da hannuwan ta. Hadi da internal bleeding a cikinta. Sai gefen goshin ta data samu rauni shi ma sosai.
Duk suna zazzaune a babban parlorn da ke cikin dakin Hajia bintu. Tana kan wani gado an nannade ilahirin jikin ta da bandeji fari.
Kafafunta wani karfe ya daga su sama da hannunta daya shima . Ya yinda dayan hannun ke gefe shima ya sha wasu mugayen zare.
Alhaji Hammadu ya daga kansa ya dubi Hajia Bintu da kanta shima an nannade rabin sa. Tausayin ta ya sake shigar sa ta na kwancen yace,
"Tsautsayi ba ya wuce ranar sa... Anty Kulu sai kawai kikaji an kira waya Bintu tayi hatsari."
Anty Kulu mata ga Alhaji Hydar kanin alhaji Hammadu. Kuma uwa ga su Na'eemah tace,
"Wallahi Bappan su. Sai kawai ji nayi wannan tsautsayi ya afku. Nan wajen unguwar mu ba nisa da mu. "
"Wallahi kuwa. Inaga bayan ta baro gidan ku din ba jimawa ya rusketa. Don ni tsautsayi bata gayamun zata zo wajen kun ba ma. Saboda kwanaki na ce mata inde gidan ku zata ko wajen su Harith ba sai ta tambayeni ba. Ashe tsautsayi ke kiran ta."
Duk suka zubawa anty Kulu idanu jin me zatace. Tayi Dan jim kafin ta ce,
"To inaga bata 'ee da zuwa nan din ba hatsarin ya afku."
Alhaji Hammadu yayi shiru. Saboda ya kira me gadin sa tun da wuri kan ya dakko masa a bayan dayan motar sa a booth ya karbi mukullin awajen Hajia Bintu me dakin na sa. Inda mai gadin ke cewa da shi. Ai tun da sassafe ta fice daga gidan.
Jin abunda Kulu tace sai jikin sa yayi sanyi. A sanyaye yace,
"Zai iya yiwuwa. Allah ya kyauta ya rufa asiri."
"Aaamen " suka yi jam'in amsa shi.
Rayyan da ke gefe ya girgiza kai kawai. Shi ba abun ya fito ya fadi dukkanin abubuwan da mahaifiyar tasa tayi ba akan Madeeha..
Wani bangare na zuciyar sa na ingiza shi da ya fadi komai. Ya yinda dayan bangaren ke tuna masa da mahafiyar sa ce itan. Idan kowa baya bayanta ya kama ta shi din ya rufa mata asiri.
Ha sunkuyar da kansa kawai yana sake jimamin abun baki daya. Yanzu gashi nan abunda ya fado kanta bayan gori da fadan bakaken maganganun da tayi a gidan su Madeeha.
"Allah ya baki lafiya... Allah ya tashi kafadun ki, Allahumma Aamin " ya fada a kasan makoshi yana mai goge hawayen da ya dugo daga idanunsa sakamakon juyaear da yayi da kansa ya hangota kwance akan gado cikin mawuyacin hali.
====
====
====
===
===
Suna tafe acikin mota. Madeeha kan ta na wundo. Tunani ne fal acikin kanta.
Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana matsa yatsun ta.
Fareeha ta dubi Madeeha na tsawon mintoci kafin tace da ita,
"Tunanin me kike ne?"
Madeeha ta sake jan iska daga bakinta ta furzar.
"Ba komsi."
"Uhm uhm dai rabin rai. Ina hankalce da ke... Ko dan maganganun da Rayyan ya gaggaya miki ne ki ke nazarin su "
Ta sake sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin ta ce,
"Ba komai rabin rai.."
"Allah kika sake cemun ba komai ba ruwana da ke."
Madeeha ta dan kakaro.murmushi. kafin ta saka hannu ta janyo Fareeha jikin ta,
"Haba other half... Kawai abubuwan ne se a hankali. Tunani na ke ta wadanne hanyoyi zan bi na dena haduwa da Rayyan..."
Fareeha tayi shiru. Hibba da ke tuqin motar ta juya lokacin sun tsaya a traffic jam tace,
"Gayen yana kaunar ki sosai... Sai dai magana ta gaskiya alaka ko ince soyayya da irin su na tafe da hadari. Fareeha ta gayamun dukkanin abubuwan da suka faru..Kiyi hakuri Madeeha. Ki kuma futa a harkar sa kawai."
"Ba zaku gane bane... Na fita wallahi. Sam na cire shi na ajiye a gefe. Su Nour sukaci amana ta. Mun futo da ga central mosque sallah zamu wuce lecture hall suke ce mun wai kafin nazo an canza inda zaai lectures na 1301. Nace ina ne ? sukace ga inda za'ai. Mun mike zamu shiga tare sai Nawal ke cewa Nour tazo ta rakata ta dakko jakarta ta manta ta a masallaci inda mukayi sallah. Wai na tsare mana waje .. Sai na shiga class su kuma su ka koma masallaci. Inata zaune ba su ba dawowar su fa. Sai ga shigar sa cikin ajin. Sai na gano dabara suka hada mun su da shi. Na sauka da sauri zan fita na saka hannu akan kofar ashe ya saka mukulli... Ya shiga cewa....
