← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 66

Sashe 37

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

_IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE AKWAI RAGIN KUDI DA HADI NA MUSANMAN DA ZAA YIWA DUKKANIN KAYAN DA KUKA SAYA._

_KYAU!! INGANCI! RAHUSA!! KAMA JIKI DA GIDAH!! AIKI!! ADADE ANA MOREWA SAI KAYAYYAKIN TURARUKAN KAMFANIN:*YERWA INCENSE AND MORE*_

_____
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼: 31_

______________

  *Ranar* asabar itace ranar da ta kasance semester break party. Wanda jami'ar Birmingham ta shiryawa daliban da ke cikin ta...

Tun safe su Hibba da Fareeha ke shirye shiryen kayan da zasu saka hadi da takalma da yar jakar da zasu rirrike.

Madeeha na kwance akan yar katifar ta. Dake al'ada take yi don haka ta cigaba da kwanciyar ta tun bayan data karasa dukkanin abubuwan aikace aikacen ta.

Fareeha ta shiga dakin na su tana bubbuga kafafunta.

"Wash Allah! Nagaji wallahi . Kinji yadda gabobin jikina ke sarawa?"

Madeeha ta daga kai ta dube ta. Kafin ta mayar da kanta kan yar rediyon ummy dake gefen ta tana saurara. Can tace,

"Sannu."

"Yauwa.. wai ba zaki tashi ki fara shiri bane?"

"Shirin me fa?" Ta fada tana rage sautin rediyon da ke hannun ta.

"End of the semester party..... "

"Chab"

"Meye abun chab? Yanzu fa sai kice ba zaki ba ko?"

"Me zanje nayi acan Fareeha?"

"Amman kinsan dai idan ba kije ba ba zanji dadi ba ko?"

"Kiji ki ke kuma... Mu da ba department daya muke ba. Bayan haka ma ai ga Hibba itama she's family. "

"Duk da haka dai Madeeha kinsan ba zanji dadi ba idan ba ke awajen."

Madeeha ta kyalkyale da dariya kawai tana mai girgiza kanta. Fareeha ta qulu da dariyar Madeeha. Ta kada kai kawai taja qwafa.

"Ai shikenan."

"Sorry tawaje na."

"Nabi sorry da gudu na kwarfe."

"Kash dan Allah ki kwarfo kwarfewar da kikayi masa ya rabin rai tah..."

Suka tuntsire da dariya. Nan dai Fareeha tayi ta yiwa Madeeha magiya da naci. Har dai ta samu ta shawo kanta ta amince zata je ...

"Ki dauki daya daga cikin kayan da Hibba ta bamu ki sa ka kinji?"

"Wallahi ba zan saka ba. Nawa zan saka, ko wancen dayan dana saka aciki Allah ji na nake wata daban... Nawa zan saka idan yaso idan naje su kore ni. "

"Madeeha harkar manya ce. Sai ka daure kayi shiga irin ta su. "

"Allah zan fasa zuwa."

"Yi hakuri tawan. Saka nakin"

"Yauwa."

Hibba ce ta kira waya ta intercom. Tana neman Fareeha. Fareehan ta mike da sauri cikin rawar jiki ta nufi sashen su.

Sun bata lokaci wajen shiryawa. Dan har ummy ta nufi sashen su Hibba basu tafi ba. Dake ummyn da mahaifiyar su hibban wata Malama na zuwa ta musu karin Qur'ani da sauran littattafai da suka shafi addinin islama.

Wata kawar su Hibban ce ta biyo musu don tafiya wajen partyn. Alokacin mahaifiyar su Madeeha ummy ta futo daga cikin gidan . Haj Ruwaida ta rakato har kofar fita. Don sam Hajiya Ruwaida bata da jin kai ko dagawa da nuna na ita din matar mai kudi ce.

Na'eemah ta tsugunna har kasa ta gayshe da su.

"Lafiya kalau ... Hibba ? Tana ciki."

"Eh ita. Nagode " Na'eemah ta amsa Haj Ruwaida. Hadi da juyawa ta kalli ummy bayan ta kalleta a karo na uku.

Ummy ta yi dan murmushi bayan sun gaysa. Naeemah ma ta mayar mata murmushin kafin ta saka kai ta shiga cikin gidan. Tana mai sake waiwayen Ummyn.

