← Book details Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 66

Sashe 17

Ki Kula Ni Part Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tahir ma dan gidan Abu Himma shima har da shi a makaranta da zaku fara. Da dan wajen Dawud. Bashir Dawud . Sai Sa-jeedah yar deputy governor Ismail Auwalu Wadau. Daman ai tare kukayi sakandire ko. ?"

"Eh Bappah... Abokai na ne...T-Boy, B-junior. Sai itama saa-jeedah muna gaisawa da ita ."

"To Allah ya sa ku fara a saa."

"Amin Bappah."

Ya sake musu sallama ya fita. Kai tsaye ya shige cikin motar sa. Bai dauki hanyar ko'ina ba sai joint dinsu da suke zama shi da abokanan sa.

Ya na karasawa ya samu waje yayi parking. Ya wuce inda sike buga snooker. Suna tsaitsaye sunayi.

"Mr Ray... "

Mika musu hannu yayi suka gaggaysa. Ya samu waje ya zauna.

"Maza meya faru ne? Naga kamar ranka a dagule." T-Boy ya fada hadi da bude robar ruwa ya na sha.

"Ba wani abu fa. Zancen karatu ne again Bappah yayi."

"Ka tunamin ma. Wannan Birmingham university din ko?"

"Ita fa."

"Haka popsy yake ta jaddadamun.. Nima kan lalle na fara shirye shryen komawa makaranta. "

B-junior ya dawo wajen su ya samu kujera ya zauna. Hadi da zaro wayar sa yana dannawa.

"Guy an maka zancen makaranta a gidah ko?"

B-junior yaja dogon tsaki yana yamutsa fuska. Kafin yace

"Ka bari kawai. An mun mana. Ni idan na tuno da ku ne zamu koma sai na dan ji sanyi. Saajeedah ma ta cemun itama haka. "

"Yeah nima ta kirani." T-Boy ya fada yana bin Rayyan da kallo.

Rayyan din ya daga kansa sama yaja jan kasan leben sa. Ya dan jima kansa a sama kafin ya ja dogon tsaki kawai.

Kai kana kallon su duka kasan ransu a dagule yake da zancen makantar da zasu koma.

Don haka wunin ranar ba suyi sami hira ba sosai suka watse.

Ko da Rayyan ya koma gidah. Mami ta saka shi agaba tayita ja masa kunne kan ya mayar da hankali yayi karatun nan .kar ya saka shiririta a kansa .

Ya bita da tom kawai. Ya koma dakin sa ya kwanta. Hakan ranar ta shige masa sukuku. Har kwanaki suka ja. Shi da su T-Boy suka kammala dik wasu shirye shryen da cike ciken na karatu.

Sati na zagayowa suka fara orientation activities Wanda su dukkanin su hudun ba zuwa suke ba. Karatun ma adha ruwan tsuntsaye zasuyi masa

×SULTAN ROAD×

Madeeha ce a farfajiyar boys squatter din su tana karasa tattare dattin sharar data share.

Sallama ta jiyo ana bankawa. Mutane hudu ta hango. Dattijo daya da wata babbar mata. Sai wasu yara biyu.

Da take da tabbacin Yaya da kanwa ne saboda tsananin kamar da su ke.

Fuuu matar ta shige da sauri har tana tuntube. Yayinda dattijon ke biye da ita yana doka mata kira.

"Safiya.. safiya. "

"Umma ga dankwalin ki.." Budurwar da ke bayan su dauke da dankwali a hannun ta tashiga fada tana nanatawa.

Ya yinda dayan saurayin da ke bayan su. Na tafe yana danna waya. Tsabar hankalin sa baya jikin sa.

Yana tafe hannun bibiyu yana danna wayar kansa a kàsa. Ya buge da wani gini da ke gidan flower.

Madeeha ta saki baki tana duban su duka da mamaki. Da alama sune mutanen da yazed ke cewa sun tafi ganin gidah a kauye.

Haka dai ta karasa hada sharar ta zubar. Ta wanke hannuwan ta. Kafin daga bisani ta shige sashen su...