Ta shiga labarta musu dukkanin abunda Rayyan din ya fada mata. Ta karkare da.
"Wai dan Allah kar na dena KULA shi.. Ni din na zamar masa MALLAKIN ZUCIYAH..."
Fareeha taja tsaki tana yamutsa fuska.
"Yaje can ya karaata da kalaman sa. Babu ke babu shi atoh."
"Ato sai wani zubo zance yake ba. Na yadda yana kaunar ki. Amma tunda mahaifiyar sa bata kaunar ki gaskiya ki fita a harkar sa kawai." Cewar Hibba da ke tuqa motar da suke ciki
"In shaa Allah! Ko dan wulakancin da tayiwa Ummy har gidah ai na dena kula shi. Ballanta na wanda tamun ni ma a makaranta. Ai ruwa ba sa'an kwando bane.. Da wannan shaheeda take ko wa."
"Saj-jeedah ko.?"
"Wata baby Saj yar deputy governor ba"
"Tabbas kuwa... Saj-jeedah baby Saj. Haka ta ci mun mutunci itama... Ni tausayi ma take ban. Son ma so wani"
"Son ma so wani kwandon jidalin wahala."
"Wahalalliyar gaske. Yar iska, Ai in shaa Allah ba zai taba kaunar ta ba ."
Haka dai suka shiga maganganun su har suka karasa gidah...
Fitowar sa kenan daga cikin gidah. Yana daga tsaye a wajen farfajiyar gidan sashen da ake adana motocin gidan.
Number ta ya lalubo ta wayar sa. Dake tunda ya sassaya musu waya karama haka da da zasu dinga waya da sauran su. Ba dai babba bace ta chatting yar baby Nokia ce. Sai laptop daya sassaya musu suna browsing akanta da sauran abubuwan da suka shafi harkar makaranta.
Yauma lamarin me ya kaishi karshe. Ganin yadda mazan faculty dinsu da sauran na wasu departments din ke dafafin zuwa wajenta.
Kada wani yayi masa shigar sauri. Yasa ya yanke samun ta da zancen komai zai faru ya faru.
Ya sauke gingimeriyar ajiyar zuciya yana mai furzar da iska daga bakinsa. Ya kirata hade da dora wayar a kunnen sa. Yayinda yake jan kafar ta cikin takalmin sa ,zuwa baya. Dayan hannun kuma yasa babban yatsan sa a baka yana cizawa.
Yana kiranta bugu biyu ta dauka . Ya sauke zuciya a lokacin da muryar ta ta doki dodon kunnen za. Yaja baya zuwa bango ya jingina hadi da lumshe idanun sa.
A nata bangaren jin ya kira yayi shiru bai ce mata komai ba. Yasa ta dan sake daga sautin muryar ta tana,
"Hello....."
Nan ma shiru bai amsa ba. Sai wani murmushi yake kamar gaula. Ta zare wayar daga kunnenta tana kallon fuskar wayar... Da gaske bai kashe ba kuma baya magana.
Zuciyar ta ta bata amsa da maybe bai san ma ya kira ta ba. Ta saka hannu kenan zata kashe kiran. Muryar sa ta doki kofar kunnenta.
"Fa.., ree... ha" Ya fada a rarrabe yana mai dafe saitin zuciyar sa da hannun sa na hagu..
"Na'am.. Yaya Yazed."
Yaja kasan leben sa ya taune hadi da daga hannun sa ya sauke shi. Ya shiga zarya a inda yake tamkar zai zauce dan dadi.
"Hello Yaya Yazed..." Ta sake ambata tana kara sautin muryar ta ko baya ji.
"Fareeha..." Ya sake kiran sunan ta a karo na biyu.
"Naam Yaya Yazed. Ina wuni?"
"Kina lafiya?"
"Alhamdulillahi..." Ta fada tana kallon Madeeha da ke kusa da ita.
"Kina Ina?"
"Ina daki..."
"Ke da wa?"
"Ni da Madeeha.."
"Rakiya zaki mun.."
"Ni ko Madeeha?" Ta tambaye shi. Saboda sunfi sabawa da Madeeha. Duk a tunanin ta baisan da wa ma yake magana ba.
"Fareeha nace ba Madeeha ba....Ina da number Madeeha ai ko?"
"Uhm.."
"Yauwa good girl..Sa mayafi da takalmi ki mun rakiya..."
"Yanzu...?"
"Yes... Ki tambayi ummy amma ."
"Toh."
"Ina jiran ki awajen mota ta.."
"Toh."
Ta katse kiran tana bin wayar da kallo.
"Wai mensne?" Cewar Madeeha.
"Ni duj dauka ta ma na zata ke yake nema... Wai na saka mayafi da takalmi ma masa rakiya.. Anya yasan da wa yake magana kuwa?"
"Ya sani mana kiji ki ke kuma."
"Allah ni doguwar hira bata hadani da shi. Ke yake nema gaskia."
Madeeha tayi dariya. Hadi da gyara kishingidar da tayi zuwa kwanciya.
"Ba dai dadi kinbar dan mutane jira. Ki tashi kije."
Fareeha ta mike dakyar. Hijabin sallar ta ta zura hadi da dakko takalmanta ta saka ta rike wayar ta a hannun ta.