← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 66

Sashe 5

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

_ASSALAMU ALAIKUM JAMA’AR KWARAI.. JAMA’AR AMANA… JAMA’AR ZAFAFA… MASOYA KUMA MABIYA MASU ALHERIN SAYAN ZAFAFA A KODA YAUSHE BA GAJIYAWA…GODIA MAI TARIN DIMBIN ALBARKA DA FATAN ALKHAIRI AGARE KU.._

_KUNSAN DUK INDA ABUBUWAN ARZUKA SUKE MUNA SHIGA MU KURDA MU NEMO MUKU SU DOMIN JIN DADIN KU..🥰💕SABODA KU DIN NA GABAN GOSHINAN MU NE._

_TAMKAR KO DA YAUSHE.. YAU MA MUNZO MUKU DA WATA TSARABAR.. TSARABAR DUNIYAR KAYAN KITCHEN, DECORATIONS DA SAURAN SU… KU MARMATSO KU JI…_

*_MAAB LUXURY HOME_*
*_MAAB LUXURY HOME_*
*_MAAB LUXURY HOME_*

_KUN GANI KO? TO INA AMAREN? INA UWAYEN GIDAH INA YAMMATAN DA KE SHIRYE SHIRYEN SHIGA DAGA CIKI? INDA ZAKU JE KU KANKARO MUTUNCI KU DANDALO ARZIKI NA KECE RAINI.. INDA ZAKU WUCE RENI DA GANIN KASKANCI..INA MAZAN DA KE BURIN FARANTAWA MATAN SU DA ‘YAYAN SU DA KANNEN SU? _

_MAAB LUXURY HOME: RIGIJI GABJIN KENAN! WOHOHO WANI KAYA SAI AMALE KAN DAUKA.. MAAB LUXURY HOME : ALJANNAR KAYAN KITCHEN KENAN, INDE AKACE KAT TOH KARSHEN MAGANA TA KARE KENAN.. MAAB LUXURY HOME ; A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY KITCHEN UTENSILS, HOME DECORATIONS AND MUCH MORE_

_ADIRESHIN MU: MUNA KAN TITIN AHMADU BELLO WAY, KANO STATE. ZAKUGA TAMBARIN DA MAAB LUXURY HOME.._

_DAN SAUKAKA MAKU FITA ZUWA SHAGON MU. ZAKU IYA ORDER AKAWO MUKU DUKKANIN INDA KUKE A FADIN NIJERIYA DA KETARE. _

_INSTAGRAM: @maabluxuryhome._

_FACEBOOK: @maabluxuryhome._

_KO KU NEME MU TA LAMBAR TARHON MU: 08034631010_

_KYAU! INGANCI! RAHUSA! ADADE ANA AMFANI DA SHI SAI KAYAN: MAAB LUXURY HOME_

_100% TESTED AND TRUSTED😍☑️_
______

Ya tsugunna agaban Yayan na su . Cikin ladabi yace,

"Ina wunin ku...?"

"Lafiya kalau Junaid ."

"Lapia..."

"Kalau muke maza."

"Kanin mu rabajau kalau mu ke ..."

Suka shiga amsar gaisuwar tasu da yayi... Aqeel ya gyara zaman kishingidawar da yayi yace,

"Akwai hamsin awajen ka?"

Junaid yayi 'dan dum... Yana mamakin irin bushewar zuciya da rashin tashi a nemi na kai na Yayan su Aqeel. Yanzu hamsin dinnan ita kadai ce a aljihun sa kuma akwai abunda ya ke so yayi da ita. Don haka yace,

"Sai dai ashirin Yaya... "

"Ban ashirin din kawai."

Littafin sa ya dakko ya bude tsakiyar shafi. Nera ashirin ya dakko yan nera biyar biyu da nera goma guda daya.

"Ga shi..."

"Yauwa... Idan ka samu ciko ka kawo mun." Aqeel ya fada hadi da cusa ashirin din a aljihun gaban rigar sa.

Junaid yayi murmushi kawai. Halin Yayan nasu sai shi. Wai idan ya samu ciko ya cika masa tamkar ajiya ya bashi. Ko kuma wani aiki yakeyi da ake biyan sa. Mikewa tsaye yayi ya karkade jikin sa.

"Kar fa ka manta idan ka samu cikato ka kawo mun."

"To..."

"Idan pi network ya fashe. Wabillahi jeep takwas zan saya ma ka Junaid. Sannan duk wata sai na kai ka Dubai. Bayan wata biyu kuma Saudi Arabia zaka je. Daga nan kayi branching a Egypt..."