"Kin gane ta kuwa?"

"Ban waye ta ba"

"Anan gidan dake jikin gidan nan suke."

"Allah sarki."

"Ina lokacin da kika rarrakani makota muka gaggaysa. Kinsan ranar wata laraba ana'i gobe zaku tafi kauye da su Madeeha . Da nace ki rakani ma sai na ce ki barshi tunda aiki ki ke..?"

"Eh tabbas anyi haka. Ranar ke kadai kika shisshiga makotan ban miki rakiya ba muna ta shirye shryen tafiya kauyen rafin kanya. "

"To a ranar na shiga gidan. Sai kuma wani abun mamaki yarinyar gidan ajin su daya da su Hibba. Sunan ta Na'eemah."

"Allah sarki .. "

"Samu da kokari hadiza . Ni bari na koma ciki."

"Sannun ki dai Hajiya. Allah ya saka muku da alkhairin sa ya kara arziki"

"Aamin hadiza. Tare da ke."

Sukayi sallama . Ummy ta koma boys squatter inda suke. Madeeha ce zaune a parlorn ta saka wani material ja ta ci ado cikin mayafi baki. Tana shafa basilin a leben ta. Bayan ta zizara kwalli a idunun ta.

"Shiryawar ake?"

"Eh ummy. Sannu da dawowa"

"Yauwa Madeeha.. "

"Ya karatun ummy?"

"Alhamdulillahi Madeeha. Mungode wa Allah."

"Wai su Fareeha nake jira ni na gama shiryawa."

"Ba zaki sauya wasu kayan ba.?"

"Wannan ma sun isheni ummy "

"To shikenan Allah ya temaka ya baku sa'a. Allah yasa ayi taro lafiya agama lafiya."

"Aamin Ummy "

"Yauwa ku dai tsare mutuncin ku."

"In shaa Allahu ummy."

"To ma shaa Allahu."

Suna dai zaune suna yar hirarrakin su. Madeeha na zaman jiran su Fareeha.

Ba jimawa kadan sai ga shigar Fareehan taci ado cikin daya daga cikin kayan da Hibba ta bata. Na doguwar riga yar kanti fara mai dogon hannu. Ta yane kanta da mayafi kalar toka. Takalmanta ma kalar tokar ne.

"Ummy da rabin rai nayi kyau?"

"Ma shaa Allah sosai ma duk kunyi kyau. "

"Godia na ke ummy."

"Kin kyau sosai Fareeha na.. Kyau iya kyau..."

"Godiya na ke madeeha na... Kema kin tsatso kyau sosai "

Suka kyalkyale da dariya. Ummy dake binsu da kallo tanata murmushi. Kafin tace,

"Allah ya kai ku lafiya. Ya dawo daku lafiya. Ku tsare mutuncin ku."

Suka amsa ta, Kafin daga bisani suka tashi suka tafi.

Hibba ce mai driving motar ta su. Fareeha na baya itada Madeeha. Yayinda kujera ta kusa da direba kuma Na'eemah ce a zaune.

A haka suka karasa makarantar ta su ta Birmingham university Nigeria. Dalibai nata dafifin shiga cikin makarantar. Ta cika makil ba masaka tsinke. Anyi decorating auditorium din cikin customized color da ke jikin badge/logo na makarantar .

Hibba ta faka motar ta su awajen ma'adanar motocin dalibai. Kafin daga bisani suka shiga wajen taron. Sunyi matukar kyau su duka hudun. Kowanne acikin su yana ta haskawa gwanin ban sha'awa..

Wani waje suka nufa dake jere da wani teburi da aka kawataa shi cikin kwalliya ta alfarma.

Bayan sun zazzauna ne dalibai da suka sansu suka jajje wajen suna gaysawa. Madeeha sai raba idanu take. Domin yawancin wadanda suka je wajen su yan department din su Fareeha ne.

Don haka ta kasa sakewa. Cikin haka sai ga zuwan su Nour . Dadi ya sake mamaye zuciyar ta da gewaye.

Sunata yan hirarrakin su . Har dai aka fara gudanar da liyafar party din. Bayan an bude taro da addu'oi. Aka shiga hadahadar liyafar. Wajen zayyano gundarin liyafar ya zuwa refreshments da aka faffara kai wa daliban..