..
_INA JAMA'AR TA MU? KU MARMATSO KUSA . GA TAGOMASHIN ARZIKI. SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI. MUN GWADA DOLE MU BADA SHEDA_

_INA AMARE, UWAYEN GIDA, YAMMATA? IYAYE MAZA DA KE SON FARANTA RAYUKAN MATAN SU DA YAYAN SU DA MA KANNEN SU?_

_ALBISHIRIN KU. GA GORO. DOMIN WANNAN DADDADAN LABARI DOLE MU BAKU ALBISHIR DA ALHERIN GORO. GORON MA FARI KAL KAL_

_WAI AKACE KAMSHI RAHAMA NE... KAMSHIN MA MUSANMAN ME SANYAYA ZUCIYA DA RATSA MAGUDANAR JINI DA TSOKA._

_INA MASU NEMAN KAMSHIN TURAREN SAUDI ARABIA? T'CHAD DA MAIDUGURI? IRE IREN KAMSHIN DA BAYA BIN ISKA YANA KAMA WAJE YA RIKE GIDAH..._

_KAMSHIN TURAREN KAYA, TURAREN GIDA, TURAREN JIKI, TURRARN GASHI, TURAREN TSUGUNNO, TURAREN WANKA, TURAREN WANKI, TURAREN MOPPING, TURAREN BANDAKI, TURAREN LABULAYE DA ZANNUWAN GADO, AIR FRESHENER DA TURAREN AKWATUNA DA DRAWER DA MOTA... KAI HAR MA DA TURAREN DA KE CIRE BACIN RAI YA MUSANYA DA FARIN CIKI SABODA TSANANIN SANYAYAWAR SA DA YAYE DUHU DA DAMUWA_

_BA ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNADA NAU'IKAN TURARUKA NA KHUMRAH KALA KALA. SUNADA TURAREN RUWA NA FESAWA DANA MAIKO. SUNADA KAYAN GYARAN JIKI.._

_SUNADA KULACCA DA SAURAN BODY BUTTERS MASU YAYE WARI KODA KUWA AN YI KWANAKI BA WANKA BARE WANKI._

_SUNADA KABBASA TA TURARA KAYA DA KASAKEN TURARUKAN WUTA NA KARFE DANA KASA DAMA NA ZAMANI YAN WAJE._

*_YERWA INCENSE AND MORE_*

_YERWA INCENSE AND MORE_

_YERWA INCENSE AND MORE_

_MASARAUTAR KAMSHI KENAN. KAYAN SU NA AKAN FARASHIN SARI DA SAYA DAYA DAYA.. SUNA YIWA AMARE HADI DA UWAYEN GIDAH DAMA YAMMATA. SUNAYIN NA TARON SHAGULGULAN BIKI DUK AKAN FARASHI MAI RAHUSA_

_BA'ANAN KADAI SUKA TSAYA BA. SUNA DA TARIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA RAHUSA HADI DA INGANCIN DA ALKALUMA SUNYI KADAN WAJEN BAYYANA MUKU._

_SUNA TURA KAYAYYAKIN SU FADIN NAJERIYA DA KETARE BAKI DAYA._

_ADIRESHIN SU. SUNA GARIN KANO DAURA DA TITIN DA ZAI SADAKA DA GARIN MAIDUGURI_

_SUNA KAN MANHAJOJIN SU DAKE KAFAFE DA DAMA KAMAR:_

_INSTAGRAM: @yerwaincense_and_more_

_FACEBOOK:yerwacollection_

_WHATSAPP: 08095215215/09044191709_

_A YANZU HAKA KAMFANIN TURAREN YERWA INCENSE AND MORE SUNA SALES DIN KAYAN SU NA 250ML NA TURAREN WUTA DA KUMA 240 DA 190ML NA KHUMRAHS_

_IDAN ANJE ACE DAGA ZAFAFA NE AKWAI RAGIN KUDI DA HADI NA MUSANMAN DA ZAA YIWA DUKKANIN KAYAN DA KUKA SAYA._

_KYAU!! INGANCI! RAHUSA!! KAMA JIKI DA GIDAH!! AIKI!! ADADE ANA MOREWA SAI KAYAYYAKIN TURARUKAN KAMFANIN:*YERWA INCENSE AND MORE*_

_____
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200

*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*🔥🔥🔥🔥🔥

0022419171
Maryam sani
Access bank

*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*

09166221261

🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*

+22799643131

Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA

*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*

*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*

*Thanks for choosing us*🔥

_𝕂𝕀 𝕂𝕌𝕃𝔸 ℕ𝕀!!_
_(𝕄𝔸𝕃𝕃𝔸𝕂𝕀ℕ ℤ𝕌ℂ𝕀𝕐𝔸)💕_

_ℕ𝔸ℕ𝔸 ℍ𝔸𝔽𝕊𝔸𝕋_
_𝕄𝕀𝕊𝕊 𝕏𝕆𝕏𝕆_

_ℙ𝔸𝕀𝔻 ℙ𝔸𝔾𝔼:15_

---
*Kai* tsaye ta shige parlorn su bakin ta dauke da sallama . Turaren wuta dan tsinke na tashin kamshi mai dadi da saka nutsuwa.