Dan murmushi kawai yayi wa Yayan na su..

"To..."

"Karfa ka man ta da cikwan"

"Okay" Kawai yace. Ya wuce hanyar gidah abun sa.

××LAYIN MARIGAYI SHEIKH SUFYAN ZUBAIR××

Gidah ne babban gidah ginin daaa. Da wasu rassa na ciki da aka buge aka gyara bisa zamani. Dai dai gyaran talaka mai godewa bisaga ni'imomin da Allah yayi masa da buwayar sa da rahamar sa..

Junaid ya sauke nannauyar ajiyar zuciya alokacin da ya shigo layin gidan na su. Ya dubi signboard din da gwamnati ta tallafawa unguwanni da su.

Kowane layi an saka sunan wanda yafu dadewa a layin. Ko da bako zai zo zai gane inda akai mai kwatance da sunan jikin signboard din da ke layin da ake son zuwa.

Ya tsaya agaban Mari me soya awara. Tana jingine da signboard din layin na su. Mai sunan mahaifi agare su. Marigayi sheikh sufyan zubair.

"Ina wuni?" Mari ta gayshe shi tana dashare hakora.

Fuskar nan tata tayi jagalaf da hoda mai ruwa (foundation) Ta caba jagira hadi da goga jambaki ja.

"Lafiya kalau Mari ta mu...Aban awara." Ya fada hadi da mika mata nera talatin.

"Ka basshi., " Ta ki karba hadi da janyo farar leda ta cikata taf da awara. Ta debo yankakkun tumatir da albasa dake gefe ta zuba aciki.

"Ga shi...."

Kin amsa yayi. Wato da gaske su Fareeha su ke? Yarinyar nan kaunar sa take? Duk sanda suka gaya masa yadda take basu awara kyauta ko ta kara musu da yawa idan sunzo siya .. Sai suce saboda shi ne. Wai tana tambayar su ya yake tana mai tula musu awarar. Ya cika da madaukakin mamaki.

Abun ya so bashi dariya. Ya langabar da kai hadi da dan rage tsayin da yayi ta hanyar dukawa yace,

"Aa bazan karba ba... Ki bani ta iya kudi na dai..."

"Nayi niyyah.." Ta fada tana sake murmushi.

Girgiza kai ya yi. Banda shirme irin na yarinta. Dan jarin awaran ma nawa yake.?

"A'ah Mariya.... Banason musu kinji?"

Ta danyi rau_rau da idanu.. Ya kada kai alamun tabbatarwa. Ba yadda ta iya. Ta cire wadda ta kara din ta mika masa. Idanuwan ta suka cicciko tamkar zata yi ku ka. Ya girgiza mata kai kafin yace,

"A'ah... Kar muyi haka da ke.. Nagode sosai Mariya. Kinji ko?"

Batace komai ba. Sai daga kai da tayi. Bai tashi ba ya sake lankwashe murya zuwa ta rarrashi yace,

"Ki ce kin amince kinji?" Ya fada. Hadi da zuba mata manyan idanun sa akan ta.

"Na amince..."

"Yauwa yar kanwa tah. Allah ya miki albarka. Ya sawa kasuwancin ki tarin alheri da albarka ma kinji?"

"Eh..."

"Yauwa to godiya na ke...." Ya mike tsaye ya shige gidah bakinsa dauke da sallama.

Sashe biyu ne da ka shiga ta kofar da zata saadaka da cikin gidan. Sashe daya na kallon daya. Kowanne dauke da dakuna biyu da dakin girki da bandaki a wadace dai dai karfin talakawa. Dayan sashen mallakin kanin mahaifin su ne. Kawu Ashiru zubair.

Kan sa tsaye ya wuce bangaren su. Ko'ina tas tas an share an killace komai a muhallin sa. Dakin da yake a matsayin na mahaifiyar sa da yan uwan sa mata ya shiga..

"Ummy....." Ya kira sunan mahaifiyar ta su.

Sallah take yi, Ta dago daga sujjada.

"Okay sallah kike ummy.? Ga awara ba yawa." Ya ajiyeta daga gefe

Fita yayi daga dakin ya wuce na sa. Yana shiga bakinsa dauke da sallama ya ajiye littafan sa akan yar katifar sa. Ya bude bokitin ruwan sa ya saka kofi ya ebo ruwa yayi basmala ya shiga sha. Sai bayan ya kammala yayi hamdala ya mike tsaye.