____
Yana zaune akan kujerar dakin Sa. Ya yi kyau sanye cikin kananun kaya da suka amshi zatin kirar sa da kuma kyawun sa

Wayar sada ke hannun sa ce ta fara kukan agajin a dauke ta. Tamkar ba zai bude wayar ba.sai kuma ya daure ya bude yana duba missed calls din wayar ta sa.

Mami ta kira shi. Baby Saj ta kira shi. Hakama Hajiya Bintu ta kira shi. Don haka ya fara kiran Mami tambaya ta masa akan ko yana tare da bappan? su yace a'ah...

Daga nan kuma ya kira hajiya Bintu da tayi masa missed calls uku. Nan ma magana ce data shafi yammatan da take hada shi da shi ko zai auri daya daga cikin yaran iyalan kawayen ta.

Daga karshe kuma ya kira baby saj-jeedah data ke sake sheda masa hadi da masa tilashe akan zuwan sa liyafar party da makarantar ta dauki nauyi.

Bayan ya karashe amsa wayar ya saka silent ya ajiye ta agafe. Ya debi wajen mintina goma kafin ya karasa shawara da zuciyar sa ya mike ya nufi makarantar..ransa da zuciyar sa na adduar Allah yasa ya hadu da muradin ran sa wato Madeeha.

_INA JAMA'AR TA MU? KU MARMATSO KUSA . GA TAGOMASHIN ARZIKI. SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI. MUN GWADA DOLE MU BADA SHEDA_

_INA AMARE, UWAYEN GIDA, YAMMATA? IYAYE MAZA DA KE SON FARANTA RAYUKAN MATAN SU DA YAYAN SU DA MA KANNEN SU?_

_ALBISHIRIN KU. GA GORO. DOMIN WANNAN DADDADAN LABARI DOLE MU BAKU ALBISHIR DA ALHERIN GORO. GORON MA FARI KAL KAL_

_WAI AKACE KAMSHI RAHAMA NE... KAMSHIN MA MUSANMAN ME SANYAYA ZUCIYA DA RATSA MAGUDANAR JINI DA TSOKA._

_INA MASU NEMAN KAMSHIN TURAREN SAUDI ARABIA? T'CHAD DA MAIDUGURI? IRE IREN KAMSHIN DA BAYA BIN ISKA YANA KAMA WAJE YA RIKE GIDAH..._

_KAMSHIN TURAREN KAYA, TURAREN GIDA, TURAREN JIKI, TURRARN GASHI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN WANKA, TURAREN WANKI, TURAREN MOPPING, TURAREN BANDAKI, TURAREN LABULAYE DA ZANNUWAN GADO, AIR FRESHENER DA TURAREN AKWATUNA DA DRAWER DA MOTA... KAI HAR MA DA TURAREN DA KE CIRE BACIN RAI YA MUSANYA DA FARIN CIKI SABODA TSANANIN SANYAYAWAR SA DA YAYE DUHU DA DAMUWA_

_BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA NAU'IKAN TURARUKA NA KHUMRAH KALA KALA. SUNADA TURAREN RUWA NA FESAWA DANA MAIKO. SUNADA KAYAN GYARAN JIKI.._

_SUNADA KULACCA DA SAURAN BODY BUTTERS MASU YAYE WARI KODA KUWA AN YI KWANAKI BA WANKA BARE WANKI._

_SUNADA KABBASA TA TURARA KAYA DA KASAKEN TURARUKAN WUTA NA KARFE DANA KASA DAMA NA ZAMANI YAN WAJE._

*_YERWA INCENSE AND MORE_*

_YERWA INCENSE AND MORE_

_YERWA INCENSE AND MORE_

_MASARAUTAR KAMSHI KENAN. KAYAN SU NA AKAN FARASHIN SARI DA SAYA DAYA DAYA.. SUNA YIWA AMARE HADI DA UWAYEN GIDAH DAMA YAMMATA. SUNAYIN NA TARON SHAGULGULAN BIKI DUK AKAN FARASHI MAI RAHUSA_

_BA'ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNA DA TARIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA RAHUSA HADI DA INGANCIN DA ALKALUMA SUNYI KADAN WAJEN BAYYANA MUKU._
Chapter 37 · 0% Book details