Zubewa tayi a kan kujera tana mayar da numfashi.

"Ya akai Madeeha? Ba dai hakin ne ya dawo ba ko?"

"Da sauki ummy. Wannan ulcer bansan ya take so tayi da ni ba."

"Allah ya kara sauki rabin rai ta." Fareeha fada mata. Tana tsaye tana mayar da labulen da ta wanke ya bushe akan karfen sa.

"Allah ya baki lafiya Madeeha. Da sauran dukkanin musulmai baki daya na gidah dana asibiti. Amin."

"Amin Ummy."

"Aamin ummyn mu." Madeeha ta fada hadi da mikewa tayi hanyar dakin su.

Har ta kutsa kai zata shiga kuma sai ta juya ta dawo.

"Au na manta. Ummy inaga fa mutanen da Yaya Yazed ke fada na can bangaren sun dawo fa. Ba dadewa suka shiga su kayi bangaren su."

"Kai amma Madeeha da soko ki ke. Ai yanzu hakan ta faru shine baki fada ba? "

"Na manta ne ummy. Yanzu ne fa."

"Yanzun din. Ke Fareeha miko mun hijabi na a daki."

"Tohm ummy."

Fareeha ta dakko mata hijabin .Ummy ta zura shi ta fita zuwa bangaren na su.

"Kuma har su nawa ne?" Fareeha ta kalli madeeha tana tambayar ta.

"Su hudu nagani. Iyayen su biyu. Sai wata budurwa da wani saurayi."

"Amman kin tsaya kun gaisa ko?"

"Ke a gigice na gansu yasin. Yar na bin maman da dankwalin kayan maman. Ya yinda wani saurayi ke tafe kansa akan waya yana dannawa hannu bi biyu.. tsabar hankalin sa baya jikin sa ma fa buguwa yayi da bango. "

"Kan babban balai..."

Fareeha ta rike ciki ta shiga babbaka dariya. Hawaye na zuba. Sai da tayi mai isarta tukun sannan ta dena tana me girgiza kai kawai

"Kice mun samu kawu Ashiru part two ko?"

"Kai Allah ya mana tsari da irin su kawu Ashiru kinji."

"Toh Aamin dai. "

Suna cikin hirar ta su. Sai ga ummy ta dawo. Bakinta dauke da sallama ta shiga parlorn.

"Wa'alaykm salam ummy."

"Wa'alaykm salam ."

Zama tayi tana lalubar yar rediyon ta.

"Ummy ya akai kuma?"

"Ya akai a Ina?"

"Eh! Dan Allah ummy.  Ya kukayi?"

Ummy ta dube su tayi murmushi kawai tana girgiza kanta.

"Kamar irin aiken nawa dinnan kukayi ko ? Naje na dawo na sanar muku yadda akayi ko?"

"Wh ummy ba haka mike nufi na."

"Kalau muka gaisu.," Ta fada hadi da karo sautin yar rdeiyon dake hannun ta.

Kasan zuciyar ta kuwa. Mamakin yadda suka karbe ta ta ke. Tamkar ta watsa musu wuta alokacin data saka kai tashiga bangaren na su.

Haka zalika sai da ta yiyyo sallama sama da hudu kafin su amsa ta shiga ciki. Gaisawar kuma dakyar safiyan ta amsa . Haka zalika yaran su biyu sai ummyn ce ta musu magana.

Da taga zaman bashi da amfani basu ji dadin shigar da tayi ba sai ta mike ta musu sallama ta kuma koma cikin na su bangaren.

"Ai agigice suka shigo ciki.. Nace wadannan kuwa ko lafiya?" Madeeha ta katse wa ummy tunanin da ta tafi.

"uhm.. Allah yasa mu dace."

"Amin Ummy.."

Haka dai suka shiga wata hirar ta daban. Gwanin ban sha'awa su ukun. Yanzun sun samu kwanciyar hankula da nutsuwar rayukan su.

Suna ci su na sha. Ga wuta da ruwa shaa daka bude famfo. Ga fanka tanata wulwula musu iska. Sosai sun samu sauyin rayuwa mai tattare da nasarori..

**********

       *********

                    ********

Tashin sa kenan daga bacci. Ya farka yana mai rufe bakin sa da hammar data taho masa. Hadi da hadawa da hailala. Ya daga hannuwan sa sama ya sauke yana miqa.

Daren jiya bai samu yayi bacci ba saboda sakawa da warwarar da yake ta yi. Da asubah ma dakyar ya hana idanun sa rufewa da nannauyar baccin da ke kwasar sa.
Chapter 17 · 0% Book details