"Fareeha... Fareeha... Madeeha... Madeeha." Ya shiga kiran sunan yan uwan nasa mata. Ganin tunda ya shigo gidan bai ji motsin su ba.

Fita yayi daga cikin dakin ya nufi wajen bandaki yana kwankwasawa,

"Da mutum?"
Ya maimaita har sau uku. Rashin amsawar hakan ya bashi tabbatar lalle ba kowa aciki.

Ya juya ya kallo bangaren kanin mahaifin su. Cikin kuryar kofar dakin ya hango Rahila matar kawun su a zaune akan buhu tana yanke faratan kafar ta.

Kai tsaye ya wuce bangaren yana kasa kunne.

"Mama su Fareeha na nan?"

Yamutsa fuska tayi. Ta kauda kan ta gefe. Hakan ya tabbatar masa da suna ciki ..

"Ba zaku gayamun gaskiya ba? Wacce shegiyar ce acikin ku ta gurgunta mun zakara?" Kunnuwan Junaid suka jiyo masa karar sautin muryar kawun su Ashiru.

Yaja siririn tsaki ... Shi ko gajiya bayayi da dukan su Fareeha..? Duk sanda ya kwaso bolar bacin ran sa. Babu inda yake saukewa sai akan 'ya'yan Yayan sa marigayi Sufyan.

Har zai tura kofar dakin ya shiga sai kuma ya fasa. Gudun bacin ran ummy mahaifiyar su. Don ta tsawatar masa akan kada ya sake shiga yace zai yi rabiyar tsakanin kawun nasu da kannen sa mata. Uba ne agare su don haka su bashi girman sa.

Ja yayi ya jingina da bangon dakin. Zuciyar sa na masa zafi da zugi. Ganin yadda kawun na su yake sake kurmama tsawa ga kannen sa.

Ya runtse idanu . Zuciyar sa na tafarfasa.. Jiyo yadda ya daga koma menene ya laftawa daya daga cikin su. Muryar Fareeha yajiyo tana,

"Ka dakeni ni daya kawu... Ba abunda Madeeha ta yi."

"A'ah Kawu... Ni ce nan na kore shi amman ba ruwan Fareeha aciki .."

Takaici ya dankare a wuyan kawu Ashiru. Ya saka tafun kafar sa ya shure Madeeha a gwiwa. Ya sake kai wa gular Fareeha duka. Cikin takaici da bacin rai yace,

"Ku tashi ku fita dan uban ku . Matsiyata. Koma wacece tayi acikin ku. Da girman Allah sai masifa ta hau kan ta. Yan gaba da iska. Ku ta shi..." Zai sa ke kai musu gula suka tashi da sauri suka fita...

Suna fitowa Madeeha ta juya ta hararo kofar dakin hade jan karamin tsaki da Allah ya isa a kasan makoshi..

"To malam ga ta tana wulkita maka idanu da qunquni"Rahila ta fada tana nuni gare su

"Wacece acikin su?" Cewar malam Ashiru

Nan da nan Fareeha ta nuna kanta.

"Ni ce nan."

"Dallah matsa. Kawu ni ce nayi. "

Takaici ya sa kawu Ashiru dago silifas zai duke su suka gudu da sauri. Banda Junaid da ummy mahaifiyar su da kuma su Asmau yaran kawu Ashirun dawasu kawayen na su babu wanda ke gane su .

Kasancewar su din identical twins ne (yan biyu masu kama daya) Babu abunda ya raba kamannnin da suke da junan su sai wata tawadar Allah da ke gefen wuyan Madeeha... Kuma Fareeha batada magana sosai tanada hakuri kuma. Madeeha na da tsiwa, Amman tanada saurin sabo da mutane. ... Banda wannan basuda wani bambamci. Shiyasa idan suka hada kai wajen yin abu. Zai yi wuya agane dayan su.....

"Zo nan Fareeha... Ai har da ke madeeha .. ku zo.." Junaid ya kira sunayen su . Yana gaba suna biye da shi a baya...

_ANAN MUKA KAWO KARSHEN FREE PAGES_🙏
---

_Tirqashi.., Mai karatu na san na jefa zukata a kwadayin son karance yadda labarin zai kaya., Tafiyar ta dabance wadda ta dauki rassa daban daban na rayuwar dan Adam ayau da kullum .. Domin tun ran gini tun ran zane. Ha kama kowacce iriyar KULA na ta'ammalli da kaunar da ke cunkushe a rayuka. Haka zalika ita kan tumbatsa ta zama MALLAKIN ZUCIYAH..._
Chapter 5 · 0% Book details